chapter 18
BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Part1:chapter 18
Case1:she is ours
Nannauyan Ajiyar zuciya yaa sheik ya sauke tare da baje babban garen sa ayayin da yake nemawa kansa wajen zama,cikin babban cushion din dake falon ya nitse tare da jingina kansa a hnkli wani lumshe Idanun sa yay tsamm sannan ya Kara Bude su cikin maida wata sihirtacen numfashi.
Gani yay mufrad yanata daddana wayar sa da alamar layin imad din yake nema,tare da sake yar gyaran murya ya kalle sa muryan sa sounding soo unhappy yace"
.."Kabar neman layin sa, dannima har yanzu bamuyi magana dashi ba, dama nafada hakn agabansu ne Dan kawai hanklin su ya kwanta,yanzu haka kaine zaka kula da gidan Nan mufrad,nikam inaga i must have to go to Vegas yau yau insha Allahu cikin sauri mufrad ya juyo ya dube sa..
yace "pls Abbu,
kabari nizanje nariga na tura sako ma pilot dina within 10 min ma ya shirya cikin dakatar dashi yaa sheik Yace No,Lamarin Daya shafi dan uwana bana son Kuna tsoma kanku aciki For God sake da tuntuni yana Jin shawara da bazai aurar da yarsa ma
Irin wayannan muguyen mutanen ba,Yanzu wannan lamari da maiyayi kama?ace mutum shikadan sa yabi ya tayyyara rayuwar mutane harda yar da na yaya cikin sa? kasa cewa komi mufrad yay ganin yadda mahaifinsan yay maganan cikin kunan rai da tsantsar takaicin halin dan uwan san
Daga Nan Sallamar hjy jasmine ya tun karosu shigowa tayi jikinta a sanyaye ta karasa kusa da yaa sheik ta zauna cikin yanayin tagumi
Vibe dayan wayar mufrad ya somayi ya ciro a aljihun sa yana ganin sunan dayake kai sai ya Danna silent cikin sauri baice musu uffan ba ya sabule jikinshi daga wajen yayi waje, Sauke Ajiyan zuciya yaa sheik yy yana mai dubar matarsa yace Hajiya Ni zan wuce
Ta juyo cikin sauri tana kallon sa Tace "bangane zaka wuce ba ?Yace jasmine dole na inje can din,abune wanda ya shafemu gaba daya,sun tashi sun Dora imad akan case din da zai iya dawo masa matsala Nan gaba a daya bangaren kuma Dan uwana ne da yarsa victims,inaga zuwana can shizaifi min alfanu,so In akwai Wani abu da kike bukata ga dai mufrad zan barki dashi..kekanki kinsan inba an sasanta wannn lamarin ba bazan iya tunkarar mama ayanzu ba Wani Ajiyan zuciya ta sauke tayi shiru, can cikin sanyin yanayi tace Toh shikenan,,, Allah ya baka sa'a Allah ya kare min Kai,..pls in Babu matsala kacewa imad din yanemi Ina son magana dashi mama tun jiya ta daga hanklinta akansa,kasan jiya an report din Wani aircrash mama kwana tayi fa tana kuka,kanshi ya girgiza Yace a'a ki kirata ki kwantar mata da hanklinta sannan kibar maganan magana da imad ayanzu,ku dakata mai shi zai kiraku dakansa,doc Mehra ya gaya min case din nan is very delicate,har kotu za aje dasu,so kinga kuwa dole imad sai yayi takatsantsan da irin wayoyin da zaina yi,we are talking Abt power here,bamu San ya gwamantin kasar Bulgaria zasu dauki case din ba, so u can imagine why aka nemesa tunma Kan anemo iyayen yarinya,inaga US basa son arufe case din ne Hala,so In har na isa lpya dai zakuji komi,Dan Allah a kula da ita hadizar Hjy jasmine tace ok,toh babu matsala Allah ya tsare,yace Ameen ya miqe zai wuce ta dakatar dashi cikin sauri.."tace yaa sheik dama dazu hjy goggo take magana akan wai zasu wuce abuja da yara kuma already har mufrad ya basu go ahead da mamaki a fuskan sa ya juyo yace abuja kuma?tace eh..yace hmm gaggawan me sukeyi haka,batace mai uffan ba,Dan Tsaki yay yace toh Allah ya kyauta ai sai suje din, tunda everything is set inyaso mu zamuzo daga baya,cikin sassauto da muryan ta kadan tace Toh Amma dai zaka mata bayani ko?Kasan dai hjy mama da nikaina bazamu iya tafiya acikin wannan yanayi ba Kuma kasn hjy goggo sarai da iya mita yanzu saita dau abun nan da zafi,hmm kawai yace "kiyi abunda ya dace kawai jasmine,insha Allah zan nemesu ma kafin na wuce yau kwata kwata bamu hadu ba..tace eh Aikuwa hajiya tayita mita,baka saba fita baka gaya mata ba,murmushin kawai yay baice uffan ba,a hankli tace Allah dai ya kareka muje in taka maka..Yace A'a na yafe,Ina shi mufrad din?tace Kamar waje naga yayi,Yace ok to ke saiki koma ciki kisamesu I Wil meet him on my way out Tace ok Allah ya tsare Murmushin sa mai taushi kawai ya mata sannan ya saka kansa ya fita,fitar san keda wuya yaga ko ina shiru Babu alaman mufrad a waje sai daidaikun masu aiki da masu ban ruwa can saiga driver ya leqo ta bayan mota bai tsaya amsa gaisuwar sa bama yace mufrad yay Ina?yace shugaba ban San Inda yayi ba,kallon agogon hannun sa yay agaggauce yace duba min shi yanzun nan yana gama fadan haka driver ya juya,shima dialing number sa yashiga yi jin ance masa user busy Yasan Hala yana kusa, Bude masa motar akayi ya shiga ya zauna yay shiru a Gidan baya cikin yanayin nazari time to time yana dialing number mufrad da har yanzu ba adena cemai user busy ba,
Jikinshi ne ya basa Hala da imad din yake waya Duk dama bawai ya yarda bane cancan dan ko da sukayi waya da doc Mehra daxu bai samu ya hadasu ba
Ata bayan gidan Inda katoton swimming pool dinsu yake ya tsaya daf da bakin ruwan
Hannun sa daya na cikin aljihun sa daya na riqe da wayar dake makale a kunnen sa tun tuni bayani yakeyi.
Daga ta dayan bangaren cikin mamaki imad ya rinka sauke Ajiyan zuciya Jin alakar su da yarinyar bai taba tsammanin ita na gida bane, shi kawai ya dauka tausayi ne yake sa shin kamar ya Santa arayuwar sa,Jin bayanan mufrad ya sanyaya masa gabobin jiki sai gaba daya abun ya dada daure mai kai,Aransa yaso ace mufrad ne zai taho ba yaa sheik ba,sabida yna mugun jin shakkar haduwan su,kwata kwata baison yazo ya tuhume sa akan Hana doc mehra gaya masa halin da ake ciki tun farko, yasan yaa sheik zaice ai ansan zai iya taimakawa tunda case din ta shafi citizen din Nigeria Kuma kano state Inda yake da iko da sharia ga abun ma ya zamto na gida
Yaa sheik ya zame masa Tamkar mahaifi ko ince Wani jigo na rayuwar sa shiyasa arayuwansa sam baya cika son saka shi acikin wani damuwa,Amma a Kullum kuma yaa sheik din baya gajiya da son yaga ya kula da shi da damuwarsan, har Yau kulawar sa da damuwarsa akan su na tun Suna kanana bai sauyaba,yana kaunar imad din sosai tamkar shiya haifesa haka yakejin sa aransa.
Imad yana juyowa yayi Ido hudu da doc Mehra daga can nesa yana tunkarosa hakan yasa yay saurin katse maganan sun cikin nuna tsantsar matsuwar sa
Yana cewa muffy promise me dat zaka jirani a kano har mu dawo,akwai abunda nake so muyi ne pls,muffy yace a kano kuma?I tot a Abuja kawai zamu hadu..imad yace A'a.,tunda kaga komi ya zo cikin sauki nasan bazaifi 3 days angama case din Nan ba so zamu dawo duka da yarinyar atare,and I just want to make sure she is being taken care of..
Mufrad ya dage kafadun sa cikin cewa "ayt babu matsala,yana juyo ya hango driver dake faman kame kame Duk ya rasa ta Inda xai masa magana"Dan dauke kansa yayi yace,imad bari na je kawai Abbu yana kirana,Daga Nan sukayi sallama wanda yy daidai da isowar doc Mehra wajen sa
Mikewa tsaye imad yay cikin katse masa hanzari yace
Doc can u believe dat yarinyar ma namuce,she is from our family,ashe fa cousin sister su muffy ne,no wonder nayita Jin kamar na Santa,damn,... I felt sumting odd abt her, murmushin gefen
Baki doc Mehra yay yace kayi waya dashi ne?"gyada kansa yay yace yanzun Nan,doct yace ok..dats wat am about to tell u sai kuma na tsaya kallon news acan naga wai kano state division sun bada oder a nemo musu babban aminin mutumin Nan dake can in person of Alaji okene,yanzu yaa sheik yake fadamin ashe abokin San ne yay introducing Alaji Bature ma uban yarinyar har akayi auren,yanzu haka hukuma suna zargin definatley yasan da business din ya hadasu, Dan jinjina kansa yay kafin ya Kuma cewa hmm ,..Allah sarki,ashe ma cire yarinyar a makarnta yay ya mata auren dole badan son ranta ba and look at how she is suffering now,A Dan rude Imad ya juyo da kyau ya kallesa cikin dakewar da bazakace ya ruden ba..Camly yace what?Auren dole!..what d hell is dat, ni wallhy na dauka an dena irin wannan jahilcin
But atleast koma Yaya ne ai zaiyi bincike ko,ko dama can sun sanshi ne?
Doc yace No,Nace maka fa alhji okene shiya kawo masa shi dake sister yarinyar ta tana auren sa,dama a aqidar yaa malam Babu ruwan sa da wani bincike,idan har kana da basic requiremnt dinsa shikenan zai baka yarsa Imad dake kan kallon doc yace this is ridiculous,
doc ya daga kafadun sa cikin furta.."I'm not suprise in yay wa yarsa haka,elder bro din yaa sheik ne fa Amma kwata kwata halayen su da dabiun su ya bambamta shifa baiya Jin shawarar kowa Kuma babu mai saka sa bare hanasa Kaga abunda yasama kwata kwata ni ban cika Saka kaina a lamarin sa ba kenan dats why I cudnt even recognize d girl,yadda yake treating din mutane with no regards is out of dis world,,
...Ahnkli imad ya shafe kanshi cikin nazari mai zurfi,can yace wow,but this is really serious,ya Kara shafa kansa ahnkli ya Kuma maimaita kalaman "Auren dole?..I need to talk to d girl,,,yana fadin haka
saiya juya cikkn sauri babu jira ya nufi dakin da rufaida take kwance doc Mehra yana biyo sa abaya saidai shi daga waje ya tsaya dake only one person is allowed in at a time inba Wai ta kama dole ba,so imad din ne kawai ya shiga ciki,a hnkli ya turo kofar tare da yar sallama abakin sa yana takawa ahankli kamar mai tsoron Kada ta tadata a bacci
Samu yay nurse tana tattara tarkacen maganganun data shigo dasu Adan surgical tray da alaman tagama ne zatayi waje"Gyara kwanciyar suman kanshi yay cikin sexy voice dinshi mai dadi mai ratsa dodon kunne ya dubeta yace mata "hi pretty"..tuni nurse ta juyo a dan tsarge tana binsa da kallo Murmushi ne ya kufce mata tace.."hello sir" Dan batayi tsammanin ma zai kulata ba
Tryn to play cute ya Mika mata hannun shi dats so fair and soft yana cewa am barister imad,da sauri ta cafke hannun tace I know..I mean everybody knows who u are...girar sa na sama ya daga cikin salo mai daukar hankli ya sake Dan karamin smirk baice komi ba ya cigaba da rikita nurse din da Wani irin kallo mai rikita tunani,he just want to get some personal informations from her Abt rufaida wanda yasan inbaiyi Hakan ba bazai iya cimma burinsa na taimaka mata ba
Da haka yajanye ra'ayin nurse din Nan ta tsaya a dakin Suna Dan hira,yana hadawa da flirts yana jefo mata tambayoyin akan yanayin jikintan,within 10 mints ta kwashe bayanai masu muhimmamci ta gaya masa harda extent din raunin dataji a vaginan ta
Wanda ahalin yanzu shiyake hanata motsa kafafunta sosai,harta kammala basa labari bai dawo daidai ba Dan Wani iri yadingaji a xuciyarsa duk dama Murmushi ne akan fuskan nasa sanda ya gama Jin komi sannn ya lallaba nurse ta tafi da karyan cewa zai nemeta su je shan coffe anjima da daddare.
Tana ficewa ya sauke Ajiyan zuciya,jiki a sanyaye ya karaso gaban gadon da rufaidar take kwance tayi lufff,ya tsaya daf da Ita yanata kallon fuskarta wanda already yay fayau yay Wani irin haske bakinta ya bushe kayau har yanzu saukar numfashinta baiyi daidai ba Dan daga yanayin saukar sa zakagane hakab,gyara ma hannunta zama yay sannan ya Dan dofano a gefenta ya zauna yana mai cigaba da kallonta sosai kalar kayan asibitin da aka saka mata yay mata kyau kasencewar sa dark green ne Kuma sakakke,Babu tantama qashin wuyarta suka bayyano cikin nuna yar ramar datayi maganganun da nurse tagaya masa yanzun su suka shiga bijiro masa ya lumshe Idanun sa sosai yana famar imagining yadda abubuwan suka faru da ita,Wani irin zafi ya rinkaji a saman kirjin sa,kwakwaln sa sai maimaita kalman auren dole Nan yakeyi at same time yana imagining tayi karama ma sosai,ya dau kusan 20 mint ahaka kafin ya bude idanun nasa wanda suka cikke da ruwan hawayen tausayinta wanda motsi kadan yay to tabbas zasu iya kwacewa,a lokacin Babu sauran karfi ajikin sa bare kuma zuciyarsa wanda zai bayyana maka cewa shidin Jan namiji ne agaban alumma mai tsananin taurin kai da kokari,when Eva he sees a weaker vessels kamar mace ko karamin yaro sai gaba daya ya soma imagining insu a matsayin nasa yan uwan, har cikin kokon zuciyarsa yakejin matukar tausayin su da matukar son yaga ya taimake su.
Bangaren mufrad kuwa yana kammala wayar ya taho cikin sauri yana mai cin Karo da motar mahaifin sa dake shirin fita da sauri ya isa wajen ya same yaa sheik cikin sauri baima samun daman masa tambayar da yakeso yayin ba Adan gaggauce..yace to ni zan wuce..pls ka kula,in jikin mama bai yi sauki ba kasa keeyan yakaita can asibiti a dubata.
Sukuma da zasu wuce abuja their flight shud be tomorw,Duk abunda ake ciki do let me know pls..gyada kai muffy yay batare da yace mai uffan ba yana kallon sa har aka bude musu gate suka tafi,site din hjy maman ya nufa Kai tsaye,yana yin sallama a kofar falo ya same su duka biyu Suna kewaye da Ita sunyi jingum jingum kowaccen su cikin jimami..
Hjy maman ne a kas ta mike fararen sawunta Babu abunda takeyi sai kuka,laifin duka wa kanta ta dora,sai dai abune da bayau aka saba ba,bukar ya wuce Duk yadda ake tsammani
musammn inta kalle yadda umma hadiza ta dawo,
gaba daya matar tafice a cikin hayyacinta,da alama gangar jikinta ne akwai a zaune Amma kwata kwata hanklinta baiya gare su tunanin yarta kawai takeyi tana zullumin irin halin datake ciki ayanzu,..
Zama yay akan kujera baice musu uffan ba tukun,sai can yay gyaran murya ya shiga musu bayanin cewa su kwantar da hanklin su Nan da kwana uku insha Allah dukan su xasu dawo,kowa ya gamsu da bayanan nasa Amma umma hadiza ji take kamar karya ake mata Dan muddin bata kalle yarta rufaida Ido da Ido ba bazata taba Jin Wani abu ya ragu mata ba,can mufrad dayaga bazai iyaba ya tashi batare da sake cewa kowa uffan ba ya fice daga bisani hjy jasmine ta miqe tabi bayansa,can da yamma liss umma hadieza ta farka daga dan baccin wahalar datayi,tun safe da aka zo aka tattare yaa malam Wani abu na ci bata iya sakawa abakinta ba,nan ta miqe cikin yanayin jiri da tsananin mutuwar jiki tace ma hjy mama zata wuce gida,masifa ta soma yi mata akan Babu Inda zataje ta zauna anan din harsai rufaida ta dawo,ita dai ta yadda cewa zasu dawo din Nan da kwana uku kamar yadda mufrad yace don tasan shibai cika musu wasa ba,haka umma hadixa ta dawo ta zauna ta rafka uwar tagumi,yau kusan kwana zanne sukayi kowa da abunda yake damun xuciyar sa game da lamarin wanda kusan kowa makan sa yake dorawa laifi.
Writer contact 08060712446
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top