Chapter 1:Guns &Roses

NOTE:Alhamdullahi As promised part 1 is free,zan fara muku posting ne yau sabida wayanda suka matsu afaara amma badan am ready ba,i cant promised evryday post But amount of your coments and interest towards the story may change my mind.

Abu na farko kasani cewa littafin na kudi ne,part 1&2,part1 is free but inka zama ready anytime xaka iya fara biyan kudin karatunka for part2 to my acct 0152983148 mohd sule surayya,GTB
Or MTN pin to 08060712446 turo shedar biya wa 08060712446.
Zan saka ku a reading group INSHA Allah.

THE FEE IS 300 NAIRA.
DIAMOND PACKAGE IS FOR PRIVATE DELIVERIES AND THOSE WHO DONT NORMALLY LOVE NORMAL GROUPS THE DIAMOND FEE for GROUP is 1000,PRIVATE is 2K WITH LOTS OF BONUSES.

Abu na biyu shine in labari bai miki/ka ba, kindly stop reading it and find ur way babu dole anan okay?SMILLING FACE.

Abu na uku in kana/kina so kiyi min gyara ko tambaya misali inna saka wani information ko hoton abu bawai nace lallai abun bane ina nufin look alike dinsa ne wato misalin shi,so bance ma saikin bini private dole da wani magana ba.but do it in d coment box here honourably,constructively not comanding and condeming cos i may lash u back oo im a human too lol.

Soooo are we reaady for the romance story full of awnnnnnnnnnnns?

Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!

BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Dedicated to HRH Malama Hau'wa mu'az omar.

Part1:chapter 1
Guns and roses

District mogue no 25 Ahmadlawal street:6:34am

Kuka yake sosai gurfane a gaban wani kabari wanda yanayin kukan nasa kadai zai iya tabbatar maka cewa haqiqa wannan mutumin yayi babban rashi,musamman ma yanda idanuwan sa suka kumbura sukayi wani irin jajur ta yanda duk wanda ya kalle sa bisa kallo daya to dole sai nashi idanun shima sun ciko da qwallah tsabar tausayi.

A nan gurfanen da yake,wani kyakkwar saurayi ne mai masifar kama dashi yazo shima idanun sa sunyi jajur tsabar kukan dayaci,a sanyaye yake tahowan har ya karaso daf dashi jikinshi yayi matuqar yin laqwas bai iya daurewa ba sai kan kukan shima yakeyi,hannu yasa ya Dan dafa shi ya kuma rungume shi sosai a jikin sa ayayin da suka buda suka rungume junan su cikin wata iriyar kasalallen shauki da rauni mai tafe da ciwo da azabtarwa,babu abunda suke zubarwa junan su face hawaye masu saukowa da turirin numfashn su mai zafi da ciwon rashi.

Na tsayen da kyar ya soma iya bude muryan sa,rarrashin na tsugunen ya shiga yi yana bashi kalamai masu taushi da sanyi acikin kunnen sa wai koda zaiji sanyi aransa amma sam shima ya kasa daina kukan har sai da yaja shi da qarfi kawai suka fita daga maqabartar.._.
              

      Baya Kafin faruwar hakan

Da Yamma ne lis gari yay sanyi yara suncike kan tituna da hayaniya da alamun lokacine na sakosu daga babban islamiyar dake anguwarsu ta bayan gari dake garin kano,wasu Yan mata uku na hango suna tafe bisa tsarin takawa juna hanyar komawa gida,duk jikin su a killace yake acikin dogayen dark green hijab dake shine kalar uniform din islamiyan sun, kalar bakaramin yi musu balain kyau tayi ba saboda yadda ta amshe hasken doguwar fuskarsu da tsarin su na yan mata masu fallin tasowa,a shekaru dai dukan su bazasu wuce shekara goma sha bakwai ba,dogaye ne kyawawa kuma kawayene na tun asali tun suna yan kanana,gaban su gadi suke takawar su cikin nitsuwa dan inda sabo yanzu sun saba da yanayin yadda idanun kowa ke satan kallon su daga nan ma zaka san sudin nadaban ne acikin yan matan dake yawo a cikin makarantar.

Sunayen su Amal da batul sai na ukun sun ita akecewa RUFAIDA wanda ita kawai tafiye killace fuskarta acikin niqabi kuma dama tafiyin tafiyarta a gefe gefe musamman ata gefen dama..

Yau ma Tafiya suke suna yar hirarsu akan jaruman maza wayanda zasu dace da su da kuma irin auren zamani da akeyi yanzu wanda  suke so suma ayi musu,Kaf anguwar su har yau ba ataba yin auren kece raini irin auren manyan yayun rufaidar ba,ga na dayan dadantan wato Adda suhan shima ya gabato wanda ake cikin shirinyin sa a yanzu...

Ita dai rufaida za'a iya bayyanata acikin irin siffar matan nan masu kamala da mugun son boye kyaun fuskar su acikin hiqabi,she is very reserve duk dama ba sanyayya bace,sai dai ita maganan ta baya kamawa sai a inda ya dace da kuma wanda ya dace.

..rufaida tana da kyakkwar fuskar shagwaba wanda kota boyeshi baya fiye boyuwa,she is soo smart nd very romantic at heart,rufaida tana da burin tayi rayuwar ta mai kyau mai tsari..mai aji..kuma na wayayyun mata.

Saidai yanayin yadda ta taso shiya boye duk wani alama da zai bayyana maka hakan atattare da ita,duba da ita yar malami ne,malamin ma qarza, mai bala'in mugun son abun duniya,shiyasa a duk hirar dasu Amal sukeyi ita sam bata fiye saka musu baki aciki ba,dan har yau a Zuciyarta batajin sha'awa ko kwadayin yin auren gaggawa kamar yadda taga ko wace budurwa na burinyi bayan gama secndry schl dinta ,awajen ta auren gaggawar is a never an option for her,sabida tana da mugun burin nemar ilimi domin ta gabatar da rayuwar ta cikin inganci da nagarta,kawayen ta har sun gaji da jin ra'ayin nan nata sun kyaleta Shiyasa koda sun fara hirar samarukan su ita batace musu cikan ku,bata ma iya kula namiji arayuwarta musamman ma dake asalinta ita ba a far far bane.

Kamar yadda suka saba kullum adaidai hanyar da yabi kwanan lungunan gidajen su sukeyin sallama da juna bayan sun rabu sai kowacce ta nufi cikin gidar iyayen ta.

Shigar rufaida gidan su ke da wuya ta tarar da tsakar gidansun a kacame da zalamamun mata kwadayyu anata rabza uwar surutu har ba ajin kunne,atake saita tuno da cewa ashe tun jiya aka kawo lefen dadarta suhan wanda ake ribibin shirin bikinta a satin nan,kaf taron matan anguwar ne a gidan su wai anzo ganin lefen mace mai goshi,g'uda kawai akeyi ana shewa wanda hakan yake kara sa gaban rufaida fadi...

Kanta ta sauke kasa cikin sauri sanin bamai yin lokacin kula gaisuwar ta,tafiya ta shigayi cikin saibi da sanyin jiki tanajin yadda kananan zunde da gulma kala kala yake tashi ako wani tsirkon taron mata dake tsakar gidan sun,tabbas mafi yawan matan dake zuwa shagalgulan biki agidan su ba dan Allah suke zuwa ba sai dan gulma munafurci da nuna hassadar su a fili,kaf anguwa an ririta cewa yayan yaa MALAM wanke hannun kataba ne shiyasa saiwa masu kudi kawai yake bawa auren su bai taba ba marar karfi ba,but she just hates when ppl wll talk abt her parents dat way.

Kullum gulman mutane bai wuce yadda mahaifinsu yaa malam yake ruwa da tsaki wajen neman masu hannu da shuni ba, da yadda yake saka tsantsan jahilci da rashin bincike da azababben nuna kwadayin kudi aryuwar sa wanda har ya mayar da hakan kamar wani future ambition dinsa na tafiyar da sha'anin rayuwar sa akan auren yayan sa mata.

A hankli ta saka hannunta ta bude kofar dakinta so slow tamkar wacce bata son asanda shigowarta gidan,a nitse ta shige ciki bakinta yana mai dauke da Salam duk dama bataga alaman wani halitta a ciki ba,kallon scnd biyu kacal ta bi koina dashi tana mai wara kyawawan fararen idanunta Wani ajiyar xuciya ta sauke na samun relieve dan yadda ta fita ta bar dakin a kimtse hka ta zo ta same shi dauke kanta tayi sannan ta sake jakar islmiyarta dake rataye a kafadarta ta nemi waje ta zauna a bakin katifarsu ta zabga uban tagumi,Wani uban shiru ne ya gifta har na dan wani lokaci ayayin da takejin sautin kirjinta da kanta na kara tsananta bugunsa wanda batasan dalili ko aufin sa ba..,tun sanda aka fara maganan aurar da Adda suhan takejin kamar hanklin ta na balain tashi tunanin ta gaba daya sai yake gushewa hakama duk sanda ta dosu kofar gidan su taji hayaniyar mata sai taji kirjinta da  zuciyanta na bugawa da karfi sosai har tamkar wanda zai fado waje.

Ta dade ahaka tana meison sanin dalilin dayake jefata cikin wannan bakon yanayi,ganin kamar hakan bazai samu ba ta miqe tsaye ta zaga bayan gida tayi tsarki tayi alwalan sallan magrib sannan ta dawo ciki ta shimfida sallaya ta hau gabatar da sallah magriban ta a tsanake, Bayan ta sallame waje ta nema ta zauna akan sallayar tana yan aduoi.

Daga tsakar gidan su kuwa A hankli sautin muryoyin mata ke dishewa  da alama kowacce mace tana shirin kama gabanta sai kuma gobe in anzo a dora daga inda aka tsaya....

Koba dan haka bama Yaa malam bai kaunar ya shigo gidansa bayan sallar ishai ya tarda wani baqo ko taron matan makwabta Dake ma ansan al'adarsa ne kowani dare saiya zauna yin karatu wa almajiran sa kuma yadan musu jawabi game da qur'ani wanda yake yinshi da tsantsar harshensa na warash,a fadar sa ta tsakar gidan sa yake koyarwa inda kowani almajiri zaina bitar karatun sa amma fa duk iyawarka bazaka taba kama kafar yaa malam ba dan shi gadon karatun yayi ba tsantsar iyawa yay ba.

..hakan ya dade dasa shi jin wani irin girman kai da son nuna isa,ganin kansa yake a matsayin babban malamin addini da Allah ya riga ya daukaka bayan ilimin nashi baikai har nan ba

Kaf anguwar gidansa ne kawai akwai dokan shige da fice matar sa umma hadiza Tace gadon hakan yayi a wajen mahaifinsa shiyasa duk rintsi duk tsiya baqo baya wuce sallan magrib a cikin gidansa.

Har yanzu zaune take akan sallayar tana kammala idar da addointa bata miqe tabar wajen ba, shiru tayi kanta na cigaba da kallon qasa,Wani tunani ne  ya bijiro mata wanda bata tsaya kula shi ba tasa hannu ta jawo jakar islmiyarta ta dauki qur'anin ta ta budeshi daidai kan suratul yusuf tayi bismillah ta soma karantawa da qira'arta mai tsananin sanyi da dadin sauraro

Fidda karatun ta takeyi a natse cikin bada haqqin tajwidi da kowani irin nau'in qalqala,Jim kadan taji sanyi ya shiga mamaye zuciyarta,cunkuso da damuwar dake bugar mata zuciya saiya farayin sauki
Karatun ta ta cigaba dayi ahakan har aka kira sallan ishai ta miqe ta dora niyya tana mai yinshi akan lokacinsa, daf tana shirin idarwa saiga sallamar ummansu umma hadiza inda aka bude kofar dakin aka shigo ciki.

Kallon minti daya tayi mata tana daga tsaye fuskarta ba yabo ba fallasa tace
"Rufaida daga kin idar da sallan maza kifito ki same mahaifinki awaje yace yana son ganin ki..."

Duk dama hanklinta naga kan sallar datakeyi amma cewa hakan da umman ta tayi bai hanata jin Wani rassssss akan kirjinta ba,tuni zuciyarta ya shiga bada sautin dukan uku uku,a gurguje ta
Sallame sallar bayan ta kammala yan addua bata tsaya yin komi ba tayo waje da sauri ta nufi fadar yaa malam dake can tsakar gida.

Tafiya takeyi tana karajin Yadda kirjinta ke kara tsananta sautin bugunsa,gani tayi kowa a gidan ya hallaro tamkar ma ita kawai ake jira,dan
Sunkuyar dakanta kasa tayi harta karaso gabansu tana mai neman makanta wajen zama adan gefe.

Tana kuwa rabewa ta cigaba da kallon qasa batace wa kowa ufffan ba

"Tabe baki yaa malam yayi ayayin da ya kauda wutsiyar idon sa akanta yana mai kada kansa gefe yanamai tsananin jin takaicin halayyayr yarsa rufaida.

A matsayin shi na babban malami mai alhini da girma so yake duk wanda zaizo gabansa to ya rikito ya fada har qasa yayi gaisuwa yana mai kaskantar da kansa agaresa

kuma kafff cikin almajiransa da yaransa kowa hakn yake masa rufaida ce kacal take da nauyin aikata masa hakan Dan ita ko hade ido dashi bakasafai take iyawa ba,dayawa daga cikin yan uwanta sun fahimce cewa tsantsar girmamawa da kunyane da ita amma yaaa malam ya balain tsangwamar hakan aransa sabida koda wasa baison raini,shi gani yake tsantsar gadon rashin da'a da taurin kai tayi awajen uwarta umma hadiza shiyasa bata girmama shi..

Umman su hadiza ne agefen sa sai babban almajirin sa yusha'u,sai Adda suhane da sauran yayunta mata su uku wanda suka riga sukayi aure..wanda
Ba sai an fadi musu silar taron nan na yau ba,dukan su sunsan yana da alaqa ne da bikin suhane da ake shirin yi ayanzu.

Gyaran murya yay sannan ya dada gyara zaman sa irin ta malamai masu son nuna mulki da isa,gaba daya manyan idanun sa nakaga kan kowa yana bin kowa da kallon daya dace dashi,Wani irin shiru ne ya gifta wajen ayayin da yaja lokacin sa yana kula da motsin kowa can sannan ya shiga rero salatin shugaban mu Annabi muhammad saw yabi ya dinke ta da adduaoi irintasu na malaman zaure snn ya fara jawabi

Wani irin zaro idanun sa waje yakeyi yana kallon uban kowa a tsakar kan sa "yace ..Toh Alhamdullahi Abunda ya saka na tara ku anan bai wuce in sanar da kaina da kuma ku fadin Allah da manxon sa ba..

Amma kafin nan inaso dukanku ku bude idanunku da kunnuwanku kuyi duba da niimar da Allah yamin arayuwa,nidin nan da kuke gani dan baiwa ne Allah ya riga ya daukakani  ya bani yaya mata daddaya har guda biyar amma ban taba butulce mashi Nace bana son su ba,ni nan bukar dan malam ahamadu jikar malam gambo,da iko na da karfi na nayi tarbiyanku kaf na kuma kareku bisa tafarkin addini na,Jajurcewa ta da kokari na KADAI shi yasa yau kaf yayana suka same mazaje nagari masu tausayin su da ni karan kaina,Anan saiya gyara zaman rigarsa yana kada kansa fuskar san nan sam babu alaman wasa"..To ku sani babu iko ko dama inba na Allah ba,snn duk wani dan mutum,maqiyinka ko mahassadinka saidai yay ya barka.

Tunba yau ba na haneku da jin gulma,Ku quji maganganun da kukeji a waje akaina game daku ku toshe kunnuwanku ku yarda dani bazan taba cutar da ku ba
Snn Ku godema ma Allah akan abunda yayi muku,,kudai ku cigaba da gode masa,in yaji dadi saiya kara mana.

Ni dai Nauyi na sauke akanku,Ke suhane saiki bi sawun yan uwanki wayanda suke gidajen mazajensu kema ki zauna lumui...Kunaji na daiko?Atake Dukan su suka amsa masa da eh kuma a girmame.

Dan shiru yyi sannan yace kowa yasan dokata dan haka bazan bata baki na wajen kara maimaitawa ba.

Ku zauna agidajen ku bana son inji ko ingani domin duk wacce ta kawo mun butulci zataga baqar tijara a kwanon cin tuwon ta..duk ku tashi ku koma ciki yana gama furta hakan kowa ya tashi tsaye domin bin umarnin sa suna masu godiya.

,Yunkuri umma tayi zata miqe  ya bita da wata hararar gefen ido, muryan sa a shake ta fito daga can kasar wuyar sa yace..."ke hadiza? juyowa tayi Tace naaam malam,da sauri ya dauke kansa ya murtuke fuska dammm kamar bashi yy maganar ba,sai can yace"Dawo nan ki zauna,bamu gama magana ba, tabe bakinta kawai tayi ta juyo tun batama karasa zama ba ya maida idon sa kan hanya yana cewa....ina ita rufaidar take?cikin wani irin yanayin fargaba rufaida ta dakata da tafiyarta ta juyo cikin sauri tabi ta rusuna a gefen su kanta na kallon kasa a hankli Muryarta can kasa tace"gani nan baba"..dan shiru yay fuskan sa na kallon gefe kamar badasu yake shirin yin maganan san ba
Kaf dinsu shiru sukayi suna sauraron sa shikuwa Sanda ya dan ja lokaci snnn Yace"..."toh kema saiki shirya dan da alamu kema bazaki karayin sati biyu agidan nan ba..

,babu shiri rufaida ta miqe tsaye kuma a mugun razane
"Sati biyu kuma baba?Wani Ggggaffffff kirjinta da kanta suka Sara alokaci guda,da alamun sam bata fahimce wannan kalaman ba,saidai ganin irin kallon banzan da yabita dashi yasata kasa furta wani abu Umma ne ta kalleta ganin yanayin ta sai tayi saurin ce mata ta wuce ta shiga ciki,Nan Ta wuce summ sum Kamar ruwar kankara aka watsa mata dan har Wani Nauyi da bari bari jikinta ya shigayi shikadansa

Wani doguwar tsaki ne ya biyo baya
"Allah ya wadar naka ya lalace
Mtswwww,Yaa malam ya furta hkan yana shirin miqewa tsaye Umma sai tayi sauri itama ta taro sa
"Malam ban fahimce maganan ka ba game da rufaida..."kace ta shirya nan da sati biyu..itama auren zaka mata ne?
Babu aufi yace mata Eh Aure zan mata,.Itama bataja ba Tace toh Allah ya sanya alheri..Amma naji kace nan da sati biyu naga rufaida bata kammala karatun ta ba tukuna Nace ko kamanta bana zata gama ne?

Tsaye ya miqe a hatsale yana kallon ta yace
"To ina ruwa na da karatunta?Ba bana ba ko damina ne babu abunda ya shalleni,ni Aure zan mata...umma
Zata bude baki ya dakatar da ita da hannu ya kuma shiga nuna ta da yar yatsar sa, yace
"Keeeee hadiza,toh ki kiyaye ni, karki kuskura ki kawomin jahilci a lamurana
Nace nanda sati biyu zan aurar da rufaida yarki ce ko yata?

Kallon scnd biyu Umma tabishi da shi batace uffan ba..ta kau dakanta gefe dan tyi calming kanta Sai can ta dago tace Haba malam To laifi ne dan na tambayeka?,naga wai haka aka sabayi agidan nan.Kowa dai saiya kammala sekandare ake aurar da shi ,cikin tsawa Ya tsareta har yana huci
...toh baza'a ayi hakan akan rufaida ba..gwara ma ki nitsu kihau tunanin yadda zaki shiryata dan Jiya wajen karban baqin suhane naga wanda ya dace da ita itama,jibi zasu dawo daurin aure zasu ganta..kuma ni na yanke hukunci rufaida shizata aura Kaiwa nan ya baje garensa ya wuce cikin sashin sa ya barta wajen atsaye batare dayama saurare mai take shirin furtawa ba,umma ta dade a tsaye awajen cikin rashin sanin abunda ke mata dadi,Wani jimm taji iska ya dauke mata,jiki babu kwari ta koma dakinta da kyar tana nazari,anan ma ko zaman minti uku batayi ba taji kamar ana bugun mata kofa,da mamaki ta miqe tsaye dan batayi tsammanin ganin kowa aynxu ba,can tace"..Waye ne?..jin ba a amsa ba yasata karasowa ta bude kofar da kanta,ganin yarta tayi a rakube da mabudin kofar fuskarta cikke tam yake da yanayin fargaba da tsoro,..
cikin danniyar abunda ke damunta da jarumta irinta mata tace "..ah'a
Rufaida?...meye kawoki nan da dare?meyafaru?dan shiru tayi sannan ta dago kanta sama a shagwabe kamar wacce zata fashe da kuka Tace umma naxo wajenki ne. sake kofar kawai umma tay ta bata hanyar shiga ciki,kallo ta dinga binta dashi har sanda ta shigo
Tace"lafiya daiko?Ta maida mata tambayar tamkar bata gane metake ciki ba.

Itama bata ansata ba tukuna,waje ta samu a kasa a gefen gadontan sannan ta zauna a takure tana mai shirin kife kanta a tsakankanun cinyiyonta Umma ce ta dada gyara tsayuwarta cikin kauda duk wani alaman dazai bayyana damuwarta itama tace"A'a dakata min
Karma ki soma min shure shure anan,Kinga yanzu mahaifinki zaice zai shigoyin bacci ki fadi abunda ya kawoki kawai ki fice min adaki na...

Dago kai sama rufaida tayi ayayin da hawayenta da suka cike kwarmin idanunta suka zubo bisa kan kyakkwar farin fuskarta yuuu suke saukowa tamkar da an kunna famfo daya na bin daya..Umma Tace "Lpya daiko?
Tanaji Umma ta kara tambayar amma bata iya amsawa ba,da kyar ta miqe tsaye cikin tsananin rawan Murya"..Tace
.um..mah.sai kuma tayi shiru tana faman zare idanun ta"kanta ta dada sunkuyarwa kasa kamar mai shirin fashewa da matsanan cin kuka..cikink wahalliyar nishi Tace.."Dan Allah ki fahimtar dani  abunda baba yake nufi dazu dayace nan da sati biyu zanbar mai gidansa.
Umma meye hakan yake nufi?umma kardai Aure baba zaimin? Umma dan Allah ki fada min gaskiya,Wasu maqudan hawayen ne suke saukomata ta shiga sharesu da yatsun hannunta tanajan sheshkarta ahankli batare da ta iya karashe sauran maganan ba da alaman kukan ya shigeta sosai

Dan shiru umma tayi bata amsa taba tukuna sanda tanaimawa kanta wajen zama sannan ta sauke Ajiyan zuciya irin wanda bazaka taba cewa wani abu makamancin damuwa na gudana a zuciyarta ba..dan kallo tabita dashi a ranta Tace Allah sarki Rufaida ta..
"Tace toh akan wannan maganan zaki zo kina dagamin hankli ke wai yaushe zaki girma ne rufaida?
Cike da magiya Tace "A'a umma dan Allah ki fadamin aure ne ko?ganin hawayen dake saukowa a idanunta yasa Umma Tace toh banfada ba uwata..Daga kawai yace hala nan da sati biyu zaki bar gidan shikenan saiki dora ruwa ma zuciyarki?
..shikanshi cewa yayi hala ai bai tabbatar ba,hala so kawai yake ki kula tunda daren dadewa dai yau kece kadai kika rage masa agaban sa ya aurar..jin haka yasatajin dan dama dama aranta amma sai dai sam hanklinta yaki kwanciya...can tace
"Umma ina son nayi karatu naje har babban makarantar gaba da secndry
,Umma inada burin intaimaka ma al'umma arayuwata ,Inda ace baba zai fahimce ni dasaiya dagamin kafa akan maganan auren nan,nikuwa Insha Allah bazan taba bashi kunya ba,nan gaba sai yayi alfahari dani sosai

Murmushi kawai umma tayi Tace Hmm Rufaida kenan koni nasan da hakan,nasan zaki saka muyi alfahari dake wata rana amma Kisani "shi gugan da yasaba Jan ruwa a rijiyar kwari bazai taba juriyar Jan ruwa a rijiyar dake sahara ba.

Shima aure da kike ganin sa alheri ne rufaida..Kisa hakan aranki haka sannan ki roke Allah ya axurta ki da miji na gari kinji?A sanyaye ta dago ta kalle fuskar umman dan gaba daya bata gane yanayin murmushin karfin halin data ke ganin atattare da ita tace"Ameen umma na, amma kina ganin baba zai taba barina incika burina na rayuwata kuwa?

Umma Tace hmm nima bansani ba rufaida,Nide abu daya zan gaya maki KIYI HAQURI akan duk hukunci da Allah zai yanke akan rayuwarki Ki dauka bayin mahaifinki bane qaddarar kice.

Tabbas in kika rungume qaddararki mai kyau da marar kyau toh Allah dakansa zai ji kanki ya kuma albarkace rayuwanki

nan umma ta shiga mata nasiha,sosai ta ja hanklinta akan ta rinka hakuri karta na tada hanklin ta akan abu kalilan sunfi mintina talatin sannan sukayi bankwana rufaida ta fice ta koma dakinta.
Please coment and votes na roqa.
SURAYYAHMS contact/08060712446.
Follow my Wattpad acct @SURAYYAHMS.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top