chapter 19
*™✓SHADE OF RUFAIDAH*
_BY_
_SURAYYAHMS_
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_
BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Part1:chapter 19
*Case1:on blind matters*
A bangaren su imad kuwa yau ya dade yana tare da rufaida a asibitin dake yaudin aka soma bata abinci kadan kadan domin tasaka acikinta dayay kwana biyu baiga Wani abu ba, saidai da ta fara tabawa saita Firgita ta ajiye ko tayita kwaza amai,kusan wuni cur sukayi tare da ita yana kulawa da Ita sosai,doc Mehra wanda already shima ya hado nashi magungunan tare suka hadu Suna lallabata yana Dan bata tana sha dan yana rage mata tunani da yawan razanar datakeyi Koda zata samu nitsuwa..
10:30pm US
Isowar dare yay sheik yay dan haka direct yasa aka wuce dashi public ministry Inda aka tsare yaa malam ya samu har an gama masa tambayoyi,but banda izgili da muguwar girman kai Babu abunda aka tsinta daga garesa Dan har ayanzu shi bai Wani yarda cewa Alaji Bature ya aikata laifin da ake tuhumar sa akai ba,a tunanin sa an hada baki ne da matar sa Dan a cucesa a rusa auren yarsa rufaida,daga an masa bayani sai ya juya Kan zancen yay kyam kamar baijin me ake cewa musamman akan halin da yarsa take ciki,Dan har ya mutu aransa ya qudira cewa bazai taba amincewa da xancen Wai yarsa rufaida tayi kisan Kai ba, kawai sai ya aje hakan a matsayin karya kawai ake sheka masa,isowar yaa sheik wajen yasa yaa malam dada tada rikicin sa,ya fara zage zage yana cewa "Allah ya isa masa Kuma yafi karfin su"Tunda har hade mai baqi sukayi aka kawo sa cikin kafurai ana tutsuyesa,da kyar yaa sheik yyi shige da fice ya zama valid quarantor ma case din Dan uwan sa,Inda ya bada cikakken bayanai akan yadda abun ya Kullu,by no means dai haka suka bada bailing sa ma yaa sheik ya dauke sa suka fito,doc Mehra dakan sa shiya taho da mota daga can hotel din da suke ya dauko su suka wuce can masauki..
Yaa malam Duk a galabaice yake da tsoro amma girman kan Nan ta jahilci Sam taki ta barsa ya saduda Tamkar da wanda bakin sa baiya gaijya ya rinka fade fade yana tsinuwa,yaa sheik yana shiru baice masa uffan ba har yanzu Dan a lokacin shikan sa bayya cikin mood din da zai kulasa dan bakaramin takaici da zafin abun yakeji a xuciyarsa ba.
Haka suka isa hotel apartment din,inda ko gaisuwar doc mehra bai amsa ba,amma Daga sun soma magana akan case din rufaida caraf sai yay malam yay shiruuu yana mai sauraran su in aka Furta Wani abunda bai gamshe sa saiya hau zage zage..
Yau Imad ne kawai asibiti,doc Mehra na tare dasu da niyyar washe gari sassafe zasu shirya su ukun su taho...
Alhamdullahi rufaida is little bit stable now Dan tunda imad ya kasa ya tsare a wajenta sai ya zamto bata yawan Firgita tana Ihu tana ture kowa saidai ma tayi shiruuuu tayi ta kallon irin hidiman da imad din yake mata wanda tanajin sa sarai amma kwakwalta bazai barta tace Wani abu akan komi ba
Alluran da doc Mehra yay mata kafun ya wuce shiya rinka sakata gyengyadi da kasala time to time tana maganganu kamar ba acikin hayyacin ta ba daga bisani sai bacci mai mugun Nauyi ya dauketa,waje ya samu ya makale Adan gefenta yanata latsa wayarsa Dan kokadan baida bukatar yabar asbitin ayau dan yasan tabbas Inda aka fahimce cewa tana Dan samun sauki sauki daga gobe ma zasu iya turo agents a takurata da tambayoyi
Washe gari da sassafe shukra ce ta fito sanye da abayar ta black colour wanda daga ganin design dinsa kasan yaci uban kudi,Wani tafiyar yanga takeyi tana baza takunta daidai akan wata golden highheels hannun ta rike da jaka tana shasshn qamshi tamkar wata hamshakiyar sarauniya,direct ta nufi sashen hjya mama dan already ta gama shirinta Nan da 30 mint takejin zasu wuce airpot akaisu gidan su na abuja,kasar wuyarta tayi sallama a sashen bata ma jira an amsa ba ta shigo ciki,ganin babu kowa anan yasa ta haura tabi ta kan step, har cikin dakin hjy maman ta isa daidai lokacin umma hadiza ta idar da lazimin ta kenan ta rafka uba tagumi tana zaune
Ajikin gado cikin tsananin yanayin tunani
Babu ko uhm bare sallama ta fado har tsakiyar dakin,ganin umma hadiza bata dago kai ba yasata Jin haushi Dan ta tsani a raina isowarta wani waje,
umma hadiza kuwa dake tayi nisa cikin tunanin yarta batama San mutum ya shigo ba
Wani irin kaskantacen Kallon sama da kasa tabita dashi ganin kalar kayan data saka,normal avogan wax ce ta dubu biyar amma Duk ya tsofe ta kife dankwalinta a sukurkuce Babu marabarta da mabarata Wani dauke kanta tayi cikin yauqi tana gatsine Can ta nitsa gefe tace"Hajiya mama fa? Umma hadiza ta dago kanta Adan takaice ganin yar yarinyar data haifeta agabanta tana Wani fadi tana ciccin magani tanai mata kallon kashi,ba yabo babu fallasa tace "sun fita da keeyan Amma yanzu zasu dawo..Wani Shiru tayi bata ko irin nuna tajitaba daga bisani taja karamar tsuka ta fice a dakin cikin sauri,kallo daya umma tayi ma kofar tabi ta dauke idanunta da suka cikke da ruwa cikin tunanin yarta rufaida..
"...Rufaidar ta yar albarka wanda har abada bazata iya cewa ga laifin data taba yi mata ba bare tayi ma wani,Amma yau gashi munanan abubuwa sai faruwa sukeyi da Ita hawayene masu rauni ne suke biyo kuncinta Suka dinga sauka tamkar ruwa ta dade ahakan sannan ta miqe ta nufi toilet ta wanke idanunta ta dawo ta sake sabuwar zaman laximi tana Kai kukanta ma Allah cikin addo'in
6am dot imad ya dawo daga masallaci dake a asibitin ya kwana sai Duk jikinsa yake masa tsami dan bai Wani samu baccin kirki ba Shigarsa dakin keda wuya ko zama baiyi ba rufaida ta soma bude idanunta wanda a hnkli suke budewa harta sauke su duka akansa.
Wani irin kallo suka shiga aika ma juna batare da sunce uffan ba,Wani irin kyau take masa
Aransa saiya dingajin kamar kullum canza ta akeyi zuwa Wani siffa nadaban mai kayartawa,tabbas tsarki ya tabbata ga ubangijin halittu daya kero wannan kyakkwar fuskar dat need no make up or adornements,hanklin sa gaba daya ya bayar wajen kare mata kallo batare dayaji gajiya aransa ba,her skin colour ba irin nashi bane da zaka iya cewa tsantsar hutu ne da dukiya,her's is naturally fresh and beuttiful Kai baima San tayaya zai fasalta smoothnes da kyaun kalar fatar jikintan ba,her eyes are dark and illuminating wanda suke Yan daidai baxakace musu manya manya ba har sai ta wara su,Gashin girarta a kimtse daga yanayin kwanciyar da suman gaban goshinta yayi tabbas daga nan zaka fahimce cewa kanta da doguwar gashi Koda ace bamai tsayin hauka ba..
Cikin rasa wanda zai fara motsi ajikin sa yasa rufaida Lumshe idanunta tayi luumui saukar numfashinta kawai yake kallo yadda take ajiye numfashin a hankli kamar yana mata wuya.
Matsowa kusa da ita yay batare da sannun sa ba ya Dan shafa saman goshinta,Kara bude idanuntan tayi suka Kuma Sarkafe kwayar idanun su a juna sun Dan jinma ahaka sannan ya Dan ja cikin sake gyaran murya tare da sauke murmushin sa mai tsananin sanyi da taushi yace..."good morning sweetie"
Tayi shiru,ganin kamar da wasa a muryan sa yay maganan,Duk da haka bai hanasa cigaba ba ya dube ta yace "ya jikin?
Kanta ta sauke kasa,sai yay murmushi atleast da shejaranjiya ne da saidai yaga ta barke mai da kuka but it seems she is getting better now,
Matsowa daf da Ita ya karayi cikin yanayin kulawa yana Kan kallon sunkuyayyar kanta."
Yace"Akwai abunda kike bukat ne?bata amsashi ba,aranta tanajin kamar dai zata amsar Amma bakinta ya kasa buduwa,she dont even know him but hakka kawai Taga ganta tana ta mu'amala dashi
Ko shi din wayene oho?ita dai tasan tana bukatar taimako musamman wanda zai kaita wajen ummanta Amma takasa gane komi she is mixed up gaba daya kwakwalta baiya gaya mata daidai.
Wani irin murdayawa cikin ta yay wanda yasata tayi Dan Kara tare da damke karfen dake jikin gado Nan imad ya matso kusa da ita marmaza yace lpya?..cikin bai saketa ba ta runtse idanun ta sosai tana rike da karfen cikin mayuwacin yanayi,
Yace toh toh
"Bari in kira maki likita,.yana juyawa cikin sauri zai fice ta fashe mai da Wani irin matsanancin kuka wanda ya dakatar da shi ya hanasa kasa iyayin wani motsi,dawowa kanta yay Babu shiri yace menene?I need to call ur doctor Yanzu zan dawo
Cikin sauri ta girgiza Mai Kai alaman bata son haka,cikin nata data danke ya kalla sannan ya kalli fuskarta yace"
Meyasa baza'a kirashi ba ba cikinki me yake miki ciwo ba? .Nan ma girgiza kanta tayi hawayenta nakan saukowa bisa kuncinta,zai kara budan baki yaga ta miqa mai hannunta da alamn tashi tsaye take so tayi,Babu musu ya amshe hannun nata ta Dan miqe zaune,shima zaman yay a setin fuskarta yana kallon Duk Wani motsin datakeyi gaba daya hanklin sa da dukkan imanin ya Dora a gareta
Rawa rawa jikinta ya somayi idanunta a Dan lumshe banda uban rawa Babu abunda Gashin idanunta da suka jikke shataf da hawaye sukeyi,looks like she is Tryn to stop Amma Ina daga ta farka daga bacci sai kuma taji tsananin damuwa da tashin hankli yaa mamayeta,kawai ta fashe da kuka
,kukan takeyi tsakanin ta da Allah tana Jan sheshhekar da yake balain wahalar mata da nunfashi
Atake atake yaji nashi hawayen sun yanko kafin yace zaiyi controlling kansa sai zirrrr sun soma sauka masa akan kuncinsa saiya tsinci kansa da ce mata "Am sorry"
Am really sorry rufaida,muryan sa sosai yake rawa sabida acikin raunin shima yake furtawa
Wanda Hakan ya matukar bata mamaki,Dan a tun afarkon ganin ta dashi zuciyarta ya amince mata da shi
Sosai,But right now bazata ita cewa tasanshi ko ta gane sa ba,tasan dai Meyake yawan gaya mata nacewa zai kaita wajen ummanta Kuma shi lawyarta ne,but why he is cryn now?lumshe idanunta ta karayi tana dada bulbulan hawayen daga bisani ta sassauta Jin yadda ya nitsa yanata bata hakuri Dan motsawa tayi ya Firgita ya miqe tsaye kamar wanda zata fado akasa ya taro ta,ta kwace hannun ta da sauri tana mai rage sautin kukan ta bude idanunta ahankli,Wani mamakin ne ya Kara rufeta ganin yadda ya birkice Duk ya gama daga hanklin sa ya zama abar tausayi kamar ba Shiba,ko hawayen dake kan fuskarsa bai iya sharewa ba,Wani kakkarfan Ajiyan zuciyane ya kufce mata ta Kara miqewa zauna,can ta Dan motsa kafafunta Jin yana mata Nauyi Nauyi yasata ta Dan dago kanta kadan tadan kallesa ayayin da yay saurin goge hawayen fuskar sa ya karaso kusa da ita,Kallon cikin idanun ta yayi snn yace,"u need sumtin? Pls talk to me rufaidah I'm ur family, kinsan yaa sheik ko? I'm like his son kinsan hajiy mama?da uban sauri ta wara idanunta cikin nashi,sai kuma ta dauke kanta da wuri..a hnkli ya dada furta"u're safe with me okay,pls relax kifadamin abunda kike so ko yake damunki..I swear I will Neva let you go throu this again ...kinji?Wani damke hannun ta yay cikin tsananin shauki da bayyana mata dagsken yakei ya karashe maganan sa da cewa"I PROMISE YOU..Kallon scnd daya tamai ta Kara dauke kanta,a hnkli ta shiga sauke Ajiyan zuciya,tuno abubuwan daya Furta kawai takeyi
Yaa sheik,haj mama?a Ina to yasan su,ita dai tasan yayan ya sheik Amma ta dade bata gansu ba banda Anty fareesa she don't even knw
Them by face right now, Dan itace agidan su kwata kwata bata fiye zuwa ko ina ba daga islamiya sai schl sai kuma gida..
Shima Yaa sheik din Dan yana yawan zuwa da hj mama ne da zata iya cewa shima bata Wani sanshi sosai ba.
Aranta tace koma wannan shine yaa mufrad din?but no,ai ance shi soja ne or navy,aiforce wateva, batama San meye asalin aikin san ba,Koma yaya ne dai but Tasan dai shine babban Dan kawu zaidu.
Ta dan dade tana ta lailaiya tunani kala kala aranta can taga ya miqe da alamar zai fita
Cikin sauri ta miqa hannunta kamar mai shirin dakatar dashi Adan takaice ya juyo Suna Kara hade ido sai kuma ta sauke Kanta can kasa
Bakaramin bugu zuciyanta yakeyi ba,
Saidai a Duk sanda ta kalle sa saitaji Wani abu daban maisa ka nitsuwa sai sa ma kwata kwata take Jin saukin ganin shi a inda take bakamar sauran ba
Dawowa yay ya tsaya ta dago kanta a hankli batare da ta bari sun kalle juna ba,kofar toilet ta kalla kafin ta lumshe idanunta tayi pointing masa wajen da yatsar hannun ta,sanyi yaji aransa tadanyi Hakan atleast ya gane metake bukata Babu bata lokaci ya taho ya tallafo ta ajikin sa ta mike zaune sosai,Wani Shiru tayi sanin bazata to taba iya takawa dakanta ba,ga Wani Dan uban damuwar data cusa a xuciyarta game da Hakan,ta gama sallamewa akan ta riga ta rasa virginity ta,Dan Babu ma yadda za'ayi ace zafin dataji akasarta kwana biyu bai mata Wani illa ba
Ganin ta kasa dago Kai bare yin motsi yasa shi fahimtar matsalarta na rashin iya motsa kafafunta, tausayi ta Kara bashi sosai yanayi yana kallonta da gefen idanun shi,Duk saiyaji bayajin dadi.
He just have to forget everything and take care of her tunda ma dai yar uwansa ce..
Rufaida tamkar amana ce awajen sa,tunda yasan Inda ace shukra ne ko nazli da saiya musu abunda yafi haka
Da wannan tunanin aransa ya fixge hanklinsa cikin tunanin ya riko hannun ta so calmy yasa murmushin sa mai taushi "Muje in rakaki? Atake ta girgiza Mai Kai alaman a a,yace but u can't move..ko ciwon ya warke,da balain karfi kirjinta ya buga Jin ya Furta mata Hakan,aranta tace "Wani ciwo,
how d hell did he even know? Na shiga uku,maza ta sauke Kanta kasa daga Nan bata kara dagowa ba ga cikinta na mata Wani irin ciwo wanda she is sure yunwa ne Dan magangunan da doc Mehra ya babbata jiya akwai nasa cin abinci
Da kyar da fitina imad yay convincing dinta ta barshi ya tarkato a hannun sa suka miqe tsayen atare,Sam Sam taki ta Kara bude idanunta bare ma su kara hada Ido,tunda ta fahimce cewa yagane abunda take ciki taji Wani abu na mata mugun Nauyi aranta kamar ta nitse kasa haka ta dingaji,a kofar toilet din ya ajiyeta tana tsaye ya shiga ya bude famfon ruwan zafi ya shiga tarawa a bath,sannan ya dauko Wani new toothbrush ya saka tooth paste ajiki ya ajiye akan table sannan ya karaso batayi aune ba taji har ya dauketa chak sun shige daga ciki..
Bai rufe kofar ba tsaban rawan dayaga jikinta yanayi,a hnkli sosai ya ajiyeta aksa ta tsaya still akan kafarta bata motsi kamar wata yar kwai,Nan ya kunna mata ruwa abakin sink ya umarceta data kurkure bakinta,daga Nan sai bai barta tayi komi ba banda kuskure bakinta datayin harta brush shiyayi mata dakan sa Dan haryau bakinta bai dena fidda Wani zarni zarnin jinin datti ba
Yana kammala mata brush din ya ajiye ya fice cikin sauri Jim kadan saigashi ya dawo da nurse din datake tsaftace ta,"..she was so in a hurry kamar masifa akayi mata,jikin ta na rawa ta shigo bathrum din ta dau ragamar komi she Neva tot dat rufaida tafarka da wuri haka sun saba Wani bin har aci akare safiyar bata farfado ba,fita yay ya barsu Inda nurse din ta harhada maganin da ake xubawa aruwan wankantan sannan ta umarceta da zama aciki,..
Kukan kawai rufaida takeyi sabida azaban datake sha dacan da bata cikin hayyacin ta Amma Koda anzo mata wanka takanji balain zafi ajikinta sosai.
Hakan yasa nurse din ta sha wahla da Ita wajen sit bath Duk dama su basayin shi yadda ya dace komi bisa qa'idar aikin su sukeyi basu damu ba,har aka kammala tsaftace ta bata dena kuka ba.
A tunanin su imad yana dakin yana jiran su yasaka nurse din lekowa Gani tayi harya gyara mata kan gadontan tsaf yayi waje,fitowa tayi da rufaidar wacce da kyar da bala'i take daga kafafunta da taimkon nurse suka karaso har bakin gado,slighly ta dago kanta ta juyo ganin bayanan sai kuma taji kamar ta damu,
Dafa ta taji anyi wanda hakan yasa ta juyo cikin sauri nurse ce atsaye hannunta dauke da Wani tray din kaya ta umarce ta data zauna a shiryata Dan da ayi mata allura,Kai kawai ta gyada tana shirin dafa Kan gadon gaba daya ya koma kan yadda ya kimtsa mata shi tsaf,da kyar ta zauna slighly sannan nurse ta taimaka mata ta kwanta a rigingine.
Shasshare mata jikin ta tayi da towel sannan ta goga mata wasu ointment da magangunan kashe skin infection da diseases espicillay thos dat are caused by micro organisms
Gaba daya sai batajin dadin warinsu tun da aka fara take kaudakai har aka kammala bata San ya akayi ba Wani irin hausinawa hanjin cikinta yakeyi shikadan sa yana kuri,kawai sai ta soma jin Babu dadi
,kwantar da Ita da kyau nurse tayi domin ta duba vaginanta,Nan ma batayi gardama ba har aka gama mata komi ba,warware wasu sabbin kayan tayi ta sakamata dis time is sky blue hospital uniform shima bakaramin amsar kalar ta yayi ba,juyawa nurse tayi tana famar hade haden magani da allurorun da zata mata,"rufaida dake kwance Babu abunda yake neman hallakata banda azaban ciwon ciki sai taji kamar tana tsananin bukatar abinci nurse tana juyowa da syringe suka hade ido Wani matsanancin kukan ta fashe da shi tana kokarin miqewa wanda yasaka nurse din dakatawa
Cikin kuka mai cike da shagwaba tace
"Ki kyale ni nikam"
Nurse kam Bata ma San metace ba sabida da hausa tayi maganan.
,..matsowa ta karayi da niyyar rarrashinta rufaida ta takarkare ta tsala wani azababben ihun da saida nurse din ta tsorata ta ajiye alluran batare da tasan tayi hakan ba.
Ni ki kyaleni
Ciki na yanai min ciwo
Ni Wajen umma na zanje
Imad dake manne ajikin kofar Wani bugu kirjinsa yakeyi da sauri sauri cikin contemplating on weda ya shigo ko ya cigaba da jira su awaje ya kasa samun nitsuwa cos baisan ko sun gama kimtsawa ba.
Jim kadan saiyji kamar rufaida ta fara rikicewa sosai,hakn yasa shi yankar shahada aransa kawai ya turo kofar,Gani yay nurse ta koma gefe da alamar razana bazata iya control dinta ba
Bai tsaya bin Kan nurse ba ya wuce direct gaban rufaida
Zama Yay tare da riko hannunta zuwa nashi,yace shuhhhh rufaida meye faru?cikin bori da kuka
Ta fauce hannun ta
Anashi"..ni bana so
Ni uumma na nake so...Wani Kukan ta Kara barkewa dashi,bai kara kulata ba ya kalli nurse yace pls get her sum tea Tace yes sir,Da sauri ta fice rufaida tana ta kuka,baice mata uffan ba har saida nurse din data dawo,tun kan ya amshe cup din yaga yadda ta dago kanta tana kallon kopin da alama yunwa take ji Dan haka Baiyi wata wata ba ya juyo ya miqa mata atake takai bakin ta ta kurba,"da sauri ta kuma tufarwa wanda ya fettu har ajikin sa,kukan ta Kara fashewa da shi tana shirin Kai hannun ta kan harshenta ta daya kone,"..I'm so sorry ya Furta yana amsar tea din a hannun ta,cikin lallai yace "yunwa kikejin ko?..da sauri ta gyada kanta tana kuka kamar yar karamar yarinya,gyara xaman sa yay ya dauki tea spoon Yana deba kadan saiya hura da iskan bakin sa sannan ya bata Tasha,haka suka dingayi nurse tana tsaye tana jiran su danta mata alluran data riga ta hada,ganin kamar zasu bata mata lokaci yasa ya shiga hura tea din gaba daya da bakin sa yanayi yana girgizawa dan yy sanyi,...
Ajiyan zuciya kawai rufaida take saukewa tana ta Satan kallon sa,Wani iri iri ta dingaji aranta ganin yadda ya damu sosai akanta,kode dagaske Dan kawu xaidun ne?but but...kamar dai wani suna daban fa ya gaya mata And he is not a soldier bataga alaman ty mata debi da sojiji ba sai can kuma Wani tunani ya yanko mata Data tuna ashe kawu zaidu yanada Wani Dan sa keeyan,bt no no ance baiya kasarsu,"Where am I?tuni kwakwalta ya bijiro da wannan tambayar,saima yanzu ta lura da cewa bataga bakin fata ba tun datazo
Daidai yana shirin saka mata shayin abaki ta riko harda hannun sa"..cikin tsananin sanyin Muryan tace pls where am I?Kallon ta kawai yy ganin yadda tayi maganan so innocent,Dan kadan ya sakar mata murmushin sa mai taushi,"take ur tea ai zan gaya maki inda muke..batayi musu ba ta bude bakinta ta shiga amsar shayin sanda ta shanye tas ya dauki wiper yana goge mata xufan dake fetsowa a saman goshinta
A hnkli take sauke Ajiyan zuciya,yana kammalawa ya hada harda hawayen fuskarta ya goge mata shi tas"..dawani sanyayyn murmushin ya dago ya kalleta,"yace Kin koshi?..,can u eat sumtin inje in kawo miki abinci?..da kamar zatace eh saikuma ta maida kanta kasa tayi shiru,habarta taji an tattaro cikin maida idanunta acikin nashi,yace"..hey,I promise you in har kika mike da kyau Babu abunda zai hanani kaiki wajen umman ki,kefa musulmace yakamata kisan rantsuwa tamkar alkwarine..don't u think is best for u to eat and be strong,Kuma nasan baki son wajen Nan ko?..gyada Mai Kai tayi batare da tasan tayi Hakan ba..yace inje in kawo abincin?tayi shiru can kuma sai ta dago Kai ta kallesa suka hade ido Wani irin kallon sukayi ma juna Jin yadda kirjinta yake bugawa kamar zai fita daga kirjinta yasa maza ta dauke kanta akansa,
Aransa yay Dan Murmushi he take dis as her yes,Nan da nan ya miqe tsaye tare da umartan nurse akan tayo mata Alluran
Ganin harya fice a dakin rufaida bata fashe masa da kuka ba yasa yarda aransa cewa lallai abincin take bukkata Dan haka Baiyi wata wata ba ya wuce nearby bukataria da niyyar Nemo mata simple abincin kasarsu wanda baida Nauyi sosai,yana shiga wajen yayi odern soft chicken paper soup wanda aka dafa shi da romon oysters yay laushi sosai yasan intaci wnn kam bazai Wani dameta ba dan daga waje daxun yaji tana cewa nurse cikinta namata ciwo,Wani irin hadin shinkafa da ganye da tumatir wanda aka anyayyanka ganyen basil akai shima da chicken wings ajiki ya Kara odering
Sai Yace ahada masa harda fresh grape juice a masa packaging dashi zai tafi.
Gefe ya koma yana jiran su kafin Nan ya ciro wayarsa a alijhu yay dialing number doc Mehra
Yasha mamakin yadda wayar harta katse ba a daga ba.
Daga bangern su yaa malam kuwa tun safiyar Allah da suka farka suketa muhawwara Dan Duk iya kokrin yaa sheik na kin masa magana saida ya tursasa shi yayi
Samun su yay sunyi jam'i Suna sallahr fahjr tun daga Nan ya soma tsaki yana cewa sallan su sallan Yan wuta
Haka ya Kare ma doc Mehra tanadi yana zagin sa cikin zamba akan cewa ba musulunci yakeyi ba dake shi suite ma kawai yake sawa.
Abun daya ishe yaa shiek ne suka haura ma juna,tun asubahin fari basu dena ba karankatf dinsu saida ransu yay mummunan baci
Anan ne ma yaa malam kejin asalin abunda yay ma yarsa rufaida danshi har aynzu bai dau abun da tsanani har haka ba,yadai bari a wasa ake masa game da mutuwar alaji bature.
Sanda yaga tabbas yaa sheik ya bata ransa ya harxuka cikin fushi ya gaggaya masa bakaken maganganu sanda jikin sa yay sanyi
Ahakan ma a zuciyarsa ne kawai yakejin hakan Amma afili nunawa yake maganan bai taba shi ba Shi shiyasan komi Kuma basu isa su gaya masa gaskiya ba Dan aganin sa basuda ilimin da zasu ma fahimce menene gaskiya
Da kyar da bala'i doc Mehra ya sassaita tsakanin su don kowa yahau dokin xuciya Babu wanda yake shirin saukowa,hatta hawayen yaa sheik yau saida ya zuba.
Gaba daya sai yarasa tayaya uba zaiji wannan lamari game da yar cikinsa ace Kuma bai damu ba,Wani irin tsananin fushi ne ya turneke sa yy fushi sosai da kyar doc mehra yake ta famar daddane sa
Yaa malam kuwa ko ajikinsa Wani sabon salon magana dayake cewa "daga zarar mun koma gaban wanda ta haife mu saika gaya mata Kai ba jinina bane Don banga amfanin hada jini da jahili kamar ka ba zaidu..
Writers number
08060712446
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top