THE SCORNED

*🅱BRILLlANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™\jan\2019
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
🍒🍒
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@  SURAYYAHMS*

_YA AZZA WA JALLA_

_Page12_

Jirgin ta na sauka ta yi godiya ma Allah,dan Sauke ajiyan zuciya tayi tana tafiya a hankali kamar ba ita har ta iso inda sukayi da su hadu da sakon ummahn..

Bata lura ba ummahn ne dakanta agefe tana murmushi ganin yadda rayuwa ya juya mata,yau sarahtu ce ta dawo wannan?

Murmushi ne a fuskan ta amma Kuka ta ke yi a zuciya,tana cewa gashi dai yau na cimma buri na..ya Allah ka yafe mana kuskuren mu.

Kamar an tsakure Sarahn ta dago sai suka hade ido da ummahn da dan gudun ta ta taho suka kankame juna...

Hawaye ne mai dauke da murmushi da rawayan murya kowa na gode ma Allah da yadda ya tsince kansa alokacin..

Ganin ummahn ya sa ta dada jin karfin gwaiwa,ummah kuwa ba abunda take mata sai albarka da aduoin cigaba a rayuwa...

Ana jan su a haddaden motar su kirar dodge chager nan ummah ke sanar da ita cewa dama suprise tayi planning shiyasa tace mata ta dawo ta lagos..ai ta dade da barin kano ta dawo lagos da zama anan take sanaar ta da duk wani business din ta.

Sarah ta sha mamaki amma dama ita duk abunda ummah tayi a wajen ta dai dai ne..

So Cikin farin cikin sabon rayuwar su lokacin suka koma gida Cike da labarai kala kala na rayuwa.

Sai dai taki sam ta fada ma ummah abunda ya faru tsakanin ta da  mahfud ko kadan sai ta ma nuna mata aiwani abu urgent ya sa bai biyo ta sunzo tare ba kamar yadda da cahn ya fada...

Ummahn ta so ta gane daga yanayin mood din da ta sa tayi magana amma sai ta kauce..

Haka suka cigaba da rayuwar su Bayan hutun sati biyu da tayi washe garin da zata fara aiki suka yi waya da catherine.

Cath kam ta gama dagowa sarah na matukar kaunar mahfud wani bin gani take kamar rayuwar sarah ba mahfud zai mata wahala..amma ko da ta fada hakan ma sarah sosai ta karya ta..

Har ma ta dada ba da catherine tabbacin zata tabbatar musu da cewa  zata iya rike rayuwar ta batare da taimakon kowa ba...
She wants to be incharge of her phsychie.

Catherine tace toh Allah ya bada sa'a,sai dai cewa da tayi bata sake ganin mahfud din ba ta lura ya dan dame sarahn a zuciya har suka gama wayar bata kuma nuna hakan ba..

Juye juye take akan gadon ta ita kadai tana tunani cahn tayi Ajiyan zuciya  ta dada kore tunanin sa, tafara kawo me zata fuskan ta a goben

Adress note ta dauka ta duba sunan da catherin ta bata dazu"hafsat fulbe..
Itace kawa kuma abokiyar aikin da cath ta hada ta da shi a sabon office din ta anan nigeria..

Hafsat fulbe yar niger ce gaba da baya Sai dai ta dan girme sarah da shekaru biyu sannan tana da auren ta na shekara guda..

Washe gari da safe ta shirya tsaf ta sha suite riga da wando kamar yadda suka saba a kasar waje.

Tun saukowar ta, ummahn ke kallon ta
Har ta iso falon fuska ba yabo ba fallasa suka gaisah ,ummah tace ya haka kuma saratu? Ina zakije da
Da wannan kayan ajikin ki?

Ta dube kanta da kyau wando ne da riga na arman suite sai dan karamin half hijabin ta,
yace ummah kar kice kin mance da yau zan fara zuwa sabon wajen aiki na?

ummah tace ya za'ayi na mance da hakan,ni kayan jikin ki nake magana akai sarah wannan shigar ni sam baiyi min ba...

murmushi kawai sarahn ta danyi ta nemo waje kusa da ummahn ta zauna "tace kiyi hakuri ummah na,kema kinsan tsarin aikin ne ya zo da haka da bazan saka wannan kayan ba.
Ba kinga hotuna na ba?kema fa kinsha zuwa kina ganin yadda ake mana a makaranta

ummah tace ai n dauka don kuna karatu ne,amma banyi tsammanin ya zama lallai kisa riga da wando ganda ganda a matsayin ki na ya mace kina fita ba,

ajiyan zuciya sarah tayi, tace haka ne ummah nima nayi maganan haka amma shuwagabbnin mu sun riga sunsa doka akai...
Cewar su a ynzu  tamkar hukuma muke duk da ma bamu sa kayan yaki irin nasu, amma ya zama dole mu fito da official look sabida duk inda aiki yakaimu asan da matsayin mu..

Ummah ki duba ki gani kamar lawyers ne, ssa da special agents we cant dress anyhow kinga aikin ya shafi cudanya da mutane daban daban,idan na je ma wani da dressing din da bai masa ba baza a samu biyan bukata ba,kamar irin racist,social norms
Religous fanatics,cultural  mindsets da sauran su..
Ummah Kowa da tsarin rayuwar sa

so dan mu zama neutral dole mu sa kayan da zai nuna officialityn mu..kin fahimce ni ummah?

Ummah tayi shiru,daga bisani tace toh shikenan...Allah ya bada sa"a..ke dai ki kula da kanki.

yadda tayi murmushi ya sa sarah gane cewa dan doke ta aminta da hakan bawai har ranta bane.

a haka sukayi sallama ta wuce,

Karfe 8.00 ya mata a sabuwar offishin ta mai taken WHRA jnr1(world human right activist jnr1)

Duk da sarah tana da shares din ta na nata na kanta sai ya zama dole ne sai ta kasance a under organisation  kamar yadda harkokin su ke tafiya a cahn france kafin nan ta rika tazo tayi zaman kanta.

Sabida haka babban companyn datake yanzu is like a share inda za'ayi zaman survival of the fittest da suaran upcoming graduates kamar ta.

Yau Rana ne wanda bazata taba mancewa da shi ba,
Sabida anan ta ga ma'aikatan ta da zasu yi aikin karkashin business din ta at the same time tana harkokin ta na humanatarian tare da su.

babban waje ne sosai duk dama bai zama mallakin ta ita daya ba tukun akwai sauran kamar irin ta suma anan sai dai kowa da nashi tsabgar sannna akwai comitte mai karfi dake lura da su....

sai dai da shike tana da qwali mai nauyi sai nata shares din yayi karfi sosai fiye da sauran mates din ta...

Sarah bukar ta kasance sirriiyar bafulatana ne amma ba sosai ba don tana da shape mai dauke da hankali da tafiyar da imani wanda yake dada bayyana model size height din ta..

She's alwys preserve bata da surutu,kuma takan nitsu sosai kafin ta furta magana ako yaushe, nitsuwar ta da sanyin halayen ta abun burgewa ne wajen kowa

sakamakon wayewa da kudin da ta yi yasa hatta kalar fatar ta ya banbace sosai da mata yan gayu na ajin farko da ake ji da su
she's very beautiful din duk shikakan kyau tana da su.

Hakan ya sa da aka zo nuna ta a matsayin ta na  sabuwar oga a companyn kowa yake nuna zumudin sa wajen ta ko dan ta san da shi amma she was casual iya kaci idan ta sha hannun da kai ba abunda yake biyo baya sai smiles
Idan yayi tsanani to ta furta kalmar thanks ne.

Dadin abun shine haduwar ta da hafsat fulbe anan yayi mata sauki sosai itama activist ce bata da girman kai tana da taushin hali da saurin sabo..sai dai ita kam tana da magana sosai ba laifi she's a very cheeful and amiable lady
Lokaci guda ta samu shiga rayuwar sarah duk dama basu da time yanzu sosai.

Sarahn Sosai ta shiga ran ma'aikatan ta, gwarjinin ta kullum razana su yake..
Musamman,femi,jalal,sakinah hajarah da david...

Wani bin har rige rigen kallon ta suke idan ta zo aiki...

Haka ma kowa naso ya shige private office din ta ko dan ya kare mata kallo..

haka sarah ta cigaba da gudanar da rayuwan ta as days goes by ta na cigaba da danne tunanin mahfud tana forcing kanta akan harkokin dake gaban ta har ta samu sauki

a kullum kuma tana kokarin kyautata sa suturan ta duk sabida har yau ummah bata sake jiki da hakan ba amma ba yadda suka iya..

kwance tashe sai ta saba sosai,
A watan ta na shida da fara aiki tayi suna wajen kwarewa da iya tattali da kyautata rayuwar dan adam..

wanda ya dada ninka soyayyarta wajen ma'aikatan dake wajen kowa fan din ta ne..

Har ya kasance ma ba so ayi missing din wajen aikin sabida ita

Yadda take handling issures da mutane cikin nitsuwa fasaha da saukin kai ya sa ta samu alots of secret admirers..

Mrs SARAH B, kowa yake ce mata.

ranar da ta samu wani  gagarumin yabon samun nasarah daga sama chan kasar waje a fannin aikin ta
Ranar ne aka shigo mata da wasu sabbin mutane wanda bata taba ganin su ba sai yau..

Su ne commitee of veterans and matrons of human right and business law makers na profession din baki daya.

As usual black suite tasa mai dauke da hijabin ta dan karami,tana sauri ta wuce conference room inda ake sauke manya manyar bakin na su,


Wani irin dum dum kirjin ta ya buga da ta doso ciki, sabida wani irin munafukan idon dake binta da kallon kurel.

dama sai da hafsat ta gaya mata wayannan mutanen sai tayi da gaske kafin tabiyar musu amma bata san abun zai razana ta ba sai data gansu

jajirtaccun mata ne hamshakai masu fada aji,masu kuma ji da ilimi da matsayi

kowacce acikin su tana iya fada a yi kuma bari a kafafen kungiyar su na duniya...

Duba da shekarun sarah da status din ta na har yanzu karamar yarinya ce yasa wasu daga cikin su suke mata kallon sama sama da wani irin kas kantaccen tunani..

Manyan jigon guda biyar ne,kuma su aka fi  tsoro
Fiye da kowa domin akalla sunyi girman da wasun su sai dai suyi jika dasu wasu kuma yaya.

Hajiya fareeda,hajiya asmau,mr fidelis,mrs ruth emenike and finally alhaji nafiu A.

Alhji nafiu shine current and most active president na kungiyar human right activist a yanzu amma babban industriliast ne yana da kudi sosai, haka ma matar sa hajiya billy itama wata zakanyar ce wanda ake matukar tsoro duk dama tana matsayin displinarian ce a kungiyar tana lura da su..

Tunda aka shiga meeting din sarah take gane halayen su daya bayan daya,sabida itace gaba da kowa a jajircewa so most of maganan da ake yi anan kamar da ita suke yi in person.

Theyr are too tough babu wasa ko saukin kai al'amarin su, duk maganan su yafi zama akan doka doka doka...
Kowa a murde yake kuma kowa naji dakan sa sosai

Duk cikin su sai da kowa ya ji bugun zuciya dan dole nitsuwa zai zo maka ko baka da niyya, kuma amsa su a cikin ladabi da saukar da kai yake kasancewa.

ita Hajiya fareedah babu ruwan ta da kwainane, ita dai kawai idan gaskiya ya fito a fade ita,amma hajiya asmau ita ce gang leader wajen sa ido ta fidda fice tare da mrs ruth emenike, don kuwa duk motsin da akayi anan sai sun so su san dalilin sa..

Shikuwa mr fidelis tuni ya sa ma sarah ido musamman da yaji bata da aure budurwa ce, sai lashe baki yake yana fakon idonanun ta..

Anan Har Alhj nafiu ya gama bayanan sa cew a yau da dare zasu hada su da sabbin opponents dinsu sai a sanar da wanda zai fafata a karo na farko domin su tsayar da shugaban WRHA a zango na uku.

Tun kafin meeting ya kare mrs ruth da mrs asamu suka fara tsangwamar sarah a zuciyar su...

sabida ko da wasa fuskan sarah bai nuna tsoron su boro horo kamar na sauran ba duk dama tana ji

Bayan sun fice, aka bar zallan su ya su anan office din

mrs ruth take cewa duk yaran kamar ma basu da da'a shes not convinced da tarbiyan su duk dama an gwada su da cahn..
Tace "dubi Kayan jikin su duk ya matse su ya kamata mu fa dauki mataki tun wuri this isnt the ethics.

Hjy asma ne ta amsa as usual tare da cewa bari kawai zamu gyara musu zama ai ni kaina naga abubuwan dayawa wanda basu min ba..

Mrs fidelis yayi mumurshi yace, its okay
Ya kamata muyi abunda ya kawo mu..this night, we have alots to do.ya karshe da kyakkwan murmushi

Mr president alhj nafiu yace hakan ne ayi abunda ke gaban mu first,duk wani korafi sai agaya ma hajiya bilkisu wato hajya billy discplainarian.
Off suka daga kowa ya fita..

Tun daga nan mr fidelis ya so ace ya samu private glance da sarah ko da na minti biyu ne suyi magana amma sa idon mrs ruth da hajiya asma yasa ya tara plan dinsa zuwa daren yau da zasu hadu duka.

Misalin karfe 8.00pm zasu shige meeting din gaba daya ummah ta kasa zama sabida sarah bata kaiwa wannan lokacin a waje ba..

Gashi presnce din su hajya da mrs ruth ya takura su sosai sun hanata sakat da idon su da jefe jefen magangaun da unnessary complains.

ko waya basu bari tayi ta gaya ma gida abu ya rike ta anan ba..

hafsat ke dada bata karfin gwiwa tace sarah nasan ke ce zaki dauki nauyin wayannan old thugs din, sai ki kwantar da hankalin ki kibi su kar asame matsala ..

Sarahn sai dai tayi murmushi kawai tace hapsy tunda kina tare da no ai bani da matsala..

on time suka shiga hall din inda kowa da kowa ya hallara..

yanzu mutane sun dan shigo sosai har da  sauran kananan ma'aikatan kowanni fanni,.

Bayan jawabi dan gabatar wa.
Alhaj nafiu da matar sa hajiya billy suka gabatar da kansu makowa  da kuma matsayin su

Hajiya billy tace" a wannan muhimmiyar taro zamu sanar da ku sabuwar jajirtaciyar  opponent din ku daga wani sashin na daban,

Wanda zasu fafata da jajirtacciyar wannan sashin, a WHRA competition mai kama wa daga gobe..

Itace wanda zamu hada ku da ita muga wanda ya cancanta ya tsaya a matsayin shugaban ku na  gaba daya shashin...nan akayi tafi raf raf raf

daga hannun dama hajiya asmau ce ke jefo murmushin ta  mai cike da kasaita da jin dadi

da shike ta san yarta ce wato"Safeenah moh.
itama jajitacciyar humanatarian ce amma ta wani tsarin na daban ..

kamar yadda sarah take haka itama take sai dai akaro na biyu tana lashe gasar zama kan kujerar girman idan taci wannan ta kafa tarihin zama na sau uku kenan.

Hajiya asma da mrs ruth Tsaye suka mike suna ma yar nata tafi ayayin da aka fito da ita fili don kowa ya ganta...

kyakkwa ce itama babu laifi sai dai tafi kala da turawa sabida ubanta asalin bature ne so she's a halfcast.

Bayan waje ya lafa hajiya bilkisu ta kuma cewa
a fannin mu nan companyn zamu kira mrs sarah bukar WHRA jnract1.....

sai wajen ya yanke kyat aka shiga murmuring kowa naso yaga fitowar ta,...

Ita kuwa Duk da kirjin ta ya buga haka ta mike da murmushin mai dauke da kwarjini ta fito fili itama

Wani irin yanayin kallon kishi da rashin aminta su hajiya da mrs ruth suke maida mata musamman da ta suka ga boro boro sarahn ta dauke fuskar kowa da ta tsaya gefe da jikin safeenah,wasu ma sai yau suke dada kare ma tsaban kyaun hallitar sarahn kallo ayayin da ake introducing dinsu officially ma manyan su...

cikin masu kare mata kuwa harda babban dan mr president alhaj nafiu,
Wato YAZEED ELNAFS dake gefe kan kujera shida abokan sa

Bayan an kammala komai an basu tsarin aikin su.

Misalin karfe 10 saura tana sauri take don ta raka hapsy wajen mijin ta a waje  itama ta dawo ta tarkato kayan ta tayi gida

Anan ne sarahn ta fara ganin shi.......

*Alhmdullhi ...The real meaning and title of the story is about to begin at this point.... Idan baka gane pages din farko zuwa nan  ba zaiyi wuya ka fahimci kan littafin baki daya😊...*

_Share,and share your views_

*WATTPAD AND FOLLOW SURAYYAHMS*

*OFFICIAL CATTY*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top