passage18

*🍒🍒SAMU YAFI IYAWA🍒🍒*


Passage 18.

Dont forget we r stiil counting down free words💋


Nikam tunda da seif yayi bacci, nake kwance ina tuna abubuwan da su anty hanifa da mumy ke gaya min.."

Fargaba ne tam araina amma abu ne wanda ko ni nan na san ya zama min dole na aikata su ,
Gashi tun da anty hanifa ta tafi Mumy salamtu ta yi min fada akan jajircewa da hakuri in har mallakan mijin na ke nema..

Ta kuma gaya min ba gamsar da miji ba shi kadai bane hanyar mallaka ah 'a , mumy tace, shi Aure da nake gani ya na da pillars kwarara wanda suke rike da shi,masu nauyin su daga ciki shine hakuri, shi sex din, da kuma tattali....but most of all namiji yafi daukar mace mai biyayya da respect a zuciyan sa
saboda ita ce kadai mai ikon mallake sa har abada Ba maganin boka ko sex ba..

Tace min "Da jikin naki mai dadin amma idan baki da da'a, da tarbiya watan wata rana zaki gane ke ba komai bane a wajen sa sai engine kashe wutar gaban sa..

Sannan tace"shi kazan ta yana kashe ma namiji karfin shawa'ar sa kamar yadda qamshi da tsafta ke daga wa, inda chan kina ganin tsaban dadin jikiin ki bazai bari ya daga miki murya ba,to kijira a kwana a tashi kazantar ki zai kore sa karfi da yaji kuwa zaki ga yadda zai guje miki..
abu mafi muni da kazanta shine "tsana" yake cusa ma mutum aransa game da ke sai miji yana jin ya tsane ki altho wasu bazai hana su kwana da ke din ba..

Amma Ranar da ya cika sai dai kawai kiga miji m
Na hantarar ki yana bata rai dake haka kawai baya ma son ki zo inda yake bare companyn ki a tare da shi...

Mumy tace
Shi kuma biyayya kuma ba off head ake yin sa ba garan gatsau,..dole mace ta zama mai nazari da basira da kuma lissafi wajen sa kafar ta  ..

Hakan kuma baiya samuwa sai kin kwantar da hankalin ki kin nitsu kin tara hankalin ki waje daya..

Anan ma ta kawo min magana mai muhimmnci"tace shi nitsuwa baya samun matar da bata ibada ko da ace sallah akan kari ne, ko macen da ta dauki addu'a ma kanta da iyalan Ta a banza ,

sai kiga a yi wata agidan mace babu kira'a ko karatun Qur'ani,toh idan ma ace har baki samu ilimin addini ko islamiya agidan ku ba sai ki yi kokari ki shiga agidan miji ko shi dakan sa in ya samu lokaci yana koyar miki,

nitsuwa ma dan adam baiya samuwa a zuciya sai ya cika addinin sa dam dam yadda ya kamata...ta kuma ce min kar ma mance da dan sallahr daren nan da azumin lada kai har ma sadaqa da taimakon yan uwa da dangi a duk lokacin da na samu wadata da sarari....

Tace"Biyayya wa namiji cikin fasaha ake sa shi,bawai zaki fito karara kina nuna masa eh ena maka biyayya ba ne ki kyale sa shi da kansa ya gane haka,don wasu matan ma idan hakurin su ya gaza sai suyii gori akan ai ina maka biyayya baka gani, Hakan ya nuna ba don Allah kike yi ba Babu kyutatawar niyyya akan neman aljannar ki..

A matsayin ki na mace ki sabar ma kanki salo na masa godiya da sama miki abinci da muhalli da sutura abu ne mai girma,

sannan ki tuna fa mijin ki shima yana da na shi damuwar da kuma farin cikin sai ki dinga tunawa da shi a duk lokacin da zaki yanke wani hukunci.

idan ya nuna bacin rai akan dan wani qaramin abu da kikayi masa ko ma aka masa a waje sai ki bashi hakuri bakiyi musu da shi ko kiyi masa fada ba ,

Kar kuma daga shigowar sa ko zama baiyi ba ki soma kawo masa matsaloli  da complains atleast ki dan barshi ya nitsu kafin ki kawo maganar ki zai fi saurara,

namiji baya son mace kamar maza misali ko da tambayar sa zaki yi ajere ajere muddin kinsa shi cikin fahima zaki samu biyan bukata a saukake ba sai da maganin mallaka  ba ko sex.

Duk abunda mummy ta lisaafo min kenan atakaice Kuma tayi min gargadi da tuni nayi shi don Allah ba don komai acewar ta ba insha Allah zan ci riba..

Ni yanzu Tunani na shine ,yadda zan koma gidan jabir, haka kawai nake jin wani iri araina, gani nake kamar bazan iya ba Duk da hakan daga zuciya ta ce
Amma karfin gwiwa  kam na samu..
Im all groomed up har dilka da sauran gyaran jiki ina samu, na murmure nayi bul bul fata na na sheki adan kankanin lokaci na haska..

Gashi mumy bata mancewa wajen bani abinci da abubuwan da suka tanada min na gyaran hq na sabida haihuwan da nayi..

Tuni ta sa aka rubuce min suratul yusuf, suratul maryam da suratll rahma aka wanke min su da ruwan kankana ta sa nayi bisamillahh na shanye su tassss..wannnan hadin tun ina budurwa aka mana sabida shikan sa ma kariya ne daga wulaknci da juya baya daga da namiji ko da kuwa asiri akai masa bazai taba mancewa da ke ba.

Shi mumy take wa lakanin mallaka.

Sannan ta sa aka dafo min kazar gida da nonon raqumi aka yi mata barbaden ridi shima na cinye..
Tace to ko wannnan ma ya isa ya iya min da duk wani dawainiyar miji n amma duk da haka ta hada ni da wasu tarkacen.

Ajiyan zuciya nayi na jawo ledojin da ta zuba min  hadin dakakken
Garin furen zogale,zanjabil habba da garin raihan tace na dinga deban karamin cokali ina hadawa da zuma safe da yamma  ina sha..sai  man tafarnuwa
Dear musk
auduga
Tace ki hada deer musk cikin cokalin shayi man tafarnuwa cokali biyu ki gauraya kisa auduga ki dangwala kiyi inserting a hq awa uku ki cire amma tace once in a while ba kullum ba
Sai  kankana
Zuma
Madara
Kinsan kankana uwar ruwa ce sai ki matse ruwan ta ki tace ki juye madarar ruwa a ciki kisa zuma ckl biyu
sai
aya
Dabino
Gyadar mata
Gyada mei gishiri
Minannas
Sugar
Kanunfari
Yougurt ko nono
Ki hadasu ki daka ki rika diban cokali biyu kinasha da yugurt ko nono
saiwar kankana
Saiwar zogale
Kanunfari
Mazarkwaila
Tace Ki sami saiwowin ki tafasa ki tace ki maida ruwan inya dahu ki sauke kisha sau uku a rana.
Sai  ruwan rake
Da Ruwan kankana
Tace Ki matse ki rika sha sau uku a rana yadda kikasha kinajin dadi hka shima zai ji ki
Sai kuma aya
dabino
Mazarkwaila
Farin dankalin hausa
gyada
Tace Ki gyara dankalin ki ki yanka ki shanya ya bushe ki zuba kayan kamshi ki dakashi ki daka dabino da mazarkwaila ki soya gyadar ki sama sama ki turmushe ta ki daka su duk ki daka ayanki ki hadasu guri daya ki rikasha da madara peak
Sai hadin Gwanda
Kankana
Zogale
Abarba
Citta
lemun tsami
Tace Ki hada ki markada ki tace kisa lemun tsami kadan da zuma kisha
Sai na kanun fari
Zuma
Garin ridi
Nonon shanu mara tsami
Ki dafa kanunfari ya dahu kisami garin ridi da nono ki hada ki gauraya kisa a frigde ki sha idan yayi sanyi ki maimaita duk sati ba ruwanki da rashin ruwa kuma
Sai ki sami minannas kadan da kanunfari ki dakasu kidora ruwa a wuta kisa citta da hadin ki tafasa kisa sugar da lipton tace kusha keda shi.
gyadar mata
Dan bashanana
Yayan kankana
Yayan zogale
Minannas
Farar biya rana
Idon zakara
Asuwakin mata
Mazarkwaila
kidakasu luguf kina diba kinasha da madara peak
Sai zogale
Zuma
nonon shanu
Ki shanya zogale ba a rana ba idanya bushe ki daka ki tankade ki debi ckl daya ki zuba nono da zuma kisha

lemon zaki
Madara peak
Zuma
Ki matse ruwan lemun kizuba madarar da suma kisa a fridge yayi sanyi kii sha

kwakwa
dabino
Madara
Ki markada kwakwa da dabino ki zuba madara peak ta ruwa kirika sha
Duk wayannan na rubuce su a dan joter wasu na na haddace su kawai akaina..

Duk Su mumy da anty hanifa sun gama min komai su mummy na ba su ma sani ba..

Ranar da jabir ya soma zuwa gidan namu, a lokacin mumy salamatu ta soma nunawa karara abunda ke damun ta arai,

sabida daga ganin sa sai
mumy na ta soma declaring kawai tunda ya zo na shirya na bi shi ba sauran jira,

Tace ai kwana kadan ya rage nagama hutun naje kawai na kara sa agaban sa,

ranar da kyar na sha sai da kowa ya sa baki akan abari na karasa sati guda na gama kimtsawa

Shikuwa jabir Tun daga ranar ya samu saran zuwa gidan mu sao iban rawar kafa yake da zumudi musamman ma da ya ga yanzu na sauya gaba daya nayi kyau na kara cikowa har ma fiye da yadda ya auro ni ina budurwa,

sai dai yayi yayi na saurare shi muyi magana amma sam sai ma dauke masa wuta idan ya zo haka zai kara ci zaman sa shi da dan sa har ya kama hanya ya tafi ban leko ba,

wani bin ma bana zuwa kai masa seif din sai da na ba ma mummy sukara ta chan har ya kara da wuta..

Ita kam mumy na kullum a fushi take dani a duk lokacin da ya fice sai ta ce Allah sarki, yaron nan sai bin samha yake mutum da matar sa amma sai a ajiye masa ita ni sam wannnan abun baiyi ba

sai Ana saura kwana biyu tal mu dawo gida kano da jabir, kafi nan ma har ma yaje kanon sau biyu a kwanakin ya dawo

Da daddare ya zo gidan mu ya aika na same shi a palour.. Amma banzo ba sai da na tabbata yana dab da tafiya don lokaci ya tafi sosai kafin na tashi

Daurewa nayi as usual,amma duk bana jin dadi a raina haka kawai in na tuno da rayuwar da nayi a gidan sa ai naji bana jin  zan iya komai

Na taho na zauna sannan na dube shi a ladabce na gaishe sa..shiru yayi yana kallo na na dan lokaci sannna yayi gyaran murya
Bai wani bata lokaci ba Yace samha pls lets talk about this mana,wai meya sa kike gudu na ne?, yanzu ma har baki daga waya na in na zo gidan nan kuma bazaki zo mu gaisa ba?

Ina shiru ban ce komai ba ,,yace "tun zuwa na nake gaya miki ina so muyi magana da ke kafin mu kuma kano ko?
Still ina shiru, abun ya dada damun sa ya kawo hannu zai taba ni ma dan kauce
Na fashe da kuka a hankali "nace ni kam gaskiya bazan koma ba ai naga babu wani abun da zamu ce ma.

a take murya na ya hau rawa na soma jan masa shessheka a hankali mai shiga zuciya....ni kaina bansan meyasa na kawo wannan salon ba.

Ba shiri naga ya saukake murya abun bai masa ba ma ya sauko kusa da inda nake "yace samha meyasa bazaki koma ba?

Nayi shiru na kuma matsawa nisa da shi ,

a dame yace Ko dan  abubuwan da suka faru ne samha,?ban amsa ba a yce "pls listen to me shiyasa ma nake so nayi miki maganan dake dan Allah ki yi hakuri ki yafe min samha, samha im sorry i will do anything to make you happy wallhy nasna na dau alhakin ki,

Ya dada langwasa murya " yana duba ni kalar tausayi ..."Nasan kinyi hakuri da ni duk dam baki son ki nuna min hakan anymore, but im assuring you na gyara halaye na, just give a chance kinji?

Na mike tsaye  abuna .."nace ni dai wallhy bazan iya ba,dan Allah ka taimaka min  kayi tafiyar ka ni gaskiya anan zan zauna bana son chan din kayi zamar ka da matar ka zan zauna anan yafi min dadi da kwanciyar hankali...

Zai yi magana na dakatar da shi cikin dan karamin kuka nace dan Allah fa nace jabir, shin bazaka iya min wannna alfarman bane?
Ai ba cewa nayi ka sake ni nace ni bazan je kano gidan ka bane,ni a gidan mu zan zauna ...

Hankalin sa sosai ya tashi, ya rasa akan meye guda nake bori  sabida naki na fito fili na baje maganam dake zuciyan mu duka ..
Ga hawaye sharbe sarbe a fuskata ina jan shesaheka...

Jin alaman shigowar abba site din ya sa dan dole ya yi shiru ya kasa fadan maganan da zai gaya min...ya matso daff da ni kalar tausayi, yace kinga dare yayi min anan sosai ni zan tafi, sai ya ce to sai na zo goben ko?

samha dan Allah ki cire wannan maganan a ranki wallhy nayi nadaman abunda nayi miki ki yafe min kinji?

Na daure fuska na yam na tsime kamar ba da ni yake ba,kuma bance komai ba, har ya sulale ya fice..

Share hawaye na nayi na kama hanya na koma daki ko ajiki na...

Don Sosai na kudira araina bazan taba komawa hannun sa cikin sauki ba sai na chaguda masa tunani, duk dama nasan dole ne zan koma tare da jabir ko naki ko naso...






SURAYYAHMS

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top