PASSAGE12
*🍒🍒SAMU YAFI IYAWA🍒🍒*
Passage 12.
Tun Da na soma i don't care attitude na kuma dauke kai akan kowa da komai agidan shima sai ya dage wajen sa kafar wando daya dani
Duk dama Dan dolen sa ya sa zuwairah agaba ta soma daukar ayyukan gida kamar yadda nima zanyi na gama haka itama ta fara in kwanan ta ya zago.
Daga nan Sosai halayen zuwaira suka soma bayyana min karara kamar daman dai nine ban san yanayin tsananin kazantar ta da ballagan cin ta ba..
Gaba daya tiles din kitchen ya soma dishewa yanzu ni kaina nakan sha wahala kafin na tsaftace wasu abubuwan da muke using tare ,.
tukun ya duk da kowa da nashi ne amma har ankai biyu daga nata bola saboda tsaban yadda ya kone ya yi loosing qualitin sa da baki ..
Gashi In tana girki har tsoro nake,hankali na baya kwanciya kar wata rana wuta ya kama mu don ko wani abinci bul bul zata bul bula masa wuta kamar tana filin yaqi,
Wanka kuma kamar akuya haka suke da ruwa wannan ma bai dame ni ba kamar yadda ta nace da yawo a gidan da nite gown tamkar wacce ba a kawo ta da kayan akwati ba in tayi ne ta dan dauro zani akai .
Na dade banyi amai na amma Ranar dana ga wai tana kwaba flower za tayi taliyan murjin da ta saba sai da na kwaza amai sosai...
A lokacin Na zo ajiye danyen tafarnuwa ne da aka siya min na mance a jaka na..
Juyin da zanyi Na ci karo da ita ta tamke fuska sai kwasar waka take yi daga wayar ta na hausa film mai taken mariya, ta baje akasa akan tiles buju buju tana kwabin,ga ceiling fan amma gumi take sai ruwan datti dake biye ramin hammatan ta ke fitowa yana sauka ciki in tayi yunkuri kai ranar naga fitina..amma ko ajikin ta
Bangaren jabir kuwa sam ya kasa samun nitsuwa shi yanzu ba ma rashin girki ke damun sa ba...
Da chan ya dauka gajiya da ciwon bayan da take yawan complain yasa bata tsaftace wajen amma ya lura kamar habits dinta ne
Gashi bata son sallaj..wankan tsarki ma shi ya dauka makan sa alhakin in sun gama sex ya shiga tare da ita ya sata tayi yana dubawa,
Yanzu kam har ya saba da yadda ya tafi ya bar dakin haka zai so ya samu..
Gashi yanzu bai da lokaci
In yazo kawai sai dai yayi masifan ya bi ya karkade boxers dinsa akasan floor ya kaisu dakin sa ya tara ita kam bata ma daga nata bare na shi...
A duk lokacin Dayayi mata wani masifa mai tsanani haka fir zata hana shi sex tayi ta gaya masa bakaken maganga nu...
A hakan Babu yadda ya iya, sabida yanzu yayi zuciya bayayi da ni, nima na nuna masa tafi nono fari,.
Shiyasa duk azaban wulakanci ya koma ya na dauka...
Haka zai lallabata gobe ma ba shi zai hana su sake kwabewa ba
Ranar Abun ya ishe sa
ina kwance naji shi,.
Ina kwance shiru Hannu ya kawo zai taba ni na firgita na mike
Ya wani daure fauska Yace min meye haka..nace masa kar ya taba ni bana so..
Ya jawo ni da karfi, na gantsara maa cizo a hannun sa..cikin masifa nace ka tashi kaje chan inda kasaba ni ka kyale ni bana yi..
Ya ce bazan je ba anan zan karba dole zaki iiya min bukatuna ..na kan rasa irin rashin Kunya irin na jabir wai shin ba shi bane yake ce min yana da wacce ta fini akan gado?..ranar fa har gori yayi min akan zuwaira
....amma sai gashi yau ya dawo wai na bashi..
Haka muka dinga yi har ya karbi hakkin na shi as usual ba wani dadi sai tulin bacin rai,..
Tun Daga wannan lokacin ya min fada akan idan banyi hankali ba sai ya kai kara na gida kuma ya tabbatar min sa bazan ji dadin abunda zai faru dani ba...
Naso nayii masa taurin kai
Amma ina tsoron su mumy gaskiya,
sai kawai na soma shiru shiru bana dai amsa shi,sannan zanyi masa abunda ya ke so muddin akan gado ne ban damu ba...
Don yanzu ma na dan samu sauki sauki bana jin yanayin da nake ji ada chan sosai ga shi ciki na ya girma sosai..
shima kwana biyun sai naga ya shiga hankalin sa baiya wani nuna min rashin hankalin sa a fili kamar da ,ina lura,.. it seems like zumudin amarcin ne ya dan fita ajikin sa
but we are not in good time ne yana harkan sa ina nawa..
Ana haka, ..karime ta kawo ziyara ma zuwaira niki niki da kayan mata a buhun bakko bag
Nice da girki..so ina kitchen a lokacin
Amma Dan wulakanci sai suka ki zaman dakin nata suka zo falo sai shewa suke suna hira kamar gidan kaji..
Yau abubuwan da suke faruwa wanda banjiba bansani ba sai yau naji a bakin zuwaira.
Kafff ta kwashe labarin yadda take cin jabir da yadda jabir yake mata itama akan gadon babu gargada babu kwana ta zuba ma karime
Tadi yayi dadi Har blackmailing dinsa data keyi in tana so ta samu cikar burin ta akan wasu abubuwan tace shi yake bata kudi take tarawa ta ke tura ma karimen ta mata shoping kayan mata daga maiduguri..
Inji ta wai komai ta sa ido a gidan
Musamman ma dangin sa da bata shiri da kowa...
In kuma yayi motsi ko takk yace sai tace bashi ba sexx..
tuni sai ya rusuna ya lallabata don ya san ba samu yadda yake so zaiyi awaje na ba..duk ta sa a cikin labarin nata
Karime sai hangame baki take don kuwa ta ji dadin abun aganin ta ai kwalliya ya biya kudin sabulu,
Tace to ita wannnan bushiyar fa me kike jira da ita..wato ni kenan"
zuwairah ta dan leko tayi dariya mai sauti bata ce komai ba, karime ta cigaba
Tace meye aikin ta agidan ko da shike ai ko da na shigo ma ke kadai nake gani fa,kawata kece star, full option, mowar mai gida, sukayi tafi zuwairah tace yesss ooo..fada da kaurin murya
'Wasu kam ai inda kikasan kwatami haka gindin su yake miji karara yake nuna baiya ji dadin su sai kiga ya nanike har na rasa jaeaban irin na jabir..ama fa ba laifin sa bane im sure da yana jin mau wallhy bazai haukace min ba..
Karime tace tabbasss ga mallakar miji ga shi dole yayi biyayya ai kema kinsan tamkar ke kadai ce to me ya rage..
"Tace dama fa,.in ba nikadai ba har na isa ina karban kudin kaya wajen sa kuma ya debo su loadi ya bani..ai kinsan girkin dayafi maka dadi konawa ne zaka kashe masa wajen kayan miya ...
Ire iren hirar da suka yi kenan kuma ina jin su suma suna sane sarai da hakan,amma nayi kyam naki na bar zuciya ta ta debe ni
Tunda naje daki Zuciyan nawa ke bugawa ,amma bana so na bari ta dimauce da tunani nace ko da gaske ne jabir yana gaya mata banda taste kamar kwatami..amma meyasa zaimin Haka?
Abun ya mugun sosa min rai bana wasa ba...
Duk da ena fushi But i neva tot of na fara amfani da maganin mata irin nata sai na ce to shikenan zanje na nemi shawara in Har cikin ne har yanzu ke sani haka zan ti hakuri
In ba shi bane kuma sai na nami gyara cos na tabbata zama da zuwairah ba karamin jihadi zai zame min Ba nan gaba..
Haka na harhada naje aka sake duba ni amma babu komai normal nake haka ma abun ciki na....
na kuma nemi shawara anty hanifah tace min kawai nayi hakuri komai zai wuce..
na dawo gidan sai dai kamar an tsawwala komai ne ma bayan tafiyar karime da sati guda abubuwa suka dada jagube min
Jabir Ya soma nuna min karara zai iya komai akan dadin gindin zuwairah..
Har yake cemin wallhy shi yaa fara ganin kamar dama itace first love dinsa bai sani ba sai yanzu...
Raina yana baci amma Bana taba reacting in yana gaya min Magana baya kuma tashi gaya min Sai yagama amfani da ni son ransa .
In Ya fuce nayi ta kuka kamar zan cire raina amma nakasa gaya ma kowa komai...
Abu sai gaba gaba yake kamar wani tsafi Yanzu kam ma dan fadan kazantar da yake mata ya dena sai lallabi,
Ta samu dama yanzu sosai har aikin hidan takan sa shi ya yi da sunan soyayar gasu wai zasu sa min Bakin ciki,
To musamman in yana weknd dashi da ita ne a kitchen ko da kuwa ranar girki na ne duk sai su Kwabe waje .
Gudun raini da bakar magana ya sa na fita hanyar su bana tankawa har suci su kare....
Zuwairah ta dada bankadewa A kullum yaumin wani sabon sara take fito wa da shi na wannan karon yafi tsamaro don karara take gaya masa ya bata kudi ta tara na siyar kayan aiki...
Shi dai yana so ya san meye ne don inta siya bata nuna masa wasu abun sai wanda taga ya mata..
Gashi sam bata san me ake nufi da cewa nagode ba, sometimes in Ya bayar ma sai ta yi complain din Baza su ishe ta..
Duk yana hankare amma rudin zuciya da dadin gindin zuwairah ya shagaltar da shi baiya iya tabuka komai sai abunda tace mafi akasari...
Ina gefe Duniya tayi min zafi
Cikin raina babu dadi sosai na soma ramewa
Abun ya ishe ni ,..
yau ana saura kwana Biyu na shiga wata na takwas na yanke hukunci na je dakin sa na same sa da sassafen Allah...
Hijabi na sanya mai kyun tsari picth wanda ya dadaa fitowa da hasken fuska na..
Na yi sallam a ladabce na tsuguna gaban sa ban damu ba duk da ma bai amsa ba..
Nace ina kwana jabir,...
Ya nemi waje ya dake yace to, lpya kuwa?
"Na dan sauke kai na kasa nayi shiru na dan lokaci guda zai yi magana na dago cikin wani irin sigar yaudarren magiya cike da nadama nace dan Allah kayi hakuri jabir ka yafe min...
Na dan fashe da kuka mai ban tausayi mai taba zuciya na dada rusunawa kasa na iso daff kafar sa na tsuguna..
Im sorry, na dada cewa cikin shessheka nace" nasan duk abunda kake min laifi na ne duk nina jawo hakan amma na roke ka kayi hakuri ka yafe min ko da bazaka dawo min kamar da cahn ba..
Na yarda Nice matar ka mai zama a karshin ikon Ka kaine shugaba na wanda ya zama min dole na girmama nayi masa biyayya
Jabir Nayi kuskuren kamanta sabanin hakan ka gafarce ni...pls jabir.
" yana kallona shiru,..acikin ransa Sai ya rude ya rasa me daya zaiyi, gaba daya ya kasa kamo komai ba wani bangaren ransa ya kwanta don dama so yake nayi masa hakan tuntuni na amsa nayi masa laifi akan komai shine da gaskiya,
Sai dai wani bangaren ya san ya zalunce ni sosai ya kuma ci amana na..
nikam na qudira zan saukake komai tsakani na da shi koma yaya ne na amince aje hakan..
don gidan mu nake so na tafi gaba daya nagaji da zama da shi amma bana so muyi rabuwar a haka im already feelling miserable zaman da nake a karka shin sa..
Haka na cigaba da kuka agaban sa ina kawo kalamai nasu taushi masu kashe zuciya..
Karshe dakan sa ya dago ni daga kasa ya zaunar da ni bakin gado ya kasa cewa komi,
Sai ya isa haka samha ita ok,
Ai Magana ya wuce a waje na..
Nasan tausayi na kawai yaji da hakki na dake binsa
Ban damu ba na share hawaye na nace na gode..
Nayi masa alkwarin bazan sake masa abunda ya saba zaman auren mu ba..
Daga nan muka dawo normal sai dai shi ya ke shan wahala sam ya kasa sakewa da yadda Na dawo da kaina tamkar baiwar sa sai yace nayi nayi bana kuma fasa zuwa gaishe sa da gyara masa daki da sauran su..
Na dada dawowa sokuwa agaban idon sa dama chan bana shiga hidimar zuwaira,ni ka dai nasan me nake ji a raina
Sati guda Kawai nayi hakan Na lura ta sha jinin Jikin ta,duk da bidirin haukar na su sai ya dena bari suna yin wasu abubuwan a inda zanji ita kuma ba hakan takeso ba...
Yanzu baya min Fada ko tsiwa agaban ta
A cikin na sati biyun kawai sai ta soma kawo bori ba gaira ba dalili..
Haka kawai in ya sani masa abu misali dauko masa ruwa ko wani aika sai ta zo ta bangaje ni amma itace zata fada kasa tana zagi na...
Ni dai bana amsawa muyi tayi,.amma guda daya in na gaya mata har hawaye takan yi yakan mata zafi sosai.
Sai dai bata fasawa Abun mamaki ranar dakan sa ya karbe min baki yayi mata tas tas yace bazai lamunci raini ba kuma ya soke hakan agidan sa...
Ranar ta sha mamakin sa matuka .don masifa yayi kamar zai wanka mata mari sabida abinda tace min..
Itama ta bore Tace masa wallhy shi da zaman lpya agidan sa ya kare kenan Tunda ya bi baya na ba irin magangan da bata fada ba..
A lokacin Ina shiru agaban su ina kwasar points a kwawalwata washe garin ranan ne na samu dama na gaya masa qudiri na na cewa ina son haihuwa ta ya kasance achan gida gaban iyaye na...
Yaki har yaki amma Na kawo masa reason cikin salo na dana saba ..na nuna masa cewa zan taya shi ta kowa ni hanya wajen samun kwanciyar hankali da zaman lpya a tsakanin sa zuwaira.
Don haka ina ganin idan bana nan na wani lokaci wani abun tan ma Zai ragu zata fi samun nitsuwa ta saurare shi Har na kawo masa cewa ita zuwairh ma yarinya ce tana bukatar kulawar sa sosai ,.in ta na gani na kishin irin namu na mata bazai bari ta nitsu ba kuma duka alhakin mu nakan sa yayi hakuri ya bata dama a cikin kwanakin da bana nan ya fahimtar sa ita manufar mu..
na kuma nuna masa a shirye nake na zauna da ita lpya idan na dawo daga jego bazai taba samun akasin haka ba.
Yaji dadin wannan shawara tan amma bazai iya nuna min sosai ba sabida kunya na ya soma taba ransa..
So har zan iya saurin mancewa sa abubuwan da ya min so sooon na daura makai duka laifin kamar ban damu ba?..
Kawai sai ya bani dama naje gidan na haihu zai duba ya gani..
Naji dadi sosai na je na shirya na sanar da su mumy
Washe gari da safe ma Na fito ma zan tafi naga ya shirya...
Yace shi zai kaini har kaduna...
Ban yi musu ba duk dama Allah Allah nake na rabu da shi don wallhy bana kaunar gani fuskn sa..
Sosai nake so na rabu sa shi na huta ma raina
Na daure nayi na mata na buga sallama daga bakin kofar ta amma
Zuwaire ko ta leko bare ta amsa ni har muka fice
A motar nasa zan iya girka sau nawa mukayi magana har ya kaini gidan mu..
Hira sosai suka yi da su mama da kowa da kowa kamar ba abunda Yake afkuwa a gidan mu
Su mumy har da bashi tsaraba ya kawo ma amarya...
Sai wajen asr ya tashi tafiya anan na ya dauko 50k ya bani ya kama gaban sa..
Wani sassanyar ajiyan zuciya nayi
Na gode ma Allah.
Kwana biyu kacal nayi agida amma an dame ni da tambayar ya na rame amma haka firr naki fadan komai har mumy ta kyale ni akan ko cikin ne ya jeme ni..
Ni dai yanzu tunda na bar musu gidan zan haihu gaban iyaye na shikenan Banida da case.
Kafin nan ranan da ya kaini gida dawowar Sa
Ya zo ya samu zuwairah ta hada tarkacen ta wai zata bar masa gida...
Tun Daga kofa ya soma salati, tana shiru sai kada kafa take gana watso masa harara..
Yace meye haka kayan maye wannan ?
Ta mike tsaye ta watsa masa mugayen kallo tace hey malam dakata, dama kai nake jira ka sauwake min anan zan bar maka gidan ka
..munafuki kawai azzalumi,macuci ta watsa masa harara tana dirin masifa mai zafi..
Tsayawa yayi a daskre zai yi maganan ma ta katse sa tace kai tsaya.
Zaka bani ta karda na ko sai na nuna maka asalin wacece zuwairah?
VOTES LIKE URE waving me bye😹
_SURAYYAHMS_
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top