PART
*🅱BRILLlANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™\jan\2019
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
🍒🍒
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*
_YA HAYYU YA QAYYUM_
_PAGE8_
Bayan isar su ummah da minti 20 sai ga shi ya shigo da yan mata biyu wanda akallah bazasu fi shekaru 22 zuwa 23 ba...
Kowacce ta rike sa sai wasan banzan su suke, anan ummah ta dauke kai tana Allah ya sawwake ta ga yarta saratu a wannan irin rayuwar,tunanin haka ya sa bata wani dago ta kalle su ba har ya sallame su ya zo ya zauna suka gaisa da ummah da anty sahura..
Tunanin sa ko anty sahurah yar uwan ummah ne amma haka fir suka ki gaya masa asalin relationshp din su.
Chan ya sa aka kawo musu abinci da sauran su,suna ci yana tanbayar ummah abun da ke tafe da ita,
Ba bata lokaci tace "ranar kace idan ina bukatar taimako zaka taimaka min,
Dama aiki Muke nema ta wajen ka.tayi nuni ita da anty sahura..
"yayi shiru domin kuwa dama Ya sha mamakin zuwan tan sosai amma bai kai mamakin da ya sha ba yanzu data furta aikin take nema kuma tawajen sa.. .
kenan fadima zata iya kwana da namiji? Ko dai wani abu ne ya same ta?..yana rayawa aransa yana kallon ta...
Cahn yayi murmushi yace fadima kenan,ai ni dama na baki a farko sabida nasan baki gane ni waye ba ko?
a hankali ta gyada ka
Yace, aiki kam bazaki rasa shi ba ko dan abun da ya faru tsakani na dake zan duba na gani
Sai dai akwai sharadi,ta dago ta dube sa yace "kin tabbata kin shirya ma aikin da kika kawo kanki?
Ummah tayi shiru, wani bugun zuciya ne take famar danne shi amma sai tayi yake,tace na shirya Zanyi...
Sai dai fa kasan damuwa ta baifi na sami abun da zan tallafa rayuwata ba ne,so acire maganan jin dadin rayuwa da rudin duniya aiki kawai zanyi...
yadda tayi maganan yasan kunci da takaici ya sata furtawa Sai yayi karamar murmushi yace toh ai shikenan,
Ki rike alkwarin aikin ki nima zan rike miki naki alkwarin deal?..
Ta dan gyada kai ta dube sahura..
Nan ya cire kudi kimanin 5ok da kati mai dauke da adress ya ajiye kan table yace ga wannan ku saka kaya ku zo nan anjima da misalin karfe 9.
ummah ta dauka ta bada sahura ta duba,strip club ne amma na manyan mutane...
sahura tace mungode sir,yayi murmushi yace idan dokan aiki tafara ba gudu ba ja da baya...
ni ne shugaban ku.
ummah ta mike da cewa mun maka alkwari yace to sai na ganku...nan suka fice suka koma gida..
zuciyar ummah cike yake da damuwa amma haka take bunnewa suka siyo kayan da zasu sa da dan abinci da sauran abunda zasu bukata na kansu da sabon sana'ar su
ummah cemin tayi ta same aiki amma zata fara gwadawa domin aikin dare ne, kuma yana da kyau sosai za a bata kudi dayawa.
ganin ita da anty sahura ne zasu tafi yasa na kwantar da hankali na ban yi mata musu ba..
Misalin karfe 9 suka isa gida ne madaidaici daga bakin kofar duka bada kati aka barsu suka shiga motici ne manyan manya wanda akalla sunkere masu tsayi kuma basu da yawa sosai.
Dim Blue and red light ne gaba daya daga compound din har ciki inda ba agane fuskan mutum da kyau..
haka suka shige suka isa gaban ssa danjuma,
sahura ce ta san wasan su su a cewar ta manyan manyan mutane ne anan suna hutuwa ,wasu na shaye shaye wasu hira kawai suke yi yan mata suna rawa hapf naked agaban su suna nishadi...wasu kuma asalin karuwan su suke tare da su..
sai dai da shike is highly confidential tamkar club suka maida shi kamar kungiya haka suke gudanar da harkokin su,
Anan aka kasa su ummah a kasuwa,
Inda aka zabe ummah a matsayin wacce zata nayin club special strip dance a kowanne karshen dare arabian title sabida kyaun jikin ta da surar fuskan ta.
and then ta dan manyan ta sun san wannan bazai mata wahala ba tunda zata sa kaya wadatacce.
Bakamar yan mata ba,
Ita kuma anty sahura sai aka yi rashin sa'a ,wani ne yace zai dauke ta as personal mistress dinsa gashi shi bai cika zuwa nan ba so dole tana binsa duk inda yake..
a haka aka basu tsarin aiki, duk damaa ummah taji dadin bazata kwana da kowa ba amma it dosnt make any differnce to her,
haka suka rarrashe zuciyan su aka musu 3days training ana basu rabin kudin aikin su,
har suka saba sosai,
A kullum Ita da anty sahura Zasu fito daga gida tun 8pm,sai kowa tayi hanyar ta
Wani bin ummah kadai take dawowa gida don duk rintsi itakam agida take kwana..
Wani abun mamaki shine
A duk aikin da tayi a duniya da fadi tashin,da wahala, babu inda farin jinin ta da sa'ar ta yake haskawa kamar wannan rawar larabawar datake yi agaban maza
Sati biyu tayi amma ta fara dawowa evrybodys favourite.
Doguwar riga ake bata baki kirin wanda ya dan kame round and sexy bodyn ta, da shike ma gaban kayan akwai dan tsagu kadan ta kafar ta yana bada balance wajen rawar ta da rausayawar ta
Kuma ana daura musu alragaya wanda ke rufe kansu da gwalagwalai agaban kamar mayafi irin na masu rawar karuwan larabawan da chan zamanin manzanni..
Sosai ta kulle zuciyan ta ta nitsu waje daya tana abunda ya kawo ta,
Gashi ba hayaniya babu wanda ya taba ci mata mutunci sai ma yabo da tarairaya datake samu daga clients,wasu ma suna daga zaune har manni suke mata bayan makudan kudin da take karba bayan kowani dare..
Bayan tayi complete 1months tana zuwa akai kai kullum.
Har Aka dawo da ita a sati sau uku take rawa,
Shikan sa ssa danjuma sai da ya yaba da hasken tauroron ta,ta jawo masa arziki da mutanen arziki bana kadan ba..
Sai ya kasance a kowani rana cikin kwana uku akalla zata tafi da 250 to 300k..
sabanin 30 40 50k da dachan take karba...
Ummah Ta wanku ta dada karo wayo da sanin me duniya ke ciki sai dai har yau bata mance da kuncin dake zuciyar ta ba.
Wata biyu da fara wannan aikin suka tara kudi na ban mamaki da shike ma idan ba abinci da sutura ba ba sa sayan komai na jin dadin rayuwa ..
Anty sahura ta koma zama da saurayin ta,
Ummah sai ta kama mana haya 3 bedroom flat mai dauke da komai aciki,ta siya min kayan sawa sosai da dan karamar wayan android mai kyau..
Daki na daban nata daban sabida yanzun bata son nasan wasu abubuwan da take yi,
ni dai nayi mamaki nayi godiya har na rasa me zance ma Allah da naga lokaci guda rayuwar mu ya sauya..
sai dai har ila yau idan nace ma ummah nima ta nema min aikin ina taya ta, sai tace min ah a, ai yanzu ta sami wajen mai kyau ana biyan ta sosai so babu amfanin nima nayi wani aikin..
A cewar ta ma tana tara kudi ne zata saka ni a makaranta mai shegen kyau...sosai nake cikin Nishadi da ta fadi hakan ..kullum sai na mata adduar sa'a da fatan alkhairi
ita kuma kullum sai ta sa na mata alkwarin bazan fita waje koda nan da nan ba,bare na kula wani na miji
Hakan na dauka kullum ina gida ina kallo ko karatun littafin hausa dana turanci a online ..
Lokaci na dan tafiya,abubuwan suna dada kamawa yadda yakamata ma ummah,sai ta soma daura buri mai tsauri akaina,ta tara kudi amma tana so ta tara wanda zai kaini babban makarantan sai wane da wane a lissafin ta idan tayi wasa da damar ta wata rana baza ta kai labari ba.
anan club kuwa ssa ya soma daura nashi dogon buriin akanta, daf tana cikin nema min makarantar daya dace ta sani ya zo mata da maganan ko ta sauya saka kayar rawa zuwa mini gown ko ya sauya ta da wata clients..
hakan ya jawo sa'insa sosai tsakanin su, har ummah tayi fushi ta dena zuwa aikin na kwana biyun.
Ita tana nan ta damu gashi tana so tafara aikin sani a makarnta bata so kudi ya yanke mata a hanya..
shima acahn ya damu
Clients sun taslkura sai dai a nemo musu ita,
Dan dolen sa yayi hakuri ya kira ta aamma da sharadin dole zata yi tunanin nan da kwana hudu idan ba haka ba sai dai ta shiga layin bin maza kamar anty sahura..
Sam hankalin ta bai kwanta ba, amma haka take cigaba da rawan ta..
Batare da ta yanke hukuncin ko zatayi yadda yake so ko bazata yi ba
A ranar da kwana hudun ya cika ta zo adaddafe cike da shakkun makoman ta sai ta ta riske baya nan abun ya bata mamaki sosai,
Domin Babu abunda yake hana shi zuwa nan sai ciwo ko mutuwa.
Tayi tambaya aka ce mata bai fito ba yau
sai tayi aikin ta normal zata karbe kudin ta aka ce sai taje ta same shi,
Ba laifi ta shiga motar haya ta je inda akace mata yana nan,
A wani palou aka mata jagora tana jira...
chan wajen minti 30 sai ga surutun su daga ciki shida wasu mutane su biyu..
ummah ta mike tsaye tana binsu da kallo kamar yadda suma suka bita da shi,a ladabce ta gaishe su suka amsa..
Ssa danjuma yace kiyi hakuri ga aikan ki ya zaro envelop dauke da kudin aikin ta ya bata,
Tunda ta karba tayi godiya bata sake kallon kowa ba anan ta juya tafice.
Tasan dole wayannan mutanen akwai su da muhimmanci wajen ssa shiyasa ya kasa dago wani magana..
duba da yadda ya sa arai yau zai sauya mata aiki muddin bata amince da nuna tsaraicin ta boro boro ba.
Tafiyar ta ke da wuya
Wanda suka tare da shi din ya ce masa yana bukatar magana da shi in private akan matar nan.
washe gari da Safe ummah na gida,ta ga sakon tex messege mai tsayi wanda ya bata mamaki..
bata wani bata lokaci ba tayi wanka ta shirya .
ce min kawai tayi yau aikin safe zata yi don ko karyawa batayi ba naga ta wuce..
Bata tsaya ko ina ba sai gidan ssa danjuma.
zaune ta samee shi yana karyawa
Aka mata oder ta zo ta same sa..
Bayan sun gaisa
tace oga Gani sai dai bangane sakon ka da kyau ba..kayi min bayani.
Kai tsaye yace zaki gane fadima,yayi gyaran murya ya sha ruwa" ya dube ta,ai dama nace zan sauya ki da wata sai gashi yau Allah ya kawo mafita akan lokaci.
Ummah tayi shiru daga bisani tace"zanyi tunani akai kabani lokaci...
ya mike tsaye yace ah a,wannan ba aikin da zakiyi tunani bane fadima don kuwa ba ma ni zaki cigaba da aiki ba
Daga yau kin bar aiki a karkashi na...
Ummah tace mene? Me kake nufi....
Akan me? laifi nayi, ko dan akan maganan nan ne ?
yace dakata
Ni kaina da kike gani na a karkashin wani nake,sannan tunda nake a rayuwa ta ban taba jin
Yace yana bukatar mace ba sai jiya da ya ganki,
wani dum ummah taji, aranta tuni ta mike tsaye ta tsaya itama.
Yace fadima zakiyi aiki ma ogah na nasani, in dan wani abu ne kar ki damu sabida sai asirin ki yafi na yar uwan ki rufuwa sannan kudin aikin ki zai iy ninka wanda nake biyan ki,sa'a biyu babu wanda zai san me kike zuwa yi sabida bai taba tarayya da wata ya mace ba,
Ummah ta budi baki zatayi magana yace tsaya kar ki ce komai
Nifa nasan duk abunda kike ciki na rayuwar ki,kuma kisa ranki hakan yasa nake daga miki kafa
Tun farko,do this job ke ma zaki ji dadin sa.
So gudluck .....
Nan Ya ajiye mata sakon envelope mai dan tsayi yayi gaba abun sa.
Takai minti 20 tana kallon sa daga bisani ta kauda kai ta koma ta zauna daga kan kujera
budewa ta yi ta duba,
Duk abunda take bukata na rubuce anan,
dan zaman ta da kawayen harkan ta yasa yanzun ta iya karanta abu, kuma tana jin turancin jifa jifa atleast tasan yes come go da sauran su.
Wayarta ta dauka ta kira sahura sun kai minti 50 suna magana daga bisani ta fice ta dawo gida. ..
Kwana biyu bata leka ko ina ba domin daga cikin takardan ranar sabon aikin ta zai fara daga kwana biyu masu kamawa
Da shike anty sahura ta dawo sai naga sun sa karfi sosai wajen shigar dani makaranta
Ranar da ummah zata fara sabon aikin ta ranar suka sakani avwani nigerian international academy.
wanda ake biyan akalla dubu 250k kowani session..
tsarin ilimin su na da bala'in kyau da tsari don haka ummah tayi min alkwarin zata nema min lesson teacher idan ta samu wasu kudin don nima na iya abubuwan kamar sauran yara..
Haka ma anty sahura ta min nasiha mai shiga jiki da ratsa kwakwalwa cewar ta,na dage nayi karatu don nan gaba ni zan rike su,su ma sa'a suka ci suka samu aiki mai kyau suke kokrin ganin bansah wahala irin nasu ba a rayuwa..tace amma nan gaba komin su zai iya karewa sabida haka na dage kar na basu kunya musamman ma ummah na dake wahala sosai akaina....
A Haka na shiga karatun da imanin zan yi ne don na biya ladan zufan mahaifiyata da duk wani fadi tashin da take yi,
Sosai na cire hidiman rayuwar duniya na sa jaratu na agaba duk da wahalar da nake sha wajen shiga tsarin wayewar makarantar..
Gashi an maida ni baya, sai naga duk nafi yan ajin mu girma wani bin har kunya nake ji amma su kam ba ruwan su,
Jira ma suke nayi magana suyi min dariyar don kowa ya gane ban iya turanci sosai ba.
Anan na kame kaina bani da aboki ko abokiya..
ummah kuwa ta kama aikin ta, wajen babban ogan ssa danjuma mai suna abdul aziz shayal..
A reknown popular industrialist yana da kudi kudi na fitina..
shine ya raini ssa danjuma da irime iren sa sun fi akirga shi asalin dan kano ne amma mahaifiyar sa lebanese ce so fari fatt ne kamar jini zai fito afatar sa.
Ba laifi ya tsufa don kuwa tamkar yarinya karama haka yake kallon ummah,
Farkon zuwan ta ya gaya mata asalin shi tun da ya ganta anan gidan ssa danjuma ya ji ta burge sa shiyasa yace yana so tayi masa aiki,
ya kuma tambayar ta nawa ake biyan ta a aikin ta ummah bata boye masa komai ba ta fada cikin gaskiya,
Bata sani ba ya bincika ganin tana da gaskiya sosai yasa ya shiga bata gwaji kala kala batare da ya taba kusantar ta ba..
Wani bin har ya kance ta bishi bashin kudin aikin ta, duk da yasan tasan yana da shi amma sai bata taba masa complain ko rashin kunya ba..
Haka zata zo da safe tayi masa danna a kafadun sa da kafafun sa yana shan iska a farfajiya haka zata yi jigilan dafe dafe tana kawo masa cike sa ladabi da biyayya.
ranar da na gama exams na zangon farko wato first term,sai aikin ya dan fara bata tough time sabida tulin lokacin nan a tsarge take don har yau oga shayal bai taba kiran ta kan gadon sa ba amma baya so ko kadan idan yace ta zo ta kawo masa wani complain duk dama yana mugun respecting din ta da yanayin ta,bata da hayaniya sannan tana da ladabi akan aikin ta..
Ana cikin haka ranar ya kira ta cikin dare misalin 1 saura duk sai ta rasa yadda zata yi ta fice,
Gashi nakanyi karatun dare sabida yadda na sa abun Araina
Gani take idan tace zata je aiki a wannan lokacin zanyi suspecting wani abu gashi ta tabbata in har ta fice zan ji kuma zan fito..
Shikuwa ya takura sosai har da turo driver sa,gani take hala yau ne yake so ya kira ta gadon sa,ga damuwan hakan aranta ga damuwan yadda zata min bayani washe gari.
Babu yadda ta iya sai ta daure ta fito din asace ta iso har gidan sa
Ganin ta kasa sake ranta yasa shi yayi murmushi,
Yau kusan wata uku kenan da haduwar su amma yana ganin kamar ya karance ta fiye da yadda take tsammani.
Sosai yake tausaya mata haka kawai shiyasa ma yakasa aiwata komai da ita,
ummah tana zama nikuwa dana fito shan ruwa bangan ta ba ya sa na shiga kiran layin ta,
ganin kiran yasa ta rasa ya zatayi inta dauka me zata ce min?
anya kuwa zargi bazai fara shiga zuciyan yata ba, ?duk sai ta damu
Alhj shayal Duk yana lura amma sai ya dauke kai,
anan ummah ta koma gefe ta kira anty sahura tayi mata bayani,
cikin bayanin yake jin abubuwa dayawa hakan ya sa ya kudira aransa yau sai yasan ita wacece...
tana kammala wayar yace mata wacece wannan...?
cikin ladabi tayi masa bayanin komai bata boye masa ba..
Jin tace bata taba kwana awaje ba sabida yarta yasa ya ji wani iri,
"yace mata tayi hakuri dama yana da muhimmiyar maganan dayake damun sa ne kuma baida wanda zai iya fada masa sai ita shiyasa yace ta zo..
abun ya bata mamaki amma dai ta sa a ranta cewa zata saurare sa ,a tunanin ta zai bata labarin wani abu ne ko wani matsalan sa amma sai ya shiga mata nasiha mai cike da nazarin rayuwar duniya
Sosai jikin ta yayi sanyi Gani take kamar Zuciyan sa gaba daya ya bude ya mata karatun ta nutsu akan rayuwa..
Anan itama hankalin ta ya bata wannan mutumin ya gama fahimtar ta gaba da baya,amma meyasa hakan ne bata gane ba,
yace ma umma,zai tafi wajen familyn sa sabida dama hutu yake zuwa amma bazai sake dawowa ba.
Shiyasa yake so yasan ita wacece kuma meyasa take wannan harkan a tunanin sa mace kamar ta mai kawaici sanin yakamata da tunani, bai dace ta shiga wannan layin ba..
sai yace ko dan yarki kike yi?
Ba yadda ta iya ta amsa mashi da eh,
Yace mata ta ina ta hadu da ssa danjuma?
Labari ya na tada labari har sai da ta gaya masa labarin ta kaf da abubuwabln data fiskan ta arayuwa..
Yaji abun har ransa, duk dama jikin sa ya bashi ita ba ko wata irin mace bace tun farko amma baiyi tsammanin labarin ta yakai haka muni ba,..
Bai iya cewa komai ba sabida ya jima yana kai kawo da radadin zafi da hawayen ta ke fitarwa,
yace yanzu aiki daya zaki yi min a yanzu ki kwana nan gidan gobe da safe zan nemeki ..
Tayi godiya ta koma daki ta kwanta..
Sai dai Tunani duk ya hanata yin baccin sanadiyar tono maganan da tayi sai take jin wani sabon yanayin zafi da nadama aranta
Haka har gari Allah ya waye,
kamar yadda aljh shayal ya mata umarni haka
Ta koma gida da safiyan Allah..
Ta same ni har nayi sallah ina kimtsa wajen
Gashi batayi magana da anty sahura ba bata san me tace min ba
..
bayan ta kimtsa ta fito nake cewa ummah,tunda ina hutu ki bari mana ina tayaki aikin naga kamr yanzu yayi miki yawa
Cikin hikmar ta na uwa tace waya gaya miki hakan.
Nace"ai jiya da na ga baki nan anty sahura na samu awaya take cemin aiki kuke yi...
ummah ta dan yi ajiyan zuciya tayi shiru tana kallon na daga bisani tace saratu"idan aiki kike so toh ki dubi littafan ki da kyau kiyi karatu...idan kuma tausayi na kike sai
Ki dage sosai ki cimma burin ki,..dan Allah kar ki bijire ma tarbiyan dana miki don shine taimakon da zaki min,kinji?
Nayi shiru na dago ina duban ta,a sanyaye nace haka ne ummah nayi miki alkwari bazan saba miki ba...
Tace haka nake son ji ki bar wani zanjen aiki kam ni zanyi, tunda na wuce lokacin karatu ko wani abu,sai dai na taimaka miki kema ki taimaka ma wasu
Ta dada bani close look tace "Saratu,inason Ki girma da son ki kare mutuncin ya mace aduk inda take,kar kiyi zalunci kar kiyi cuta ki zama mai gaskiya da rikon amana,kar ki bari duniya ta tayyara kowa kamar yadda ta so ta tayyara mu,kiyi adalci ma duk mai bukatar haka..
..ta dada matso hannuna tace" amma kisa aranki ke saratu ce,kar ki taba mancewa da kanki, saratu ne yar gidan bukar kar ki taba mancewa da inda kika fito.kallon ta kawai nake yi nakasa magana dabida na fahince me magana yake nufi.
Wato Tuna kaina kadai zai sa na rike dukan alkwarin datake so na rike akan rayuwa ta nan gaba.
Ganin yanayi na yasa ta sake hannu tare da maida hawayen dake so ya sauko mata afuska ta ta cigaba da cin abincin ta..
wani duniyar tunanin na shiga,sai nake dagowa hala rayuwa na mugun ma ummah na wahala fiye da yadda nake tunanin no wonder naga take samun karfin gwiwa da wayewa who knows whats shes going trou amma har yau ban kawo wani zargi araina ba.
sai na shiga kulle kullen yadda zan tabbatar mata da ni yar halak ce,daga wannan ranar na kudira araina zan yi dukan abunda da ummah na tace tana so na zama a rayuwa..
bayan kwana biyu da faruwar haka,alhj shayal ya kira ummah.
Daga wannan ranar rayuwar mu ya fara shiga wani sabon tsari,
bisa adalcin sa ya yanke ma ummah wani gurbi daga cikin arzikin sa na sabgar sa da harkokin gona da kiwon kaji da da dabbobin gida na zamani
Sai ya mallaka mata halak malak tare da gida madaidaici mai dauke da komai da komai har da mota nissan mai kyau na mata...
A cewar sa yayi tunani tunda bata yi karatu ba,zata iya jan jari ta kuma rike sa da kyau da ilimi da basiran da Allah ya bata.
Duk dama ya bata shawaran tayi makantarr yaki da jahilci bai hana shi jan kunne ta ta lura da duniya ba
Duk da karfin gwiwar ummah da kuma buri da ta sa akaina yau sai take ga kamar bai kai na alhj abdl azeez ba saboda tausayin labarin ta daya keji yasa ya dauki nauyin karatu na, daga yanzu har lokacin da zan gama masters..
signed and sealed.
ya kuma cewa ummah ya mata haka ne sabida yaga zuciyan ta kuma ya tabbatar da cewaa ta cancanci taimakon sa fiye da dubbai da ya taimaka musu suke lalata rayuwar su da na wasu.
Tayi kuka mai cike da godiya,ranar ji take tamkar qayar dake soke azuciyan ta aka cire mata,kamar amafarki haka take jin kalamn sa
yace mata lokaci yayi da zata yi aikin halak din ta don ta cimma burin ta na rayuwa sannan ta dawo da kimar darajar tarbiyan ta da qaddara ya taba mata shi..
hatta sahura sai da ta ta niko gari ta zo ta yi godiya ma alhj shayal wanda har i yanzu gane yake ma bai mata komai ba...
Ganin rayuwar ummah ya samu babban rabo ya sa sahura ta soma jin aranta tunda itama ta samu rufin asiri sosai yaci ace ta itama ta sake harkan tsira tun wuri kar abun yayi nisa...
Su ukun da ummah da anty sahura suka dawwama wajen bani rayuwa sai dai na kanji suna maganan sa amma bantaba ganin sa ba
Cikin kankanin lokaci aka samo min lesson teacher wanda baijin ko zo da hausa shiyasa ni agaba da karatu har nakan ji na tsane kaina amma da wasa da wasa har muka saba da shi soai
da shike Allah yayi min baiwar daukar abu dawuri sai gashi kafin hutu na ya kare na iya abubuwa fiye da yadda ake tsammani
Acikin kwanakin su ummah na faman tsara min rayuwa ta shima aljh yana shirin komawa inda ya fito kamr yadda ya fada
sau daya ta bani awaya muka gaisa da shi,nan na dada tababatrwa cewa gaskiyan ummah ne yana da kirki sosai
don anan ma bai barni ba sai da yamin nasiha yasa na masa alkwarin akan zan rike mahaifiyata duk halin da take ciki
Har ana zan koma makaranta sannan ummah ke ce min ai ogan ta ya sauya min makaranta
Amma yace idan ya shirya zai sanar da ita. .
Ni kuwa abun sai bai dame ni ba don ban kawo komai araina ba tukun..
Ummah kuwa ashe yadda zata min bayanin abubuwan da ake ciki yake damun ta,sun sa Ranar akan zasuyi maganan da anty sahura amma tayi tafiya
Duk sai ta shiga damuwa don ko gidan da aka bata ta kasa komasa sabida bata san yadda zata tun kare ni da maganganu dayawa ba
Ana saura sati biyu tafiyata france aka min visa da sauran su in a very official way ranar na fara kawo tunani kala kala sabida nima na san ma'anan abubuwa da yawa tunda ina karantawa kuma ina ganewa
sai nadan shiga rudani musamman da na lura idan nazo ma ummah da magana sai ta kaucar da ta rufe bazata rmtaba saurara na ba
Sai na damu sosai wani tunanin yasa nace zan tambaye anty sahura kawai don nasan ita kam bazata boye min komai ba
Dazu da safe naji ummah na waya da ita kan cewa ta dawo.
bayan fitar ummah da kamar awa biyu nima na fito na tara adaidaita ya kaini gidan anty sahura.
Ban taba fita nayi nisa ba ba sai ranar dan haka
Nake ta faman rakube rakube da kwatancer da ranar tayi na samo na iso
Gidan shiru ba kowa sosai yayi min kyau dama ta gaya min ta siya gidan kanta sabida naga ta bude saloon dan dai dai sai bai dame ni nasan sauran details din ba..
Mamakin da nasha shine ganin motoci har biyu manya,nace baki tayi ne ko duk wannan arzikin anty sahura ne,?
Wani bugu zuciya ta tayi, nace "ummah zata sa a kaini kasar waje ga anty sahura da uban arziki wani irin aiki ne haka suka samu?
na isa daf bakin kofar ta da har na daga waya na zan kira ta sai naji muryan ummah na tana kuka cikin tashin hankali
da har zan bude kofar cikin azama sai naji muryan namiji yana mata magana abunda ya dada shawo kaina suna na danake ji yana ambata yana cewa Dole agaya min meke faruwa..
Wani irin bugu zuciya ta yayi amma haka na daure na koma ta jikin window na sa kunne na da kyau ina kallon su da madubin glashin da aka dan bude shi kuma ina jin duk abunda suke fada
Alhj shayal ne da naty sahura da ummah a tsakiyan su duka suna tsaye,
anan na ji wasu mahaukatan bayanai wanda suka juya mini setin kwalwalwata sam sai na dena gane komai daga abunda nake jin ummah na furtawa da bakin ta.
kafata ne ya kasa dauka ta sai bari nake ina karkarwa, don bansan kokacin dana koma bakin kofar ba shiri na bude na kuso kai na ciki....
*WATTPAD VOTE AND FOLLOW @SURAYYAHMS*
*OFFICIALCATTY🐈*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top