passage17countdown

*🍒🍒SAMU YAFI IYAWA🍒🍒*


Passage 17



Washe gari da safe,abun farin ciki ne ya same  zuwairah, ganin kiran karime ya sa ta bulbukan farin ciki a kan fuskan ta sai barin jiki take tun kafin ta kai kunne..

Nan ta dauka tace Alhamdullh, karime?
Dan shiru ne ya biyo baya kafin karimen ta amsa

Sai dai taji wani dum da yanayin  karimen"
zuwairah kina ina ne?

Tace karime lpya kuwa gani nan a gida!

..tace to ina zuwa daga nan ta katse wayar..

Kasa zama zuwairah tayi
Duk dama Yanzun ta tashi a bacci so ko sallah bata yi bare wanka ko brush tana tsaye tana zirga zirgan jiran shigowar karime...

After 25minutes aka buga kofa da gudu ta taho falour lakatar lakatr ta bude kofa
da tsananin shauki suke kallon juna, amma sai suka kasa rungume juna sabida yanayin da kowacce ta sauya.

karime na mamakin yadda gidan jabir ya dawo datti makamalan bakamar yadda ta saba zuwa ta gani ba, ita kuma zuwairah na mamakin ganin yadda karimen ta ta dada mokadewa ta dawo kamar mai tallen sigari da goro..

Kawata lpya kuwa ta jawo hannun ta ciki,

Kafime tace"Ina masu gidan?
Ina nufin ke kadai ne haka.?.

Eh ni kadai ne karime har kin mance samha ta je wankan gida?mmmmm daga ina haka
Ai nayi ta neman layin ki kamar nayi hauka baya shiga..

" ajiyan zuciya tayi Cikin jimami tace bari kawai ke dai ki bani abinci na ci,

Tace tabbb kinsan wannan mai wuya ne anan kam gaskiya nifa tunda matar sa ta je wankan gida ban sake daura komai ba don bazan kashe kaina ba..

Karime dai na kan kallon ko ina tace ni ki  san nayi  yunwa nake ji...
Tace to in kin iya sai muje ai
Ba musu suka shige kitchen nan ma dauriya kawai tayi ta dafa abincin duk dama halin su daya amma sosai take shan mamakin kazantar zuwairah shinkafa da mai da yaji suka daura daga nan ta zauna suka ci..

Karime Bata samu daman magana ba sai da taji dumi aciikin ta hawaye ne suka soma saukowa..

Hankalin zuwairah ya tashi sosai don dama tayi ta tambayar ta meke faruwa bata ce komi ba

gashi tunda ta zauna zuwairah ta ke sharo mata abunda ya wakana tass tasss ba ragi

Yanzu ne tace hmmmm zuwairah kenan" kina cin duniyar ki ashe har yanzu,uhm uhm ke nikam naga duniya  lallai rayuwan nan bata da tabbas

A tsorace tace wai meya faru ne karime..

Bata kula ba tace
Wato ke har yanzu baki dena kazantar nan naki bane zuwairah?

Ta dan murguda baki tace kin fara kenan ko karime..tace am seriious na dauka ko danki samu gida zaki dan rage wasu abun ki waye amma jibi muhallin ki kamar gidan mahaukaciya anan a gidan nan ba inda yakai dakin ki wari fa..

A fusace zuwairah tace ua isa, ta bi ta daure fuska..wai meye haka daga zuwa zaki fara soka min maganan ni bana son iskan ci msww...

Karime ta dan fashe da dariyar takaici mai ban mamaki tace ai bani da lokaci ne zuwairah
Gwara na soma gaya miki abunda nake tafe da shi tun kafin lokaci ya kure mun..

Ki sauya halin ki zuwairah a duk dama ke kadai ce agidan kin kasa yin komai sai bin gado?,to wallhy wannan rayuwar taki ba mai bullewa bane,

Kinsan me ya faru dani kuwa? ...anan ta bata labarin bakin hakin data shiga a hannun mijin ta malamin zaure...
Shi babu wani maganin ko kisisnan mata da bai sani ba don har shi dakan sa yake bda taimako....sannan ya kafe ta akan kishiyoyi wanda suka koya mata da maganin matan ma sai ta rike Allah da tarbiyan ta kafim tayi zaman aure

..sosai suka wajiga ta suka nuna mata halayen da ko a mafarki bata son asake nuna mata irin su
Wannan ma bai dame ta ba, yanzu ance bazata iya daukar ciki ba sabida mahaifan ta ya kamo da ciwo sanadiyar dure duren magani..

Karime Ta dan ware kafan ta kadan wani guntsurarren wari ne ya taso wanda ya gautsina musu ciki baki dayan su..

Tuni zuwairah ta mike tana kakarin amai..
Gaban karime kamar famin shadda har wani baki baki yayi yana fidda diwa mai shegen wari...

Amma da shike ta saduda da sha tana kuma karban magani ya zamo sa sai ta bude ake jin gumi..

Tuni hankalin zuwairah ya tashi sai ma ta kasa zama kusa da karime baki na bari tace
kan uban chan in gindi na ya dawo haka ai na mutu..

To ke Wani magani kikayi ta sha haka karime?.tace zuwairah ba wani maganin da na sha wanda baki sha ba kema nazo nan ne na sanar dake tun wuri kije aduba lpyar ki kafin ki naki ya dagargaje irin nawa..

Nayi ta dura abu ba kakkauwatawa Gashi ni ban samu na tara komai ba ga miji ya kora ni sabida dama amfani na kenan sex..

"Tabbbb kamar ya amfanin ki kenan?
Amma lokacin da yake jin dadin ki ai bai kawo amfanin ki bakenan ko..

Tace ki bar maganan na nikam zuwairah ni na san me nake ciki..

Ni dai Zuwairah na rike ki da girman Allah ki sauya rayuwar ki kafin lokacin ya kure miki

Zuwairah "Tace tabbbbbb......

Akan dan wannan abun,?toh Nikam banga ta wani sauyawa ba karime kknajin abinda na gaya miki jabir fa ya lalace yanzu wulakanci yake min gaskiya sai na saita shi kafin koma miye ya biyo baya  ....

A fusace karime ta dakatar da ita zashe kuwa kin da aiki ...wai To ya baza'a miki waknci ba zuwairah  ki dube ki fa hammata duk wari baki kamar shadda,
Atlest ki bar wannan shegen son jikin naki mana ki tsaftace kanki

Wuf ta mike tsaye"Ah"a dakata ba wanin nan , da chan ma haka nake amma bai ta shi mun tsiwa ba sai yanzu Kawai in zaki taimaka min ki taimaka min, dama tunda na rasa maganin da kike kawo mun na soma ganin hau hau a al'amura na...

"Hmmmm zuwairah kenan...
to bari kiji gwara ma ki sake ranki ki ajiye maganan magani ki fara gyara halayen ki tukuna dama chan bangaya miki bane,..wallhy wata mata ce ta kaini wajen wani mutum shima wai bada maganin yake..
Shine na siya miki maganin da kuke using da wannan jinin al'adan naki daga baya nake jin ashe asiri yaje yumi da aljanu'....

Wai muddin miji ya hada ido dake bazai iya tabuka komai ba sai yanda kika ga daman yi da shi.

Ke banza kin dauka ko maganin mata ne zallah ko?toh Sannu mai gindin zinare
Wallhy ki shiga hankalin ki zai iya kasancewa jabir yana jin dadin kin amma ki sani mallakar sa da ki kayi fa asiri ne..kuma inaga karyewa yayi,

Hannu zuwairah ta daura akai ta budu ido tace na shiga uku zuwairah asiri ?
Tace kwarai kuwa..

Yanzu kuma gaskiya bazan sake tsoka kai na a wannan halin ma don naji ajiki na nagaji da wannan harkan..

Ta mike tsaye tace shawara ta gareki ki sauya halayen ki

Ki sauya ko dan tsaftan nan kina yi sabida kija mutuncin ki a idon sa  haba zuwairah??..wallhy idan jabir ya gama gano siffar ki fa zaki ci ubanki anan gidan..dakan ki zaki kwashe kayan ki bashi waje ah toh..

Tana shiru chan ta ce "A ganin ki ba?
Ni nasan jabir
Wallhy kawai wani abun ke ruda sa kuma zai dawo dai dai..

Kema ki tsaya kiga na sami kudin.
Kinga sauki ma ya samo kawai bani nunber malamin zanje ya bani tunda ke kin saduda
gaskiya bazan iya komai ba..don ban iya ba..

Murmushi kawai karime tayi ta buga shewa tace iska zai wahakar da mai kayan kara..
Anan ta dauko abu ta rubuce mata nunber malam mai mallaka..

Tace Allah ya baki sa'a zuwairah ni na tafi,.

Ko sai anjima bata fada ba ta soma zagin ta..
munafuka kawai don nata gindin ya rube duniya ya juya mata baya tana so ta durgushe nawa mu dawo daya..

Jabir kam kamar na  mallake sa daa asiri ko babu asiiri ba abunda ya dame ni..

Daga nan ta koma daki ta shiga nazari
Kawai sai ta tashi ta shiga kimtsa wajen ta shirya ko ina da kyar da bala'i kamar zata yi amai awasu abubuwan ma dan dole ta kyakem.

Itama tayi wanka ta dan tsafatace wajen...

Ta zauna rigijin tace to yau na sauya Ai zanga karyan nasa,in ma wasu ke juya masa kwakwalwa akai na duk zan gani...

Cikin ranta ta na kawo tunanin ko abokai ne suke zuga shi, ta dan girgiza kai ta kuma cewa tabb
Toh walllhy ba a haka dani uwar mutum zanci idan na na sami kudin nan kaf sai na raba shi da yan iskan nan shegu masu dogon baki..

Shikam Sai 9.30 ya dawo already ya ci abincin sa awaje ya kammala komai yana tahowa dakin sa ya wuce straight ko noticing din gyaran nata bai yi ba,duk dama banbancin kadan ne cos dama ba iyawan tayi ba

Tana jin motsin sa ta fito, ta shigo dakin sa sai dai bata iya da'a ba, a tsaye ta tsaya ringim a kansa tace har ka dawo ne jabir..

Yayi shiru kamar baiji ba ... Wani tunanin ta yi aranta a take sai
Ta tsuguna,tace" desire magana fa nake da kai

Ya dago fuskan sa a dan daure yace tashi kije ki jira ni a dakin ki ina zuwa...

Ganin ya dada tamke fuska ya sa ta tashi ta fita...

Bayan kamar minti 30 ya shigo ya same ta a dakin ba laifi babu wani kaya a kasa ko a cunkushe..

Bai wani bata lokaci ba  ya afka mata suka samu gamsuwar junan su...

Ba yadda bata yi da shi ya amsa ta ba amma gum ya kame bakin sa har ya sauka akan ta nishi kawai yake saukewa

Bawai baya jin ta bane har yanzun kawai rashin da'ar ta yake ganin bazai dauka ba, Don kuwa tunda tayi barin ciki jinin ya wuce mata komai ya since daga asirin mallakan da ta masa shiyasa ma da yayi tafiyan nan kwana biyu sai yaji ya dawo cikin hankalin sa wasu tunanin anan suke shigo masa

Washe gari data ga ba samun kansa zatayi ba sai ta tayi nasha nasha ta na kwakwalo amai tana nishi...

She tot ko na dan lokaci zai yaba kokarin datayi ta kimtsa kanta amma baiyi hakan ba kwata kwata sai taga bata da wani amfani yanzu in ba akan gadon sa ba..

Sai data ji motsin sa daf falo sai ta kara kakarin tana wyyo wayyo Allah
Anan ne a shigo ya same ta tayi nasoo akasa tana kifi kifi da ido..

Daga tsaye ya dube ta fuska ba yabo ba fallasa yace lpya? Dama baki da lpya ne zuwairah?

Cikin dan karamin nishi da sanyin jiki tace , ai baka damu ba yanzu ina kuwa zaka san halin da nake ciki..

Zai yi magana ta dan daddafe ta mike sigar kuka da tsananin jin takaicin abun
...tace jabir ka fada min gaskiya wa yake shiga tsakani na da kai, ? Ni ka fada min sabida abubuwan naka sun wuce misali in so na me bakayi ka sawwaka min mana, yace stop it, ke ma ai kinsan abunda kike yi,  tace "eh na sani
kace kazanta amma na dau gyara yau still baka canza  ba, hakan yana nufin ba shi bane akwai munfrcin da ake kulla min a wajen ka kuma Allah ya isa tsakani na da munafukai duk wanda yake so ya raba ni da kai ba zai ci nasara ba...

Tasan zai amsa sai tayi saurin zubewa kasa ta shiga kakalo amai da baya ma fitowa sai ruwan yawu datake fetsowa..

Ya dan duka ya riko ta yace wai meke damun ki ne?
Toh dauko mayafin ki kije asibiti...

Batayi musu ba ta tashi ta kimtsa ya dau ki 5k ya bata sannan ta fice..

Shima office yaje ya cigaba da abubuwan da ke gaban sa,.

Yana tafiya ta dawo,
Ta cigaba da kulle kullen ta

Chan da yamma ya tashi amma bai kuma dawowa ba ya je chan wajen sabon ginin sa  dayake kerawa babu wanda ya sani daga matan nasa..

Sai dare ya sake dawo wa anan tazo ta ke kawo masa maganan tayi barin ciki,alhalin karya take duk shirin da ta hada ne don ta sami kudi

Tace Kuma ina bukatan kudin wanke ciki kamar yadda doc ya fada...

Baiyi musu ba ya jimanta ya kuma tambaye ta amount...nan farin ciki ya balbale ta a ranta , jin zata sami kudin da zata koma wajen malam mai mallaka..budar bakin ta tace, duka duka dai dubu 150k ne.

Yace what? A wani asibiti kenan..

Toh ni bani da shi,kai kima bari kawai ni zan kaiki wani asibiti gobe aikin su nada kyau...

Nan take taji ranta ya baci, dama daurewa take yi taga ko zata karbe ta wannan salon amma sosai take ganin kamar jabir zai raina mata hankali...

Tuni ta shigo da tsegeran cin ta,
Tace akan me?yanzu kudin jinyan nawa ne zaka ce babu Kai dai kace bazaka bani ba kawai..

Yace eh,bazan bayar ba.. wateva, kije ki jira goben ni bani da150k,..haba da Allah ai ko operation albarka kar ki maida ni shasha sha..

Tana shiru can ta kuma a shsance murya tace,jabir dan Allah ni ka bani kawai zanyi komai da kai na..!
Dama so nake idan nayi wankin cikin sai na siya maganin mata, kasan in ban kula da nan ba bazamu ji dadi ba..

Yace,nace banda shi..kije kawai gobe zamu je asibiti... Ya daure fuska

Tsaki ta ja tana kallon sa da mugayen ido daga bisani ta tabe baki tayi waje...

A hakan ma ko bacci bata iya yi ba ,gashi tunda ta gaya ta yi bari zai bai zo dakin ta yau ba..

Hakan ya sa ta zauna tayi dogon tunani taga ba abunda ya rage mata illah ta debi gudun ko da ta sata ne.

Da asubah tana jin  ya wuce masallaci ta shiga room dinsa.

Straight inda yake ajiye kudi taje sai dai sholl babu ko sisi sai ma transaction slip na kudi dayawa anan ya zuba wasu yayi using wasu baiyi ba

Ba lokacin tsayawa karantawa don haka kawai sai ta  kawo tunanin ko ya daina ajiyewa kudi ne a gida sai a banki?

Nan ta jawo wayar sa ta bude messges ta soma dubawa
Anan ne ta ke sanin ma na haihu, kuma take ganin tex mesges dinsa da kudaden da ya tura min dan kwanaki Akalla dani da yaro na munci almost 360k daga wajen sa..

"Fushi ya sa ta jefar da wayar akan gado tayi waje..anan ma zirga zirga kawai take ji da wani sabon shaukin jin dole ne ma ta mallake jabir ko da tsiya ne..

Bayan ya dawo daya gama kimtsawa ya buga mata kofa akan tafi zai kaita asibiti,

Anan ta soma masa borin da bai da kai baida wutsiya cewar ta ai yanzu ta gane mai shiga tsakanin su,ai tunda ta zo gidan sa bai taba bata kudin da yakai rabin wanda yake turamin ba..
Acewar ta baida adalci..

Ire iren abubuwan da yake dada sa shi yaji tafita masa akai kenan
..amma sam yau din baida niyyar masifa sai ya kyale ta anan ya fice...

A office ne da yayi bako daga lagos wani baban abokin sa suleiman..
Tun secdnry schl suke tare,kuma sun san juna sosai sai dai hardly suke sharing matsalolin su musamman na gida..

Dama umar da usman ke yawan magana akan nasu har suke jan shi shima ya tofa,...

Yau sai ya sha mamakin tambayar da Suleiman din ya masa yace masa ,"jabir anya kuwa lpyar ka kuwa?tun dazu nake ganin kana katse wayar matar ka i hope dai ba wani abu bane kasan mata fa sai da hakuri zama da su...

Abun zuwairah na mugun damun sa amma ya kasa sanin ta ina zaiyi bayani sai yace ma suleiman kawai 'ya shiga confusion ne matar sa na gida tana ganin kamar baiya adalci amma a ganin sa yafi rashin adalci ma uwar gidan sa sai dai ita bata fada masa hakan shiyasa ma yanzu kansa ya kulle..

Suleiman yace" indai haka ne kai kafi kowa sanin yadda zaka warware matsalan ka ba sai an baka shawara ba..
Wanda kasan kana mata acikin su ka daure ka nemi gafarar ta ku sasan ta ita kuma wanda kasan baka mata sai ka fahimtar da ita sosai ta gane hakan...

U have to be a man duk abun daga zuciya ne ka nitsu..

Yace, toh suleimam bakomai insha Allah zan yi tunani..

He just didnt think that har zai sami shawara mai inganci batare da fadan komai in details ba..
Har suka rabu da suleiman yana nazarin yadda zai dena jin nauyin samha ya budi baki ayi ta ta kare..

Yasan zuwairah kam lokacin sa take bukata ya qudira sosai aransa zai nuna mata shi miji ne wajen ta ba abun wasa ba....

Haka ya dena kula su kwana biyu bayi shiga harkan ko daya daga cikin su ..ya dai nemi nitsuwa makan sa yana tunanin yadda zai tallafi familyn sa har ya fara rayuwa mai inganci

ya san saura sati biyu zuwa uku na dawo daga wankan gida so he have to move fast..

Duk wannan lokacin Zuwairah sam bata cikin hankalin ta gashi , abubuwan sai dada tsami suke mata
Yau tayi kwana uku chur ba abunda ya shiga tsakanin ta da shi kuma yana gidan sai ta gwammaci da ma batayi masa karyan nan ba..

Sai dakanta ya soma neman kuncewa tsaban tunanin yadda zata samu kudin da zata siya magungun ta..

Kawai sai ta yanke shawarar sata,
dakin sa ta sake shiga ta sake dube dube, agogon sa da wani  chain bracelets sabo ta kwashe guda hudu ta kai ta boye a dakin ta..

Yana dawowa daga sallah, bai kula ba har ya shirya zai fita aiki..

Da mamakin sa saiga ta nan ta fito, ba gaisuwa ba komai tace masa zata fice gidan kawar ta anjima..

Harara ya watsa mata tukun na yace bazata je ko ena ba..

Sannnan in ta sa ka fa ta fita a bakin auren ta..ko sauraron ta bayi ba ya fice..

Ta so ace ta fitan kawai in ya so in ta cika burin ta na siyar da abubuwan da ta kwaso sai tayi shirin sanin yadda zata hadu da malam mallaka..

Gashi wayar sa baya shiga gani take kamar karime wrong number ta bata amma ta kudira aranta sai ta nemo sa..

Ba yadda ta iya sai ta kira maman abdul ta tambye ta ko zata sami me sayan abubuwan,?

Bata dai bata amsa ba amma sai tace zata mata tallah da karfe 12 na rana zata zo ta karba..

Nan ta baza su akan gadon ta tana lissafin ko wanne kudin da zai ci a kasuwa Tun daga lokacin take jiran ko za'a bata iya yi ta dau kusan awa 3 tana zaune tana sake sake aranta
Tana cikiin haka
Kashi ne ya matse ta, ta shige toilet agurguje

Cikin rashin sa"a, sai dawowa tayi taga babu komai akan wajen da ta ajiye ..

Hankalin ta inyayi dubu ya tashi tayi ta dube dube bata gansu ba, gashi dai yanzu 11 ne jabir  baima sa lahadin dawowa ba bare ta ce shine...

A girguje tayo hanyar waje ta duba ko barawo ne ya shigo tana bude kofa suka hada ido da shi yana tsaye alaman shima wucewa zaiyi,

Wani garas ta ji a kanta, haka kawai jikin ta ya bata ya kamo ta,

Hakan kuwa akayi dama ya zo ne ya tabbatar da ko ta fice ko ba ta fice ba,, a lokacin ne ta soma sanin ita din ba komai bace,sai da yayi mata lilis yace bazai dauki kazan ta sannan ya dawo ya dauki sata ba,

Daga lokaci ya kuma kafa mata doka kar ta sake shigo masa daki akaro na uku kuma ko tsinke ya bata dakin sa daga yanzu sai ta biya shi ko ita ce ko ba ita bace...

"taci kuka ranar Haka duniya ta murde mata ta rasa abunyi,
Washe gari da faruwan haka, gaba daya sai  ya kasa samun sukuni gani yake don ya hana ta kudin wanke ciki ya sa ta sata ai da zuwairah bata dauke dauke,kawai sai ya dauki 30k ya ajiye mata don ya mata adalci..

Gashi yanzu ya mugun sama mata ido y Tsaban bata da wani mafita  sai ta kudira kawai gwara tayi ta siyan maganin mata tana sha tana dada zaki harta samu ta sake zumma zuciyan sa kan ta Kafin ta samu kudin siyan na mallakan.

A dan wannan lokacin zaman sa da zuwairah, ya sa ya fahimci abubuwa da yawa..

Wato Lokacin da Allah zai azirta ka da mace na gari mai tattali da biyayya da sanin ya kamata a lokacin kai kuma kake jin a duniyan nan  kai kadai ne  kuma ka isa ne.. So you  just take her for granted.

Sannan ya gano cewa , ba ma abokai ba kawai har mutanen da kake tare da su wasu zasu baka shawara ne yadda ransu yake so bawai don su magance maka matsalan ka ba,sabida most of them basu ma san ya kake zama da iyalan ka ba sai dai suyi harshashe suyi judging yadda su suke zama da nasu iyalin..

Kai kana nan baka sani ba hala ba ka fisu ma nesa ba kusa ba wajen kyautatawa da iya bi da  tsarin zaman takewa..

Abu daya ne dan adam bai gane ba har yanzu,
Yawanci maza dake zama suce sun iya kaza ko matan su basu kaza ...99.9 %dinsu karya suke yi,..

so kawai suke ka dulmuya ku dawo dai dai Saboda su baza su iya ba kai kuma ka iya, da su sauke kai su tambaye ka shawara ko taimako sun fi so suga kana tagumi suma sun jera da kai suna yi..

Most of them sum fika damuwa amma bazaka taba ganin sun damu awaje ba amma su suka san halin da suke ciki a gidan su..

You must be carefull with  duk aboki ko abokiyar da take fitowa karara tana buga kirji tana bare deden  ta iya da gidan ta ko mijin ta ko namijin da zaice a gidan sa shine kaza shine kaza ...

always see for your self ance wai masu mulki da saurata ba sai sun fada baa na ganin su dole za basu girman su....

Shikan sa jabir ya gani, tunda ya soma shiga tarkon zuwairah ,har yau babu wanda ya taba ce masa ga shawara ko meke damun ka?
Kowa sai dai ya zuba masa ido..

Abunda ya bashi mamaki bai wuce a office da ake gulman sa ba cewa ya auro dai dai da shi kuma har da umar da oga yisuf aciki.. Shiyasa a yanzu ma ya dena zaman  majalisan su ya dawo kawai ayi frndship kawai a zauna lpya

A washe garin ranar ne ya shirya zai je shi kaduna .
Saboda samun tataunwa da ni akan matsalan da muka fuskan ta abaya..
  
Ga kudi yanzu kam Allah ya dada masa budi, ..

Yanzun bai da wani buri illa ya samu kwanciyar hankali kamar ko wani magidan ci.

A ranar juma'a da safe ya bar kano ya kamo hanyar kaduna.



Tsakani da Allah duk kun fini kokarin ma wattapadians kowa da kowa yana taimakawa  Allahu ya saka muku da alkhairi nagode sosai da shawarwarin ku Allah ya sa mu dada karuwa da juna ameem....

Ina Miko gaisuwata na musamman wa
Mamuh gee kishiyar zuwai d kuma
Ummafreen😍




_SURAYYAHMS_

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top