FINALE
*🍒🍒SAMU YAFI IYAWA🍒🍒*
_Pasaage 20 FINALE_ .
Ko da na fita zuwa gida don na sami jabir, anan ne zuwairah ta samu dan bakin magana" cewa tayi a kira mata doc.yana zuwa kuwa anan ta yi masa tambayoyi akan abunda ke damun ta
sam likitan ya ki cewa komai, amma haka tayi ta nace wa, a haka ma da kyar don ya so ace mijin na ta ya soma samu amma sai ta birkice masa dan dolen sa ya shiga mata bayani ...
Anan ta fahimci cewa fa ta samu wani babban matsala ne da mahaifar ta bazai taba rike ciki ba sakamakon wasu maganin da ta sha su a da chan marasa inganci wanda suka tara mata sinadarin da yayi sanadiyar gurba ta jijiyan da yake rike da mahaifan ta,
Gaba daya idan ciki ya shige ta bazai wuce 2 3 month ba zai kwabe...
Haka yaki fir ya gaya mata sauran results din ya bari aransa sai jabir ya iso,
Ko da muka iso asibin Nikam ina daga waje a kayi musu bayani shi da ita
Doc yace"She is diagonised with cervical cancer da kuma wani dan gulando a bakin farjin ta sai dai baiyi tsamari ba amma yana dab da dawowa wani babban ciwo...
Sannan doc ya gaya masa zai daura ni da shi da zuwairahn ma duka akan maganin infection wanda akasari aka fi samu jikin zuwairah,
A cewar sa don maybe muna tsaftace namu wajen yasa baiya nuna wa sosai amma idan aka yi sake wata rana sai muga muma muna fama da shi kamar ita zuwairahn .
anan ya rubuta kudin jinya da dan aikin da za'ayi mata da sauran su sannan ya bata shawaran ta hakura da shan duk wani magani in ba wanda za bata yanzu ba....
Zuwairah Tunda aka fara bayanan take kuka tana kukkuni,shikam jabir sosai abun ya taba zuciyar sa...
Sai kawai ya yanke hukuncin cewa toh a cigaba da rike ta ana bata kula zuwa monday zai bada isashhen kudi a soma mata full treatment,
Ita dai zuwairah kuka take har yanzu bata ce komai ba har suka fito kwata kwata ta share kowa ta hade rai bata dago ta dube mu ba,
Musamman da jabir ya zo yana maida min maganan doctor agaban ta..
Muna jimantawa muna dada bata karfin gwiwa
Acikin zuciya na tausayi ke dawainiya dani amma Sam bamu san cewa ita a ranta ba haka bane,
tuni ta kaw cewa duk kisisi na da munafurci na ne Yasa aka shirya wayannan maganganu akan ta
Tunanin ta tunda ni na kwana da ita asibiti its obvious ni na shirya ma doc duk karyan nan daya fada musu don ya raba ta da mijin ta jabir,
Baifi awa 3 mukayi mata ba, Haka jabir ya sa muka koma gida duk dama banso ba, anan ma na dan ja hanlakin sa da nasiha akan abubuwan da suka faru
A raina Ni na dau alkwarin zan ja ta sosai ajiki na na koya mata sauke kai da tausasa murya da duk wani abunda take lacking,
shi kuma sai na roke sa ya rika mata uziri har Allah ya sa ta gyara..
A tunani na hakan da yake mata ba zai kaimu ko ina ba dole mu hadu mu taimake kan mu...
To alokacin da na kawo maganan Ni dai ya gwada min ya gamsu..
Don har naga canji a washe garin da muka koma asibitin da safe sai naga zuwairah ta nace zata dawo gida kawai tare damu...
akan tana mafarke mafarke anan asibiti.. Toh baiyi musu ba muka dawo din
Haka taayi ta zaman kurmaye da mu
On Monday ya dau kudi dubu 250 kamar yadda likita ya rubuta ya sa a mota tare da ita zasu je asan abun yi
Ni dai fatan sauki nayi mata na raka su har suka bar gidan,
"Daga hanya ta ce masa ya taimaka ya siya mata pad kamar tana jin jini yana sauko mata,zata tafi da shi in yaso in sunje asibiti sai ta samu ta sauya a toilet,.
Anan ma baiyi musu ba ya sauka ya barta a mota,
Minti 5 mai kyau bata kara ba ta kwashe kudin gaba daya ta wuce tasha motar ma bai cika ba ta biya kudin sit aka cahle da ita maiduguri..
Ko da jabir ya dawo bai ganta ba sai ya dan saurara amma abu yaki ci yaki karewa har ya hankara ya fara neman ta..
Neman duniyan nan jabir yayi amma bai same ta ba,
Sai dai daya zo ya zauna cikin mota yana shir8n kai case din station anan ya lura da ita ta dauke kudin ta waske, don har jakan ta bata bari ba abun ya kulle masa kai sai ya kasa gane manufar ta na yin masa haka..
Ba shi ba har ni na da mu..
Ga wayar ta na dhiga amma bata dauka,
Anan maiduguri ita kuma taje gidan su babu kowa anan ma gidan su karime hakan ne ance mata inna zulai na chan taraba karime ta samu sauki har an sake mata aure suna wajen bikin tun shekaran jiya..
Ta sha mamaki kam amma sai ta basar Kawai ta fanjama neman malam mai mallaka
Idon ta arufe
sai daii bata same san ba sabanin haka Yasa aka mata kwatancen wani waje na daban
Anan ta je taga mata tatil irii iri suna layi akan tabarma a zauren gidan itama ta bi layi har Allah Allah take kuma azo kanta..
Duk dama munsan da qamshin cewa zuwairah da sannin ta tayi hakan bai hana hankalin mu duk ya tashi ba,
Musamman ma ni a daren Da kyar muka samu muka runtsa...
Da safe bayan an idar da sallahn fajr sai ga kiran ta,
Seif baida lpya nima yanzu nake idar da nawa Sallahr ko mikewa banyi ba ,saiga shi ya shigo daga masallaci agauggauce ya nayi min hannu alaman naji abunda zuwairah ke fadi don ya sa ta a handsfree
Anan take gaya masa dalilin ta na tafiya akan bata yarda da abun da doc ya fada ba, shima kar ya yarda da hakan ai kawai makirci na ne kawai,
kuma ya gaya min tafi karfi na, don zata ta amshi matsayin ta a gidan kamr yadda na sani...
Abun sosai ya bata ma jabir rai ,bai taba tunanin dabbancin zuwairah yakai haka ba...Jabir yayi zuciya zosai ya haura mata da fada tana yi yana yi duk suka kidima ni da musu da sai'ns har yana bari yana kumfar baki,nikam na sha tsinuwa da zagi abakin ta,..abun babu dadin ji karshe sai da nayi masa kuka sannan ya nitsu ya saurare ni, acewar sa shi sam ya turje shi zai saki zuwairah that minutes ya huta maran sa.
Abu yaki ci yaki cinyewa har akayi kwana biyu bata dawo ba
Har aka ci sati guda,
Gashi zata kira ko sau dari ne sai ya dauka sun yi ta yi..Anan ma sai da na hada da su umma mahaifiyar sa sannan Jabir ya hakura ya barta hakan nan
Itama umman data ji bayan nasa akan abunda zuwaira tayi cike take tamm da zuwairah tana jira ta dawo
Dangin sa kuwa ba wanda bai tofa albarka cin bakin sa ba..
Wasu har da masa gori akan auro ta dayayi tun farko dama basu yaba ba,
Abubuwan sun faru da babu dadin ji..
Ranar juma'ah anan kan sauraron ta don yanzu kam kowa yasan tana maiduguri
Ranar Jabir baya nan don tun safe ya fice yana chan wajen interior decors ana jere a sabon gidan mu da ya gina,
Anan cikin haka aka sanar da shi baban zuwairah na neman sa..
Abun ya bashi mamaki amma,tunanin sa ko zuwairah ya dawo da ita a sasanta.. Bai yi niyyar zuwan ba amma sai ya daure ya je din
anan baban zuwairah yake sanar da jabir jiya da daddare fa an kama zuwairah turmi da tabar ya da malam mai mallaka,
tare da sauran mata customers da ake lalata da su da sunan basu magani,acewar malamin idan ya kwana da mace ne kawai zai gane siffar yada zai tsara mata magani..
A halin da ake ciki sauran matan suna na kulle a cell
ita kuma zuwairah da malam suna nan a garkame anan za'a zantar da su gobe a kotun sharia, kotu zasu yanke musu hukunci bisa tsarin addini dama chan rashin hujja ya sa ake zuba masa idi amma jiya sai Allah ya cika masa mugun kaidin sa....
Jabir Yaji bakin ciki bana wasa ba, ba don komai ba sai dan tunowa da yayi zuwairah ta amsa sunan matar sa na sunnah...
Haka dai ya daure Bai yi wani reaction ba ,amma sikinini ya je ya dauke kawun sa da kanin sa sa salihu suka kama hanyar maiduguri a ranar ba jira
So nikam ma bansani ba sai da ya isa chan dare yake gaya min yayi nisa da mu amma zai dawo gobe.
haka suka kawana a maiduguri washe gari
Har inda aka tsare zuwairah yaje ya sameta,..ta na hargowa tana surutan bakin ciki da borin kunya, bai kula ba ya bata sakin ta daddaya har uku...
Bai ma jira jin hukuncin da aka yanke musu ba
Ya juya kan mota suka dawo kano...
Abakin salihu kowa yake jin labarin abun da ya faru.. na jimanta sosai sai na ji gaba daya duniyar nan ba komai bane face miiraji ma yaudariya ga wanda ya bita da imanin sa..
Amma nayi addu'ar Allah ya sa hakan shine mafi alkhaiiri a gare ta damu baki daya..
Wasa wasa muka koma sabon gidan mu Shirgegen gidan sama ne mai hawa uku... anan muka baje sabon salon zamantakewar mu cikin tsaftataciyar soyayya da girmama juna.
A ciki na na biyu dana haifi y'a mace saudat.. jabir sai da ya siya min mota mai taken nissan maxima yar dai dai mai aji..
Muna zaman mu cikin aminci da godiyan Allah.
_Alhamdullihi_ 😆
_kuskuren da yake ciki Allah ya yafe mana ya kuma bamu damar amfani da positive lesson dake ciki..nagode wattpad._
_SURAYYAHMS_
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top