PASSAGE 15
*🍒🍒SAMU YAFI IYAWA🍒🍒*
PASSAGE15.
Dedicated to all comenters JazakhAllh khairan.
Zuwairah Ihu ta tsala tana yarfa hannu, wayoo Allah na ta sake kafa ta wangale tana ganin jinin na tsiyaya..
A daddafe ta kamo wayar ta sai ta rasa waye guda daya zata kira gashi bata shiri da ko mutum daya daga dangin jabir...
Uwa uba mahaifiyar sa ummah..
Kuka ta fashe da shi, tana wayyo wayyo tuni ido ya raina fata tana nishi sama sama,
Chan da abun ya tsanan ta ta shiga rolling a kasa tana damke ciki data ga haza ta yanke hukuncim kiran maman abdu da suka hadu da ita wajen siyan kayan mata
Anguwan su na dan nisa amma haka ta daddafa ta zo,
ITa taimaka ta kai zuwaira asibiti akan zata biya ta kudin ta tunda yau jabir zai dawo.
Anan aka bata gado aka duba ta,
Da shike ma asibitin ba wani mai karfi bane
Ya sa aka musu komai yar sharp sharp..
Likitan ya sanar da zuwairah ciki ne ya zube acikin ta ،sannan tana bukatar proper medical check up..
Ita dai Bata damu na tunda tadan ji dama dama
Basu ma gama shan ruwan ba ta sa maman abdu ta dawo da'ita gida ana neman karfe hudu na yamma..
Mamaki ya gama lullube ta ita kam, don bata taba ganin kazantar irin na zuwairah ba ,
Yau da za'a dan duba mata cikin ma sai da aka mata shaving tsaban yadda yanayin wajen yake babu gyara nurses sai da sukayi gulma..
Amma mai yaci mata rai ai dama haduwan kan titi
So bata ko yi tunanim gaya mata ko tambayar ta meyasa take hakan ba, ita kanta amman abdu tasan tana son amfani da maganim mata bUt she just wonder wani maganin ne zaiyi aiki acikin wannan daudar kazantar zuwairah in ba ma ikon Allah ba...
Sai wajen shida suka rabu, ta koma gidan ta..
Jabir kuwa tunda yayi magana da ni ya soma tsintar kansa a wani yanayi, sai ya na ganin kamar sam bai min adalci ba da baiya kiran na yana tambayar lpyan mu har tsawon wata guda, but ya zaiyi? Gaba daya zuwairah ta gama rikita masa lissafi in har yana kano a hargitse yake baya ma cikin hankalin sa barw ya san ne yake yi..
Yanzu ne dai ba ya tare da ita kwana biyu yake jin
Shaukin samhan sa..
Ni kadai yake so ya tuna Ko kadan yaji baya kaunar ya kawo zuwairah aransa amma he's still confused about that...ya dau waya zai kira su umar ko da yayi dialing wani tunanin yayi sai ya fasa ya mayar ya ajiye
A washe garin da ya dawo daga uk anan abuja ya zauna
Kuma haka ya yanke hukuncin Zai na kiran na akai akai koma yaya ne is not too late, so dis night kafin yayi bacci sai ya kira ni ..
Still mumy na nan tare da ni ganim yanayin fuska na ya sa tace in shine ki dauka
Ai in baka iya kama barawo barawo sai ya kamaka kar ki sake ki nuna masa komai yadda kika fara haka zaki cigaba har sai ya zo nan gidan ya same ni tukun.
Na gyada kai nace to mumy ...tashi tayi ta fice a karo na biyu da ya sake kira sai na dauka
Muka soma magana wanda mafi akasari dhiru yafi yawa shikan sa guilty consience baya barin sa ya fito fili yace nayi hakuri nikuma na cigaba da nuna masa ban damu ba..
Ciwon ciki ke damun Zuwairah sosai saboda ga zuban jinin mahaifa ga yunwa don tea dama take hadawa sai dan cereals toh duk ta karar yanzu lipton ne da sugar da madara suka rage, gashi tana ta bare dede azuciyan ta tana jiran jabir ya shigo tun tuni har wajen karfe 12 shiru...
Kawai sai ta fashe da kuka...
A haka har tayi bacci ta wani irin bakin haushin sa.
Da safe dan dole ta sa ruwa ajikin ta ta tsame jinin da yake bin ta,
Sai dai sam ta kasa tattaer kayan jinin data bata a haka ta dungula su ta ajiye harta pants din da suka jike da jini ta tarkata su agefe tayi zaman ta..
Around 10 naga ya sake kira na,muka sake gaisawa
Anan yake gaya min yana aiki ne a abuja in 10 days zai gama ..na ce Allah ya bashi sa'a.
Yau ma da muka kashe wayar kudi ya sake tura min...dubu 30
Nasan duk dan nayi siyayyan kayan baby ne amma bakin sa ya kasa buduwa ya gaya min hakan saboda kunya...nima sai na biye ma move dinsa inyace kinga aika ko? sai kawai nace eh nagani na gode..
Yana katse wayar kiran zuwairah yake shigowa kawai sai ya fito daga sarari ya yadauka, tare da sauke ajiyan zuciya yace salam tace kutuman uban salam jabir Allah ya isa tsakani na da kai,
ya lumshe ido yayi shiru, yana maimaita subhallhi Astagfullhi, masifan take har tana sarkafewa cikin raini da gadara anan ba abunda bata gaya masa ba sai dai ko daya baijin ta don tuni ya soma fahimtar zuciyan sa ta sauya akwana biyun da baya tare da ita wani na daban yake jin kansa ba soko ba. he's probably tired of her,
masifan ta ya soma ishen sa ..
Yace zuwairah yanzu akan kudi ne kike wannan masifan ?
Toh Ki je daki na ki dauka ai kinsan inda nake ajiye su..
Yanzu aiki nake yi in nagama zan kira ki bata kara samun daman tankawa ba ya kashe wayar sa baki daya..
Wani irin ihun haushi ta sa tana ciza baki idanun ta sunyi ja jir ,
Tasani sarai babu ko sisi ta riga ta sha maganin mata da su.
Shikuwa tunda ya kashe wayar sa bai sake kunnawa ba,
Sai chan dare daya dawo
Anan ma yaga jerin sakon rashin mutinci cewar ta kudin ya kare, he just cant believe that kudin dake gidan sa har sun kare don yasan suna da yawa alokacim samha ma kwata kwata bai taba cewa ta dauki ko sisi ba sai dai in shi ya dauka ya bata da hannun sa..
Bai son fitina a daren ya tura mata 10k
Bai kuma sake kunna wayar sa ba sai washe gari..
Ranar ena kwance Bayan kwana uku da faruwar hakan,naguda ya turnuke ni,
Lokacin har su anty hanifa sun iso
Anan babban asibitin kaduna aka kaini na haife santalelen da na namiji..
Kowa na murna,
Musamman dangin jabir don koma basuyi kasa agwiwa ba mumyn jabir ta aiko da mata har biyu niki niki da kaya irin na jego aka taho min da su
Anan waje ya rude da murna..
Elder sis da sis zainab ke faman kiran sa amma switchh off sai ta turo masa sakon na haihu..
Shiru shiru bamu gan sa ba bare kiran sa,
Washe gari da sasaffe sai ji nayi su anty da mumy suna gaisawa da shi a falor ana masa sannu sa zuwa..
Na sha mamaki matuka.haka ma mumy slamatu wanda tuni ta kasa boye maitan ta na fushi da shi..
Don koda ya zo duba ni a dakin da muke ina lura gaisuwan sa ma da kyar ta amsa..
Ya ce min yaya jiki na amsa mishi ba yabo ba fallasa..ya kuma cewa.,ko da akwai abunda nake bukata nace amsa a'ah.
Dansa ne a hannun Sa tuntuni ya kasa sauke wa kasa yayi nan yayi nan da shi..
Kiran da suka shigo wayar sa sunfii akirga
Su usman kaf sai da ya sa na amsa gaisuwan su
Ban taba kawowa ko dai dai na lokaci guda cewan jabir zai yi wannan rawar jiki Akan abunda na haifa ba..
Kwana biyu yayi anan kaduna tare da mu duk abubuwan dake kansa achan abujan,
Su mumy sai albarka suke sama sa ganin yadda take hidima
Da zai koma bakin aikin sa abuja wani sabon 50k ya ajiye min anan bayan uban kayan nama da kwamulashe da aka cika dakin da muke da mumy salamatu da shi,
Har ya tafi bai wani samu cikakken Sakin fuska waje na ba bare mumy salamatu, amman haka dai yake daureqa da alkwarin zaizo sunan dansa kafin ya wuce kano.
Ana ta shagali gida ya cika da yan uwa..anan mumy salamatu ta fara kawo nata tarzoman wasu mumy na
She make sure ta jadda da musu cewan duk tsiya anan gidan mu zan yi wankan jego sai kuma nagama tas tas sannan asan nayi...
Anyi sa'in sa kam ba laifi, don mumy na tun asali takan dauka cewa mumy salamatu ita ke daure min gindi nayi rashin hankali na yadda nake so,
Acikin wannan chakwaiyar har anty hanifa ta soma gano cewa akwai wani abu kasa tsakani na da mumy salamatu amma bamu fito fili ba..
Itama kawai sai ta sa karfi suka taru magana har wajen baba ya kai, sannan aka samu daga karshe aka ce eh na zauna na yi wankan jegon tun da haihuwar fari ne
Abun yayi mim dadi sosai.
Amma Sam abun baiyi ma mumy na dadi ba son ranta na koma da jabir chan kano idan ya dawo shagalin suna nayi jego a daki na...
Dan dolen zuwairah ta soma fita,amma ba wajen zuwa sai ta shiga neman layin mamam abdu
tana isowa anan ta samu ta dan ci abinci mai kwabi shinkafa da miya suka danyi hira
Tana bata hakurin cewa ai jabir bai dawo ba shiyasa bata biya ta kudin ta ba...
Matar tace babu damuwa ai anzama daya hajiya zuwairah...
Wasa wasa Tun da zuwaira ta samu sakin fuska shikenan ta nanike ma mata, yau ta jera kwana uku in ta taso a bacci sai ta wanke kafafu tazo ta bazu mata angida taci na rana dana dare sannan ta kada bujen ta tayi gidan ta.
Kullum dai Na ciki na ciki,
wannan karon kuma mummunan kulli ta ajiye a ranta game da jabir
tayi fushi sosai da shi don yanzu baya ma daga wayar nata hidimomin sa sun sha masa kai sosai gashi ko labarin haihuwan ma bata ji bare sunan
Wannan ma bai dame ta ba, karime har yau ba labari bata san kuma inda zatayi ta same ta ba
Har aka zo ranan suna
Aka sha hidima sosai na bajinta don ranar ya zo dai dai da ranar da jabir ya samu wani babban karin girma a wajen aikin sa sakamakon wannam project din dayayi...
Sanadiyar hakan na samu alkhairi sosai, harda kyautar mota bmw yar dai dai kuma sabuwa kar,.
Banda akwatuna da aka sake yimin daga shi daga dangin sa daga nawa dangin na tashi da set kusan goma sha hudu
Kayan yaro kuma ba a magana
Anyin komai cikin wadatuwa da godiyar Allah yaro na yaci sunan sa saifudeen...
Jabir bai wani daga hankali ba da mumy ta kawo maganan zan zauna wankan gida,
Don sosai ya soma jin wani yanayi na daban daya samu kanshi acikin kwanciyar hankalin kasancewa acikin yan uwa da dangi.
Tun bana son maganan yana zurfafa tsakanina da shi har na sake dan dole ina amsa shi don yanzu so yake ya cire guilt din karfi da yaji ya dawo da martaban sa a ido na..
Ranar da zai tafi ma haka ya jawo ni , ya kawo ni gaban sis zainab
Don sosai ta dena kula shi tun wancan lokacin akan zuwairah kuma basu hadu ba..
Haka ya rinka roko na akan na bata hakuri..
Ba yadda na iya na sa baki sannam anty zaynab ta sauko suka dawo dai dai..
Har cikin zuciya bana son wannam yanayin da shi.
Amma yau abunda na lura shine kamar jabir yana cikin wani halin da shi kadai yasan meke masa zafi...
Kafin ya isa kano, ya kira ni ya kai sau hudu..
Da naga abun nashi na so ya zarce sai na kashe wayata nayi biris na kyale tunanin abun ma raina..
Yau ma zuwairah batayi wanka ba, da shike batayi tsammanin zai dawo din ba kwance take tana latsa wayar ta.
Shikam dakin sa ya nifa
Duk dama Ko ena a wargaje yake ga dirty boxers dinsa anan daya tafi ya bari a sink ba a wanke ba,dama gaba daya shi baya kulawa sabida na sabar mai da wanke su sam bana tara kananan kaya irin haka,
Yau gashi yaje ya dawo ya same su anan inda ya bari karshe ma zubarwa kawai yayi,
Duk bata sani ba tana faman kokarin dube duben farjin ta, jini ya dauke kam tabbass amma wani orin ruwa mai wari yake fitarwa abun ya soma bata haushi
Tasan dai da chan tana tsami amma bai kai wannan ba..
Ko da suka hadu, haka ya sake dirar mata bazata duk dama da kyar da wahala ya shawo kanta, sai dai duk masifan da take yi bama ji yake ba,kuma bai amsa ba
Har ya kashe wutar gaban sa
Bata ko gaya masa cikin sa ajikin ta ya zube mata ba, damuwar ta ya ci ta yau ya dawo karban oders ,.. ai dama maman gayu tace maganin nan data siya na nan ajikin ta daram daram na tsawon lokaci.
Da safe ma With full confidence ta soma kawo masa romance..
Wani warin baki da ta huro masa ya sa yaki sam yayi kissing din ta
Haka dai ta daure ta biye masa
Ko da aka soma harka,
Tana ta iyo tana hawa kansa amma sai taji yayi shiru nishi kawai yake saukewa.
Chan tana sauka ya mirgina ya kwanta bai sake komawa..
Ta kama shi cikin shagwaba tace" meyeh hakan ya bamu kai ko ina ba zaka wani juya min bata...
Da mamakin ta ya mike tsaye, yace ki tashi dan Allah ki ke ki tsaftace jikin ki,
Haba da Allah.
Ke bakijin warin da nake ji ne gaba daya ya hana ni sakewa..
Ya ja tsaki alaman bacin rai yayi waje..
da Wani irin shock tabi bayan sa da kallo..tace tabb di jam
Ta mike tsaye ta biyo sa da uban gudu ba babu irin bugun da batayi ma kofar sa amma gam a rufe kuma bai bude ba sai da ya zo ficewa office.
A tsaye ta ke daram karfe 9 saura sai ga kiran maman abdu ,tace lpya kuwa zuwairah? Naga miscall dinki ..look imma zuwa zakiyi wallhy yau kam bana nan a gidan surkuwa ta na kwana..
Tace ah a ni bazuwa zanyi ba malama, dama na gaya miki ne zan kawo miki kudin ki an jima miji na ya dawo
Tuni ta washe tace ayyo, to ansha lagwda kenan amarya kike yau ashe zuwairah..
Ta dan yi tsaki tace , hmm barni da abun takaici, anan hira suka dan taba har zuwaira ta samo daman gaya ma matar matsalan warin da gabanta ya soma yi..
Matar tace mata ai wanka ne kawai bata samu ba.. Don dama chance take nema tuntumi ta gaya mata ta rika wanka akai akai ko wani kazantar zai ragu amma tana gudun rashin m
Tace kiyi wanka sosai ko durje kanki ki gani
Zuwairah Ba yadda ta iya bayan sun kammala wayar ta shirya ta shiga wanka
Ba laifi taji kanta daban.
Ta kimtsa taaf, shikam har ya fice yayi take away ya dawo da su..
Anan dakin sa ya baje ya ci ya na sha
Sam ransa bai masa dadi ba
Don ya lura babu ko sisi a dakin masa..
Da bankaman ta ta shigo da niyyar masa masifa amma ganin yaci magani ya sa ta sha jinin jikin ta ta tsime tarw da bata rai..
Kan ma tace zata kawo masa wani magana ya dago ya dube ta rai a bace yace "waya ke shigo min dakin bayan bana nan?
Tace nine kawai a gidan nan ko akwai wance ka ajiye ne bayan ni..?
Yace inda nace ki debi kudin kin deba.to ena wanda na ajiye a wardrob dina?
Ta murkuda baki cikom salon kukkuni tace na nan din basu ishe ni ba ne shiyasa na hada da na ko ina ma na cinye....
ya mike tsaye ransa a bace yace kina hauka ne zuwairah?
I tot fitinan ki ya sa kike ce babu kudi agidan na ashe abunda kikayi min kenan..
To bari kiji daga yau sai yau kar na sake ganin ki anan dakin..yayi mata nuni da waje a fusace " my friend get out ya daka mata tsawa..
Tace kutuman uba?jabirrrr mani kake gayan ma wayannan maganga nu
Yace kin fita ne ko sai na wanka miki mari.
Wani irin mamaki mai dauke da farhaba ya sa jikin ta rawa ta kasa cewa komai ta buga tsaki ta kada kai a zafafe alaman na san maganin ka..
Haka ta danne zuciyan ta ta koma daki tana sake sake duk ta sa a ranta cewa Ai dare zaiyi zai ce zaizo kuma sai ta masa wulakncin kare in yace zai taba ta
Shikuwa ya na gama komai ya ajiye mata take way ya kara da gaba..
Har wajen 9.30 na dare bai dawo ba ta hakura ta koma daki.
Nityn ta sake sawa tana jiran sa har past 12
Ganin bazai zo baa Ta dada yin wanka kamar yadda maman abdu ta gaya mata gudun kar amaimaita irin na jiya..
Shikuwa yayi liff Tunani na me fall cikin ransa saboda sam bana sake masa fuska ko awaya ne baijin dadin yanayin yadda anke nuna bana son na saurare shi kuma gashi sosai zuciyan sa take neman karkatuwa waje na yanzu
Daga kwance ta tarar da shi ,idonsa alumshe
Cikin salon ta na makirci ta hauro sama zata fada kansa ya mike ya zauna ya dan turo ta gaba baice uffan ba
Fuskan da ya sa ta dan yi slow ta kasa kawo kisinan tace yau kuma anan zamu kwanta ne desire..?
ko fushi dani kake har yanzu
Yace just shut up bana ce kar ki sake zuwa min Daki na ba..
Tace haba desire yanzu akan kudi ne kake wani bata rai
Pls stop it mana ta shiga narkewa tana zame hannun nityn ta,tana yuwowa kansa
Da haka ta ja hankalin sa yana yi yana basarwa duk dama ta so ta dan masa irin na wulakancin data saba kamar da amma ganin ya kwayance ya sa ta dau matakin hakan.
Suga shiga romancin juna
Anan ma sam yaki ta sa masa bakin Ta ana shi..
Yaune ta soma gane wani abun da ya tayar mata da hankalin matuka
Jabir yi kawai yake amma hankalin sa baiya nan sai taga ma ihun datake yi baya amsawa sam ranshi babu dadi..
Yau Ta kasa ganin wannan zaucewa sa radadin kuwwan dadin da da chan yake yi har suka ci suka kare bata ga ne masa ba
A daren ta kasa bacci,.jifa jifa tana daga sa yayi wani bin tayi ta magana yayi shiru kamar baiji ba..
Qashe gari da safe ma hakan ne
Tun kam ya fice yake tashin ta sallah amma tayi burus da shi
Ya idar da sallah ya dawo ya kwanta cike da haushin ta.
Yana cikin fushin Ko wani minti 30 baiyi da runtsawa ba da ya shago wani gwamutsen warin baki baisan lokaci Daya yi zillo da ita daga kansa tayi kasa ba...
A hatsale yace bana ce ki je kiyi wanka ba? wannan wani irin bala'i
.. Zata yo magana Yace
Get out ki duba ko sallah bakiyi ba zaki fara neman fitina..ki fice min anan kar na tattaka ki
u disgust me ya fada kasan makoshin sa ,jabir haka kawai yake jin babu dadi aransa kamar wansa aka tunzira shi.
Tsananin mamaki da Tsoro ya sa ta razana ta wuce dakin ta da dan uban gudu bata ce komai ba..
Kuka ta sake ta fashe da shi ta dire kasa ta ce na shiga uku..
Ko dai maganin nan ya warware ne ?
JaBir ne wannan
Ko sauya min shi akayi
Ta daura hannu akai tana kuka kamar aka mata tsinnanen duka
Har ya shiya ya fita basu hadu ba..
Haka suka ci satin gaba daya bata gane jabir ba
Zai kwana da ita suyi sex ishasshe kam amma in banda hantarar ta ba abunda ya koma yi yanzu.
bayan sati biyu tayi zugum tana tunanin meke faruwa da ita
Gashi matan nan ta sake kira da kyar jabir ya biya bashin da taci.
kudin da ya aika mata 10k da chan sune kawai da ita aciki kuma saura dubu 6 da dari biyar
Ga shi yanzu ya dena sake mata ko sisin sa, as punishment na kwashe masa kudi a daki
Yanzu ma cewa yayi idan bazata koyi abinci ba shi ba ruwan sa,
Shi daii yanzu ya iya cin abinci awaje har ya soma sabawa
Da abun ya ishe ta Dan kudin datake dannwqar Shi ta dauka ba wanka ba wanke ido
Tace maman abdu gata nan zuwa
Anan ma karya ta buga mata akan cewa mijin ta ya sake tafiya kauye cikin sati amma yau zai dawo
Yanzu ita dai araka ta gidan maman Gayu tana da tambaya...
ba tayi musu ba
Takai ta har gidan maman gayu..
A mutunce ta karbe ta don tasan tana caskar kudi wajen zuwairah bana wasa ba.
Anan zuwairah ke kawo kukan ta na cewa bata ga canji ba.. Sai ma sabanin haka
Har ta gwamma ce maganin da karime take kawo mata da cahn fiye da wannan
Manan gayu kam cewa tayi ai maganin ne bai karbe ta ta kawo wani dubu 100 za'a hada mata wani maganin mallaka mai karfi
Anan ma still ta samu yan sa baki suka dada zuga ta, wasu matan suka ce mata ai dama idan kayi jinin haihuwa yana karya karfin maganin mata saboda haka tamkar daga farko zata sake shiri ..
She was convinced,amma ai jabir yana jin dadin ta ,
Kawai halayan sa suka sauya tayi nazari aranta amma Sai kawai ta basar ,
Tace ko da bura uba zata karbo kudin aiki azo a sake hada ta da cahn ai shima yana bata kudin siyan kayan aiki why not now?.. Tafada tana tuno yadda tayi shagali a danyen amarcin ta
Da haka suka koma gidan tayi zaman diris tana jiran sa.
JABIR FOR MAMUH GEE FOR LOVE😹😹😹
_SURAYYAHMS_
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top