who is he

*🅱RILLlANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™\jan\2019
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
_The scorned_
🍒🍒
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@  SURAYYAHMS*

_28.._

Abun bai daga mata hankali sosai ba, sabida tasan maybe yar fushin nan Ne daya saba idan bata bashi attention dinsa ba,..

Hakan ya sa ta koma bakin aikin ta tana yi tana gwada layin sa amma babu wani sauyi,

Haka har ta tashi daga aiki ta koma gida bata ji shi ba.

A chan bangaren yazeed kowa haduwar su da zulkhi ya sa ya tambaye sa yadda za'ayi su samu tarihin sarah da mahaifiyar ta a garin kano shekaru da suka wuce.

Ya nuna masa hotunan sarah da na ummahn ta,

Sannan ya bashi dan detail din da ya samo daga binciken sa  akan ummah da shekarun da ummah ta zo lagos.

Toh shi zulkhi shiya binciko musu cewa ai gidan kaji da gidan gonan da umma ta mallaka na shahararren Mai kudin nan ne alhaji abdul azeez shayal...

Daga nan yazeed ya sha dammara suka wuce kano ba bu wanda ya sani,suka shiga neman diddigin labarin ummah dana saratu..

Da kyar da wahala suke samun bayani daya sabida rayuwar su sunyi shi ne a cikin sirri  wanda akalla sahura ce kawai ta san komai..

Amma da shike abubuwan mamaki da yawa sun faru, a ko yaushe idan wani sirrin ya fito sai ya dada sa ma yazeed din son yaji karshen bayanin..

Yanzu haka har kudi ya biya ana nema masa inda zaiji gaskiyan lamarin rayuwar su.

Anan kuma lagos sarah day by day tana shiga tashin hankalin rashin samun yazeed

Tunani dayawa ta kawo aranta nacewa ina zai je wanda har iyayen sa basa zu sani ba

Don ta tambayi kowa har gidan sa taje amma shiru babu shi ba labarin sa

Gashi yau ya cika wata guda chasss bai dawo ba.

Shikuwa da sannin sa yake yin haka ,so yake ya kwaba mata lissafi
Don shika dai yasan me ya ke shirya mata one big time...

Haka ta lalace da tunanin sa, bata iya cin abinci sosai bare bacci,

Saukin abun ma shine yanzu hapsy ta dawo nan branch din ta..

Ita kanta hapsy tausayin sarahn ke damun ta
A ko taushe da duba wayar ta sai taga dialled calls din yazeed yafi a kirga

Har ta gaji ta sa ta gaba tace,sarah dan Allah ki sassauta makan ki mana,
Ai inda ya damu dake bazai bace miki rana guda kiyi ta neman sa baki same sa ba..

Please this is getting too much baki ganin yadda kika dawo ko?

Abun na damun ta sosai duk dama kullum idan hapsy ta kawo magana bata tankawa yau kam sai taji dole ta sawwake ma zuciyan ta ko zata samu saukin zafin da yake mata.

Tace hapsy wallhy na kasa ne,kaina ya daure
I just cant hepl it na shaku da shi sosai...sai ta dan fara sauke hawaye..

Hapsy na shiru itama din tunani take yi,chan ta taso ta zo kusa da ita ta dafa ta
Sarah"?
Dago ki kalle ni,

A hankali ta dago.

Tace kina son yazeed ko?

Wasu hawayen ne suka taro mata lokaci guda tace eh hapsat ,ena son shi..kuma nasan shima yana so na
But we dint make it official

Hapsat tace ohhh crab .. now thats your problem,ya za'ayi ku rinka azabtar da kanku haka? Wai shin baku aminta da son dakuke ma wa juna bane ko yaudarar kanku kuke da bazaku furta shi ba?

Idan dukan baku bar wannan wasan banzan ba fa zaku yi illah ma zuciyoyin ku.

Cikin kuka ta ce to ni ya zanyi hapsy,nice zan ce ina son shi ya aure ni,ko shi zai fara fada min haka.?

I just dont get him...kinsan kuwa ranar da na vata masa rai ma haka nayi ta neman sa ban same sa sai daga baya ya zo yana gaya min wai bazai iya jure rashina kusa da shi ba ne"

I think don ban samu time dinsa sosai kwana biyun nan ba yasa ya tafi ya barni,this is tooo much for me
Yau kusan wata kenan Ban sake ganin sa..
Im feeling the pain i love him sooo much..

Kuka ta keyi sosai har da kife kanta akan teber gwanin tausayi..

Itakan ta hapsy yanzu tana cikin rudani

To wannan wani irin salon soyayya ne sarah ta dauka makanta..

Nan dai ta shiga rarrashin sarahn tana bata baki har ta nitsu tare da bata karfin gwiwar cewa tabbas akwai babban dalilin da yasa yazeeed yayi haka

Idan kuma ta yadda da yana son ta tayi hakuri ta bashi dama.

A cewar hapsyn maybe yana cahn yana shirya rayuwar su ne yadda idan ya dawo sai taga komai ya wuce..

da haka ta samu gwarun gwiwa

Amma sai dai kamar ko wani rana kara mata zafin son sa ake yi aranta

Kewar sa duk sun nakasa hanyoyin jinin ta,tunanin sa ya gauraye brain din ta..

Sometimes ji take kamar ta hadiyi ranta ta mutu
Da bakin cikin rashin sanin inda yake da dalilin sa na boye mata..

Haka rayuwar ta kasance
Hapsy ke jan ta da nasiha da shawarwari har ta samu tana sakewa

Kowa anan offishin sai da ya gane cewa rashin yazeed sosai ya taba walwalan sarah.

Wasu har tunanin yadda zasu faranta mara rai suke ganin yanzu sam bata samun peace of mind.

Shikuwa yazeed cikin wannan kwanakin suka bi hanya hanya har aka kaisu gidan sahura na da chan.

Anan aka basu labarin zuwan su da rayuwar su, hatta yadda akayi raping ummah agidan alhji sabo ya sani..sai dai suma cewa sukayi basu san inda suka koma ba

Har sai da suka hadu da wannan saurayin da da chan yake zuwa wajen sahura,

Shi ya basu labarin cewa ai ssa danjuma shi sukayi ma aiki

Yasan shi amma baisan inda yake ba yanzun

Daga nan su yazeed suka shiga neman adress da information akan ssa danjuma

In the process suka gane ba mutumin arziki bane, sannan ga sana'oin sa.

Anan yazeed ya san ummah tayi aikin strip club tun kafin ma yaji daga bakin ssa danjumA.

Toh aranar da suka hadu da shi,.aranar yaji sauran sirrin saratu da ummah don kuwa yayi playing cards din sa sosai akan ssa danjuma  har ya samu jin Tun daga farkon haduwar sa da ummah
Da duk wani taimakon da ya mata a rayuwa ita da sahura

Sai dai iyakan sa daya hada ta ogan sa bai san ya suka kare ba....

Shima yazeed anan ya dakata da jin labarin nasa sabida jin ance ai alhj abdul azeez ya mutu

Samun wani information akan sa kuma zaiyi wuya
Tunda har shikansa Ssa danjuma bai sani ba...

So, yanzu yana da masaniyar duk wani rayuwar ashah da zubewar mutuncin da ummah tayi akan sarahtu

He just concluded dat tunda har ummah zata iya rawan kan karfe a club ana bata kudi..

To tabbas kwana take yi da alhj abdul azeez

shine ya bata dukiyar da take juyawa yanzu..

Its so clear to him,
Kenan shiyasa ummah ta samu share akan gidan gona da gidan kaji,kenan ummah karuwa ce?

Abun na matukar shakin kwakwalwar sa
Yana jin Tunda aka haifesa bai taba jin yanayin mamaki da tsanstar nazari kamar na yanzu ba

A ko wani dare sai ya yi tunani daban daban akan su..

Sai dai bai kyautata tunanin sa akan su ba ko kadan
Musamman rayuwar ummah na baya..

Ya  dauki lokaci mai tsawo yana shirya kansa da plan dinsa wanda daga shi sai zuciyan sa suka sani.

Sai dai wani abu na damun sa,sosai yake jin kamar zuciyan sa tana tsananin kewa da son sarah..

Wani bin idan ya kawo tunanin haka sai ya sha giya akai ya fice hankalin sa Yayi ta dariyar da shi kadai yasan ma'anan  ta

Yana nan agarin kano abokan sa kuma suna sane da hakan amma ba wanda ya sani bayan su

A yanzu haka ma shiri yake na tarban su ranar juma'ah ya gayyace su akan Zasu zo masa weeknd Dukan su.

Faisal ne mafi kusanci da shi, dan gidan senator ne
Shine kuma yafi comunicating da sarah
Akan bacewar yazeed din

Sai yaji nata sai yaje ya fada ma yazeed din  abayan idanun ta....sometimes har rercoding zaiyi ya tura masa yaji suna dariya..

Sukan su sun sha masa tanbayar ko dagaske yake akan maganan sarah..

Amma har yau yaki fitowa fili ya gaya ma kowa mai yake tsakanin sa da sarah na asali

Bare kuma nufin sa.

Bayan azuciyan sa shikansa fighting yake da yanayin rayuwar sa da sarah amma yaki ya fuskance gaskiyan hakan

Labarin sarah dayaji abun al'ajabi ne kuma abun tausayawa ne,.but sai yaji babu hakan aransa.

Bai san zafin abun ba sabida a labari kawai yaji,bai san me ake nufi da qaddara ba sabida mummunan qaddara bai taba rabar shi ba bare iyayen sa..

Bai san me ake nufi da bakar talauci da cin zarafin mutunci ba sabida rayuwar sa tun da ya taso acikin girmamawa da karamci ya ke ganin sa

Sai ya kasa bada rayuwar sarah da ummah wannan uzuri..
Gani yake suna da laifi akan dukan abunda ya faru da su
Infact su suka so hakan ya same su...
But how cud he be this judgemntal

Hmmm duniya kenan,dama bature yana cewa" ppl only judge you from their own point of view " ba haushe kuma yace
Yadda mutum yake kallon kansa haka zai kalle wani..

Toh ranar friday da su faisal suka zo kano wajen yazeed.

Shikansa yaji dadi sosai sabida tunanin sarah ba wai yana barin sa bane,.amma kullum acikin shan giya yake din ya karya ta cewa ya kamo da son yar karuwa.

Daga nan kuma tana nan tana fama da zaren son sa dake ninkuwa bayan kowa ni jan numfashin ta a duniya.

Hotun sa ne gaban screen din wayar ta

Cikin dare kullum sai ta karance chats din su tsaff ta bi tana karanta tex messge dinsu tana yi tana hawaye tana murmushi alokaci guda cike da kaunar sa..

Yau yana neman cika wata guda da sati..

Zaman su faisal anan suka kusan sauke gidan da surutu da kide kide da shaye shaye...

Anan ana shan shishan nan hayaki da warin giya ya gauraye su ana ihu ana surutu

Wasu na buga game ana ta shagali.

Faisal ne ya Kawo zancen sarah,sabida sun gama lura da yazeed a dame yake amma sai yana boye wa da buguwar giyan daya sha.

Don su sa shi dole yayi magana suka haura masa dukan su da tsiya
Mai ban haushi

Cewar javeed soyayyar sarah ya sa zaki buya abun mmaki
Abun tun yana wasa har ya fara dawowa na bacin rai
Sai Ya musu bayanin shi ba wata sarah a zuciyan sa amma sai tunzira shi suke yi

Musamman faisal da ya sake ya na bayyana wa gaban kowa don suji maganganun da sukeyi da sarah  a wayah cikim kwanakin nan

Sai ya zamto sun maida shi kamar mahaukaci

Ransa yayi matukar baci da suka daura masa cewa lallai soyayya suke da sarah bai fito fili ya gaya musu ba..

Haka ya sa ya sa makudan kudi har kimanin millliyon 20 akan bet mai taken

"Game of love"

Sun sha mamakin da sai da ya sa suka yi shiru suna jin sa..

Yace" nan da sati biyu game din zai kare

Zai gwada musu abun mamakin da su kansu bazasu taba tsammanin sa.

He wll become a lion in the eyes of all ladies
Idan haka bai faru ba ya basu kudin daya sa yanzun duka.

Jin haka ya sa suka amince, amma sunsha mamaki...

Kowa kuma sai ya shige kogin tunanin me zai faru?
Good or bad?
Me zai yi ma sarah..
whats is the suprise worth 20million

A haka suka bar kano da zullumi gashi ko faisal da ya same shi in private sukayi magana

Yaki sanar da shi me yake shirin nuna musu akan sarah..

Su dama damuwar su kawai su san gaskiyar sa amma Basu da wani nufin na daban..

Haka dai suka rabu ya kuma sanar da su ranar dawowar sa lagos..

Anan bangaren sarah kuwa,ba laifi sai da raman rashin sa ya nuna
She became quiet and cold

In kaga tana magana toh hapsy ce ta zo ta same ta..

Agidan ma ummah sam ta dena gane mata

Ita kanta sai da ta soma tunanin rage haddarin son yazeed daya addabe ta don ta samu nitsuwa

Ya mata wahalan sosai wajen yanke wannan hukuncin amma dan dole ta bar komai ma ranta tana dada kawo wa cewa..
Hala akwai dalilin daya sa ya bace..alherin sa kawai take roka wajen uban gijin ta yanzu.

A ranar data soma sawa ranta zata cire yawan tunani
Ta fito cikin shirin ta mai kyau da tsari tana tafiya cikin sanyi da rigima

Dai dai kofar shigan ta office tana daga ido suka hada ido da shi......

Lokaci guda ta tsaya"Ji tayi kamar zata sulale kasa tafada don mamaki

Lokaci guda jikin ta ya fara rawa da kansa
Ta kure shi da idanun ta tana sauke faffadan murmushi

Sai ta rasa Murna zatayi ko kuka
Ihu zata tsala ko dariya zata yi?

Shima tsimewa yayi yana duban ta,shikam sai da ya sa hannu ya share dan guntun hawayen sa..

Basu da wani nisa sosai

Amma bugun da kirjin ta take yi bai hana shi gane wa

ba wanda ya tanka tsakanin su sai aukin murmushin da suke aikowa juna...,
ta dade da sumewa cikin idanun sa tana kallon murmushin sa mai cike da kalamai da yawa

Shikuma yana duban yadda gabobin ta suka taso gaba daya cikin tsananin farin cikin ganin sa.

A take ta rugo aguje tayi kansa tare da sake wasu zafafan hawaye.

Ko da ta fada jikin sa taji ya rungume ta sam sai ta fashe masa da kuka mai shiga zuciya...



*To waye wannan din?*




*Official cat*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top