chapter 22

BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 22
Back to Nigeria

8pm daidai jirgin su ya sauka a aiport din aminu kano within 40 mins aka gama clearing dinsu suka dau hanyar fitowa waje su ukun atare,kafin Nan already driver yazo da wata mahaukaciyar land cruiser jeep tana Parke tana jiran su
Suna isowa driver ya bude musu kofa dan su shisshiga
Rufaida ce abaya tare da kawun ta yaa sheik,wanda tun shigarsu banda nasiha da wa'azi masu shiga jiki babu abunda yake mata,ahnkli yake bi da ita yana aikin lallabarta cikin son ya kwantar mata da hankali,shikuwa Yaa malam tsayuwar sa yayi awaje baima yiwa motar kallo daya ba,anan bakin airpot din ya dakata harsanda ya same adaidaita sahu snn ya tare shi ya shiga zaune yayi a bayan adaidaita sahun ya buga Wani uban tagumin takaici da izza ta girman kai fuskar Sa a matkr turmushe, mita da bambami kawai yakeyi aransa dan tamkar zaiyi hauka ya zauce haka ya rinkaji acan kasar xuciyarsa,bakin cikin bin umarnin mahaifiyar sa datace masa marmaza ya biyo zaidu dukan su su sameta agida shiyake so ya hallaka sa, shi Allah ya sawwake masa ma ya shiga motar zaidun barema ya hada kafa dasu,in banda bacin rai da konan zuciya Babu abunda yakeji a xuciyarsa,haka
Suka har suka isa kofar gidan yaa malam baice ma kowa uffan ba.
Wani fadi yake yana tsikarar haqwransa da yar tsinke yana takun sa mai cike da nuna alfahari dakansa dayakei yana hura hancin sa cikin tsantsar yanayin bunkasa.

mai gadi ne ya bude gate suka shigo ciki still bai daga idanun sa ya kalle su ba ya Sallame mai adedeta,sashen mahaifiyar sa ya wuce direct sanda ya Wani bangaje labulen ya shigo har tsakar katafaren palon sannan ya doka wata mahaukaciyar sallama da sautinsa kadai ya isa ya ganar da Kai tsananin jahilcin dayake Kan wannan halittar daya shigo.

A lokcin hjy mama tana cikin bayi tana fitsari bata fito ba, Umma hadiexa dake karatun qur'ani akan sallaya ita ta soma tsinkayo sautin muryan san kirjinta ne ya hau bugu ta miqe tsaye a gaggauce,can ya isa har bakin kofar ta bude a hankli ta dada kasa kunnuwanta Jin muryan yaa malam din karara yasa ta juyo cikin sauri,kofar bayi ta je ta dan tsaya cikin rasa abunda zatayi can tace "hajiya mama kamar fa muryan yaa malam nakeji?maganan kawai tayi a Dan birkice dn batada cikakken sanin cewa ko ma anjita caraf saiga hajya maman ta fito durus agaban ta kamar wata fatalwa...
A mugun hargitese ta fito tare da xanin ta a hannunta da alaman ko gama kimtsawa bata yi ba
Ganin daga ita sai yar underwear yasa umma hadiza sauke Kanta kasa ita kuwa sai hamdala take tana kokrin daura zanin tan cikin sauri tace wuce muje da sauri rufaidar mu ta dawo, Alhamdullahi Allah Alhamdullah Allah na gode maka,sai kuma ta barke da Wani sayayyar kuka Jin Hakan ya saka umma hadixa Jin Wani irin sanyi da sabon yanayin kwanciyar hankli a xuciyarta hawayen fargaban ganin yarta da suka cikke mata idanunta already su suka soma gangarowa bisa kuncin ta banda motsi Babu abunda lebbenta yake na tsananin godewa Allah daya nuna mata wannan awanni masu matukar muhimmanci acikin shafukar rayuwar ta Yaune ranar da zata sake Dora idanun ta akan yarta rufaida"..banda hailala da salati Babu abunda take furtawa acikin xuciyarta da bakin ta,cikin sauri hjy mama ta wawushi hijabin ta ta wuce gaba umma hadiza na biye da ita abaya a mugun rikice suka nufo falon

Daga waje kuwa tunda suka sauka a mota yaa sheik ya riko hannun rufaida da kirjinta yake tsananin bugu Dan batasan mezataji aranta inta taji kanta ajikin umman ta ayau ba,Dan tun a jirgi kawu zaidu ya gaya mata Suna Nan gidan sa Suna jiranta ,da mugun dokin hakan aranta wanda shi yasa ta yarda tabiyosa gidan sa Dan ita har Yau gani takeyi kamar kowa yaji abunda ya afku da Ita,za'a ce ta kashe mijin ta ko taci naman mutum wannan maganan na matukar cusa ma xuciyarta da kwakwalta damuwa bana wasa ba

Tafiya kawai sukeyi tana tafe a hankli abayan yaa sheik Jin yadda kirjinta ke  kara tsanan ta bugun sa tamkar zai fado waje,kallo daya zakamasa kasan baiso tahowar su Nan din ayanzu ba,atunanin sa ai yakama abarta ta huta komi sai abisa a hankli,but ya riga ya san dokin ganin ta bazai taba bari subarta ta Dan huta ba,shikuma tausayinta yake ji,duba da long journey da suka sha a jirgi,ga ita kanta rufaidar ba wani karfin kirkine da Ita ba,Sam jikin ta Babu kwari, cikin layi layin ciwon Kai ma take tafiyar ga Wani uban dingishin datakeyi sosai,

Saukowar su hjy mama keda wuya suka tardashi a tsakar falon yana tsaye kyam yana famar zare idanun sa waje fuskrsan Nan a turmushe wanda kokadan Babu sauki ko rahma ayanayin sa..

Da sautin muryan kuka wanda ya taho a birkice Hjya mama ta yi sallama tana cewa "Bukar Ina jikata rufaida take?Ku nuna min rufaida rufaidata nake son gani,Kara hade ransa yay tamau musamman ma dayaga umma hadiza cikin shigarta na Kamala Dan doguwar hijabi ta saka har kasa tadan rufe fuskarta da tafin hannun ta tana hawaye kallo daya zaka mata ka fahimce irin halin da zuciyarta yake ciki na tsantsar tsumayin sake haduwa da yarta

Wani tsanar su yake ji aransa yanajin tamkar lefin su ne da komai ya faru,aganin sa sakacin su da rashin jinsu yasa Duk wannan ukubar ya afko akan yarsa.
Shi sam baiga laifin sa ko daya ba,daman can ya riga ya gane take taken su kawai basa sone rufaida tayi zaman aure sabida Suna son tayi rayuwar kafurai

Har sanda suka karaso cikin falon sannan ya nemi waje a katon cushion ya zauna ya wani baje shegiyar Malum Malum dinsa,cikin sauri umma hadixa ta Dan rusuna agaban sa tace San barka malam,sannu malam Allah ya dada karewa ,An dawo lpya..matukar tausayi ta bashi data Furta hakan aransa yanajin zafin ganinta a azabar damuwar data shiga ciki ganin yadda tayi maganan cikin tsantsan dauriya da jarumta irinta mata Amma ba ason ranta ba shikansa a xuciyarsa yasan bai wani cancancci gaisuwa da jaje daga gareta ba duba da yadda tayi ta gargadin dinsa akan maganan auren rufaida wanda ba sanin halin da take ciki ba sukayi ba,ya tuna yadda ta daga hanklinta tun farko tace ayi rufaida adalci,Sai kuma ya ji Wani girman kai da fushi ya turnuke sa aransa yace hadixa ita ta soma tsine albarka a auren rufaida ya ukuba da jaraba bazai fado kansu ba?,aransa saiya somayin tirr da mugun hali irinna hadiza
,wannan ai raini ne,in banda raini mezaisa ya ce zaiyi abu subi suyi masa taurin kai suce a'a,sai anan ya dago ya kalle mahaifiyarsan datake tsaye akansa cikin kuka tana tuhumar sa Inda rufaidar take,sallamn da sukaji akansu yasa shi hadiye Wani mummunan kalamin dayake shirin furtawaa ya dauke kansa ya mayar gefe ya dada hardewa

Yaa sheik dinne agaba sai rufaida abayansa,ita kanta umma hadiza bata San ya akayi ta miqe tsaye zumbur ba,jikinta ne ya hau Wani irin karkarwa hannun ta ya shiga rawa,hjya mama datayi tunanin zata iya debawa a guje da jikin tsufa ta tarbo rufaida sai gashi ta kasa Koda motsawa Wani irin sabon yanayin azaban tausayi da karayar xuciyace ya nane mata kafafunta ya Kuma baibaye mata gabobin jiki cikin tsayuwar dirshan take ta Kallon rufaidar datake Dan bobboye kanta abayan kawunta tana Dan dingisawa da kyar,a hnkli rufaida ta dago fuskarta ta kalle su dukan su kallon juna sukeyi cikin Wani irin maraitacen yanayi Wani kuka mai qarfi ne ya kufce musu gaba daya,a ba cikin hayyacin umma ba ta taho da gudu ta janyeta daga bayan yaa sheik ta rungume ta gam gam ajikinta da tsananin qarfin shauki tana sheqa matsanancin kuka
Mai tafe da takaici zafi da ciwo Wanda tsaban karansa yasa ba ama Jin sautin na rufaidar sosai suka kankame juna da mahaifiyarta Suna kuka mai taba zuciya atare,hjya mama dake cikin Wani yanayi itama bata San sanda ta karaso kansu ta rusuna kasa tare da su ta rungume su duka ba,"..Wani irin shafa Kan rufaidai takeyi cikin muryan ta na kuka tana cewa "Alhamdullahi Allah,rufai?..rufaida Ina kika shiga kika barni rufai?rufai meya Sameki haka  Duk naga ciwo ajikin ki?dukan ki sukayi ko?,Allah ya isa miki rufai Allah ya isa,ta Kara fashe wa da uban kuka cike da bacin rai da tsananin takaici tace"Allah ya isa akan Duk Wani mugu, azzalumi marar Imanin daya tayyara rayuwan ki,Allah ya isa bazan taba yafewa ba...
Duk wanda ya jefaki acikin halin da kika shika shiki saiya ga ba daidaba arayuwar sa,anje an cuce yarinya kawai,zaidu ka dubi yadda rufaida ta kwanjeme ta zauce nide Allah ya isa min acikin  kuka mai mugun qarfi take furta hakan"..Hakan yasa Yaa sheik lumshe Idanun sa sosai sam baiji dadin kalamnta ba "Nan ta miqe tsaye a xuciye tayi gaban yaa malam dayay matikar bata ransa Jin Allah ya isa datajajja kamar da shi akeyi da yar yatsa ta nuna sa Duk jikinta na rawa tsaban bacin rai tace..bukar kaga abunda ja jawo mana ko?malami kaji tsoron Allah arayuwarka kasani ni ko mahaifinka bamu azabtar da Rayuwarka haka ba,rayuwar da kakeyi kaika daura makanka ka xabar ma xuciyarka
..Amma bazaiyuwa in kara zuba Ido ina kallon ka kana Dora mummunan qaddara Akan rayuwar yayanka ba in nice na tsuguna na haifeka bukar daga yau Na haramce ka da wannan mummunan aqidar daurawa yayanka auren dolen Koda Hakan shizai sa ka guje ni,Wani irin kuka mai tsuma ta fashe dashi
Kan ta Kara furta Wani kalami yaa sheik yayi saurin janyeta kusa dashi ya rufe mata baki yana girgixa mata Kai alaman hanata Furta Wani kalma akan Dan uwansa wanda aganin sa cewa hkn babu amfani

Gaba daya Hajiya mama ta rikice cikin fushi ta shiga kallon cikin kwayar idanun danta Zaidun dake cike tam da hawaye shima,magana zata furta sai taji kuma ta kasa iya bude bakinta,"..aranta tace Meyasa bukar  ya zamto marar Jin kai?meyasa baya daraja maganata meyasa bukar ya taurare ya zamto tamkar dabban da baida tunani..
Janta yaa sheik yay ya zaunar da Ita akan babban kujera  sannan yaje ya bude fridge ya dauko ruwa mai sanyi a gora ya taho da shi har gabanta ya rusuna ya bude ruwan ya shiga bata abaki da kyar ta amsa ruwan ta shiga sha tanajin yadda sanyin ruwan yake ratsa wutar dake ci a tsakiyar kirjin ta,hawaye ne kawai yake xirya akan fuskarta kamar ba tsohuwa ba,..haka yaa sheik ya kammala da Ita ya sake nufo su umma hadiza wacce take gurfane akasa tare da yarta data rungume ta gam gam danji take kamar zaa iya kwace mata ita ,Mika hannu yay kamar wanda yake shirin dafo kafadun ta, a zumbur yaa malam ya miqe a matukar a hatsale cikin daka mummunan tsawa da masifa,nuna shi yakeyi yace,"..Ahir dinka da tabamin jikin matata zaidu.

Allah ya tsine ma kafurci Shashasha wawa kawai da can saika dora hannun ka ajikin matata muharramar kace?

Wani chak wajen ya dauke ganin yadda jikin yaa sheik ya hau rawa da tsantsan bacin rai
Dan Daga yadda ya dunkule hannun san zakasan maganar ta matukar shigansa Babu abunda yakeyi sai huci.

Cikin sauri umma
Hadiza ta janye rufaida ta zube daf da kafar yaa sheik tace "Yaa sheik Kayi wa Allah kayafe masa"Har abada bazan manta da karamcin ka ba,ka rufa mana asiri, inba kai ka ba bamai  ceto rayuwar yarmu rufaida, Allah ya saka maka da alherin sa ya bika da ladan har kabarin ka,Allah ya rufa maka asirinka duniya da lahira Allah ya sa alherin ka ya lullube yayanka da zuriar ka...Allah ya huci zuciyar ka...tana furtawa cikin tsananin nuna gaskiyarta tana sauke Wani irin hawaye masu rikitarwa da ban tausai

Atake atake ta sanyaya shi saiyaji Duk fushin nasa daya hargitso ya dan sau Ka,duba da yadda yartan ma ta labe ta mannu ajikinta suka zuba masa ido tamkar wasu marayu,jiki a muce suka rusuna agaban sa Suna ta gode masa,take ka saiyaji Babu dadi aransa Sam,gani yake shima bai cancanci wannan yabon ba Dan da tuni yana da Iko da isa daya raba rufaida da shiga wannan ukubar rayuwa, saida halayyar Dan uwansa ne komin haqurin ka dole ya girgixa ka...

Hjy mama ce ta soma karasowa gaban su ta rirriko umma hadiza tana cewa ya isa haka hadiza ku tashi kuxauna,tana miqa hannun ta ta tallafo rufaida cikin yanayin tausayawa tana cewa taho nan
Ko zauna magajiya ta yar albarka Allah saiya saka miki rufai.."sauke Ajiyan xuciya yaa sheik yay ya nemi waje kawai ya zauna,at same time suma suka zazzauna Kan rufaida na Kan cinyar kakanta tana shafo kanta banda hawayen tausayin kanta Dana mahaifiyarta Babu abunda takeyi

Zaman su keda wuya haj mama ta rinka fada tana mita
Wanda ya janyo aka tusa rufaida agaba tayi bayanin dukan abunda ya afku da Ita da bakinta agabansu kowa yaji,sabida yaa malam cewa yay Duk abunda xaidu yake fada karyane,kawai an hade Mai Kai ne ana so a walkantasa anzo anata zaginshi agaban yar cikinsa sai yayi fushi sosai yanata nuna bacin ransa a fili..

Umma kuwa tun dataji cikakken labarin abunda ya afku abakin rufaida ta tashi tayi sama a gigice ta haura har cikin dakin surkuwanta ta kulle kofar ta fadi kasa ta rinka sheka kuka tana birgima cikin tsananin takaici da Dan danasanin sanyin datayi abaya

As usual yaa sheik din ne ya rirriko rufaida cos Duk sanda ta bada labarin abun da ya afku da Ita sai ta fita a hayyacinta
Gwara ma na yau da Dan sauki dake ya bata adduaoi tanayi shima yana famar aikin tofa mata akai yana lallabata ta

Hjiya mama da already ta daskare acikin irin yanayin zama Nan na zaucewar hankli da tsananin baqinciki Babu abunda take sai sauke hawaye masu tsananin rauni tana kada kafafunta a gaggauce ta gama zautuwa,wani tamke yatsun hannun ta idanunta duka tayi kallonta sunaga Kan danta bukar wanda Allah ne kawai yasan metake sakawa aranta game shi

Yaa sheik bai barta hakanan ba ya rinka musu nasiha da shi da Ita har da rufaidar.

Ganin sukam bazama su saurare shi ba yasa ya janye hannun rufaida yay waje da Ita suka koma can sashen shi...

Yana fita hjy mama ma ta miqe tsaye,shima Yaa malam din saiya miqe,kallo daya ta masa ta karance shi tsaf,bakaramin damuwa da azaban tausayin yarsa yakeji ba Amma duhun jahilcin Nan bazai taba barin sa ya fahimce Hakan ba.."ya Wani daure fuskan sa yana ta bambamin sa kasa kasa,yau baiso yay magana da qarfi sabida sosai yashaqi bacin ran mahaifiyar sa akansa wanda har a zuciyarsa ba son ganinta ahaka yakeyi ba.

Tunda dai zaidu shikadai ne danki ni zan tafi saiki xauna dashi da su hadizar suma na bar maki su dama can nasan basona kikeyi ba sabida ki haifi danki mai Ido nikuma ubana bai gaji komi na arxiki ba dole zakina tsine min har akan abunda bai shafeku,rufaida yata ce,Nina haifeta, Kuma koma miye ya sameta ita tajanyo data kimin biyayya ta biye muku akan raayin arna da kuke rayuwarki akai.

Allah ya kara ni sam banji tausayinta ba,Duk wanda yaci tuwo da ni miya yasha,daga yau in na ajiye Kara Nace karta tsallaka ai bazata kara tsallakewa,Yan uwanta da sukamin biyayya suka zauna agidan nasu mazajen yau meyasamu su?

Baima karashe maganan ba yaji saukar wata makahuwar Mari akan fuskar sa..

A daddagee tsofuwar ta cakumo wuyar rigarsa ta kurma ihun da bata taba yin irinsa arayuwar sa ba

Cikin tsananin fushi da takaici Tace ka kasheni kawai bukar,ka Doki wuka ka cakka min acikina na mutu,ka ka Nemo bindigar da surkin ka ya kashe kansa dashi ka harbeni..bukar
Bukar ..bukar..
Wani mahaukacin ihu da tsawa take daka masa tana zaginsa gashi bata sakeshin ba,sai jijjiga shi take yi acikin yanayin bacin rai tana kuka yana huci
"Wani ne zakace madalla wa rufaida?
Wani zaka dorawa laifi?zaikara magana ta fallasa masa Wani hatsalallen Mari nau balain kara.
Kawai Marin ta shiga jefo masa tako ta Ina duk jikinta na rawa tamkar zata yanke jikin ta fado akasa ta mutu..

Jin hayaniyar yay yawa yasa umma hadiza saukowa da uban gudu Kuma a mugun rikice ta tarar dasu ahaka,
Wasu irin kalaman da basuda dadi hjy mama take furtawa
"Tace saiya Gani a kwaryan cin tuwon sa,tunda ya jefa yar cikinsa a cikin yanayin da taci naman mutum tayi kisan Kai ta rasa hanklin ta ta muzanta ta tozarta
Allah ya isan data ja masa a daren ranan baiya kayyaduwa
Dan shi kansa sanda hanklinsa ya tashi xuciyar sa tayi mummunan raunana yana masa zafi,baice uffan ba sabida bayan kanin shi xaidu Babu wanda yake gaya masa maganan datake raunana sa kamar mahaifiyar sa hjy mama,kasa ce mata yayi kansa ya mayar kasa yana huci sai tsaki yakeja, a xuciye ya shiga cewa
"ni ki sakeni"..
Niki sakeni kije na barki da zaidun
Ita kuwa bata fasa ba maganan rufaida kawai take masa tana nunamai illar abunda ya aikata arayuwarta wanda tamkar muzanta mata rayuwrtan yayi mai gaba daya..

Arikice umma tayi ragwaf agabansu tana ta rokon su da su yayyafa ruwan sanyi aransu

Hajiya mama cikin Jin haushin ta itama ta juyo ta hankade ta da kafa ta shiga zaginta a zafafe.

Da laifin ki hadiza
Da laifinku rufaida ta muzunta
Allah ya isa tsanina dake kunci amanar da Allah ya baku
Tun farko nake cemiki ki tashi ki karban makanki da yaran ki yanci kin bar jahili yana abunda yaga dama akanku?da lefin ki hadiza,tun awancan lokacin da kin kawota kikace min gatanan da koni sai gudu da rufaida,nidai Allah ya isa ma rufaida kuncuce rayuwarta kunsa ta aikata kisan rai taci naman Dan adam..wayyo Allah ni hasiya,da Wani irin kukan kura ta dada girgixa yaa malam,shima ya rike hannunta dake wuyarsan tam,alokacin shikansa yasan badon bazai iya bambamreta bane ya kyaleta,so kawai yake ta rage zafin abun akansa Hala ko shima zai ji a xuciyarsa  kamar an hukunta sa akan abunda ya aikata akan rayuwar yarsa rufaida tabbas yasan ya cuce rayuwar yarsa,son zuciyarsa yasa ya jefe rayuwarta da wannan mummunan tabon da baiyi tsammanin zai fado akansa ba.

Yanzu haka abun yana matukar damunsa Saidai shifa bazai taba karaya ba Dan aganin sa baiya kuskure baya laifi kuma Babu wanda yakaisa sani da fahimtar gaskiya
Fushin nata aransa saiya shiga danganta shi da cewa Kawai so ake anuna xaidu ya fishi
Tarbiya da nitsuwa
"Dan kawai nayi kuskure akan yata kwalli daya?..rufaida ce kawai aka samu akasi akanta amma ba a dube sauran da suke zaune lumuim da majazen su ba anhai tsine masa ana muzanta sa..

Shima kukan kura. Yayai ya soma maganganu yana cewa ta tsine masa kawai shi gwara ya bi duniya da ya zauna ganin yadda uwa take nuna banbanci atsakanin yayanta

Furta Hakan datayi yasa hjy mama Kara gaura masa Marin da saida ya kife fuskarsa, Wani daka tsalle tayi ta banke hijabin dake jikin ta ta yasar a rikice ta kwance zanin ta ta shiga birgima agaban sa tace  masa lallai ya hau dukan ta koya kashe mai gaba daya

Ganin abunsun yana neman munana yasa umma hadiza yin waje da gudu ta nufi sashen ya sheik a gigice,samu tayi harya lallaba rufaida tana Dan shan ruwan zafi da short bread a hannunta wanda ko ciza daya ta kasayi masa.

Kusan A gigice umma ta shigo fadi gabann sa tana haki tana zubda hawaye,gyara zaman sa yay yana kallon ta.."Yaa sheik kazo Dan Allah hjya mama fa ta birkice Dan Allah kaxo ka raba su tashin hnklin nan yay yawa,Kar sanadiyar haka Wani abu yaje ya same ta, Jin haka yasa Yaa shiek mikewa tsaye cikin sauri baima tsaya tambayarta meyake faruwar ba ya fice agurguje dukan su harda rufaidar suka shiga binsa abaya.

YOU ROCKKK GUYS 🔥💋💋I LOVE UR COMENTS WALLHY 😭🤭IM IMPRESSED WITH THE LITTLE MOTIVATION AM GETTING FROM FEW OF U..MAY ALLAH MOTIVATE U IN BEST OF MANNERS..I LOVE YOU GUYS, MORE PART 1 FOR YHALL,KODE ZAMU FARA BADA KYAUTAR SHAFI NE KAM😂🔥TEAM YAA MALAM RAISE UR HAND JORRR🤣🤣🥱🌚🤧🤧🙌


"0152983148
Mohd sule surayya
Gtb...08060712446!

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top