PREGANCY
*🅱BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™/SUN6th/ 2019🔞
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
_The scorned_
🍒🍒
_A TRUE SENSATIONAL STORY_
~_Story written by_~
*SURAYYAHMS*🔥
*OFFICIALCATTY🐈*
*_WATTPAD_ @SURAYYAHMS_*
@ IG:Surriem-sule_
*#Lovestory2018/19*
*#romance#purefiction*
*#Destiny at fault..*
*Any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison All my stories are strickly mine,beware copycats!.*
*For my little jewel hapsisis,ALLAH will bless you for me kinji😘*
_PAGE3_
Haka nake lallaba kaina
Nika dai ba wanda ya damu ya saurare ni...
Gashi har Kwana biyu amma umma shiru gaba daya sai na durmuya cikin kunci da tsanan kaina..
dingisawar danake yi yake hanani zuwa makaranta
Amma na dage ina jinyar jiki na iya wuya na daure don na samu daman rubuta jarabawan zuwa jss3 dake gaba na..
Kwance tashi shiru ba mai leko ni har na fara fita ina hidimomi na..
Na so na nemi duk hanyar da zai sada ni da umma amma na lura kiris baba babaji yake jira sake danne ni
sosai na gano maitar sa.
sai dai a yanzun tsoro na yake ji musanman yadda nake amsa masa magana cikin taurin rai
A haka Har aka ci sati biyu.
Ban sani ba ashe ummah na cahn tsallaken hayi anguwar sarki
..don tuni aka sake sauran yan safaran miyagun kwayar amma rashin wanda zai tsaya ma ummah yasa hukuma suka damka ta a wulakance wajen sarki hammayo ...
Anan akayi ta sai'nsa da ita akan gaskiyar ta da shike a yankin kowa yasan hammayo baida adalci sam,sai ya hana a kira baba babaji da ga garin mu cewar sa ai yan garin mu ne ke bata ma yan nashi garin suna mu muke sawa ana zagin mulkin sa a yankin alkaleri..
A haka ya yanke mata hukunci ba imani akan tana zuwa gona da maikatan sa don tana yin roron shinkafa har na tsawan sati hudu kafin ya sake ta ..
Ranar da sati hudu ya cika Tare da wasika da dogari aka sa umma agaba aka dawo da ita kurwala gidan maigari.
Kafin nan Baba babaji na sane da komai amma sai ya dauke idon sa ,sai ma dada bata umma dayayi awajen yan uwa da dukkanin dangi da kalaman bakin sa..
Sai naga Gaba daya kowa ya tsane ni ba gaira ba dalili ena zama awaje za 'a tashi kamar anga kawar shaidan
haka ma a makarnata ni kadai nake yawo yanzu..abun ya dame ni har ya dena
Sai Ji nayi a tsegumi cewa wai baba babaji yace ai ummah na ta gudu yawon karuwan ci ne ta bar ni da shi, da wasa wasa sai gashi maganan yayi kauri sosai a garin kusan kowa ya sani yanzun...
Ko da na daure na kawar da fushi na tambaye baba babaji akan zancen cemin yayi shi bai sani ba tsagumi ne kawai irin na mutanen kauye,wai ko a jiyan ma yayi magana da umman a wayar sa'idu babban dan inna wuro tace wai wani abu ne ya rike ta.
A lokacin Ban ko amsa shi ba don ji nake kamar karya yake min..amma na cigaba da adua ma umma na ena kuma sauraron dawowar ta don na tona asirin baba babaji.
"Sai dai kashhh rashin lpya yana sanda na a hankali ,
nonowa ne sai zurr zurrr suke yi ta ciki sun kumbura duk ban kula ba kuma ban damu ba sai hidima na nake yi..
A ranar da ka kawo ummah gidan sarkin kurwala Chan da yamma akayi kiran baba babaji a gidan maigari
Anan aka soma magana gaban ummah da shi baba babaji da dogarai guda uku akan lamarin.
Umma na tun anan ta soma gane waye babaji
..don sosai ya bayyana cewa bai san da tafiyar ta bama,shima ai nemen ta yake yi...babu irin karya da cin zarafin da baiyi ma umma anan ba . .ummah na rantsuwa shima yana yi.
Ganin kamar ba za gane asalin kan gaskiyan zancen ba
Yasa Sarkin kurwala yace bazai saurare maganan shi kadai ba suje gida nan da kwana uku zai tara mutane ayi sharia tare sa kashe di don a koma ja kunnen masu hali irin na ummah na.
Ran sarki ya baci sosai yace bazai lamunci mace marar tarbiya da mutunci agarin sa ba..
Wasikar hakuri shima ya rubuta ya aika ma sarki hammayo ya kuma tabbatar zasu dauki matakai nan gaba akan haka..
Ummah taji haushi musamman da ta fahimci dukan su wajen sunfi daukar maganar baba babaji akan nata
Da kuka ummahn ta iso gida ,..ta ma kasa hakuri don zuciya ya debe ta sosai tun daga bakin hanya suka shiga cece kuce da baba babaji abunda ba asan ta da shi ba kenan Tsawon zaman ta agarin nan..
Gashi dama mahaifin ta ne kawai gatan ta wato marigayi hamma aliyu mahaifin ta wanda tun bayar zuwan su garin da mahaifiyar ta ta rasu shike tsaya mata...
Yanzu bata da kowa sai ita da Allahn ta din hakan yau babu wanda ya shiga ma umma fadan ita kadai take neman kwace makan ta yanci...
Baba babaji kuwa dadi yaji ganin ya cunkusa mata bakin ciki ya gulla mata sarkaken tarko....
gashi ya sa yau ta kasa hakuri suna tahowa tana masa debar albarka akan Muzanta ta dayayi da karyan da ya hada mata awajen sarki..
Ko ajikin sa don shikam Dadi abun yake masa tana hauka a idon jama'a ana dada bata rashin gaskiyan lamarin
Cikin ransa Ba abunda yake sai Dariyar mugun ta har suka shigo gida
"Churrrrr akayi akan su kishiyoyi da yayan su don an cika gidan tam dama ana shirin bikin Sauran yayu na..
Anan a tsakiyar gida Kowa saida ya gaya
Ma ummah bakaken maganganu da habaici iri iri akayi mummanan sa'insa face face,
tun umma na kuka har ta bushe idanun ta tana amsa ko wacce
Shegiya a cikin su ba kunya ba kawaici.
Ina makaranta a lokacin zazzabin dake sanda na shike sani yawan bacci da shegen tsitt da yawu Yau ma har aka tashi ban samu na dafa na iso gida ba Sai da na dan huta da kyar dai na tarkata kaina na kamo hanya..
A Lokacin da ake ci ma umma mutunci a tsakar gida baba babaji ya sabule yayi waje ya barta da matan gida kowa saida ya gaji ummah bata gaji ba. .
anan na zo na same ta
Ban tsaya jin wani hayaniya ba na taho muna hada ido da ummahn da hanzari na zo na fada jikin ta ina fashe da ruddaden Kuka.
Anan ne itama ta dawo hayyacin ta ta kamo ni nan take jikin ta ya soma rawa tana neman yin sanyi....
Kallo ta bini da shi kamar wacce bata taba jin Nayi irin Wannan kukan ba sai yau.
Tace saratu? Kar ki bari ki ji abunda suke fada karya ake min saratu
Cikin kuka nace kar ki damu ummah bazan taba yarda da hakan ba
Wani wawan Shewa aka buga a tsakar gida baba ladidi da group din ta sai dariya suke kamar suna kallon wasan kwaikwayo,
"Suka ce Kwarya tabi kwarya ana jan wuyar rakumin dawa a gari sai ga dansa ya shigo A ka kwashe da dariya ....
Ja na daki umma tayi bata kula su ba ni kuwa tsaban zuciya
Ban tsagaita kuka na ba tsawon lokaci har saida ta rufe ni da fada mai dauke da tashin hankali da firgici...
Tashin hankalin da ummah ke ciki yasa gaba daya sai naji nauyin gaya mata abun da ya Faru tsakani na da baba babaji..
gashi dama abunda nake shaukin gaya mata ke nan amma duk sanda na dauko hanyar fada sai na tarar da ita cikin tsananin jimami
don kuwa a cikin dan kwana ukun da sarki ya bayar hatta makaranta banje ba, kullum sai anyi fada da hargitsi da ita kamar gidan zai dage haka ake masifa da mu..
Wani bin tsaban haushin wani maganan idan ya gulle ta sai ta fita neman baba babaji
Gashi ya buya ya dena nuna kansa ma kwata kwata a waje anan ne ma ta san cewa dagaske inna wuro na raye tana kuma family house dinsa tare da sauran matan sa
A nan ma sai da aka tada zaune tsaye sa ummah ta sake maimaita abunda ya faru ko da zasu fahimce ta amma hakan bai faru ba
Karshe ma a hannu a hannu aka dawo da ummah kamar mahaukaciya tana surutu.
Sanadiyar kokarin bin gaskiyar ta ya sa Duk garin sai aka daura mata laifi aka ce itace batada mutunci..
bata da gaskiya ai baba babaji baice komai ba itake tada hankalin jama'a..
Babu wanda Ya taba tsaya mata in ana zagin ta ana cin zarafin ta amma kowa yana bada muhimmaci sosai akan reaction din ta da zatayi don ta kare kanta..
Ranar da kwana uku suka cika da asubahi da azabbaben amai na tashi kamar zan cire hanjin cikina na..
Sosai hankalin umma ya tashi sosai don ita ta zo kaina..
sai yanzu ne ma take kallo na da kyau take
Gane yanayi na
Don dama Sosai jikin ta ya dan bata kamar ena dauke da juna biyu amma dai tayi saurin dannewa tana tayani kintsa kaina..
Kaina na kasa ina kan Jin Abubuwa da dama na ci na a rai nan na fashe da kuka mai radadi
"Ummah Tana dago ni na shiga kukan da dan sauti ina rawan dari gaban ta..
Tace Saratu? Me ke damin ki dama baki da lpya ne ? Cewar Umma tana kure ni da ido cikin dauriya.
Ina sane da yan labe dake jin mu amma haka na cire komai araina na mata bayanin komi daga tushen sa ban boye mata abunda ya faru ba koda na miskala zarratin daga abubuwan danake fuskan taba har yanzu
Umma ta rike ni gammm amma bai hanani jin karkarwawa da tsuman da take yi ba.,
Magana take so tayi amma muryan ta ya sarkafe yana fidda i i na tsaban bacin Rai ji kawai nake tana" b..aaa. .baji,
Dum umm..a ta yanke jiki ta fada gaba na summamiya..
tun kafin Na tsala ihu aka yo chaaaa akan mu jikin umma na fada ena bata hakuri ena kuka..
Ruwa aka dan yauyafa mata kafin ta farfado a kasale Ta kalle ni gaban ta duk na gama fita hayyaci na kuma ban fasa ba..
Ido tabi kowa da shi batace uffan Ba tayi yunkuri ta tashi ta kamo hannun na muka shige daki...
Munaji ana rade raden maganan ana raba gulma a tsakar gida..
A kan gado ta zauna Hawaye kawai take yi agaba na ta riko hannu na sai sheshheka nake tace"Allah sarkii diyata ki yafe ni, kaico na saratu, ni nayi silar shigar da ni dake cikin wannan mugun rayuwa kar ki sake daura makanki laifi ni na jawo mana fitina arayuwan mu dana auri babaji,.
Gashi ya lalata na nawa ya lalata naki tace sarahtu Inaga fa babaji kamar ciki yayi miki.
Cikin wani irin bugun zuciya Na dada kame hannun umma na fashe da kuka mai tsumayin radadi da
Tashin hankali..
Wayyo Allah na imma na shiga uku Ciki fa kikace ummah?
na daura hannu na akai hawayen na har turririn zafi suke fiddawa ena kan kuka ina cewa na shiga uku...
Tausayi yasa Umma ta jawo ni jikin ta amma
Shiru ne ya ratsa wajen
Aka rasa wanda zai dakata da nashi kukan kuncin da kyar ummah ta dago ni " idanun ta sunyi jajir tausayin ta tuni ya gauraya zuciyata naji inama ace mutuwa mutum ne da nace ta dauke mu baki daya mu huta da duniya...
Ummah ta shiga shafa fuska na cikin kulawa " yace kiyi hakuri saratu, duk da ni jahila ce yau nasan mutum ne kawai bai wuce qaddarar sa, kin kare kanki a bayan ido na ,nasan da alokacin ma ko kin gaya min ba shi zai hana ya sake fito da wani mummunan hanyar cimma burin sa ba, nima nan kinga abunda ya min ban aikata komai ba amma yanzu na dauka abubuwa da dama akaina...
in har Goguwar munafurcin babaji yafi karfin kowa nasan karyan shi ya ja da Allah don
Shi ne gata na dani dake..
nayi miki miki alkwari saratu bazan taba barin ki a wani hali ba har na mutu ina tare da ke yata sai na karbe miki rayuwar ki daga bakin qaddara dayake so ya jona miki..
Na sake sauke hawaye na rungume ummmah ina kuka bata fasa rarrashi na ba ta cigaba da cewa
kiyi shiru abunki,ko duk duniya sun guje mu ni dai nasan babu mai raba ni da ke har abada sai mutuwa.
Nace Nagode ummah, na gode da kika fahimce ni, nayi miki alkwarin biyayya duk rintsi duk wuya ba mai raba ni dake ummah ummah Allah zai saka miki Allah zai tona asirin kowa zasu ji kunya wata rana..
..Cikin shshesehka nake fitar da maganan da kyar
Ummah bata ce komai ta shiga share hawayen ta tana kan bubbuga gadon baya na a hankali
A hakan muke zauna cikin bakar kunci da jiran abinda zai faru nan gaba gidan sarki.. abincin ma na gaban mu amma bamu wani masa cin kirki ba.
Yau ne ummah bata fita neman babaji ba don tasan duk yadda akayi ya gama shirya mana tijarar da zaiyi agaban sarki anjima.
Wajen karfe 3 saura aka aiko sako cewa bayan lasar ake so mu hallara acahn.
Sosai Gaba na yayi mummunan faduwa amma hakan na yi ta lazimi ina rokon Allah ya saukaka mana lamarin.
3.45pm Makil da manyan dattujan gari a kofar gidan mai girma shugaban kurwala..
Ladiyo, laure hansato da maman dukku da kishiyon ta rabi da hassana sai dukan kishiyoyi ummah da dangin miji watoh baba babaji da mata guda uku sune a gefe akan tabar ma duk suma babaji ya sa aka kira su domin shari'ar ..
Hmm jahilci baiyi ba , ashe idan abu ya kasance na cin mutunci baza a yi shi a sirri ba sai an taro jama'an gari?
"Hakan Ni kadai ya dama amma ummah na kam tun agida na lura da babu fuskan imani a tattare da ita sosai ta dauke fuskan rahma ta bushe zuciyan ta
Kamar wasu barayi haka aka gurfanar da mu biyun a tsakiyan fada kan tabar ma..
Sarki ya soma jawabi da jan hankalin mata da dai daikun matasan dake wajen akan illahn safaran miyagun kwayoyi acikin gari da sauran garuruwan makwabta,
Yace " na kira ku ne badon komai ba sai don na yi hukunci ma wannan baiwar Allah bisa laofin data aikata ma yankin nan ..yadda kowa in yaga ni zai san bada wasa muke yi,
Ummah tasha mamain wanna furucin A zuciyan ta tace Kenan sarki ya amince da maganan su har ya laka min hukunci? Tayi shiru dai tana sauraro
Anan ya sa maga takardan fadan sa ya gaya musu duk abunda ya faru da umma na ni kuwa nasha mamakin yadda aka juya kan zancen aka laka ma ummah komai a take hawaye suka wanke fuska ta .
Bayan angama Tuni dattijai suka hau zagi da bakar magana
Ana Allah ya wadar da ummah wasu suna cewa ashe duk halayen ta da aka santa da shi na nagarta da chan na munafurci ne?
Ni da umma bamu ce komai ba muna shiru
Sarki ne ya dakatar da surutun da ake cikin raderaden,
Yace"
Ya isa haka , ya kamata muyi abunda ya kawo mu..
Yace"A matsayin na na mai gari na bada dama wa duk wanda ya san wani abu mai alaka da lamarin wannan baiwar Allah muna sauraro kafin a fadi hukunci ta.
Ah'a ranka shi dade ayi mata hukuncin ta kawai..ga gaskiya boro boro me za ajirah?
babban aminin baba babji wato dan masani ya fada a zafafe
"Tuni wasu suka bi bayan sa nan ma har da mata kishiyoyin ummah ne kawai basu tanka ba
Nan ma sarki ya tsawatar ,
Yace tunda haka ne baria shi mijin ta babaji kawai ya fada mana ta bakin sa muji,kar kuma wani ya sake tsoma mana baki
Shiru ne ya dan ratsa wajen.
Sannan sarki ya dubi baba babaji yace yayi magana"
Har da gyaran muryan sa ya mike tsaye kamar mumuni
Farko ya fara da fada ma jaama'a wai ya auri umma ne sabida ya na mata kallon kuruciya zai biye mata hakkin ta amma halayen dayaje ya tarar da ita sun dade suna sashi mamaki,
Ana shiru ana jin sa.anan ya dada bata ma ummah na suna ya nuna a idon jama'a cewa bata da tarbiya,fitsarariya ce.
Nikuma Anan raina ya soma baci..
ummma kam na shiru ta dago tana duban sa cikin wani murmushi mai dauke da sarkakkiya.
"Yace ni bani da abun da zance tunda sarki da al'umman sa masu adalci masu girma sun kama ta da laifi dumu dumu kawai ayi mata hukuncin da ya dace da laifin ta...
nima ayafe ni domin da haka nake neman shaidar mutane da yan uwa cewa na saki gambo saki uku..bazan iya zaman aure da ita ba
"A take Ummah ta rangwada guda mai kauri mai sauti tayi wani irin dariya mai cike da jin dadin wanda ya nuna alama ko ajikin ta.
" Surutun da ake yi kasa kasa ya faadada aka cigaba da cece kuce matan nan kamar zasu tashi su buge ta kowa na zagin ta,
"Raina yayi mummunan baci da irin yadda ake nunawa ummah na ita barauniya ce kuma karuwa uwa uba marar tarbiya.
Jiri ne ya soma dauka na sai naji bazan iya daukar maganan ba cikin wani irin hatsalallen fushi da ihu na ce "ku dakata...!!!
Kowa ya dakata....
Tsit waje yayi da mamakin jin haka nasan wasu sun sha ko aljanu ne dani
anan na mike gaban sarki kamar mara hankali
Na tsaya
Cikin kuka Nace" hammma, kai sarki mai adalci ne ka dada dubawa ummah na bata da laifi akan abunda ake tuhumar ta ..
Ni Nasan gaskiyar abunda ya faru in ka bani dama zan fada maka.
Kowa sai yayi shiru
Baba babaji yau a munafukin sa ya fito Sai ya sauya kama ya zauna abokin sa ne ya tashi a zafafe zai kama ni da duka wai nayi rashin kunya da katsalandan a maganan manya anan Aka riko sa.
Sarki yace" kowa ya nitsu ..kar wani ya sake motsowa idan bajaka duk abunda nayi masa shi yaso..yace saratu ina jin ki mai gaskiyar da kika sani akan wannan lamarin.
Anan nayi ajiyan zuciya kukan dake so yaci karfi na ma na tukare shi
Nan na soma zuba labari A- Z yanayin zaman mu da ummah a hannun baba babaji har rakube da nake yi a gidajen mutane na fadi daliili na,
Kukan da nake yi anan yasa ummah na kuka itama
Har cikin ranta bataso na fadi abunda ya faru dani na fyade da cikim shegen ba.
Shiru ne ya ratsa wajen tabbas zuciyan wasu ya girgiza da jin oda side of story na dana umma dana bayar ..
Cikin magiya da kuka nace in har akwai karya acikin abunda na fada Allah ya wulakanta ni a cikin wutar sa...dan Allah ka bi mana hakkin mu bamu da kowa sai Kai sai Allah
Shikan sa sarki zuciyan sa ya girgiza amma sai ya daure ya juya yace ena babaji ?
A dan rude baba babaji yace ranka shi dade gani
Sarki ya dube sa cikin wani irin yanayin damuwa yace ka fadi tsakanin ka da Allah me kasani akan wannnan maganar ?
Nikam tuni ummah ta riko ni tana kuka tana lallabani yanzu kam duk masu bakin zagi sun dan rusuna ana dai kan sauraro
Anan baba babaji yace" uhmm ai daman ni nasan za'ayi haka ranka shi dade shiyasa ma nazo da shaiduna ga su nan.
Yayo nuni da manyan munafukan sa abokan sa aciki naga har da sageer.
Yace ma sarki "wallhy wayannnan da kake gani sunyi nisa wajen makirci da munafurci amma ni bazan yi dogon magana ba gaskiya ta ita ne zata fidda ni.
Ya juya kamar da gaske yace ma ummah wallhy gambo ba dai naji kunya ba sai dai ke kiji kunya yau sai na tona asirin ki.
Umma ta dube sa ta kar kada kai tana shiru .
*WATTPAD VOTE AND FOLLOW @SURAYYAHMS*
*OFFICIALCATTY🐈*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top