END To PART

*🅱BRILLlANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™\jan\2019
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
🍒🍒
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@  SURAYYAHMS*

_welcome to the world dear boy areef Allah ya raya mana kai da imaani_

_YA ZUL JALAL WAL EKRAM_

_PAGE9_

Durus nayi tsaye daga bakin kofa ina maida musu kallon firgita da suke maido min,

baki na na bari nace ummah?me nake ji haka ummah? Abun da kike fada gaskiya ne ummah kiyi min bayani..?
Jiki na rawa yake,sai na kasa controling  kaina na ganin ta kasa amsani ya sa na yanke hukunci sai na sulale na fada kasa sumammiya

Kuka ummah ta fashe da shi tana wayyo Allahn ta ta shiga uuku
..su anty sahura ne da alhj shayal suka yo kaina
Aka debe ni ruwa ruwa zuwa asibiti..

Ban motsa ba har sai da aka samin ledan ruwan guda biyu sannan na soma dawowa hnkalin na ,wani irin ciwon kai nake ji mai dauke da cunkushe war tunani

Lumsasshun idanuna ke juyi a hankali ina kallon su sunyii cirko cirko musamman ummah dake ruwan hawayen har yanzu...

Na lumshe ido ina jin su anty sahura suna min sannu sannu ita da alhj shayal amma sam ummh ta kasa zuwa kusa dani...

Har aka sallame ni muka koma gidan mu,...
Tun daga mota nake kuka ban sake kallon ko daya daga cikin su..
sabida haka ba wanda ya iya tankawa har muka sauka

Daki na na wuce na fada kan gado na shiga kuka mai dauke da rudani.  ..

Daga palour ina ji ummah ke ce musu kar ku daga hankalin ku ni zan mata magana ni kadai...

Alhj yace mata are you sure? Cikin dauriya ta gyada kai..anty sahura tace to mu zamu jira ki anan...

Daga nan ummh ta zo ta same ni ..

Gefe da ni ta dan zauna daf ban ma sani ba ta miko hannu a sanyaye
Ta shafo suman kai na da bari a bude....shiru na dan yi ina jan Zuciya daga bisani na dada nitsar da kaina cikin pilow alaman bana bukatar jin wani maganan ta,

sai naji tace saratu" ki yafe ni saratu.
Saratu kar ki guje ni, ni mahaifiyar ki ce baxan taba yin abunda zai cutar dake ba a duniya ina kaunar ki saratu...

muryan ummah ya sauya sosai dan ni kaina jin maganan nata nake a chan kasan kwakwalta da hayoyon jini na...

hankali na ya tashi
Amma haka Na daure na mike na zauna idanun wa mu duk sun kada sunyi jajir...na dube ummah da muryan fushi nace haba ummah,anya ummh tace kuwa ke ?ummah meyasa zaKi saka kanki a wannan mummunan kazamar hanyar?ban taba tunanin zaki aikata hakan ba ummah shin me zakice ma  Allah,a kauyen mu idan suka ji kina haka ai kowa sai yace haka dama halin ki yake na gaskiya ummah meyasa kika yi haka...? Na dan fashe da kuKa.

Tayi shiru ba tace komai ba,tana sobbing a hankali tana jan hanci..
Tace kina da gaskiyan ki saratu komai ma zaki iya tambaya ta kuma duk wanda yaji nayi hakan zai sha mamaki
amma ki sani bazan taba yin wani abu haka kawai ba indan kaina ne har abada na hakura da duniya sai dan dan ke sarah,ke kadai ce madubi na bana son kiyi rayuwa irin nawa,tace saratu ki saurare ni na nema miki rayuwa mai kyau nan da satu biyu zaki bar kasan nan ki soma rayuwa mai kyau ki cuika burukan ki da alkwarin mu,ta kamo hannu na cikin jimami tace ina zaki cigaba ma mahaifiyar ki biyyaya?

  Na yi shiru, ina binta da kallo,ni dai sam sam na kejin na tsani komai i  cant believe that ummah ta dawo dai dai da karuwai sabida ni...haka kawai nake jin bakin ciki sai na gwammaci gwara na mutu da wahala da  na sata cikin wani hali..
da karfi na fincike hannu na na mike tsaye cikin dacin rai da masifa nace ba wani biyayyr da zan miki ummah muddin baki bar wannan sana'ar ba, natsane shi,bai dace da ke ba..kuma bazan taba sake karban wani abu daga gare ki muddin baki bar shi ba ayau din nan...makaratar da burin duk na yafe su..

Nan Ta mike ta kamo ni zatayi magana na shiga firgici ina magana a zuciye nace sam mu bar kayan nan anan da duk abunda ta mallaka mu koma wani wajen na hakura da rayuwa mai kyau din..muddin sai ta dawo haka kafin na same shi...

Duk iya yadda ta so tayi controling dina haka naki na turje sai maganganu nake ina borewa wanda yasa anty sahura da alhj shatal shigowa..

Kaya na ne a kasa ina kwasowa ummah na maidawa acewa na zan dauki dan tsumman da muka zo da shi, na bar mata gidan ta..

Ranar Na sa ummah kuka sosai hankalin ta yayi mugun tashi..

Karshe sai da anty sahura ta wanka min mari sannan na dawo hankali na na yi shiru,

Ita ta fara bani labarin asalin abunda ya faru da ummah tun ranar da akayi raping dinta a hotel don abata kudin jinya na kar na mutu,da duk wani abun da suka faru strip club haduwar ummah da alhj shayal kaf ta rero su tsaf bata boye min komai ba...

Tace min bani da hankali ashe? Tace toh nine silar sa ma uhmman ki ra'ayin fitar dake daga wannan bakar rayuwa sai ki kashe ni saratu, Waya gaya miki haka rayuwan take tafiya?

Wato kin gwammaci irin rayuwar da zai kaiki ga halaka da bakin ciki ya kashe uwar ki than wanda ummahn ki ta dage ta sa kanta akai bada son ranta ba don ta tsiratar da ke?

  A lokacin na dada da sumewar tsaye ina kallon ummah..

Wani irin halin bakin tausayi da razana na shiga
A sulale na koma na zauna kan gado na kife kai na in kuka mai zafi..

Haka kawai naji ina ma nasan abun haka ne tun farko da na mutu kawai na barta ta huta ma rayuwan ta,

Ganin nayi sanyi na kuma shiga wani hali ya sa alhj shayal ya kamo hannu na ya fitar da ni daga dakin ya bar su su biyun.

Shi ya zaunar dani ya shiga rarrashi na sosai yana bani hakuri da kalamai masu ratsa zuciya da sa tausayi sosai
Sai yau nake sanin duk abunda ke gudana daga
Tushen sa...
Duniya gaba daya naji tayi min zafi sosai..

Dan zaman da mukayi da shi ya bani shawaran naje na rarrashi mahaifiya ta din kuwa ta bar wannan hanyar da nake tunani yanzu burin su duk ya koma kaina ne sannan na dauka wannan shine asalin qaddara rawuyar mu..  Na mance da komai.

Na amsa shi tare da basa tabbacin zanyi hakan

bayan tafiyar su da anty sahura
Ni da ummah ne a gidan,
Gaba daya sai ina jin Nauyin naje na same ta da maganan haka itama ta ke dawainiya da fargaban haduwa da ni..

Sai da nayi bacci na tashi chan dare naje daki na same ta,
Anan nake fitar da abubuwan dake raina na tausayin ta da bakin cikin abubuwan da suka faru da ita..

Magana mukayi mai nauyi mai cike da Donkin fahinta da manyan manyar alkwari masu karfin gaske. . .

A wannan daren ummah ta ke sanar dani cewavta bar wannan harkan har abada kenan tunda yanzu tana da abunyi mallakan kanta,nika dai ce agaban ta yanzu

Nima nace,nayi mata alkwarin share mata hawayen ta kuma insha Allahu zan cika mana burin mu,zan yu kokori naga na goge mata mummunan kaddarar data gina mu akai da alkhairin da nake shirin yadawa ma al'ummah anan gaba..
nayi ma ummah alkwarin a duk inda mace ko wani marar galihu kwantankacin irin namu ke neman hakkin sa ni zan kare masa
Shi a ko ina yake,

Ummah ta sa min albarka,ta kuma ce min wannan shine bakar gaddarar mu da ya zama mana bakar siiriin da dole mu binne sa ,wani bazai sake jin wannan maganan ba.

Tace"Daga yau zamu dauki matakin gyara rayuwar mu da kanmu tunda ba abunda muka rasa...

Ta kuma ja min kunne akan na dauki sahura da alhj shayal abmatsayin yan uwan mu dun ta tabbatar min yanzu haka babu komi aransu game damu sai fatan alkahiri da samun cigaba....

Haka, har aka kira asubahi muna zaune muna tataunawa..

Washe gari da muka kimtsa nan ne ta ke nuna min komai na makaranta na,

Zanje karatu a france,
Cikin makarantar da yafi kowanne tsada a kasar ta bangaren ilimin fasaha dan adam sabida na samu kwararen ilimi da basiran sarrafa rayuwa ta cikin sauki ...

Haka rayuwan mu ta kasance.
Na dawo tamkar kwai a tsakanin su su ukun..

Anty sahura kullum tana dada kara min karfin gwiwa akan na kyautata ma ummah kar na taba mance wa da ita a rayuwa..

Shi alhj shayal ba abunda yake so na sa araina illah abubuwan dake gaba na da zan fuskanta na karatu.
so duk wani stratergies da sarkakkiya na shige shige da dogaro dakai ya bayyana min su...
Musamman yadda Ya lura ilimi na kyauta ne daga Allah ,bana daukar lokaci nake gane abu uwa masu dumbin yawa kusan komai akace min nakan sa akaina nayi shi akan kari hr sai na samu gamsuwa..

Da haka ya dada cusa min Ra'ayin sarrafa basira na ta hanyoyi daban daban. Har ya hada ni da wani computer engineer a russia akan idan naje zamu na comunicating zai na nuna min abubuwan daya kamata ta internat...

Alhj shayal ne ya soma tafiya abunsa ya mana bankwana

Sannan muka koma sabon gidan mu daya bamu kyauta mai shegen kyau .

Yanzu haka ummah na ne kawai zata zauna gidan..
Ranar da na tafi karatu ranar anty sahura itama ta je garin su wajen iyayen ta,

Munsha kuka kam amma da hakan muka rabu kowa ya sa niyyar abunda ke gaban sa

Yanzu ummah Ta fara tunanin fara aikin ta a matsayin managing director na gidan kaji da gidan gonan t duk dama  alhj shyal ya tabbatar mata da cewa bata bukatar sai ta je makaranta muddin tana da fasahar rike sana'a da tatttali komai zai tafi mata dai dai tunda ga maiakatan ya ajiye mata su kuma akwai kayan Aikin zamani..

Rayuwar ta take a tsaftace kuma a saukake Hatta ssa danjuma baisan da hakan ba,

Sai dai tunda anty sahura ta tafi ummah bata sake  jin duriyar ta,
Tun tana damuwa har ta dawo ta rusuna ta na binta da addua o...

Nikam dama baifi sau daya muke waya a sati guda ba.din abubiwan danaje na tara achan ya banbanta da wanda na ke gani anan...

BAYAN SHEKARA BIYU

... Yanzu haka shekara na 19yr dai dai kuma ina aji biyu a higher institution din mu,..

"anan din off classes nayi na wata shida ina koyan abubuwan da na yi missing sosai don na kamo standard din tsarin ilimin su,kuma sai da na kammala kafin nafara attending karatu na na gaba da secondryn a sir marknickels college france one of the most expensive,indurious and ambitous schl a kasar baki daya.

A zangon farko Abubuwa dayawa sun faru dani, sabida na je ne da zuciyan yin abunda ya kawo ni don haka bani da aboki ko abokiya kuma ban daura makaina shiga hidiman kowa ba,..

hasali ma da kyar na saba da abubuwa dayawa anan.

'Saukin da na samu shine
Bamu da yawa a duk ilahirin makaranta ba zamu fi 400 ba all over the world, Don kuwa duk wanda yake makarantar baya zama fayau nikaina a lokaci kalilan na fahince cewa duka students din makaranta ma gaba dayan su miskilai ne kowa kansa yake gani kuma yake ji

social events din is very rare a haka shi din ma akanyi organising dinsa ne in a very educative way "dalilin haka ya dada sa ni sosai na kara shiga hankali na dan dole na na waye na san me ake kira kama kai, jan aji rike mutunci da tsare harshe daga yawan surutu,

A lokacin Komai ilimi da basira na nake sawa na koya,thy all belive that dan talaka bazai taba zuwa nan ba.

"Sir marknickel waje ne wanda ake amfani da basiran dalibai ake nuna musu yadda zasu sarrafa shi ta hanyar basu daman shiga harkokin daya shafi career su da dama a kafafan harkoki na duniya...!

"Karatun littafi dana na'urar computer da nayi akallah bai fi na shekara guda ba,a shekara na biyu na fara shiga salon tsarin makarantar kamar yarda suka tana dar
i wanted  to be an influential industrialiast and a philantropist..

ma'ana zanyi harkan kasuwan ci na business mai hade da tallafin kulawa da dan adam...

Anan Malaman mu kamar iyayen mu haka suke wajen bamu muhimmaci da shawari na gari basu taba nuna maka gazawar ka karara sai dai su baka constructive critism ta inda zaka kara samun karfin gwiwan akan abunda ka sa agaba.

_wani dogon ajiyan zuciya tayi sannan ta dago ta kalle sobby eyes din sa,dake shake da nauyin zuciya, rudani da tausayin ta kusan Na tsawon minti 5 sannan ta dauke kai ta cigaba kamar ba ta san tana yi ba"_

Tace"Nima anan na hadu da kai _mr MAHFUD LINGARD_

"he's my true hero and a role model,shi ba dalibi bane amma anan makarantar ya gama  last few years,

He's now humanatarian ba sa'a na bane,don a tsaye zai bani shekara akalla shekara  8 ko 9 na haihuwa i think he's 27years old now amma ya kai duk matsayin da nake so naje a rayuwa ta..

Duk da Yanayin rayuwata ya sa na dan banbanta da sauran mata wajen sa kai da jajircewa gashi bana kula kuwa sosai amma shikam sosai nake jin kaunar sa Har cikin raina.. i don't mean love na soyyayya kawai burge ni yake yi sosai.

A zahirin gaskiya idan na dube sa sai na rika gani kamar future na ne yake displaying a hidimonin sa, don duk yadda nakai ga son taimakawa jama'a araina ya wuce nan, sannan yana da kudi sosai baya kuma da girman kai sai dai kamar ajinin mu ne miskilan ci da ni da shi we r almost the same in this aspect.....

Na dai ji anacewa mahaifin sa sa wani babban craft scientist ne wanda yake aiki da world class team wato kungiyar scientist na duniya mai taken NASA,come to think of it mahfud Lingard is every woman's dream,very gentle, he's tall
Healthy looking and a very sexy charming prince...

Duk da ma bana sa kaina  akan hakan amma nasan dole ne duk wanda  ya dube sa yace ya hadu
Cos He's no different from a perfect world class model.

Ni dai tun Lokacin da na fara ganin sa nake kokarin bin tsarin sa a dabaran ce musamman  a duk lokacin da ya zo mana presentation a humanatarian lecture hall ...

da shike fannin sa nima nake idan aka dawo layin career ta na philantropist
Yanzu haka kamar ma shine assistant official na kungiyar ilimin taimakan alumma da bada tallafi gaba daya..

Nakan bada hankali a ko yaushe wajen jin labarin sa da misalin sa dan wani bin har sai ya sa mu kuka musamman iri na da muke da boyyyaen ciwo a zukatan mu..

Ranar da na zo daliba na farko a competition dana kare wani muhawwara tsakanin mu da gwarzayen dakarun makarantar sound philantropist a america ranar ne muka dawo abokai da ni da shi.

Sabida ya tsaya min a lokacin da nake yi sosai,sannan yaba da duk himman da nake sawa wajen kare client dina

Sosai ya fahimci abubuwa dayawa a tattare da kalmomi da zuciya na wanda ni kaina bansan ina fitar wa ba...

Kullewar abokan takan mu bai dauki lokaci ba sabida nima ina yin sa sosai, i just take that as an opurtunity..

Daga nan kuma sai ya bude min hanya yana dada sa ni jagoranci a kan competiton daban daban a kasashe a duniya yana  dada fitar da danyen basira na da hazaka ta...

wani bin idan abubuwan suka mana yawa har nakan manta da gida da kowa ma sai mr MAHFUD..

I become so attached to his ways..soo talented ta kowani fanni har da wajen bani shawarwari

Don ko da na kawo masa maganan career ta na industrialiast shi ya bude min hanyar da na samu shiga young business woman  class a online daga kasar germany,

registration da duk wani hayaniyar programes din duk shi ya min..you can imagine how generous he is.

A haka Kafin na kai aji uku na saba da duk wani wahalan shige da fice
Da taimakon best friend dina mr mahfud na dada zamowa jajirtacciya abun kwatan ce cikin dalibai..

Ina aji na hudu na mallake share a companyn sarrafa wheels a japan
So mukan je a lokaci lokaci tare da shi muna harkokin mu.

Yanzu ina namen shekaru na 4 kenan a france ban taba zuwa nigeria ba.

"Ummah ne ta ke zuwa a duk lokacin data samu sarari ta duba ni..

ita kanta tasha mamakin yadda na dauki rayuwa anan da muhimmanci
Da kuma manyan abubuwan dana sa agaba na na cigaba take

gashi jinin su ya hadu da mahfud kamar yadda nawa ya hadu da shi sosai..

Yanzu haka shi nake kira hero shima yana ce min heroine.... _anan ma tayi murmushi kafin ta cigaba_

He made everything possible for me, duk harkoki na na tafiya min dai dai har ma fiye da yadda nayi zato.

His time,his money his free smiles a duk lokacin da na gaza yana tare da ni..

A shekaran da na cika karatu na chasss a france cikin sir marknickel college aka yaye mu...
A time din ina da shekara 23yrs a duniya

Nayi farin ciki sosai da gama makaranta na musamman fannin industrial dana samu baban award na student of the year all thanks to god nd my hero mahfud...

sai dai a dayan hannun kuma naji bakin ciki sabida jin sakon rasuwar alhj shayal wanda aka fi bada karfin cewa plane crash ya yi ajalin sa..

Ga ummah taki tayi aure kullum tana tsoron yadda zata tun kare zama da wani da namiji a wannan
Irin yanayin rayuwa da muka taso da chan aciki..sam bata yadda da kowa ba ga shi ta mallake hankalin kanta sosai ta nemi yaki da jahilcin nan tayi arzikin kanta har ta sauya gari da gida ban sani ba.

Cewar ta gwara ta zauna da ni a hakan idan Allah ya ji kanta zai hada ta da miji na gari amma bazata taba takura kanta ba ..

damuwar ta yanzu  yafi bada karfi wajen neman yafiyar ubangiji tunda ta kafa kanta yanzu take jin nauyin abubuwan da suka riga suka wakana da ita a da chan.

alhamdullhi kusan duk abunda akace na neman lada ne da goge zunubi ko da za'a cuce ta ne kuwa takan sa kanta taga tayi da niyyar Allah ya yafe mata kurakuren ta..

Anty sahura ce naji labarin wai tayi aure har ta haifi da na miji agarin su chan gaban iyayen ta..

  Da shike graduation ceremonyn mu ya zo dai dai a lokacin  umrah yasa ummah bata samu xuwa ba..

Dan nima na ce mata zanje chan  dev singahniah imperial college na human right activist
Nayi aikin wata shida domin na samu licend din kwarewa wanda zai bani daman shiga  organisation na  human right a united nation kamar yadda mahdfud di na ya min bayani kafin ya tafi...

Don haka ana gama shirye shiryen komai nayi ban kwana da sir marknickels college nayi hanyar kasar india don na cimma buri na na karshe a duniya...

Alots of readers that are waiting for me to sayart samarin shaho dont know that im alredy posting it aas a new story here,so pls do me a favour by helping them find it by comenting and voting👍❤...thnks alots fans


*FOLLOW WATTPAD @SURAYYAHMS*

*OFFICIAL CATTY🐈*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top