PASSAGE11
*🍒🍒SAMU YAFI IYAWA🍒🍒*
_PASSAGE11_
Girki na daura har nayi nagama basu fito ba.
Anan na ajiye kan dinning na wuce na koma daki nayi kwanciya ta.
Wani zuciyan yace kar na sake na fara daukar wannan salon iskanci
Wani yace min to me zakiyi musu in ba dai takaici kike nema makan ki ba ki barsa zai gaji ai ko giya ne komin karfin sa dole ka ya sake sa wata rana ..
A hakan Har nayi bacci na bai shigo ba..
Yau da safen ma ko kula ni baiyi ba ya fice..
Alhamdullhi, yau kam kwana uku ya kare tun da ya tarkata ya koma dakin ta ban sake ganin idon sa ba sai da ya dawo daga office around 6.30 na yamma..
Nan ne na lura da wani abun mamaki, ni dai tun jiya nake ganin ta da wani riga da skirt na atamfa shine kuma ajikin ta har yanzu bata sauya ba, sai dai bata daura dankwali ba ta fito daga daki ta same sa har yayi wanka yayi isha'i.
anan yayi zaman sa akan dinning shiru ba ajera komai ba data zo saita zauna gaban sa sai yauqi take ba har Ya gaji ya tambayar ina abincin sa?
Tace Abinci kuma desire??? Uhmm wallhy bana jin dadi shiyasa ban yi ba ..
What? Me kike nufi da bakiyi ba wallhy yunwa nake ji zuwairah,...
Ta dan sauke karamin tsaki cos habit dinta ne, nace bana jin dadi jabir wallhy bazan iya shiga kitchen ba ...
Batare da bata lokaci ba, yace"To ya zakiyi dani?wai ma meke damun ki bayan gaki nan garau nake ganin ki, ta dan daure fuska tace baya na ke ciwo..
"baya kuma? Ohh uhh god shine ko dan indomie bazaki iya daura min yanzu ba..
ah'a gaskiya ni bazan iya ba,to ka fita mana ka siyo gaskiya ni baya na na ciwo bazan iya komai ba.
Ta turje sam Haka suka yi ta
"Hmmm ya dawo ya sauke ajiyan zuciya, ya daga wayar sa kamar zai kira amma yasan sam baya cin abinci a wajen sai ya kuma ajiye wayar ya kure ta da kallo ..sosai cikin sa ke kukan yunwa gashi ya sa rai yau zaici abincin amarya for the first time..
Shikam har ma ya manta da yanayin da ya zo ya same ta, ba kwalliya ba komai alaman ma bata yi wanka ba tukun..
Amma ya marairace yace , ni gaskiya ki san yadda zakiyi da ni i dont eat out, ki dai daure kinji desire ko dan indomie nasa abiki na pls..
ta dan ja jikin ta ko kallin sa bata yi ba, cos ita daman in ana lallabata take jin kanta na hawa..
Lokacin ni kuma na ajiye plates din abincin da na gama ci kenan a kitchen doya da miyan kwai zan wuce na je room dina ban ko juya na dube su ba
Ta dube ni a fakaice tayi saurin dada tamke fuska ta soma magana kamar bata ma lura da ni din ba" tace rashin lpya fa nake yi jabir,...wallhy baka da imani ta sa muryan kuka
Ni gaskiya bazan iya ba kawai ka sa wani ya maka tunda bazaka siyo a waje ba..
Ta mike ta wuce daki ta barsa anan...
Ina shiga dakin ko zama banyi ba na ji ya ya shigo, yace samha"na jiyo na kalle sa daganan bance komai ba..
Yadda na daure fuska ya sa shi dan jan lokacin kafin Yace akwai abinci a gidan ? Nace ehmm akwai...
ya dan yi shiru daga bisani yace get me some im hungry...
nace ai ba ayi ba tukuna,
Cikin karfin haki ya ce ohhh, don bayi ba shine ni bazan ci abinci ba ?
Nayi masa shiru na dada daure fuska ta ..cikin kukkuni nace ai ba mani zakayi ma wannnan tambayar don ba bani ce da girki ba
Yana ji yayi kwafa ya koma yana kallo na"yace to ai shikenan Samha naji, zuwairah bata jin dadi pls get me somthing to eat tunda haka kike so nace miki..
Nayi shiru ban dai kalle sa kuma Banyi musu ba na wuce naje kitchen din, minti kadan na dawo mai da indomie da daddafen kwai..
"Tsaban yadda yunwa ta cinye sa bai tsaya mun wani tsegeran ci ba ya zauna tass ya lashe har yana zufa..'
Kofar daki na na rufe na yi kwanciya ta ina juy8,
Abun mamaki bai karewa ko karfe sha daya baiyi ba naji ihun sa daga chan dakin zuwairah...
dariya abun ya so ya bani i just wonder if jabir is possed akan yarinyar nan.
Washe gari da safe wajen karfe 8 na fito har nayi breakfast na koma still bata fito ba sai naji knock a kofar falor , ina kan kokarin kama handle na bude sai naji muryan sa nayi mamaki dama har yanzu baije aiki ba..?
Thats none of my business na basar, na kama kofar na bude
'Da gudu ta rungume ni nace sis zainab?
Sannu da zuwa na kamo ta nace im sooo happy to see you...Itama sai faffadan murmushi take sakar min tana miko min bags din ta,
Nace"shigo mana sis, shigo ciki ya hanya na dada a jawo troleyn ta ciki tana bina da amshi cike da fara'a..
Zaynab step sister jabir ce amma su suna zama a sokoto ita da mijin ta ...
Jabir Yana mugun kaunar ta cos ita ce kawai ke iya sauraran sa most of the time in yana cikin matsala har ana ce musu twins..
Naji za'a yi wannnan nidai Kar dai na dawo na same ki kamar jiya, kinji na gaya miki...
da masifa ya fito bai ma gan mu ba..ita ne abayan sa da nitiyn ta sai yauqi take tana yatsine.
.
Jabir?sis zaynab tace da murmushi na wuce gaba na basu waje.
Tuni mood dinsa ya sauya ,yace ,Oh my god zainab...ure soo welcome yaushe kika taho toh, why dont you call me ya dan dada a rude..
Tace"Comn quiet,ai nayi ta kira baka dagawa me kake yi har yanzu agida na dauka ai kana office ..
Ya ce ,oh yea im late wallhy, ke dai yanzu ki huta bari naje na dawo..
Suka yi sallama zai fice , yace pls sis ki dan turo min samha ,tace toh ta shigo ta same ni har na ajiye kayan nata tace naje yana kira na
A tsaye nagan sa yana kan duba agogon sa a matse , nace gani..
Uhumm, zuwaira zata je asibiti jikin nata ba kanta sai ki taimaka ki mata abubuwan da ya kamata....ni na tafi.ya juya abunsa bai ma jira amsa ta ba..
Cikin raina Nace kutuma hmm lallai ma jabir zaka zo ka same ni..
Anan dai na kauda maganan na zauna ina entertainh din sis zaynab..
Har wajen 1.30 na rana munyi sallah munci abinci
Sis tace, wai ni har yanzu amaryan bazata fito mu gaisa bane?
Da shike mun saba sosai da sis nace zata fito mana skika sani ko ciwon amare ne ya boye ta ?
Tayi dan murmushi tace, hmmmm samha ai naji anata labarin ta ne nidai ban yarda ba amma ai dole na tambaya tunda na zo har yanzu bata fito ta duba ni ba..
Nace ,ah a sis hwanda ma da baki yarda ba, yanzu halan ma bata sani ba ne don jabir yace bata jin dadi sosai shiyasa ma ki kaga nayi mata girki..
tace aiyo to why not ki kaini na duba ta..
Nace to shikenan nan muka mike...
Zuwairah Waya take yi sai tambade dariyar ta take ,daga nan bakin step din kofar corridor munaji amma sai muka basar,
Muka cigaba da hirar mu muna tahowa..
Salam alaikum, sis har zata shiga na riko hannun ta alaman mu jira ta amsa...a hujajan ta ajiye wayar cikin gatse da kaurin murya tace ni waye ne kam?
Sis ta budi baki tana dubana ,
nayi sauri nace mune zuwairh, samha ce,.
tsakin nan dai ta sake saukewa sa usual tace ok..
Muka shigo..
kallon yanayin dakin ya hanani sakewa na sake magana ga nan gadon a wargaje babu gyara da duvet din alamar anan take kwance tuntuni..
Gefe guda Ga nitin ta da boxers dinsa nan ayashe kasa gefe da gadon kai kayan kan mirror ta ma a warkaje yake bare aje ga jikin ta,
"Ina kwana, ta daure tafada cikin daure fuska cos ta san yanayin da muka ga dakin ya sa mu yin shiru.
Nace lpya na dan taba sis da tuni ra shiga duniyar tunani muka karasa zan zauna sis tace ah'a kar ki zauna samha ai ba dadewa zamuyi ba..
Nace ok, ganin bazata gaida sis ba nace zuwairah wannan fa step sis din jabir ce ta zo daga sokoto, tana so ku gaisa...
Ta dan watsa mana harara duka tace ehmm uhumm to sannu..
Sis tace tabbb, sannu? Nayi saurin mata ido sis ta dan kada kai tace, ok sannu kema
..tace yawwah ,
Dan shiru ne ya ratsa nan sai tace uhmm ni bacci nake ji dama zan kwanta,
ta kau da kai tana dan jan qamshi,
sis ta tsaya kallon ta tana tabe baki
Nace "ayyah ya jikin to,
tace da sauke nace to Allah ya kara sauki
sis bata bari na sake magana ba tace samha muje ko
Nace ok..
Muka fice sum sum a dakin
Tsaki ta ja ta koma kan wayar ta ta cigaba
Tunda muka kai site dina sis ke masifa tana maganganu "ni ai ba sa'ar ta bane wallhy ko shi jabir ma na girme sa da watanni har takwas bare wata banzar yarinyar da zai kawo cikin gidan sa..
In banda hakuri nidai ba abunda nake mata..
Duk na kawo mata cewa ai amarya ce kuma jabir na kokari duk kuma hakan normal ne a farkon aure.
sis tace sam wannan ba ta da da'a shima zai zo ya same ni..
Wani za agwada wa raini wata kazama ma da ita..
nace shhhhhhh sis dan Allah ya isa haka..
Hakan muka zauna nayi komai a yadda na saba yi,
Yana dawo yau yasan baida matsalan komai don yace nayi girkin
So wanka yayi yayi sallah ya kimtsa ya fito,
Zaune muke tara da ita yau kam am sa mu saiya sutura , wani dogon rigan kanti ta sa kalar orange ta taho ta zauna dab da shi a dole itace mai miji,
Shikuwa ganin idon mu da sis Sai neman batsarwa yake amma ina , in tayi tayi sai yace mata zuwairah sauki ya samo kenan ko?
Tace ah a, desire har yanzu inajin kashin baga na na suka.
Sha'awar naci abincin kawai ya sa na fito dama ni banci komai ba tun da ka fice,
..dukan mu muna shiru ta cigaba da zuba mana ruwan iskan ci da kisisina ko magana yake da sis sai ta daure fuska ta shiga tsitt da yawo tana tsaki
Anan ma ran sis ya dada baci har ta tashi ta bar dinning din tun kafin ta koshi
Ko ajiki na sai da nayi nak kafin na tashi na basu wuri..
Sauri take tajeta dan kwashe kayan dake wargaje akasa kafin ya shigo ya gani don haka bata ja shi sunje dakin ba kamar yadda ta saba..
Yana shiga dakin sa sis
Ta biyo sa..yace my siis kece ashe dama ina shirin..tace stop jabir, ya isa haka wallhy raina ya baci.. ta daure fuska
Yace ah'a twin sis yau kuma me nayi miki, tace jabir how cud you ?
Me wannan nake gani agidan nan wannan ne matar da ka kawo mana
Sai rainin tsiya da rashin da'a..
Yace pls enough, ya isa haka zainab what rubbish..
ohhh kinje ana gaya miki karya da munafurci kinzo zaki haura kai kema ko?
Sis ta dada bata ta kai tace"munafurci?kaima ma kasan na fi karfin wannnan am talking about waht she did to me ..nan ta dan gaya masa abun da ya faru..
Ya ce to sai me..she is sick kema ai kince samha ta gaya miki..
kawai ki saurara In ta warke zata miki yadda kike so but for now im tired
Ni bana son fitina pls leave me alone..ya daure fuska ya juya mata baya ...
Tace jabir hakan ma zaka ce yace yes..
Kawai ki je sai da safe..ta jiya a zuciye ta bar mai dakin..
Iya hakuri na ba anty amma sam taki akan cewa gobe zata bar masa gidan sa tunda bai ya ganin rainin da zuwairah ta ke yi dama don ganin amarya ya sa ta zo cos she dindt attend the weding
Washe gari Da safe ma hakan ne ya faru cos agaban ta yace na sake yin girki ma zuwairah...
ban ko amsa ba ta cafke tace masa bazan yi ba ai tunda zuwairah na da karfin kwana da shi ta fito tayi abincin ta...
Sis ta kasa gane logon abun nasu sabida ta riga ta harzuga da halin zuwaira sai ta rika masifa cikin bacin rai tana gaya masa bakaken maganganu
Daman zuwairah na nan daf abayan sa da shike a falou muke
Anan ta sa masa kuka ta soma cewaa ai dangin sa sun tsaneta basu tausayanin ta,gashi bata da lpyaa amma ana zagin ta , an juya musu kai akanta an sa sun tsane ta,
Anan ma ya tsaya ya zuba ma sis rashin m..
ni kaina nasha mamakin yadda jabir ke cire jijyan wuya akan kar sis ta sake shiga harkan matan sa.
Ni ma bai barni ba sai da ya azalzala min cewar sa bani da imani kuma idan ya dawo banyi abunda ua sani na zan ji ajiki na...
Ya wuce ya fita
Kuka sis ta rika yi tace samha?wannan jabir ne yaushe ya dawo hakan? Har da cewa zakiji ajikin ki, samha gaya min gaskiya jabir din dukan ki ya keyi?
na damu matuka zan yi magana ta dada borewa tace
Shi din waye da zai ajiye wata yana kwana da ita ke kina musu abinci ?
A sanyaye Nace kiyi hakuri sis,yanzu ne,kuma na farko ne kawai amma sam sis taki ta bar maganan tayi fushi sosai sai surutu take
Daga bisani ma ta tattara kayan ta ta wuce tasha..na roke ta har nagaji hakura na kyaleta na dawo gida...
Abubuwan na damun sa
..amma hakan yake dannewa abtunanin sa daga yanzu zai sa ido akan zuwairah sosai don dangin sa kusan kaf din sun nuna masa bata da tarbiya
Amma babban problem din shine baya son ya dago magana ta hana sa sex in yazo neman ta.
Nikam tunda lokaci na san akwai babban yaki agabana don kuwa bazan dauki yi mata komai ba tana kwana da miji ta samu bakin raina ni nan gaba ba..ance icce tun yana danyen sa a ke langwasa shi..
So yau Ina gama shirya abinci na yi zaman diris ina jiran sa ya dawo ayi ta kare ...
Ko da ya dawo Bai kula kowa ba ya shiga ya kintsa tsaf ya zauna ya ci abincin sa ...ko loma biyar baiyi ba ta fito stil ta sa nitie as usaual ta fara karo masa kwarkwasa yana shiru dai bai bata fuska ba don tunani sun soma yi masa traffic tunda ya lura cewa zis zainab tayi fushin dagaske ta bar masa gidan
...hankalin sa ya dan tashi amma yaki ya nuna sosai..
Amma chan dare ya ja wajen 12 ta ja shi jikin ta Ba don ya so ba haka ya biye mata suka kwashi gara anan falo kafin cahn dare ya shigo daki na...
Banyi bacci ba don haka ma mike na zauna..
Zai ja bargon ya kwanta na kwace nace ina da magana da kai jabir,
Fuska ba yabo ba fallasa Yace ok, ina jin ki..
Zan yi magana ya dakatar da ni da cewa kar ki bata min lokaci samha just go straight to the point
"abun ya sosa min rai Nace kayi hakuri jabir bawai bazan maka biyayya akan abubuwan da kake so bane,.amma gaskiya maganan Wani baida lpya wani yayi girki bazan lamun ta ba nayi na karshe kenan don haka kasan nayi..
Yace what? Akan me..meye amfanin zaman ku ku biyun idan bazaku taimaka ma juna ba...
Na mike tsaye na kalle sa cikin azamaan da ya dade baiga nayi irin sa ba..
nace badai zan dauka ba jabir kasan bana gaya maka magana akan son raina sai dai don samun ciganban zamn lpyar mu ko..
Nima nan ina fama da lalura dauriya nake yi nake aikin gidan nan..duk rashin lpyar da matar ka take baza dai a hada shi da wahalan da mai juna biyu ke sha ba juna biyun ma na wata 7 a gaskiya bazan iya ba..
In har ka na so ana taimaka mata tun Wuri ka nema mata mai aiki nikam na gaya maka,
nayi shiru na daure fuska ta tam bana ko kallon sa bare ya dame ni
Yayi shiru, yana kallo na hakikanin gaskiya ya kasa kawo points sai yace hmmm kya ji da shi dai samha.. Akan nace kiyi girki kike gaya min magana haka?
To Duk dai munafurcin mutum haka zai ganni ya barni..
Nace ohhoo dai, ni dai na fada maka kenan...
daga nan na wuce na shiga batrum na kimtsa kaina na fito na kwanta..
Shima bai kula ni ba Tun daga wannan rana ban sake gane ma jabir ba banda wukakanci ba abunda nake karba wajen sa..
Ranar da zuwaira ta karbe girki dafarko yana ta zumudi,
amma daga bisani hatta kitchen din sai da yasa akayi masa spray saboda wariin kaurin abinci
Soyayyen ko dai 8nce konananen plaintain kuma an zubar da shi ya kai sau biyar a dustbin a haka ya hakura ya dafa indomie dakan sa ya ci
A ranar Kuka ta dinga raira masa duk dama ya gano ta sosai kamar fa bata iya girki bane,.. amma sai ya so maida masifan kaina ba gaira ba dalili.
ba komai bane illah yasan yanzu nace bazan taba karba mata abinci ba.
Kullum idan kwanan zuwairah ce wajen girki sai ansha da shi amma bazai taba mata agaba na ba sai sunje daki
Nikuma sai ya sauke min borin yunwar nasa a kaina
Ya ci min fuska agaban ta iya son ransa ..
Nima hakan na turje bana taimaka mata da komai din..
Sosai nayi zuciya na daura ma kaina fushi ..Abu daya nake muradi a raina wato saki kuma nasan basamu zanyi ta sauki ba don haka
Na qudira In sha Allah nima na shirya bana sake nuna ma jabir shi din wani abu ne awaje na kuma bazan sake kula wani abunda ya shafe shi ba har sai ya gaji da ni ya sake ni..
Bayan wata biyu..
_SURAYYAHMS_
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top