2:fight or flight
BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Chapter 2:flight or fight .
Bayan kwana biyu
Mata ne makil a babban tsakar gidan dayasha bugun cement duk sun sanya ankon su ta rubber rubber milk colour da ja dukan su dinkunan su iri daya..
Babba da yaro tsoffi da matan anguwa sai hayaniya ake anata cin shinkafa kamar Allah ne ya aiko su,ga wasu a can gefe sun baza faranti suna famar shan kwate,wasu na warban zazzafar masa da miyan taushe wacca taji dage dagen Kan naman rago,wasu nacin dafa duka ta rice, ga zobo drink ga kunun zaki ga uwar gayya wato taliya jollof da kuma tuwon shinkafa,...
daga can gefe kuma wasu tsofaffi ne a shinfede akan tabarmai suna famar rera wakokin zube suna buga kirari irinna zalamammun makwaidatan maroka wanda sukayi degree a harkan barace barace da kwaram agidajen biki.
At same time Kidan wakar hausa mai dauke da kalaman soyayya ta mawakin nan hamisu breaker na tashi sosai sautin kida ta cikke iskan wajen
wasu matan na rawa ana shewa ana manna musu kudade,wasu kuwa banda gulma da tsugudidi ba abunda sukeyi wani irin gudan nishadi akeyi daga gani kasan gidan biki ne daya amsa sunan sa gidan biki.
Gidan Babban gidane mai fadin gaske wanda saika wuce inda ake shagalin bikin sannan kabi wata sashe dasuke kira da sashen YAA MALAM.
Kasancewar sashen yaa malam yafi kowani sashi girma agidan daga nan ma yake sauke Manyan baqin da sukazo bikin musamman domin shi
Mutane ne akoina saidai duk da haka ko ina agidan fess yake,duk dama biki ake a gidan amma basa barin koda cokali akasa, anshare cementin kasan tasss an shimfida tabarmai ko ina dai sai kyalli yake tsabagen tsaftar su.
ginin flat daya ne a sashen YAA MALAM self contain ce mai dauke da wani babban fankacecen falo da akalla zai iya daukan mutane talatin, falon na dauke da wasu irin hadaddun kujeru brown color asalin design din da can mai tumtum dan ko pilow ba ayi musu ba,sai ledan tsakar dakinsa mai shegen kyau shima bown colour da yar sallayar sa agefe sai wayansu jimammun jakunan littafai da kwalaben tawadar sa,da kwaryaye da Alluna da ake jerawa ajikin bango sak irin shigen kwalliyar da mutanen da can sukeyi ma muhallin su.
kana ganin dakin kaga dakin babban magidanci kuma MALAMIN addini zaune yake a babban kujerar tsakiya tare da baqinsa yan birnin kudu da surukunan sa wanda suka shigo ba da jimawa ba,yau yaa MALAM ya fito ras yasha fararen shadda inda akamai dinkin malum malum yy kyau kwarai kamar bashii ba.
Agefen sa wata tsohuwa ce wacce a shekaru akalla bazata wuce 68 ba taci uwar atampar ta super holland gold daketa sheqa gyalli kaman an shafa mai mangyda ajikinsa, an mata dinkin buba da zanin sa data daura akan rigan dake ma kyam take dan ita tsufar bai lalata mata jikinta sosai ba,motsatsen kafanta da gabaki dayanshi yasha jan lallai tayi irin lallen nan ne da akafi sani da dungulmin tsohuwa.
fara sol ce tsohuwar,gashin kanta dana giranta duk sunyi furfura sabida tsabar tsufa, sai goshinta d kan hancin ta daketa fidda uban zufa
Kuma dudda tsufan nata siffarta bai hana nuna kamannin ta da magidancin dake zaune kusa da itan ba,hakan ya kara bayyana cewa mahaifiyarshi ce.
A cikin muryanta na tsofaffi mai tafe da dan masifa ta kira sunan sa a hankli tace..."Bukar,bukar,bukar wai sau nawa na kira sunanka?Shiru yay dan baison ya amsa ta agaban baqinsan ya sauke kai ya maida hanklinsa kanta dan baiso tabashi kunya agaban su duk dama jin kunya ba wata aba bace data damesa.
Murya kasa kasa Tace kaga dai sau uku nakiraka ko toh wlh nagaji da zaman nan kodai ka tsawatar wa yarka ta dawo kona tattara yinawa yinawa nabarma gidanka nakoma chan cikin gari Gidan dan uwanka zaidu ai dama saida yace in huta kafafuna nayi fafur naki bin nashi,yo mai zan gani anan?abunda aka saba dai shi akayi shi nikuma an ajiye ni kamar bazaurar gawa..tsaki taja mtswww,tace aikin banza aikin wofi kawai..ni ka gayamin abunda zaka fada min kawai in kama gaba na
Dan rangwofowa yayi,baqar fuskan nan nasa a balain turmushe yana kallon ta sanin cewa yanda take masifan ne kawai yasa zai sassauto da muryan sa qasa ya kulata dan yatsani a rinka aibata shi ko akira sunan kanin sa zaidu acikin lamarin sa yace "kiyakuri
Hajiya Mama yi hakuri"..bata kulashi ba can ta yaface hakwararta da dan tsinke kasar wuyarta tace
,"bawani zancen na yakuri" ta watsa mai harara atsakar idoh tana nunashi da dan yatsa tace yau kuma wani iskanci RUFAIDA ta samo ku kuma kuka daure mata gindi?Baice komi ba,ta kuma Jan tsaki yo inba hakaba Aljanu ne mutanen datake jin tsoron su?koko mudinne Mayu da ta guje mu?Ai Cha nayi yau duk yan uwane da abokan arziki suka cika gidan nan,yau ake bikin yayarta SUHANE amma wai ace tun safe ba'aga yarinyar nan ba tasaci hanya ta sabe silihu tafice? yo kajimin yar banzan yarinya marar kan gado,nide ba waje na ta debo yawon banza ba,sai dai awajenka,ko awajen uwarta hadiza.."
Tana gama sumbatun ta taja tayi shiru sabida rashin amsa mitar ta da yaa MALAM din yayi, sallaman da akayi ne daga bakin kofa ya dada Jan hanklin su,wata kyaykyawan mace mai dan jiki yar doguwa tasaka madaidaicin Atampa an mata dinkin riga da zani doguwan riga plain
ta shigo dakin fuskarta ba yabo ba fallasa ta karaso ciki ta gaida tsohuwar a ladabce
Tace sannu da hutawa hjiya mamah"Kallo ta kare mata saf sannan ta harareta batare data amsaba hakan yasa matar sunkyar dakai ta dubi yaa malam dake kallonta tace "gani Mai gida naji ka aiko akirani" cikin fushi yana girgiza kafa yace shin wai ina RUFAIDAR taje ne?"
shiru tadanyi tana kallonshi kafin ta sauke ajiyan zuciya a hankli mai cike da damuwa tace "malam nima bansan inda take ba" ..
"karya takeyi, na rantse maka Bukar, kunma isa?wlh, wlh kajini dakyau na rantse maka na sake rantsewa in baku nemo min jikata rufaida ba yau saina tsine muku Albarkan dake kanku tas kaida matarka kafun intafiyata Gidan zaidu inda kwanciyan hankali yake achan".. ta karashe maganan tana uban huci kaman dagaske.
kallonta kawai yaa malam yayi cike da takaicinta dan ya gama fahimtar meyasa take son tada rikici,da alama so kawai take baqin sa susan me ake ciki nacewa rufaida batason auren koda ma zasuce sun fasa,sosai ya gano salon mahaifiyar san kuma yasan babu yadda za'ayi ta juya ma rufaida baya.
Dada daure fuskan sa yayi. yace "haba mamah, to kibari nai magana mana kawai ai basai rufaidar tazo bama dama akan batun auren ta ne,zata budi baki yayi sauri yamike tsaye yace nace kiyakuri ko?babu kuma inda zakije sai an gama maganar, kiyakuri wayannan baqin domin mu sukazo rufaidar dama kawai ake jira dan karkuce na zalunceta
kwafa tayi tawani rau rau da idanunta tana binsa da kallon mamakin furta mata hakan dayayi dan karkada kafafunta tyi tace toh da ba aga rufaidan ba ai sai ka yi maganan ka ai dama hakan kasaba yi".
Kasa cewa komi yayi sabida yafison sai yarshin tana cikinsu sannan yay bayanin sa a tsanake domin ya jadadda qudirin sa a zuciyar duk wnda yake shakkar yiyuwar lamarin auren rufaida acikin gidan
,lura da hakan yasa tsohuwar ta miqe tayi waje tabarsu dan sosai takejin zafin abunda dantan yakeyi ma yayansa
Na musu aure batare da son ransu ba
kallon matar sa yayi datai shiru tana jinsu jikinta a matukar sanyaye,a dake ya juyo kanta yace KE hadiza wai ina RUFAIDAR taje ne? Ki fadi tsakaninki da Allah" a sanyayei ta dago tace "wlh mai gida nima bansani ba. bansan inda tayiba, ina fama da jama'an biki ban masan bata gidan ba saida su Jadwa sukazo ta fadamin wai yau kwata kwata bataga rufai ba"
cikin fushi da tsananin takaicinsu ita da yartan yace "to kije koma ina take ki nemota kin daisan sabida ita na aje manyan mutanen dake nan ko?yaune ranar da zasu ganta kuma yau nakeso na jadadda maganan ranar auren ta agaban kowa yaji
Inhar rufaida guduwa tayi dan ta tozartani duniya da lahira bazan yafe miki ba hadiza..
Umma tace...a'a dama fa tace da ita za'akai yayarta chan anguwar gidan mijinta inaga rufaida ba guduwa tayi ba... atake ya tsareta dacewa ohon miki nidai na fadamiki kinemota ta dawo gidan nan yanzun nan"...
dan ajiyan zuciya ta sauke tana kallonshi kafin ta miqe tsaye tana girgiza kai cike da takaicin sa ta juya zata fice tabar dakin can saikuma sai ta juyo ta kalleshi da idanunta da sukadan chanza kala tace "amma malam kasan matsalan yarinyar nan rufaida ko? batun yau mukasan bata son auren nan ba tanada muguwar tsor...o..n aur..e itafa karatu take son yi
cikin wata muguwar harara ya katseta da sauri ta hanyar cewa karatun yaci ubansa Nace miki..."yanzu rufaida yarinya ce da zakice min tana tsoron aure?KE meye amfanin ki amatsayinki na mahaifiyanta?MIJI gashinan ni na samar mata kuma WALLAHI shi zata aura.Ya karashe maganan yana nuni da daya daga cikin dattijan mazan da suke zaune a falon wanda da alama hirar su sukeyi bama jinsu sukeyi ba.
Da sauri umma Hadiza tayi saurin dauke idanunta akan su musamn akan shi Wanda akace za'abawa rufaida,gashi nan dai Wani tsohon tsoho dan ko a shekaru tasan ya haife rufaidan ta,runtse idanun ta tayi jin wani qullutun baqin cikin daya tokare ta akirji ganin ko a fuska ma bai dace da yarta ba
" .. Kinga kisan yanda zakiyi kinemo ta kindaiga raina a abace yake kina kara bata lokaci karfe biyar za'a zo daukan Suhane kuma tare zasu tafi yanzu karfe hudu ne harda kwata"juyawa tayi ahankali tafita daga dakin batare datace mishi uffan ba, da kyar ma ta iya saita fuskanta ta amsa gaisuwan mutanen dake tsakar gida ke mata amatsayin ta na uwar Gidan kuma uwar amarya
Nan ta wuce ta shiga bangaren su inda falontan ma ke cike da jama'an ta dana anguwa ana zaune anyi makil
Gefe tayi tabude wani dan daki ta shiga ciki,wata babbar mace ce a zaune a dakin tana hada kayan akwatin Amarya da za'a tafi dasu kana ganin matar kaga kamanin manyan hajiyoyi maida kofar umma hadiza tayi ta rufe ta shigo ta zauna kan gadon sun dabas jikinta sam babu kwari da sauri tasa hannu tana goge kwallan dayake shirin zubo mata,cikin sauri matar dake hada kaya a akwatin ta saki kayan hanunta tazagayo tazo ta gabanta tace
"meye haka kuma hadiza!menene kike kuka Maman rufaidah?"
Duk dama hawayen sunki dena zubowa share idanuntan tayi tanadan nishi nishi da alamun kukan ne ke cinta sosai aranta tace "Hajiya jasmine,wallahi narasa yanda zanyi da yaa malam, kullum, kullum dakika sani saiya jamin rashin mutunci daga wurin mutane,zanji da baqin cikin ya aurar da suhane ga wanda bazabinta ba ne ko wayannan mugayen mutanen daya rariko wai zai nuna musu rufaida? yanzu laifinane dan rufaida Tace batason auren wurin makaranta zatayi?duka duka rufaidan nawa take? Itafa ko secondary schl bata kammala ba, Yau koni na hallice ta ai ba zan tursasa ta ta aure namijin daba ta ma san dashi ba ...ni kawai nasan rufaida dagan gan ta gudu tabar Gidan nan tun safe..inba haka ba Munanan dake ai inata kwada lamber wayarta ta baya shiga,natura yan uwanta duk sunje makota da Gidan kawayen ta kiramin ita wai ba'a ganta ba,kuma malam yaki yabar maganan, dan Allah ya zanyi? Narasa yanda zanyi na
chanza ra'ayin malam ko ita kanta rufaidar, narasa wace irin yarinya ce ita da batada haqurin yin biyayya ma iyayenta kamar sauran yan uwanta.
Amma har Ace yau bikin yar uwarta na jini sabida fitina wai ta gudu tabar gidan nan? ni yanzu a ina zanje in ganta,dan Allah ya zanyi da raina?" takarashe maganan cikin dagon murya sosai hawaye na gangarowa daga idanunta gwanin tausayi, da sauri matar ta rungumeta ta daura kanta ajikinta tana shafa bayanta sigar lallashi,tace "haba umma hadiza ya isa, ya isa haka kidena kukan nan dan Allah,ki bari na gwada kiranta kozai shiga, is okay."
Ta fadi hakan tana rarumar wayarta kirar iphone x newest version takai kunnen ta bayan ta dialing number rufaidar
,ringing yake tayi har saida ya kusa yankewa sannan aka daga...
Batama jira jin sautin muryanta taba cikin tsigar fada tace"..ke rufaida?koma daga ina kike toh kiyi maza kitaho gida yanzun nan..
Ko gama sauke wayar a kunnenta batayi ba sukaji motsin mutum ta bayan su atake dukkanin su suka juyo suna kallon ta inda ta fito da matukar mamaki a fuskokin su.
Bayan ta diro ciki A hankali ta juya cikin sanyin jiki ta karashe rufe windows din dakin sann ta juyo tana kallonsu ganin yadda suka tattaso tsaye suma suna kallonta
Karasawa gefen gadon tayi jiki babu kwari ta xauna a qasa murya can kasa tace ina yini Ammi jasmine?
Dagowa hjy jasmine tayi tunkan ma ta amsa umma hadiza ta katse ta a tsawace cikin bacin rai.. Tace..."ke Rufaida ashe bakida hankali?..Daga ina kike?nice tun safe daga ina kike?...sauri kiris ta gwada mata mari hajya jasmine ta janye ta baya tana huci..
A hankli jikin rufaida ya shiga rawa tuni koinanta ya dau kyarma tsaban takaicin dake cinta har cikin ranta wasu maquson hawayene suka shiga gangaro mata akan fuskarta wanda daga ganin su kasan bata shirya musu ba,yanayin ta mai cike da jin haushi da kuma tsananin so da tausayin mahaifiyartan.
Itama umman Ji take inama tana da ikon cikama rufaida burinta kamar yadda kowacce uwa take muradin cika ma yarta nata burin,sai dai kash Koda shike ba yau akasaba ba,yayun ta hudu an aurar dasu ahaka da wuya ne in ita ta kufce ma wannan mummunar aqida na mahaifinsu.
Tabbas itakanta da zataso tabaiwa yarta rufaida damar yin rayuwarta mai cike da haske da buri amma tasan hakan ba abu mai yuwa bane har abada auren nan dai shine qaddarar su.
Nan Ta fusato cikin sake maimaita mata tambayar ta"..Nace daga ina kika fito rufaida?ko bazaki bude bakin ki amsa ni bane?mahaifinki cewa yake har abada bazai yafeni ba sabida nice nake koya maki wayannan dabiun
Rufaida...
...cikin sauri Rufaidar ta dago kanta ta kalle mahaifiyartan jin alamar bakin ciki da kukan dake tafe a muryan ta,atake itama nata idanun suka gwaranyo da zafafan hawaye masu matukar karya gabobin jiki.
Rawa sosai jikinta ya shigayi muryan ta a disashe kallo daya zaka mata kasan tana cikin damuwa da tashin hankli,cikin wata tokararrayiyar muryan ta data kasa fita ta furta sunan mahaifiyar tan tace
"Umma dan Allah..
Dan Allah umma kiyi haquri ki yafeni,badan na quntata miki na fita a Gidan nan ba..
Kukan ne ya subuce mata mai tsuma "umma kinsan bana son bacin ranki
Jimin afuwa dana kasa danne zuciyata..umma dan Allah ki fahimce ni..umma dan All..ah..karkice na saba maki,sabida ke kawai na dawo gidan nan yanzu ,amma wallhy bana son auren nan umma..nikam mutuwa zanyi..
Ta karashe cikin sautin kuka mai qarfi da tsuma zuciya duka jikinta sai rawa yakeyi a durqushe agaban su.
Wani irin kukan fitar rai takeyi idanun ta a rufe kyammm bata ma iya budesu.
..shiru ne ya ratsa tsakanin sau dan hanklin su gaba daya a tashe yake na ganin yanayin rufaida, hjiya jasmine ta bi tarasa wazata fara tarba acikin su dukan su hawaye ne masu rauni yake sauka daga idanun su..kukan zuci sosai umma hadiza takeyi dan duk cikin yayan ta sun fi shaquwa da samun fahimtar juna da rufaida
Saidai Wani ciwon tabbas baida maganin daya wuce addua,hakan yasa Ta rufe idanun ta tsam cikin masifa
Tace rufaida ashe Kema mutuncin nawa xaki kwabar?meye na fada maki jiya da safe bance dake kiyi haquri ba rufaida?inkinyi masa biyayya mutuwa zakiyi?wato rufaida kin gwammaci kiga na fadi na mutu agidan nan sannan xaki haqura da shegen taurin kan naki ko...toh inkikayi masa taurin kan auren sai afasa yinshi dake?sanin kanki ne koda birnin sin kika tafi kika dawo sai anmiki auren nan,kidai duba dai tun daga kan babban dadarku murja har ita wacce kikebi suhane da ake shirin kaita yau ba'ayi auren fashe agidan nan ba,kisani, akanki kuma baza a fasa ba..
Wani sabon Kukan rufaida ta barke dashi durqushe a kasa agaban su ganin yaddaa hjya jasmine ta rirriiko mahaifiyartan dake a zuciye takeyi mata fadar looking both confused nd frustrated,"..
Ji take kamar ranta da zuciyarta duka zasu bar jikinta tsaban radadin azaban kuncin asaran burikan ta da tarwatsewar da rayuwarta yake shirin yi a lokaci guda..
Duk dama ta taso cikin ganin yayunta duka sunai ma mahaifinsu biyayya wa auren dolen da yake musu amma ita aranta jitake sam bazata taba iyawa ba...For what sake? Ita da ko secondryn ma bai bari ta kammala ba...?Inama ace yaa malam yadan kyale maganan auren nan har sai tayi ss3 dinta tukuna tunda dai ss2 take aynzu..
Saidai ayadda taga yasa ranshi da dukkan imaninshi akan zancen auren tan nan da wuyane ya fuskance damuwarta har ma ya saurare umman ta bare kuma ita..
Itadai tasan ance wajen karban auren yayarta suhane ya nemar mata miji kuma da alamun bayaso sukufce masa ne shiyasa yakeso ayi aure nan da wuri,dan cewa akayi suna da kudi sosai daga kasar waje ma suka taho..
Kukan fitar rai rufaida takeyi cikin tunanin yadda zatai asarar rayuwarta tun umma hadiza tana mata fada har ta gaji ta biyewa hjya jasmine suka suka dawo rarashin ta amma haka fir taki ta amshi batun auren nan aranta cewa take bazata taba iyawa ba..
Daga bisani da umma taga abun babu sauki kawai tayi waje ta barsu
"tana ficewa Rufaida ta durqusa kasa gaban hjya jasmine da idanunta da sukayi lufu lufu tace Ammi jasmine dan Allah ki kira kawu zaidu ya samin baki Wallahy zanyi duka abunda akace inyi muddin yaa MALAM zai kyaleni nayi karatuna,Ammi kirisss ya rage in kammala secndry
...Ammi bana son a aurar dani..Dan Allah kitaimaka min Ammy..Sosai take kuka ko inanta sanda ya sauya kamani daga na mutum tsabn kaduwa da tashin hanklin datake ciki..
Kasa cewa komi hjy jasmine tayi dan ita kanta tasan waye yaaa malam din
Uwarsa ma data tsuguna ta haifesa bata fiye lanqwasa shi ba bare ita datake a matsayin matar kanin shi?jikinta a sanyaye ta dago idanun ta da s sukayi sanyi a natse take kallon yanayin rufaidar dan sosai tausayin yarinyar ya shigeta,sabida tana burgeta sosai,a kaf cikin yaran yaaa malam itace kawai ta gwada borancewa dan ta karba ma kanta yanci na kokrin cimma burikan rayuwanta masu kyau Amma yayunta kam hannu bibbiyu ma suke biye masa akan lamarin sa na musu auren dolen dayakeyi..
Yatsun Hannunta ta kama sannan ta jawota har saman gadon sun,ajiyeta tayi kusa da ita ta rungumeta ajikinta sosai Babu abunda rufaida takeyi sai hawaye da kuka mai taba zuciya dan har cikin kasan ranta ta tsani abunda ke shirin afkuwa da ita..
Haquri da nasiha
Hjya jasmine ta rika bata amma ina kamar ma tunxirata akeyi,da kyar ta lallabeta ta yi alwala da niyyar haka intayi salla raka'a biyu zuciyarta zaiyi sanyi,shigarta bayi keda wuya saiga sallamar umman ta wacce ta kasa dago idanunta sama ta kalle su bare ta zauna a dakin
Daga gnin yanayin ta kasan dauriya kawai takeyi,cike da karfin hali".Tace
Hjya saiki fito masu daukar suhan din sun yi himma,ina ita RUFAIDAR? Ko itace a bayi?..dan miqewa tsaye hjy tayi tana dada gyara zaman mayafinta tace" "eh rufaida tana cikin bayi"..Ni nace mata tayi alwala tayi dan nafila naga tun dzu kukan kawai takeyi..kada kai kawai umma tayi batace uffan ba sukayi tsayuwar jiran fitowar tan Atare,dan shiru ne ya gifta tsakanin su,dukan su bakin su dauke da magana amma anrasa wanda zai fara cewa dan uwansa komi.
"Koya ake ciki da tsayuwar maganan ranan auren rufaidar oho?hjy jasmine ta shiga raya maganganu aranta itadai tasan tun shekaran jiya hajy mama take mitar cewa yaaa malam yaki jinta akan maganan auren rufaida shikuma dan uwan sa zaidu yace bazai taba saka bakinsa akan maganan ba,hjy tayi tayi akan koda ya barta ta kammala secndry schl nan da watanni amma sam yaki yace ya riga ya bada ita.
Akan wannan magana ta auren rufaida Gaba daya saida kansu ya daure,kowa tausayin ta yakeyi sabida duk sauran yan uwanta ba haka aka musu ba dan kowacce sanda yabarta tayi candy sannan ya aurar da ita,shin komaiyasa ya canza tsarin sa akan rufaidar oho?
Muryan umma ne ya katse ma hjy jasmine nazarinta,kallon kofar bayin take tana cewa
"Rufaida kiyi sauri kifito mana dan Allah,sai kuma tadanyi shiru,can Tace toh mahaifinki ne ya aiko ni in fitto dake aiko sallama kwayi da yar uwankin ko..
...hjy jasmine najinsu bata motsa ba bayan minti uku saiga rufaidar ta fito..sauke kanta kasa tayi ganin
Kallo daya suka bibbita dashi,umma Tace hjya muje ko?..Tace ok bismilla sannan ta ruko hannun rufaidar sukayo waje Umma ta saka kai wajen musu jagora har sasshen yaaa malam Inda yake acike makil da sauran yan uwanta mata da kakan su hjya mama da babbar yar Hajiya jasmine din wato barister fareesa zayd matazu.
Gaba daya hanklin rufaida baiya jikin ta,hasalima batasan awani yanayi take ciki ba,tafiya takeyi a xauce tare da hjy jasmine tamkar anajan rakumi da akala dan batama jin sautin komi face na zuciyarta dayake bugun shirin tarwatsewa dan kanshi
Tun daga bakin kofar dakinsan zaka soma jiyo sautin nasihohi da kalamai na zaman aure dake tashi ataciki,hawaye ne masu tsananin zafisuka kara ciko mata idanun ta jin Muryan yaa malam ayayin dayake bada fatawarsa har suka shigo suka zauna baima kalle su ba.
Yace:
"Aure babbar ni'ima ce wacce take kange mutum daga afkawa sharrin shaidan,aure yakan karawa mace da namiji kima acikin sauran jama a
Allah yakan sanyawa auren da akayi dominsa yardan sa da albarka acikin sa
Irin albarkar da ma'abotansa zasuji dadin rayuwar auren su ba tare da dauwamammen bacin rai ba"
Ni na sauke haqqin hakan akanku,domin In nema maku wannan kima da darajar na nema maku mazaje dakaiina wayanda zasu ji kaina kuma suji kanku.
Yau Ga mahaifiyata nan ita shaida ce duniya wa lahira".na neman wa duka yayana mazaje nagari batare da taimakon kowa ba
,"..toh wallahy, na rantse muku da Allahn daya halicceni, na rantse da kabarin baba na,
Duk wacce tayi asarar auranta duniya da lahira ban yafe mata ba.
Ke murja ke ruqayyya,atake first nd send born dinsa suka kalle sa jikinsu a matukar sanyaye
,Wani irin bushe fuskan sa yyi yace naji wasu kananan magangun banza da wofi na tasowa daga wajenku,wai bakwa jin dadin zama da majazenku ko?,toh wallhy inkuka biye ma uwayen ku suka zuga ku aka sake ku kuka fito daga gidan aurenku toh fa saidai ku koma zama akarkashin su can su ciyardaku su shayardaku
Dan Daga ranar da aka sake ku kusa aranku..."babuni babu ku"..Ni kuma ban tsine muku ba, amma kusani har abada na Haramce ku da taka kafafunku a kofar gidana.
Sabida haka duk wacce ta kashe aurenta sai ta san Inda dare ya mata amma ba a gidana ba.
Ya juyo a fusace ya kalle jadwa suhan da rufaida..
Yace Fatan maganata ya shiga kunnen kowacce acikin ku?
Atare Suka amsa shi da eh suna masu gyada kansu cikin gaggawa.
Yace Allah ne kawai zai sanya albarka acikin rayuwarku idan yaga manufarku na zaman aure saima ya sanya muku zuria dayyaba,yana kaiwa nan yace toh
"Ai saiku tashi ku kai ita suhan din yanzun..
Ba musu adda murja da adda rukayya da adda Jadwa suka miqe cikin shirinsu"
..anan kuma Hjya mama ta miqe da kyar cikin sauri tayi fafur a hanya Tace sam bazasu wuce ba...A rikice Tace kai bukar,da sauri ya shareta yyy gaba kamar ma baiji ta ba amma bata fasa ba,Nace ka dakata min,sai yaja dai ya tsaya can gefe batare dayama juyo danya kalle tan ba, "kamar ya Zakace akaita gidan miji Mu bamuyi namu maganan ba?kai waye da zaka wanice akaita?akan mubamu da abunda zamuce ma yarinyar kenan?Wani irin daure fuskar sa yy tamau,da kamar ma bazai amsaba saiya juyo ya haura mata da wa'azi, yana cewa ba a jinkirta aure da mutuwa dan haka kawai akai suhane gidan mijinta duk wanda zai mata nasiha saiya bita can yayi mata,Hajiy ta Inda take shiga bata nan take fita ba amma ko ajikinsa..baima san anayi ba..InTa fada shima saiya fada,dama can dabiar sa ne girman kai,yafiso in yayi nasiha kar wanima yace zaiyi,har yaushe akayi ilimin addini da za a nuna masa? Shi ko kunyar idon yayan cikinsa sa bayaji bare sauran nunawa yake kamar basu da haqqin yin magana bayan nashi,yanaji hjya tasa mai ihu tana cewa baiya saka adalci a al'amarun sa saidai shi ganin rakin ta yake a matsayin shirme irin na tsoffi da tsatsube tsatsube irin na mata,gaba daya saida suka tada hanklin kowa a dakin,ga mutane awaje makil ana jiran fitowar amarya
Miqewar da rufaida tayi zata fice ne ya jawo hanklinsa kanta,da alaman shirin fita take yi dake surutun sun ya soma haura mata kai Wani irin ciwo kantan ya soma mata bazata,cikin sanyin jiki ta miqe ta jikin ummanta kamar wanda zata rabe ta gefenta ta wuce,Wani wuff yaa malam yaa cakumo ta kamar zai figeta
,"shin ina zakije?idanun ta atake suka firfito a mugun tsorace ta dago kanta sama zata amsashi baima jira tace cass ba sai tssssss taji ya watsa mata Wani makohon mari akan fiskarta sanda ta sabule daga hannunn shi ta kife kasa a gigice
"...duka wayanda suka taso zasuzo kanta a tsawace yay kara cikin dakatar dasu,,Cikin tsawa da fada yace "Shasha sha kawai..Allah wadar naka ya lalace.
Ke wai Harni ne zaki nemi ki kunyartar?babu yarinyar danace zan mata aure ta gudu tun safe ba aganta ba waidon bata son aure,To kiji da kyau na riga dana Amshi sadakin Alaji BATURE akanki GOBE asabar da karfe 9 na safe daurin AUREN Ku
.
Hannu ya turmusa acikin aljihun sa ya fiddo wasu makudan kudi ya watso su kam fuskarta yabi ya kwashe ya maidasu aljihunsa A lokacin mutuwa ne kawai yaki zuwa na rufaida amma takai kololowa wajen zaucewa da baqin ciki
"Inkin ga dama saiki kashe kanki kafin goben..Auren ki kamar anyi angama,koda mutuwa kkyi
Bi'izinillah sai an daura auren nan da gawarki,domin in nuna miki cewa nine mai nasara akanki,nine gaba dake,sabida nine ubanki bake kika haifeni ba..ni ne nan mai iko da rayuwarki.
Har ke kin isa ince zanmiki aure ki bijire min?toh ga sakamakon silar taurin kainki nafasa jiran zagowar sati gobe gobe zaki barmin gidana
Makarnatar na hana,Na kuma haramta duk wata hidiman biki domin ki,daga an daura aurenki gobe zaki bi mijinki duk wanda ya daga kafarsa wai zai kaiki gidan miji Allah ya isa..Allah ya rufamin asiri babu wata yar iskan yarinyar da zata tona min
.....Wani irin birgima akasa rufaida takeyi tana kuka sanda tayi fayau tana rokon sa gafara amma ina baiya najin ta dan dabiar sa ne ya hawra can sama yana bunkasa musamman idan ana bashi haquri
Anan ya hada harda sauran borin fushinsa ya borance ya kore masu fidda amarya waje yana cewa rufaida tayi ma yan uwantan duka kallon karshe dan daga yau bazata kara ganinsu ba.
Kuka kawai rufaida take yi kanta akan kafar kakarsu da ke matse kwalla itama tana ta kwararo bambami duka abanza Umma kuwa tunda ta kife kanta akasa tana hawaye bata kara dagowa ba danji take kamar kirjinta zai fashe yy aman wuta tsaban radadi.
,"hjy jasmine da yarta faressa su suka jagorance murja ruqayya da jadwa sukayi waje da amarya suhan a cikin yaran kaf babu wanda xuciyarta baiya cike da jimamin tuna mumumunan kalaman mahaifin su akansu saukin abun daya dake su sun masa biyayya
Hasalima duka ganin laifin rufaidar sukeyi datazo da wannan sabon salo na neman wa kanta yancin yin karatu wanda aganin su hakan bata makai lokacine da neman karawa wakai takaici,dan tun bayauba kowa yasan halin mahaifinsu Yaaa malam, da rikakken ra'ayinsa na babu mai saka shi bare kuma mai kuma hanashi.
Surayyahms contact 08060712446
pleaseeeee coments na rokeku
Kwanan nan zan gama exams in sameku a Fafata dani,lets spark our burning love fanmily.
Part 1 IS FREE,TUKUICI NE GAREKU MASOYA NA U CAN READ IT HAR ZUWA INDA ZAMU TSAYA,SAIDAI CIGABAN SHI NA KUDI NE,PLS SHOW SOME LOVE AND SUBCRIBE
the ACCESS FEE IS 300 NAIRA ONLY
VIA 0152983148
MOH'D SULE SURAYYA GTB.
OR katin MTN vtu tran via 08060712446
Screenshot ur evidence to SURAYYAHMS 08060712446
OR MAMAN MUBENA
08036651119.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top