Victoria 2
*🅱BRILLlANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™\jan\2019
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
_The scorned_
🍒🍒
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*
_HASBIYALLAH WA NEEMAL WAKEEL_
_20_
a kauyen Sosai sarah tayi nasarah wajen shawo kan mutane sabida itama tayi zaman kauye don haka tasan duk wani lugga da siga na shawo kan mutumin karkara..
Bayanai ta hado masu kyau wanda bugu daya zai nuna innocent din mahaifiyar dije..
Sai dai lokacin flight din ta bai barta ta jira sun ahirya gaba daya ta tafi da su din ba..
Sai ta bada kudi isashhe akan gobe ataho mata da su su ukun har da malamin rukiya lagos
jibi da yamma za'ayi din a office
Har ta iso lagos ba wanda ya sani sai ummahn ta da aljan dake kan aikin lura da duk wani motsin ta kamar yadda hajya asma ta gindaya masa.
A bakin hapsy yazeed yaji cewa sarah ta na yola... bayan news din rasuwar mahaifiyar dije ya wanzu cikin kunnen su..
Gaba daya sai hankalin su ya tashi sosai..
Tunanin su a Yanzu ya za'ayi kenan asalin wanda ake shariar akanta ta rasu?...
Shikan sa yazeed yau gani yake kamar case din zai dan bada sarah wahalar don hes very sure hajya asma and mrs ruth has something to do with it smh...
Duk dama bai kawo aransa su suka sa aka mata alluran ba..
Tsakanin sa da safeenah yanzu abun yayi sanyi sabida kullum acikin kona ta yake da halayen sa,sai ta rika ganin kamar hankalin sa nakan sarah amma wani fannin sai ya nuna mata kishin ta ne kawai ..
Sosai ta shiga wani irin haki da zuciyar ta komai ya cunkushe mata amma bata iya ganewa..
Kiran hapsy ne ya soma shigowa bayan sarah ta sauko,
Ita ta sanar da ita abunda ya faru na rasuwar mahaifiyar dijenh.
Tsaban yadda ta ji ba dadi sai da ta nemi waje ta tsaya ta dafe kai tana hawaye mai cike da tausayi..
A lokacin sai Bata je gida ba san da taje ta duba gawan ... sannan ta ba da dije karfin gwiwa sosai kamar yadda mahfud ya koya mata.
Ko kadan batayi noticing din wanda ke bibiyan ta ba.
Tana tafiyan ma tunanin rayuwa kawai take,
A yau Hapsy ne kawai tasan cewa ta samo shaidu masu amfani.
Washe gari Da safe kamar mai zazzabi haka take jin kanta haka taci ranar baki daya bata iya ayyana komai ba in banda aikin lallaba zuciyan dije da bata karfin gwiwa..
Da yamma sai ga aljan ya kira su hjya ya sanar dasu cewa shaidun da sarah ta nemo sun iso...
Anan ma tace masa good..
Tunda sun iso yanzu zai iya aiwatar da aikin da suka bashi akanta.
Sarah kuwa Masauki ta sa aka basu sai dai bata samu daman haduwa da su ba akan sai goben kawai karfe
3.00 dai dai a wajen sharia zasu hadu.
So washe gari da safen
Batayi niyyar futa da wuri ba amma sai aka dame ta da kira cewa ta zo dije bata da lpya.
Yadda ake magana awayar gani taje kamar dagaske dije na wani hali..
Duk sai ta soma tunanin ko dan mutuwar mahaifiyar ta ne har yanzu ke damun ta..
Dama tasan zai dauke lokaci kafin ya sake ta...
Ta san an zalunce ta.
Haka ta shirya agurguje sukayi sallama da ummah ta fuce,
Tana kama hanyar gidan da su dije dake a dai dai kwana nan wasu motoci manya guda biyu suka shakure ta suka tunkuda ta cikin nasu suka tafi da ita..
Lokacin karfe 9 saura ne ma safe..
ko da ta dubi mutanen motar duk maza ne kuma bata gane ko daya acikin su ba.
Wani gida suka kaita, suka daure ta kan kujera na tsawon awa 3 ba wanda ya lekota
Daga bisani chan wani ya zo ya mata allura ta tafi unconcious..
Bata sake sanin inda take ba
Har lokacin sharia yayi babu sarah..
Kowa ya hallara babu ita sai kiran layin ta ake amma taki dagawa.
Shi kuwa yazeed nitsuwa yayi yana duban yadda kowa yake nasa bambami don yasan dole akwai abunda ya faru..
Mrs ruth ce kan gaba wajen sake kawo maganan kankatar sarah ma aikin nan..
Ita kuma hjy asma take cewa hala don taga mahaifiyar dije ta rasu ta ke ganin bazata iya facing case din ba..
Anan ba irin maganganun da basu akawo ba ,...mafi akasari suna dangan ta shi da cewa ai yaranta ke damun sarah...
Ta ajiye su tana wasa da hankalin su..
Abu tun karfe uku Har wajen karfe biyar saura ana jira,
Sai yazeed ya zame ya je gidan su.
Kamar ba abunda yake damun sa ya gaida ummah ya kuma gabatr da kansa ,amma bai fito fili ba
Anan ya nuna mata cewa daga kasar waje ya diro yanzu yana so ya san inda sarah ta ke don yaje ya same ta yana da muhimmim aikin da zai bata...
Ba laifi ummuh ta gaya masa ai kiran ta akayi a gidan su dije..
Abun ya bashi mamaki amma Ko kadan bai nuna tashin hankali akan face dinsa ba ya ke tambayar ummah, a haka har ya kama hanya yayi hanyar gidan su dijen.
Yana dosu kwana yaga wasu maza na kokarin tsallaka titii sai leke leke suke...
Ya sa ido yana dan duban su with less serioussnes sai ga shi chan dayan ya fito a cikin motar sarah suna kokarin barin wajen
Da shi..
Mamaki ya hana sa cewa komi sai ya batar da kaman sa ya shiga binsu tsala tsala..
Wani gida suka shige bayan kamar mintuna 10 suka sake fitowa amma wannan karon babban jeep ne sai motar sarahn a baya.
Sai da ya bari sun fice shima ya shiga binsu wajen har wani hotel suka shiga ..
Yana ji yana gani suka shiga da wani katoton jaka wanda su hudu ne amma suke kokuwa da shi ciki
Shima sai ya buya gaba daya bai bari sun san da shi ba.
"Wani abu na gaya masa cewa sarah ce a cikin jakar nan..
Amma sai ya fuske ya jira su har suka bar wajen suna barin hotel din
Ya je straigh wajen recptionist,cikin iya salon zance sai ya ruda ta da cewa tare da su yake sunyi mantuwa ta bashi key..
Salon sa da kuma yanayin yadda taga zubin sa yasa ta hakura ta bashi key din..
Da yana tafiyan sa ne cikin kasaita amma yana wucee ganin mutane ya haura sama da uban gudu ya kai dakin da aka ajiye sarahn.
Yana budewa kuwa ya hango ta Kwance babu dankwali bare rigar suit din duk ancire su an bar da dan karamin vest mai guntun hannu dake ciki
Wanda har shatin bra din ta yake nunawa
Sai bacci take kwasa sabida maganin awa 8 aka bata dai dai lokacin da suka shirya shirin su.
Wayar ta kuwa tuni suka kashe mata shi don haka duk wanda yake neman ta a ranan bai same ta..
Haka dije taci kuka har ta gode ma Allah....
Ganin ran kowa ya baci da abunda sarah tayi musu yau
sannan anan ma shirin maida shaidun gida washe gari ake idan ba ga a sarah ba..
Tunanin su tunda abun yakai ga haka Sai a kashe case din tunda ma mahaifiyar dije ta mutu ai shikenan..
Su hjya asma Masifan karfin hali kawai suke amma ransu yayi matukar dadi..
Wannan shine kankat gashi jira kawai suke wanda suka tsara musu zance su shigo su bada information din ai sunga sarah a hotel tun safe..
Sai aje duka a kamata
Shi kuwa yazeed baiyi kasa gwiwa ba ya dauke ta, yaune rana ta farko da sarah ta shiga hatsarin da baida alaka da sanin faruwar sa..
Sai yayi kokarin saka mata jacket din suit din za ya dagota a hannun sa yayi saurin haurowa da ita suka bi lifter
Daure fuska yayi ya fuce abunsa bai ko bada keys ba anan dakin ya bar musu..
Sai dai bai daga car dinsa ba ya shiga nata da shi suka bar hotel din
Anan organisation Ko da aka kawo news din sarah na hotel kamar yadda suka tsara maganan? ...
fitina da tashin hankali bai tsaya anan ba sai da aka kira asalin mahaifin yazeed alhaj nafiu Attah aka sanar da shi.
Cikin tsananin bacin rai da bakin ciki su hjya ke xprssing rashin jin Dadin su...cikin salo suna dada sa wuta akan case din.
Tsohuwa ta sha mamaki matuka,...batayi tunanin haka sarah take ba
Lokaci guda aka gauraye wajen aka shiga emergency meeting da hajiya bilkisu akan za aje a kama sarah red handed
Sai ayi mata hukunci
Tsohuwa da alhaji nafiu ne kawai suka rage a office suna jiran adawo da ita a mata hukunci.
Gashi informat din ya tabbatar musu da kasancewar sarah anan
yazeed kuwa bai tsaya ba sai da suka yi nisa chan cikin wani quest house ya ajiye ta daf tana firgicin farkawa
A lokacin kuma members Dukan su da suka isa hotel din a dane suke suga niyar su ya aiwatu...
Don haka basu lura da motar yazeed ne anan babu motar sarah ba.
Cikin tsananin mamaki haka suka bincike ko ina anan hotel ba su ga sarah ba basu kuma ga alaman ta ba
Zufa da ciwon kirji lokaci guda ya kama hjya asma sai insisting take adada dubawa
Har mrs abdl rasheed rani yaji haushi ya fice abunsa.
Anan suka bar mrs ruth da mrs asma suna jimamin abun suna dada dubawa cikin tsananin firgita
Sauran members su suka je suka sanar da tsohuwa da alhj nafiu cewa karya ne babu sarah a hotel kamar yadda aka fada musu..
Dai dai nan kiran yazeed ya shigo wayar mahifiyar sa, ta dauka cikin zakuwa tace wai ina ka shiga ne anata faman rigima anan?.
A dan birkice yace mum ba lokaci, its about sarah.
Lokaci guda kirjin ta ya buga tace what? Sarah
Ina take meyasa me ta ?
Kowa sai ya mike tsaye tsohuwa ce tace a samata shi a hnsfree
Don tun da chan basu ko kawo tunanin ko wani mummunan abu bane ya same ta musamman da su hjya asma suka rika cusa musu mugayen maganganun su..
Muryan yazeed suke ji garau yace musu mom sarah was kidnapped..
Amma bani da time din bayani sosai sabida motar ta nake using za ayi trcking dina.. so Do me a favour ga number daya kira ta last nan a wayar ta na samu a duba da wuri aka masu..
Hankalin su ne ya tashi sosai,kowa na jero nasas tambyar wasu suna cewa ina sarahn take? Wasu suna ce masa ina yake ,duk suka ruda shi
sai ya Kasa aje kansa waje daya yace kawai suyi bincike shi zaiyi handling komai..
Nan take case ya sauya aka turo number aka kai offishin masu bincike
Daga nan kuwa har spy din su hajya ya gaya musu yazeed ya samu wayar sarah da motar sarah har ya bada information..
Amma baice yana tare da sarahn ba
Wani sabon tashin sense Kamar zata sume cikin tsannanin tsorata suka shiga namen layin su aljan dun su san abun Yi
Cewa yayi su kwntar da hankalin su tunda yazeed yana tare da wayar zasu yi tracking dinsa kafin polisawa su gane su..
Hakan ya faru kuwa sai dai wajen da suke na da nisa sosai.
Daga nan kuma lokacin dayake wayar sarah take jinsa duk dama idanun ta a lumshe suke.
Ruwa ya kawo ya tallafa mata ta sha sannan ta shiga tanbayar sa meya faru da ita.
Anan ya mata bayani abun ya matukar tsorata
She bacome weak sai ta fada kan gado ta fashe da kuka mai cin rai..
Sosai hankalin sa ya tashi, ya shiga rarrashin ta yana bata karfin gwiwa amma ina tsoro sosai take ji yanzu kam
Har sai da ya jawo ta jikin sa yana bata comforting smooch sannan ta samu ta nitsu..
Sun kai wajen mintuna 20 a hakan yana shakar dumin jikin ta tana shakar nashi..
Wani abun yasa ya dube wayar sa anan jikin button din yake ganewa cewa ana reading locatiom dinsa
Sabida tsaro ya sa ya kame wayar su baki saya ya kashe,
Sannan ya sauya musu
Daki
Itakam Ta kasa tunanin komai sabida abubuwan sun daga mata hankali matika..
Kenan kashe mahaifiyar dije akayi dagan gan? Whats so special in this case da har za yi wasa da rai?..sosai ta shiga cikin damuwa tana kawo tunani kala kala.
Daga gida kuwa ummah ne dakan ta a ofisshin,bata ga yarta ba kuma wayar ta baya shiga..shine take tambayar ko sarahn tana nan amma sam su hjya billy suka kasa sanar da ita komai..
Da ganan kowa yake nadaman yadda ya tsananTa harshen sa akanta musamman indian team..
Cewar hya billy to lallai akwai makarkashiya mai girma a wannan case din
Dole za a tsare gardi har sai anga dawowar sarah.
Ita ma ummah ta kasa basu space daga ace sarahn na waje kaza sai ace tana waje kaza duk don sun ga ta mugun daga hankalin ta..
hankalin su abtashe yake amma sun yaba da yadda ummah ta sa ido sosai akan tarbiyan yarta sun lura cewa sarah is wel guided Nd monitored at home..
Ba kamar yadda aka cusa musu ra'ayi akan tarbiyan yan mata irin ta ba.
Ana neman karfe 10 na dare ummah ta tsanamn ta lallai sai an bata sarah tayi mata magana
Da kyar hajya billy ta zaunar da ita ta mata bayani, ranar kwana zaune duka sukayi anan ummah ba abunda take illah hawaye..
Anan guest howus kuma mrs ruth tace ma si aljan kar su bar wajen har sai yazeed ya kunna wayar sa sabida dole ne su san ko shi ya dauke sarah don su san abun yi
Ita kuwa sarah Tsoro da tunani yasa ta dukun kune waje daya,..har zazzabi mai karfi yana neman shige mata.
Dan dolen sa ya zauna da ita ajikin sa yana comforting din ta har ta samu tayi bacci da kyar
Shikam bai runtsa ba kallon ta kawai yake
A ransa yana saka abubuwa da yawa..
Har cikin ransa yana so ya mallake ta ya shiga rayuwar ta.. yaga tana mutuwa masa sai yake ganin kamar ma gashi Allah yana ta bashi daman cikar burin sa.
Murmushi kawai yake yi agaban innocent face din ta yana tunanin ranar da sarah zata furta tana kaunar sa dakan ta..
Don Shika dai ya san me ya shirya mata aransa.
Washe gari da safiyan Allah da suka tashi,
Bayan sun gaisa take cewa tana so ta kira ummahn ta..
Yace no we cant use any phone sabida ana tracking din mu..a yanzu yadda zamu tafi gida ne kawai zamu nemo..
Tace ohhh ya Allah, toh su waye wayannan me nayi musu haka? toh sai mu cigaba da zama anan kenan. For how long ?
Kar wani abu fa ya same dije ina nan.. this ppl call me bcos of her what if thy have her now?...look i need to do something now...gaba daya yazeed kallon ta yake ta na neman birkicewa tana maganganu cikin tashin hankali..
Tsaye ya mike ya karaso wajen ta tana kan magana...ya lura hawaye ne tam idanun ta masu dauke da tsoro da kuma fargaban abubuwan da suke faruwa..
Ajiyan zuciya tayi ta dafe kai" tana cewa Allah ya sa itama dijen ba wani abu za'ayi mata,i wonder who the helll is doing this
Meye riban sa toh? I wish thy cant just leave them alone and face me in dai har gaskiyan ne basu so..
Hawayen ta ne yayi droping cikin tsananin damuwa da tashin hankali ta sunkuyar da kai kasa tana tare wa
Yayi dan murmushi ya riko shaking hands din ta duka biyu yana dan murxawa... kamar zata kwace amma sai ta kasa anan ya jawo ta jikin sa a hankali ya rungumeta yana cewa its ok sarah..
Ya isa haka.. dije tana nan lpya.. kece kawai baki nan and i know sabida kar ayi case din aka yi miki haka
Yanzu abun da zakiyi shine ki kwantar da hankalin ki ,u gonna be fine
Relax ok?
Nan ta dan daga daga jikin sa ta dube sa cikin sanyin jiki tace ok"
But.....
Heyyy stopp..ya dada tsare ta da cewa..
Yanzu yadda zamu fita anan ne kawai matsalar you just have to calm down ok?..da kyar ta kwakwalo murmushi ta gyada kai
Cikin sanyi ta zame ajikin sa ..Kan gadon ta koma ta zauna yana cigaba da binta da ido..
Daga bakin gate kuwa anan mutanen aljan suke rarrabe suna monitoring din shiga da fita a boye sabida sun tabbatar da cewa yazeed na nan amma ba su san ko yana tare da sarah ba.
Cahn ana neman karfe 10 na safe tashin hankali daga both side ya hana su ma jin yunwa daga bisani...
Yazeed yace mata zai fita amma zai dawo yanzun nan..
Mikewa tsaye tayi zatayi magana, ya mata alaman a' a...
Tun da ya fita sai Bayan kamar 10 minutes ya shigo,...tace what happen zamu iya tafiya yanzu ko?
Yace no, amma zamu raba hanya...come on get ready ya fada yana dada leke ta window.
Rigar suit din nasa ta dada gyarawa a jikin ta sannnan ya riko hannun ta suka fito daga dakin a sace yana yi yana dube dube har suka kai bakin wani lungu ta baya acikin guest house din.
Gani tayi an ajiye wani drum gefe da katanga alaman shi ya shirya ..
Yace hurry up comn zoki hau..
Batayi musu ba ta hau ya dale shima ya taimaka mata ta sauka har kasa ta baya..
Ko damuwa da gurjewan da hannun ta yayi batayi ba ,ta dago tana jiran sa, sai taga ya ce kiyi sauri ki isa bakin titi,ni zan taho da car din ki yanzu if not idan suka same mu tare wani abu mummuna zai iya faruwa da ke..go now.
Har zatayi musu ya ce mata,if you dont want dije's life to be in trouble you wll hurry up you must go sarah bamu da lokaci..nan ya juya ya koma
Itama ta kama hanya ta shiga falfalawa da gudu
Zuwa bakin hanya.
Yana gama reading time din daya dauka ya taho ya shiga motar nata ya danna horn da karfi yadda zai dada jan hankalin su nan aka bude masa gate ya fito...
Yana daka nashi motar ya lura da motoci har biyu na binsa abaya..
He knew this wll happen so bai damu ba.
Sarah kuwa Duk da ta samo abun hawa hankalin ta sam baiya jikin ta sai yanzu take tuno da kar shi ma su masa illah..
Office ta isa direct babu kudi a hannun ta don haka ta shigo a dan birkice don ta sallame shi,
Da mamakin ta mutane ne cirko cirko ana faman jiran wani news ga polisawa da sauran su ciki har da ummahn ta.
Babu wanda ya lura da itace ta shigo don haka Da gudu ta yo kan ummahn ta suka rungeme juna"
Take hankalin kowa ya dawo kansu kamar a mafarki
Ummah tace ina kika shiga saratuh, waya dauke ki..kina lpya ko saratu me aka miki?....
Lokaci guda aka rufe su, for the first time kowa yaga hawaye sharbe sharbe akan fuskan ta..
Dukkanin officials din suka zagaye ta kowa da nashi salon tambayar da jajen,..
Anan ta dan bada labarin abunda ya faru briefly
Yanzu dai yazeed ake jira ya shigo
Shikuwa gudun tsira suke suke yi tsakanin sa da su aljan,.
shikansa baisan me suke shirin aikatawa ba
Basu hakura ba kuwa Yana kaiwa kan coner shiga organisation da suka ga zai tsere musu
harbe tayoyin motar baya duka biyu suka juya a gurguje suka bar wajen
Kara mai tsanani wheel din motar yake,...daga nan kowa ya fito a rikice
A kayo bakin gate
Tuki yake rougy yana neman control Duk kura ya bude shi ga shi dama speed yake yin neman control din amma sam babu.....so yana tahowa motar ta fara tumble tana juyi a haka ta je ta bugo bakin gate din da karfi...
Everyone was shocked.
#surayyahms
follow wattapd at surayyahms
Official cat..
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top