MR PERFECT-part1
*🅱BRILLlANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™\jan\2019
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
🍒🍒
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*
_For you nafeesah umar muhammad,i cannot forget ur kindness_
_PAGE13_
Suna hada ido da yazeed din sai ya kau dakan sa kamar bai ganta ba,itama sai tayi saurin dauke kai shiga ta tarkato kayan ta ta fice....
"Wow,such a beautiful creature amma babe din nan ta gama cizo na,gaskiya i must have her no matter what...
Daga gefe yake fada cikin zuciyan sa yana labe yana kallon takun ta har ta ta mule bata san da shi ba,...
Haka ta koma gida ranar da kyar ta samu ta kwantar ma ummah hankali sannan tayi mata bayanin sabon cigaban da ta samu....
So washe gari da safe bayan ummah ta hado mata dan abincin breakfast din ta a cooler take ce mata "kar ki karaya sarah,kar ki kuma mance da ke wacece insha Allahu ke mai nasara ce a komi.
Sarah tayi murmushi tayi ma ummahn light peg agefen kuncin ta tace" in har dake agefe na bana tunanin komai zai bani wahala ummah, ki cigaba da min addua sai na dawo..
A kullum haka suke rabuwa da ummah kasancewar sarahn da wuri take zuwa office don sosai ake samuso ido yanzu...
Yau sati guda kenan tana shige da fice, ga sabbin fuskokin da kewaye da ita kamar shi yazeed da kuma mr fedelis wanda kusan kullum sai yayi dalilin wani slight abu ya hada su da ita Ko da kallo ne.
Gwara ma shi yazeed din sarahn ta fahimci cewa kamar friend din opponents din ta ne wato safeenah moh don kullum yana claimimg wajen ta yake zuwa alhalin zuwan shi domin ya dada gane wacece sarahn ne..
Sosai ya qudira aransa sai ya shiga rayuwar ta yaga meye aciki,dan zuwan da yake ya gama fahimtan Stern mood dinta na shegen miskilanci da kama kai...
He was so impressed and curious shikam dama ya fison macen da za'a sha fama da ita,ba kamar safeenahn sa ba don kullum a bada kai take ko tadi suke zai iya yin shiru ita bata gaji ba...
Yazeed yana da mugun ji da kan shi, domin kuwa shidin ajin farko ne ajerin kyawawan mazan ma hes got a silky smooth killer body and sexy eyes ...
Karya ne mace mai jini ajiki ta gansa ta kasa kyasawa,ko da bata yin sa dole ta yi acknowlding ya hadu matuka...
Tun da aka haife sa Bai san talauci ba bare wahalar sa,rayuwar sa smooth take tafiya baida wani abu mai kargo da zaice ya nema ya rasa
..ilimi,basirah,mata,abokai,iko...suna, daukaka uwa uba sa'a duk nashi ne...
Don ko acikin abokan sa shi din na daban ne har yau idan suka kulla game to fa sai ya lashe bai taba faduwa kasa ba hakan yasa yake dada ji da kansa sosai kuma ya yarda da kansa a koma meye yake yi..
Tunda yaga sarah sai ya soma amfani da iliminsa da basiran sa wajen lura da duk abun da ke kewaye da ita Bataare da ya bari ta fahince sa ba,
ko da yake zuwa office din da sannun sa yake wuce ta ta wuce shi ba tare da ya juya ba, yakan yi hakan ne don ta gane fuskan sa amma shi ko kadan baiya ba ta impression din ya san da mace anan..
Itama hankalin ta bai ya wajen sa amma yadda yake playing moves din sa so smart ya sa ta gane shi sosai,
Musamman ranar da suka taba buge juna akan steps tana saurin saukowa wanda duk hakan shirin sa ne amma bata sani ba...
Ita dai ranar da safeenah ta zo take musu iyeyi a office din cewa tana lashe wannan gasar zata auri yazeed yasa ta bada hankali har ta gane sa da kyau..
Don safeenah tagama yarda da cewa ita zaata ci gasar kamar kullum so kallon su sarah take kamar bata time dinsu suke...
Ita da take ji da tana da uwa abakin murhu sannan ga saurayin ta dan gidan president, sai ya zamto ba karamin fetsa ma saratu,iyeyi da maganan banza take ba duk dama sarahn idan ta amsa ta bata jin dadi..
Amma bata fasaawa
Wani bin sai tayi kwana biyu bata leko ba amma bata hakura sai ta neme ta da maganan,
Cikin ranta alredy ta soma jin kishin da haushin miskilancin sarahn,
A ko yaushe idan abu ya taso na fafatawar ilimi da kasuwanci sai sarah ta kame tayi shiru har sai ta gama nazarin bayanan su kafin sai ta soma nata bayanin wanda hakan yake bata point sosai awajen project examiners din su.
Kowa sai ya fara karkata wajen nagartan ta, da nuna halin ko in kula don ko ka maida mata magana da zafi sai ta maida maka wanda zai sa kaji kamr bata san da ita kake ba...
Taki tayi fushi da kowa bare aje ga gaba,duk fitinan surutun safeenah da na mrss ruth bai sa sarah ta ji zata iya basu fili suyi gaba ba.
Dan dolen su suke amsa tarbiyan ta da nitsuwar ta.
bayan wata guda cikin wannan yanayin,kowa ya fahimci kowa hatta sarah ta soma sabawa da sanin mrs ruth da hajy asmau suna taya yarsu kishin gasar ne ba wai zallan powr su suke takura ta da shi ba..
Everything is tight for her wani bin ko lokacin abincin bata samu taci,
wannan satin da shike offishin mr fidelis ne zasu lura da gasar yasa
Yake cikin nishadin yanzu nesa ta zo masa kusa..
Sosai yake so ya latsa sarah yaji ko zai iya samun kanta yayi uzurin sa da ita duk dama yaga halayen ta is not easy to cope with...
Ranar da ta zo sashin sa ita da safeenah, sai ya fara bata attitude
Idan ya bada aiki suyi su kawo ,sai ya dubi idon safeenah ya kushe ta sannan ya ce mata ai sarahn ta fita iya komai shi ya fi jin dadin aiki da sarah..
Tun abu na wasa wasa har safeenah ta gaji da kushe ta da yake yi ta kai kara wajen mahaifiyarta hjy asmau,.
Ita kuwa musamman ta niko gari ta zo ranar da zaayi presntation din su..
suite din da sarah ta sa yau riga ne da skirt cool milk sai tayi rolling da pper red veil ya mata kyau sosai..
Yau ko shi mr fedelis dake ganin yawan bata credit din dayake yana nuna tafi safeenah boro yayi tasiri azuciyan ta sai daya yaba...
a yau kuma yake shirin gaya mata muradin sa akanta..
safeenahn ce babba don haka ita tafara presntation dinta...
sannan sai aka kira sarah itama ta zo tayi...
Bayan an gama komai
Da kansa ya mike tsaye yana tafawa yana cewa client da examiners su duba su gani, sarah is the best,and he likes her....
Ita ko murmushi kawai take yi tana jin yadda yake cusa ma mutanen magana mai dadi akanta..
Besides acikin ogogin su shikadai yake nuna mata full confidence da zamudin sa..
Daga gefe safeenah tace mum kin gani ko?haka yake min ko yaushe,sai yace ita ce tafi kowa nikm ma nagaji am out of here..
Ta fada cikin bacin rai zata fice
Hjya asmau tace wait....
nan ta mike taje gaban mr fidelis da sauran mutanen dai dai ku dake wajen tace masa
what the hell is going on here...sai waje ya dan yi shiru da shike tafada a dan zafafe...
Kamar ya fa? Mr fidelis ya juya tare da kallon su duka ita da yarta..
sarah na daga gefe na lura da komai sai ta dan kau da kai tana katsa wayar ta..
sama sama take jin yadda hajiya asmau take cewa" fidelis abunda kake yi sam bai dace ba, ashe haka ake yi anan?have you forgetn This is a competion?ai dole ne ka bada kowa credits u cant favour just one opponent this isnt the ethics of wHRA...i hate bias..
Sai kowa ya dakata ya dube ta ...irin whats this woman trying to say here
Shikuwa Cikin son ya dada zafafa plan dinsa yace ,ah a hajiya ban fahimce ki ba fa menayi wanda bai dace ba anan?
i gave evryone his credit,sarah did well ,ao kema kin gani da idon ki kowa abunda yayi nake fada ko ba haka bane...?
Tace i seee,so sarah did well,mmm na dauka ai mutane biyu ne anan suke fafatawa ashe mutum daya ce,
Zai yi magana cikin fushi tace dakata fidelis,na lura da kai son kai kake so ka shigo da shi and i wont allow that,
Ta watsa masa harara mai cike da alaman kalmomin " nasan ka kasani,kai dan iska ne marar mutunci so idan ma baka jiki akayi kana aiki akai it wont hapen on my doghter...
Tsaf ya karance ta sai shima ya bita da murmushi mai dauke da taken "so what? I will do what i want...
Mutane kuwa suna kallon su ba wanda ya iya motswa wajen bare su gane me suke cewa da idanun su..
Hajiya asamu ne ta juya ta dan dube sarah daga nesa cikin masifa tace" this is WHRA,im repeting myself Duk wanda ya zo da wani mugun halayen sa ma gwara ya bari dan baida mafaka anan kungiyar"a shirye muke da tone asirin sa
Duk wata yar iskan yarinya da zata kawo mana duniyanci anan organisation din zamu fitar da ita we are ppl of respect and dignity....
yadda take maganan da comanding voice yasa kowa ya sha jinin jikin sa akayi mata shiru tana kammalawa tace ma safeenahn muje...
Sosai sarah ta gane da ita ake yi,amma abunda ya dame ta shi ne wannan warning din?
a ganin ta sai dai ace da wata ake yi amma iya sanin ta bata taba tsayawa da wani da sunan wani abu daban ba inba aiki ba..
a office din su, su ya su manyan sai da aka sake shigar da maganan sabida mr fidelis ya gama nuna musu yana tareda sarah 100 percent.
anan har mrs ruth ke gaya masa idan har ta kama shi da wani abu na daban wannan karon ba rufa asiri sai ta sa an tayyara shi a media...
dan wannnan sabanin da suke samu kwana biyu ya fahimce asalin sun tswangame ta ne ba wai kawai dan yarsu ba
Ranar sarah na office sec ta turoo kofa tace mata hajiya asmau na neman ta.
Duk dama tasan nasu baizo daya ba amma haka ta daure ta taho,
Zaune ta same su achan sama sun kame fuskan su babu alaman walwala..
tace salam alaikum can i come in?
Minti 3 sannan aka ce mata yes..
Tama shigowa suka bita da kallon hadarin kaji wanda ya sata sunkuyar da kai kasa..
Ta daure tace you called me maaam
mrs ruth tace straight up to the point meye hadin ki da fidelis?
Abun ya bata mamaki amma sai ta nitsu tace hes my curent whra supevisor maam..
Kallo ta bita da shi irin naji wannan rainin wayo
Hjya asmau ta wurga mata file gaban ta tace take this and read it aloud
Ta sa hannu ta dauka gaban su ta shiga karanta wa
Its a rule and legal actions ma duk wata Humanatarins activist na org din wanda za a wanzar ma duk wanda tayi comiting zina da officials ko aka kama ta da ire iren sexual crime and culprits.
Tun Sarah tana karantawa ranta ya fara baci ,yau ne rana na farko da taji ta kai har wuya wai shin me matan nan suka dauke ni ne?
haka dai ta cije ta kai karshe tana gamawa tace ta gama..
sauke ajiyan numfashi hajiya asmau tayi tace i hope u get tha in to your skull
.
Budan bakin sarah tace i dont understand maam.
Wht did i have to do wirh this?
Sun sha mamaki yadda ta bude ido tayi maganan sun fahimci ta fara gano me suke nufi da hakan ne..
mrs ruth ne ta dubi hajy sai suka danyi wani irin glance mai dauke da kallon raini da wulakanci..
Kinji Wai bata gane ba ko..
Mmm to zaki gane...ta dube sarah tafada mata hakan a tsime.
Sarahn bata sake cewa komai ba..
Hajya asma tace u can leave now
Daurewa tayi tace thanks...
dan hawaye har sun ciko mata tam a idanun ta
so this ppl are thinking that im worthless har da zan yi tunanin bada jiki na wa namiji kana aiki?
oh ya Allah Ko kadan basu daraja tunanin su akaina ba,and i hate when ppl judge me ...ta fada cikin ranta tana saukowa daga saman.
daga gefen dayan site din mr fidelis yake ganin saukowar ta aransa ya san ba ayai mata dai dai ba, don yasan idan mrs ruth da hajya asma sun hade waje daya sai a hankali..
Sarahn adaddafe tayi aiki cike da tunanin meyasa yau aka bata sexual legal purnishment personally ta karance...
abun ya sosa mata rai sosai...ta tsani abunda zai taba mutuncin ta..
sai wajen 6.0pm ta samu fitowa as usual ita ta raka hapsy waje suna tafiya tana tambayar ta wai shin meke damun ki me yau sarah.
A kasale tace babu komai hapsy, am just tired
Tayi murmushi tace hmmmmmmmm ok, ai yanzu zamuje gida zaki huta so pls chill ok? Nasan duk don kin gaji damu ne
yadda tafada maganan yasa sarah murmushin dole tana cewa " hapsy kenan, kin nace sai kin san ko wani abun aka min to shikenan dai we ll tlk about it tomrw..
anan suka rabu hapsy ta shige motar mijin ta juyowa da zatayi suka ci karo da mr fidelis a gaban ta..
Da kyar ta kwakwalo murmushi tace good eveniing sir,
Bai amsa ba ya mayar mata da murmushi...
yace sarah bukar,ina zaki je haka?
Tace im off sir heading home..
Sai ya dada taku kadan yace are sure komai dai dai ?
Asin kin tabbata kowa ya gama duties dinsa na yau ?
cikin mamakin tambayar tace yes sir ai yawancin ma an tafi gida its late..
Yayi shuru daga bisani yace ok
ta gyada kai a ladabce zata bar wajen yace sarah...
Lets have a word in my office now..
wani dum dumm kirjin ta ya buga da har zata ce nooo sai ta kawar da tunanin..
tasa ranta indai har ka kulla gaskiya tsoron me zata ji?
besides he's only good to her bai kuma taba kawo mata maganan banza ba..
Da wannan tunanin ta ce yes sir ...minti 2 bata kara ba ta biyo bayan sa..
Ko zama baiyi ba yace Mata sit down a dan tsakure ta zauna..
Duk sai ya rasa ya zai gaya mata manufar sa da ita..
daga bisani ya dauko laptop ya kawo ta gaban ta so close jikin sa kamar zai goge fuskan ta da jikin ta..
a dan daddafe ta kauce masa ,yana daddanawa daf da daf jikin ta kamar mai shirin zai nuna mata ko koya mata wani abun amma sai taga wani abun da ban yake yi..
Kamar zatayi magana sai tayi shiru dai...
Anan yayi gathering courage yace yay kikayi shiru kuma sarah muyi tadi mana..
Ta dago ta bashi kallon irin what? Kafin ta budi baki tayi magana yace
Me ya faru ne dazu naji asmau da ruth sun kiraki is there anything serious u can tell me ..
...
Ta danyi shiruuu daga bisani tace no sir babu komi
Yasan zata ce hakan yasa yayi murmushi Yace
sarah kina da saurayi ko?
tace no sir...why?
ya dada yiin murmushi nan ya dago ya dube ta yana bata wani lallausan kallo...yace dama nasan babu ruwan ki kekam,amma duk da haka kinsan hatsari ne babba hjy asmau da mrs ruth su sa ma mutum ido...sabida idan suka kama ka da wani laifin sai Ceton Allah..
tana shiru dai tana binsa da ido...
yace amma kinga idan kina da wanda zai tsaya miki a sama ko da nan gaba kinyi wani abu ba wanda zai ci miki mutunci....
Anan tace but sir,idan har bani da laifin komai bana damuwa da opinion din wani i wll just do my job.
impressive yace, yana jin confident voice din nata dake fitar da kalma calmy
Yace sarah kenan,ure a principled lady amma am fraid bazaki kai nisan kwana akan career ki ba
Maganan sa sai ya sa ta sake murmushi tace why not?
Yace sabida kina bukatar uban gida kamar ni,wanda zai tsaya miki achan sama,ehen kin gane ko? Ya karashe da wani irin shuumin murmushi
She was shocked don sai yanzu ta dago sa da kyau
Sai Tayi shiru tana tunani...
Babu kunya sai ji tayi ya dafo kafadar ta da hannun sa yana binta da wani irin kallo, a firgice ta dan turo hannun zata mike tsaye ya maida ta da karfi yace"sarah ke ba yarinya bace kuma nasan kin fahimce ni zan taimake ki sai ki taimake ni...
and done !!ur career is safe har abada..
Wani dan banzan murmushin takaici ne ya kufce mata " tace like seriously sir? Ta dan yi tsaki ta mike ta dube sa"Amma ka bani mamaki...ta dada dan jan tsaki... im sorry im not the type sai anjima..
jakar ta ta dauka zata fice agagauce, bai motsa ba amma sai ya daka mata tsawar come back here sarah..
ko ta kula ta kama hanya shiru a hujajan ya zo ya jawo ta da karfi...
Cikin bacin rai ta budi baki zatayi magana yace ke wai tunanin ki duk abunda nake miki a banza ne? I tot ure smart,...Just imagine how i made you above safeenah gaban kowa da kowa amma wai har ni zan zo miki da abu kice bazaki yi ba? Muryan ta har na rawa tace ohhhhh dama abun kenan? But i neva asked you to help me sir...this is WHRA we r ppl of respect and diginty sabida haka babu ruwana da wannan kai kasani,...zai yi magana ta dakatar da shi" idan kuma kace zaka takura min im sorry will have to report you..
Yayi dan karamin dariyar gadara yace wollah yaro yaro ne,ai na dauka ke wayayyace ashe bakida wayo,we cant keep talkimg like kids kije nabaki nan da 2 days kiyi tunani ki kawo min kanki nan ya ajiye gurst house card dinsa ...yayi wani shuumin murmushi " yace if not zaki ga abunda zan miki..mark my words.....
Ko amsa shi batayi ba ta hankade hannun sa zata bude kofar charaf suka yi ido biyu da yazeed daf da daff ..
Gaban ta ne yayi mummunan bugu sabida Kallon kallon da yake binsu da shi alaman yaji
kaf abunda su kace..
*OFFICIAL CATTY*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top