BEIMAN LOVE

*🅱BRILLlANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™\jan\2019
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
_The scorned_
🍒🍒
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@  SURAYYAHMS*

27

Daga isowar su suka neme wajen rabewa zuwa washe gari da safe
Don dukan su ji suke kamar basu taba ganin ta ba sai yau.

Sosai suke tuno da abubuwan da yafaru sau dayawa shikan sa baba babaji jikin sa ya bashi wani abu game da ita da ta zo din amma ya kasa ganewa .

Amma kuma bai taba kawowa saratu har zata rayu ta zamto hamshakiyar ya mace kamar sarah ba.

Cikin nan zaman nasu sageer ya nemo musu adreshin da zai kai su kai tsaye babban branch din su inda suke.

Ko da washe gari yayi sai suka shirya tsaf suka nufi nan organisation da niyyar su same ta.

Sam sun kasa hakura dukan su sun sanya aransu hala idan suka yi baki da baki da ita Allah zai rage musu wani abun.

Sai dai kashhh tun safe take cikin comittee na wani muhimmin meeting
Wanda ya dauke su dogon lokaci basu fito ba

Yau saura sati biyu wata gudan da suka bayar don su fara karban mutanen da suka yi registered don basu kulawa...

Su baba babaji Gaba daya a motsare suke kauyen ci da tambarin talauci da wahala shine ke haskawa a fuskokikn su da suturan su..

Anan ma da kyar masu gadi suka amince auka shigo harabar org din

Don duk wanda yaci karo da su bazai dauka ko ba roko ya kawo su ba...

Anan suka kai ciki suka tarar da securities.
Tun kafin suce wani abu,
Aka tsare su da tambayar ina zasu je anan,kuma meye kawo su?

Har bakin su na rawa suka bayyana wajen saratu suka zo..

Anan ma ba irin juya kansu da ba'ayi ba sabida wasu cewa suke basu san wata saratu anan ba

Babu irin bayanin da basu yi ba amma sai wasa da hankalin su ake.

Sosai ran sageer ya baci, cewar sa itace ta zo kauyen su fa kwanan nan..
Wasu daga nan sun gane ta amma don sun raina shigar nasu da yanayin nasu sai suke enjoying wasa da hankalin nasu.

Cikin haka, aka sake yin baki manya daga kasar waje.
Gefe su baba babaji suka rabe suna kallon ikon Allah.
Ba don ya danyi bokon nan ba da sai yace halan ma ba kasar nigeria yake ba.

Ko ena cike yake da gwarjinin wayayyaun jami'ai da kwararrun ma'aikata

Suna tsaye anan ba wanda ya sake tanka musu,sai dai ayi ta wuce su ana zaga su.

Ransu yayi matukar baci meyasa ko kadan basu da daraja a idanun mutane?...
Sun dauka ko a kauyen su ne kawai ake musu kallon haka ashe ko ina ma zai iya faruwa.

Bakin ciki ke cin kowannen su ga fargaban ganin yadda abubuwa suke tafiya anan.

Chan wajen karfe 12 rana abu yaki ci yaki karewa
Wata mata ce ma'aikaciya ta amsa su da cewa suje kawai su dawo yau sarah bata da Time....

Kuka baba babaji ya fashe da shi na takaici, ga shi tulin lokacin da suka dauka anan ba wanda ya basu ko kyakywan tarba bare wajen zama.

Ga azaban yunwa nacin cikin su duka,..

Abun da ya fi ci masa rai ma shine yana ji yana ganin wasu daban suna zuwa ana amsa musu a mutunce amma su ba wanda yake basa kulawar sa akan su

Hawayen sa sun ki tsayawa cikin tunani yace rayuwa kenan Wai har ni babaji ake wulakantawa akan saratu?

Ganin yadda sageer yake bashi baki akan suje su dawo goben ya sa security ya tunkaro su tare da ce musu su fita kar su jawo musu hankalin mutane....

Bakin ciki sosai ya ishe sa,..abun dai ya musu zafi sosai

Cikin bacin rai,baba babaji yace"
Da Allah tafi chan, bayan kun gama wulakanta mu? Mutanen banza mutanen wofi,inche dai nan wajen offishin saratu ce?
Kasan ni waye ma saratu kuwa?....sageer ne ya riko sa don sosai ya balle yana maganan cikin radadin zafin rai da bakar yunwa

Dariya aka fara masa musamman da suka ji yace ko ansan shi waye ma saratu?

Kowa yasan mahaifin saratu ya rasu,so what?
Wannan din bai wuce yace  makabcin su bane a kauye,

Securityn kansa sai dariyar yadda mutane suke fassara bacin ran baba babaji suke cikin tsokana da raha..

"zo mu tafi baba babaji,wayannan ba su san me ya kawo mu ba?
Amma na tabbata idan saratu ta fito zasu san mu waye ne.

Lokacin idanun baba babaji sunyi jajir, yana bambami securityn na kan ce musu su fita kawai..har yakai su bakin gate....

Anan waje suka dakata yana share hawayen sa ,
Shikan sa sageer baiyi tsammanin ran baba babaji ya baci haka matuka ba.
  Yace tashi mu tafi mu nemi wani abu muci,inyaso gobe ma dawo kamar yadda suka ce..

Da ya dago ya kalle sagir din sai ya fashe da Kuka yace saratu fa yata ce,amma ganin ta kawai sai na wulakanta wannan wani irin rayuwa ce?

Kaga shiyasa na nace zan zo nan ko zata yafe ni wani abun ya ragu da ga cikin bakin qaddarar dana jefa kaina aciki.

Sosai sagesr yaji tausayin sa gashi kuka yake har jikin sa na rawa shikadai..

Duk suna wannnan yanayin yazeed da tuni ya hango su sai ya tsaya lura da me suke ciki

Musamman da ya dago fuskan baba Babaji,ai ya ma taba alkawarin zai sa akawo sa offishin sarah amma bai samu daman yin haka ba

Cikin ransa sai ya fara tunanin kar dai yaji shiru ne ya sa ya zo dakan sa?
Kai amma ban kyauta masa ba..is not easy mutum yayi rayuwar sa cikin ciwo nadama da tsangwamar mutane..

Gashi ni da na masa alkwarin samun sauki ban kula ba..

Da haka ya sa ya sauko cikin azama yayi kansu,
Sosai yaji wani irin gani su anan din.

Yana isowa suka mike tsaye, zasu gaishe sa sai shi ya riga tanbayar su da cewa yaushe suka zo?

Shikam sageer bai gane sa ba amma baba babaji ya so ya fahimci fuskan sa.

Yaxeed Yace" kamance dani ko?
Nine nazo wani lokaci nace zan sa akawo ka offishin sarah,

Murmushin bazata baba babaji ya sake Yace Allah na gode maka,nan ya gaya masa cewa ai saratun da kanta ta zo amma abunda yafi bata masa rai yanzun wulakancin da aka musu ne akan ganin ta.

Yazeed ya dauka ko duk kauyanci ya sa suke refering dinta as saratu,
Sai ya ga kuma sun nace suna magana akan haduwar su da ita,yanzu haka ma rokon sa suke yi ya taimaka su ganta..

Basu damu da yunwa ko gajiyar da ke damun su ba muddin zasu hada ido da ita..

Tuni wani abu ya basa maybe is a personal issure... amma sosai yake so yaji don ya sha mamaki kuma kansa ya daure matuka"

Me hadin sarah da wayannan? How did thy know her,ko tayi musu alkawarin wani abu ne? To meye wannan din..

yasan dole sai ya yaudare su  kafin ya san kan zancen,sai yace kuyi hakuri tukunna kunga yau sarah tana da manyan baki bazai yuwu ku ganta ba,
Amma ni zan je daku ku huta ku ci abinci gobe da kaina zan sa sarah ta saurare ku..

Murna akan murna baba babaji har da rusunawa kasa wajen sa ma yazeed albarka mai cike da godiya da karamcin nasa

Haka ya sa su a motar sa ya kaisu wani karamar hotel, anan ya odering musu abinci mai shegen dadi da tsada kaji ne nasha nasha mai qamshin dadi ga abubuwan jika magwogro.

Yana daga gefen su suka haura kai ham ham kamar dan wuta yaga gasashen nama,

Baba babaji naci hr zufa na saukowa akan nasa kamar wanda ke cikin Shower..

Duk yana kallon su, sai hiran santin suke
Time to time yana sa musu baki

Cikin salo yazeed din yace amma da cahn kasan sarah ne ko?
Anan ba wanda yake zuwa ganin Ta kai tsaye sai akan lokacin da ta basa...

Baba babaji ya dago a sanyaye ya dube yazeed yace "nasan ta sosai..shiyasa ma kaga na zo don na same ta.
Saratu ai yata ce...

Sageeer yace haka ne, yar sa sace ,ai wannan daka ke gani oga, shine mijin mahaifiyar saratu
Bayan mahaifin ta ya rasu,

Cikin tsananin mamaki yazeed yace ohhhhhhhh
Kenan kai mijin maman sarah ne? Amma ai mahaifiyar ta bata da wani miji a yanzu haka..
Ban fahimce ka ba.

Baba babaji Yace ai mun rabu ne,

Yazeed yace ohhh ayyah..
Toh meya faru ko zaka iya fada min,?
Kar ka damu aiki na ne taimako zan taimaka muku..

Su kan sun yarda da yanayin yazeed beside shekaru aru aru kenan babu wanda ya dube su da idon rahma har ya kashe kudin sa akansu ya basu muhalli da abinci sai yau..

Gashi har ya na cewa zai taimake su...rabon baba babaji yaji wani mutum na daban haka kawai yace zai taimake sa ai ya mance.

Sai abun ya taba zuciyan sa anan ya taso ya zauna shi da sageer..

Nn Suka shiga bada yazeed labarin saratu da ummahn ta in è best way thy can..

Sai dai cikin nuna nadaman su da neman yafiya suke bayanan nasu,
Sannan suka tabbatar masa da cewa lallai sarah itace saratun su.

Mamaki da rudani ya hana yazeed magana,sai baki yake basu yana gwada masu babu komai shi xai taimaka

Amma cikin ransa is full of questions .
Musamman fannin ta ya akayi sarah ta kufce ma wannan mummunan qaddara ta har ta  zamto haka?
How did she make it? Yasan dai a waje tayi karatu kuma mum din ta na da sana'ar ta da kudin ta but how did thy make it?

Amma ace a haka suka taso?Toh ya akayi suka samu duk wannnan rayuwar?Sata sukayi ko karuwanci?

ai yasan cewa ummahn sarah har yau bata sake aure ba bare ace arxikin mijin ta ne,but how?

Kenan akwai boyayyen sirrin sarah da ba wanda ya sani sai ita..

Ya dade yana kawo tots daga bisani yace ma su baba babaji,
Kar su daga hnkalin su,
Shi yasan yadda zai yi suga sarah amma su daure su bashi zuwa gobe,
Godiya sukayi ta masa sai dai hankalin sa bai ya wajen su,
Tunanin kawai yake yi kala kala akan sirrin rayuwar saratu daya dan ji yqnzu...
Now he knows where her abject inspiration to help the needy is coming from.

Babu shakkka jajircewar saratu ya samo asali ne daga ciwon qaddarar ta dake makale a zuciyan ta..

But this is not the end yana so yaji ya akayi ta cimma burin ta har tayi,ilimi da kudi haka..

according to baba babaji cewa yayi da ya fara nadama ya shiga neman su a da chan ance masa sun tafi birni a motar kano.

Kenan a kano saratu da ummah suka yi kudi?a kauyan cin nasu??,damn but they r oll women...thy r suppose to be weak,inma ba haka ba ai zai yi wuya ace mace ta shiga wannan halin sannan ta mance da shi so easily har ta tashi ta daga rayuwar ta..

Sai ya sa aransa dole sai yaji sauran kwaf kwaf din sannan ya samu nitsuwa

A daren daya koma gida sai ya tura makudan kudi ma wani  mai suna zulkhi cewar sa ya hau jirgi ya taho su hadu gobe a gidan sa.

Anan su baba babaji suka kwana,

Washe gari da sassafe yazeed ya kawo wani agents dinsa ya hada su tare yace akai su ga saratu..

Daga nan shi kuma ya wuce wajen zulkhi bai bari ma sarah ta san da shi ba..

Anan ta karbe su ba yabo ba fallsa ta kaisu wani wajen daban suka samu zama.

Kamar a mafarki suke ganin realityn su,ita kuwa bata boye musu ba ta fada musu itace din,..

Duk dama ta sha mamakin ganin su amma sai bata nuna ba,..

Anan duk suka dada warware mata duk munafurcin Da suka mata cike da nadama da neman yafiya
Suka roke ta don ta yafe musu..

Dukan su kuka suke yi har da ita don Tasan za'ayi hakan ya sa ta sa suka bar office din gaba daya suka je wani waje.

Bayan sun fahince juna ta kaisu gida har wajen ummah,anan ma suka nemi gafarar ta.

Dan itakam ummah addini yanzu ya shige ta sosai halayen ta ko da ba ace ba kasan imani ya ratsa zuciyan ta ya mamaye shi..

Duk da bata iya hade baqi ba,takan zauna ta kunna karatun qur'ani tana ji yana mata dadi sosai.

Tsaban naci har ta haddace wasu surorin cikin sauki ta haka.

Kuma zata iya daukar fiye da awa 4 tana kallon wa'azin malaman nan bata gaji ba.

Gashi dama da saratu ta samu cin gaban rayuwa sai ta rage mata zuwa aikin ta, yanzu haka managers din ta ke lura mata da gidan gonan ta da gidan kajin ta.

Su baba babaji A duk yadda suke ganin saratu tayi musu karamci bai kai yadda suka ga ni wajen ummah ba,don sosai ta mance da komai sai ma nasiha mai shiga rai data yi musu..

Haduwan su da ummah ya dada zafafa zafin nadaman da baba babaji keji aran sa....lallai ya kasance hasararre ya kaskatar da rayuwar gambo amma Allah ya nuna masa cewa gambo ce mai nasara tun a duniya.

Kwana biyu suka yi anan gidan su saratu cike da goma na alheri suka koma gida...

Sarah ke tabbatar masa da cewa idan sati biyun ya cika zata sa a dawo da su a fara masa jinya...

Tsaban dadin yanayin da suka samu yafiya cikin sauki ya sa suka mance da yazeed don haka basu ko fada ma sarah cewar sun hadu da shi ba har aka rabu

Ita kam dama yanan nade a zuciyan ta amma kwana biyu data ga kamar ya share ta ya sa ta dan bada hankalin ta wajen ayyukan dake gaban ta

Amma yau da su baba babaji suka tafi

Tana Dawowa sai ta wuce straight offishin sa ko zata lallaba sa taji meye matsalan ,

Amma da mamakin ta sai ta ga offishin sa a
kulle
Ta sake kiran layin sa shiru shi ba off ba shi ba ringing ba.

Ko da ta tambaye farida secteryn sa ce mata akayi
Kwana biyu sukan su ba su gansa ba kuma basu san inda yake ba.




*Writers coments continued*
_samarin shaho is also to ladies that have everything in life but give less important to their god,sarah na daya daga cikin wanda suka mance da wani muhimmin bangare na rayuwa...misali, Ku dubi yadda sarah take mance da yin sallah akan lokaci idan suna tare da yazeed,ku fada min meyasa hakan bazai faru da ita ba?...yan mata ku tsaya ku kalle rayuwar sarah nan gaba... its very important...."kenan dan wani mummunan qaddara  ya faru da kai arayuwa sai ka sa burinsa agaban ka fiye da komai har kula da ubangijn ka?toh wa zai taimake ka akan mugayen maza kamar samarin shaho?wayon ka ko ilimin ka?..,Kuma ina kira da kar kuyi ma labarin hanzari ku dan sassauta min i want to give more pages,nasan labarin baida dadi sosai amma sakon dake ciki is kind of more realistic than fictional#relax fans im also with you on this#sakallahu khairan,wah saka biljannat awaiting ur heartouching coments always😍_




*Official cat*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top