part27
*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
™/8/ 2018🔞
*🌺SAKAMAKO🌺*
_The pitch blunder_
_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_
@ _IG:Surriem-sule_
*#Lovestory2018*
*#romance#fiction..*
*any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.*
*ena alfahari da ku sosai duka kun mini kyautar littafi masu dadi masu ma'aana lokaci guda and yet always looking after me my besty Azeeyan😻 and my sweety Hernyluv😻 jazakahllu khairan alheri ke gaba da bayan ku this page is oll urs*
_Elle o fans 😺🙈 i dey sory😹
Ku dai yi hakurin dai kawai ba magana..nagode🌹
_
Ur votes are dicouraging wallhy 7k views amma 1k votes ena ma ace 3k duk da ma bai kai half ba habawa kawaye da yan uwa
Baku jim dadin book din ma kenan ko😣
Suhan ko juyi ba tayi ba don kuwa saida ta fito take jin wani irin tashin hankali na musamman Allah Allah take tagan ta gaban ummahn ta...
so bata ko lura da motar mijin ta a baya ba.
..
Shikam yana tukin sa calmly... Ranshi ba dadi kam amma hankalin sa bai wani tashi kamar yadda yake masa a da chan ba ..
Dan achaba ya sauke ta kudin ta dauko ta mika masa a gurguje ta shige cikin gida..
Yana kallon ta shima sai yayi yunkurin parking cikin mamaki yace nan kuma ena ne haka?
Me suhan za tayi anan...ya tabe baki
Isowar su ummah kenan daga asibiti ko minti 10 ba suyi ba..ga nan anty jamila akan tabarma ta riko ummah sai rusa kuka take yi tana cewa" anty dan Allah kar ki tafi ki barmu..gaba daya jini ya fetsu jikin su baki daya sakamakon mummuman yunkurin tarin jini da take yi...
A daskare suhan ta tsaya bata ko motsi saboda a halin da ake ciki sukan su basu ga shigowar ta ba....
Wani dogon numfashin ummah ta sake a wahale ta ce" jamila har yanzu suhan bata zo ba..bana so na mutu banga yata ba ta karashe da wani tarin jini....
wani birkitaccen ihu suhan ta tsala ta rugu aguje gaban ummah " ta kamo ta tare da fashewa da kuka...ummah meya same ki haka?
..ummah..ummah ta dan girgiza ta..ummah ko jin muryan suhan ya sa ta dago da kyau cikin dauriya ta zauna
Duk sun birkice da yanayin suhan din anty jamila ne kawai ta iya kamo ta suka mike tsaye tana dafe da kafadun ta ...cikin jimamai tace" ena kika shiga suhan jikin anty ya yi tsanani meyasa kika kashe wayar ki gaba daya...
a rude take sai ta soma gaya ma anty jamila abunda ya faru tsakanin ta da captain akan maganan satar fita restaurant data keyi don ta samu kudin jinyar "tace tun ranar daya gane ya hanani sake fita a gidan shiyasa baku ganni ba gashi ya karbe waya na..anty muje asibiti dan Allah bana so ummah na ta mutu ta barni..
Jin anty jamila tayi shiruu yasa ta gane tayi baran bara ma gaban ummah sai ta kama bakin ta tayi tsuru tsuru tana kuka a hankali
captain baiji duk wannan ba don anguwar babu space da kyar ya samu ya tsomare motar sa so yana sa kan sa cikin gida ya shiga dube dube aganin sa har mutane suna rayuwa anan??...
kuka kuka ya soma ji sai ya kara azama musamman da ya dago muryan mutumiyar sa ce...
A lokacin ummah ta na kokarin dagowa da kanta duk da ma tana cikin azaban radadin ciwo
...baki na bari tace suhan? Kika ce mena? Suhan dama tun tuni karya kika min kina fita bada izinin mijin ki ba?..
wani irin garas majeed yaji saukar maganan a kunnen sa sai ya dakata daga inda yake wanda baifi taku uku ya iske su ba'
Jikin suhan ya hau karkarwa batace komai ba wani azama ne ya taso ma ummah kallo daya zaka mata ga gane shes highly dissapointed ranta yayi mugun baci...tas ta mike zaune kamar bata jin zafin ciwon
Baki na bari suhan tace ummah..umm..ah ki tsaya kiji...cikin tsawa ummah tace bana so naji komai rike karyan ki
Ashe bakida hankali suhan duk maganan da nake miki ashe a banza nake ? Da haka zaki rike rayuwar ki a duniyan nan..kikace min mijin ki yasan da aikin da kike duk gidan ku ansani ashe yaudara ta kike yi kina min karya?
Cikin wani rudadden kuka tace ummah ai baki da lpya ne kuma....ta tsare ta da cewa toh kuma sai me ?anji ban da lpya akan hakan ne zai sa ki taka dokar ubangiji kina fita bada izinin mijin ki ba sannnan kiyi min karya suhan? Innalihhi wa enna ilahi rajiun "amma bansan ki da wannan halin ba .
ummah ta fashe da kuka mai dauke da tashin hankali ta cigaba da fada tana cewa " "Meyasa zakiyi wasa da darajan auren ki wai don kina so na samu lpya wayace miki hakan da kikayi dai dai ne?
Anty jamila ta rusuna kasa cikin jimami tace anty dan Allah ki yi hakuri ki fahimce ta ....kiyi hakuri ki saurare ta dan Allah ...tace kiyi min shiru jamila ai har dake ma aciki wallhy kun bani kunya ...dake wato take hada kai tana min karya tana taka dokokin ubangijin ta ko? To me kukayi kenan? wai a hakan ne da kukeyi Allah zai cika muku burin ku har na same lpya?
Ai shi Allah ba azzalumin ba wansa bane ku ba kusan hakkin da nidin nan nake da shi akan ki ba komai bane in aka hada da wanda mijin ki ke dashi? Ina ilimin naki yake suhan...
Toh maza ki koma gidan ki yanzun nan bana son na sake ganin ki anan sha shasha kawai.....maza fita min a gida ta karashe a tsawace... Tace "duk randa kika san kare darajar auren ki zaki zo ki same ni anan in ena raye oho in na mutu ma oho..ciwo da lpya na Allah ne in yaga dama ya dauke ni in yaga dama zai barni amma bazan taba lamun ta karya da yaudara ba ..ki fita min nace...ta karashe da wani mummunan tari
Dukan su kuka suke yi musamman suhan data daura hannu akai tana neman birkicewa....
ganin tarin ummah ya soma tsanan tawa yasa ta karaso daf da gudu zata tallafo ta cikin kuka ummah ta bankade hannun ta gefe cikin fushi ....duk dama yanzu kam ta kasa magana tsaban tari amma sam taki bari suhan ta kara taba ta ....
kuka suhan keyi tace ummah dan Allah kiyi hakuri bana kara wa nayi kuskure ummah kar kiyi fushi da ni...ummah..
ta shiga kiran ta tana bubbuga kafar ta a kasa..
Cpt majeed yana jin duk abunda ke faruwa mamaki ne gaba daya ya rufe sa so dama asalin kan magananar kenan? Wani karamar zufa ke keto masa cikin rudani yace lallai ma yarinyar nan me nayi mata haka?
...ummah ta na dada gurfana kan kafanta cikin radadi aman ya soma fita ta rike kirjin ta...ga shi sam ta hana suhan zuwa kusa da ita bare ta taba ta...anty jamila ta rude ta ce suhan ki tafi mana dan Allah ki tafi ni zan kula da ita ran anty ya baci ne kije mana
...suhan ta shiga girgiza kai alaman bazata ta iya tafiya ba gaba daya sai ta kasa magana kuka kawai ta ke yi tana cewa" ummah ..ummah dan Allah...
Ummah ta dago da kyar ta kalle ta wani irin numfashi ta sauke mai nauyi tare da bude baki za tayi magana maimakon hakan sai ta fetso jini tare da kafewa tana neman fara convulcing ..
captain na jin komai hankalin sa yayi mugun tashi he cant take it anymore kawai sai ya karaso ciki ..shigowar suhan ta sa ihu a birkice zata je kan ummah bazata taji ya finciko ta gefe ya mayar da ita baya da azaman sa ya karasa gaban ummahn
..dukan su wajen basu taba ganin sa a sarari ba sai suhan ga umma na daf da fita da hankalin ta baki daya saboda bata ko numfashi mai ma'ana.. Ya tsuguna gaban ummah cikin tausayi da sanyin jiki
a guje ta karaso cikin bori da masifa tace ni kar ka taba min mama na....ka kyale min mama na duk kai ka jawo min a rude take jan rigar sa tana fada....tun daga nan anty jamila ta dago cewa shine mijin suhan wato capt majeed..
shikam baice komai ba don sai da yaga ummahm ido da ido hankalin sa ya mugun tashi kirjin sa har dokan tara tara yake ....tana jan sa bai kula ba ya danna emergency call ya kira asibiti basu ko lura ba..
lokacin suhan na kan maida masa borin ta da masifa
Abun ya ishe Anty jamila Sai ta kamo ta tayi gefe guda da ita tana mata fada....uffan baice ba ya tsuguna ya tallafo ummah yana gyara mata zaman ta ..kan kace wani 5 minutes ummah ta suma hancin ta ke fitar da jini sai ya rasa meke masa dadi ji yayi bazai iya tashi agaban ta ba but he cant wait to see the arrival of ambulance...
Suhan na daki anty jamila ta nitsar da ita Suna isowa anty ta fito ta tallafa masa aka sa ummah a emargency ambulance na babban asibitin garin..
suhan ta biyo su waje lokacin an gama sa ummah a mota...yace ma anty jamila kar ta damu shi zai kula da ita ta zauna da suhan..yace doctors suna bukatar nitsuwa inda wani abu zai neme su...
Ita ta fahimce sa amma sam suhan ta dire tace ita wallahy sai ta bi umman ta ..nan ta je ta tsare a bakin car dinsa tayi banga banga ga hawaye nan sun wanke fuskan ta wasu nakan bulbulowa ...
anty jamila zata yi magana yace mata no ki barta kawai its ok...
Zan tafi da ita...kaiwa nan ya jawo ta da karfi ya dura ta a mota ya rufe ya bi bayan ambulance suka bar wajen...
Tam ya daure fuska yana tuki ko ajikin ta don yanzu gaba daya laifin sa kawai take gani.a tunanin ta duk a kanshi take shan wahala da chan ai ba haka rayauwar ta yake ba gashi yanzu yasa ummahn ta ta yi fushi da ita...Allah Allah take jira yace zai mata wani maganan ta fita A gidan sa yau bata tambaye sa ba tayi masa deban albarka amma shiru bai tanka ba..da shike ma ya lura masifa ke dawainiya da ita sai ya share ta tana famar kukan ta abun na cinta arai...
Suna kaiwa asibiti ko kallon ta baiyi ba ya fice a motar iya kokari tayi don ta bude kofar amma gam gam taji gashi a gaggauce ya fuce ashe kulle ta yayi yayi gaba abunsa...
Anan ta zauna ta cigaba da kuka tana masifa...wani bin tayi da karfi tana bubbuga kofa har ta gaji tayi shiru
Ruwa da ke ajiye a baya ta dauka ta sha tana calming kanta a hankali ...shikam tuni yayi tsayin daka akan doctors kowa sai da yasan wani na musamman ya shigo wajen don ko motsi baya barin ayi gaba daya sun dauka ma mahaifiyar sa ko wata ce na musamman a rayuwar sa...
Doctors manya guda shida ne a asibitin kuma dukan su akan ummah suke aiki..
Sallah kawai ya fita yayi bai ko sake kula enda take ba ...yunwa yake ji saboda tun safe rabon sa da abinci amma tsaban tunani da tashin sense ma mancewa yayi ...
Suhan yanzu kam tayi shiru ta saduda ...ta jingina kai ba abunda take illah tuno maganan ummah..haushin kanta da haushin captain take ji lokaci guda ga yunwar dake neman galabaitar da ita don ita kam ma ko break fast din batayi ba...
Leke ta shiga yi ko zata gansa koma taji labarin umahn ta amma shiru...
Sai chan wajen 9.20pm doctor ya fito ya sanar da captain shes stable.
..amma ansa mata na'uran oxygen sai ta sha enough zasu san me zasu yi mata next...not withstanding doc yayi masa bayanin komai ya kuma nuna masa alaman akwai sakaci wajen jinya altho bai son ya fito fili ya fada
....Amma sai ya zama masa dole yace masa ciwon yayi nisa ajikin ta kuma bai samun kulawar da ya dace amma idan aka dage zata farfado sosai...
captain ya tausaya ma ummah sosaii saboda tun da yaji ance cancer of the blood ne sai yaji gaba daya ya sace ba abunda yake yi a zuciyan sa illlah salati.....
Anma jin doc yace in aka dage zata farfado sai ya samu karfin gwiwa . Yace masa yana so yaje yaga ummah da kansa.. Doc dakan sa ya kaisa kafin ya bashi waje..
Kwance take luff gwanin sha'awa... Duk da ciwo ya nakasa ta ta amma kallo daya zaka mata kasan umma kyakyywan mace ce.... tana da madaidacin jiki dogon hanci da kuma kyakkyawan fuska farin su iri daya da suhan amma sai dai da tsufa kadan ajikin ta...
Ya zauna kan Chair dake fuskan tar ta ...cikin sanyin jiki da tausayi yake kallon ta aranshi yace insha Allahu zaKi warke zakiyi rayuwa damu...bazan barki ki sake shan wahala ba nayi miki alkwari. ..ya dada matsowa yana kallon face din ta kusan 3 minute ya budi baki yace" kiyi hakuri' nasan kina fushi sosai amma ya kamata da nine ba da ita ba Duk laifi nane...muryan sa ya soma rawa yace" duk Ni ne....sai ya kasa karasa magana kawai ya tashi zai fice idon sa sun ciko da kwallah ...wani abun daban yake ji aransa amma tabbas ya dau alwashi sai inda karfin sa ya kare akan ummah...
Har ya fito ya shigo motar bata sani ba..sai da ya kunna ta mike a firgice baccin yunwa tayi na dole. .suna hada ido wani mugun kallo ya mata ya tada motar sa har suka isa gida basu ce uffan ba...
Ya sata a gaba yana bin ta a baya suka haura kan step...sai ta shiga jero kukkuni kasan wuyar ta tana sa hannu zata bude kofar dakin Ta ya buge hannun" yace gaba zaki mike..ya daure fuska...ta so tayi nasa kiriniya amma babu wani karfi ajikin ta sai ta mike dakin san straigh suna shiga ya ja kofar ya kulle gam wayar sa ya juya zai ajiye muryan ta na rawa ta ce" wai ena ka kai min ummah na ne? Me kayi mata?ni ka maida ni gun ummah na ya dada tamke fiska bai kula ba ...nan ta dada sa zafi har jikin Ta na rawa ta fuskan ce shi shima sai ya juya fuskan sa adaure yana binta da ido tace ai dama kace zaka kore ni agidan nan meyasa bazaka kore ni yau ba...? Yau din ma ai na sake fita ban tambaya ba ni ka kaini wajen umm...sai tas taji saukar mari a fuskan ta....
A gigice ta riko wajen take ta sauke hawaye "
duk dama ranshi a matukar bace yake amma bai daga muryar sa ba.. yace ke tsaya na tambayeki wai shin lpyar ki kuwa?. ..cikin wani shakurarraen kuka ta dago zata ansa ya daka mata tsawa yace answeer me first Kina da hankali ?come here... ya jawo ta da karfi jikin sa tsoro ne ya soma ruda ta bakin ta ya matso da hannun sa har yana mata zafi yace " meyasa wannan baiya aikin sa da kyau? tunda kika zo gidan nan kin yaba fada ma wani abu mai mhimmanci arayuwar ki kuwa meya sa kike hakan ne wai..? Sai Ya sake ta anan ne taga tashin hankalin dake face dinsa yace meyasa suhan ..da mahaifiyar ki ta mutu yau fa? Kinyi makan ki adalci kenan? Why most you hide things like this...in ma don kin tsane ni ne shine zai shafi mama na? ai zaki iya gaya mata ko....ya dan girgiza ta yace talk me mana ko itama baki son ta ne...
Ita kam sam bata jin sa zuciyar ta ne ke tafasa
Cikin azama ta dan ture hannun sa tace" eh din bana fada din bana son kowa sai ta fashe da kuka... Ai ba ummahn ka bace to what did u care?kuma walhy kafitar min da ummah na a asibitin nan ..babu ruwan ka acikin hidimana ai ni ba matar ka bace akan sharadi nake zama agidan ka..." a raunane
Yace ohhh yau kuma igiyan auren ne baki san da shi ba ko darajar shi ?
Ta dago tace "nasan da shi mana kuma aure na da daraja amma ai ba zaman aure kake dani ba kuma duk abunda ka sani ena yi maka....now, my mum is sick sai na na zau na maka ? Akan me? duk aikin da kasa ni ena yi ko bana yi? Toh meyasa zaka ki bari na nayi nawa aikin na samu kudin jinyar ummah na...yau da badan kai ba da bazata san komai babare tayi fushi dani...da bazata sha wahala ba
ko dan kana da kudi kake ganin rayuwar kowa na da sauki irin naka ?
u dont even know the pain and cost of evertthing baka san zafin soyayya ba...
farin ciki na ko yaya yake baida amfani in babu mahifiya ta....sabida ita kadai ce min a duniya ba kai ba.
A hankali ta fashe da kuka ta sunkuyar da kai gaban sa" ta kuma cewa "gashi kayi nasaran sa ta juya min baya ummah na tana fushi dani yau
..auren nan dama ni bana son shi nake ba tun farko duk ya takura min kun sa rayuwa ta a takaici..wai ya kake so nayi maka yanzun..na barta ta mutu sabida kai? Ko so kake dama na roke ka wani abi ku zage ni kai da matar ka?toh Allah ya kiyaye ni banda wannan zuciyan na gwanmaci nayi ta maka laifi sau dubun malala indai akan gaskiya ta da kare mutunci na ne"
cikin bori tace wai meyasa ma ba zaka sake nin bane ai naga baka son auren kai ma indai kuma don mum ne im sure in ka gaya mata laifukan dana maka zata hakura ta kyale ka ....
So Pls save us both now ka yanke mana hukunci ni da kai i want my mother ni zabi mahaifiya ta..
I know Zata yafe min In har ka sake ni nasan bazan sake ma ummah na karya ba har abada bazan kuma shiga hakkin auren wani ba dan Allah ka saukaka min ko kai ba ka da imani ne?... cikin matsanancin kuka ta karasheh
Kallon ta yake a rude idon sa har sun kawo ruwa don yasan har cikin Ranta take fadan maganan
...amma sai ya daure ya ce" hmmm good kinyi dai dai suhan. ...wannan yayi...a raunane yayi maganan yadda ya sa ta sai ta dan rage sautin kukan ta dago tana kallon sa" cikin idon ta yake kallo tare da saukaka muryan sa cikin nitsuwa da dauriya yace" i know im wrong kuma nasan nayi judging din ki tun farko.. agree i dont know the cost of anything love pain amma ai nasan darajar dan adam ..
Naji mahaifiyar ki tace kina da ilimi kenan idan ni na watsar da hakki na akan ki sai ke ma ke watsar da naki don kina so ki gwada min kin fini sanin zafin soyayya?
Atleast zaki iya gaya min rashin lpyar mahaifiyar ki ko sannu zan gaya mata..hakki ne akan kowa .. in kudi na ne baki bukatar su bazan saki dole ki taba ba...yanzu ke da kika yanke makan ki wannan hukunci ki gaya mun ribar meye guda daya kika ci? Na farko Kina sane da zunubin da kike kwasa a duk lokacin da kike fita batare da izini na ba baki tunanin in kin mutu anan wata rana me zaki tarar?..waht about inda ban biyo ki ba ranar ba me zaki ce ma ummahn ki inda wani katon banza yayi raping dinki kuma da aure na akan ki kinyi mata adalci kenan? Ko farin cikin da kike nema mata kenan a hakan zata samu lpya?
Suhan kwanan nan ni dake ne kawai a gidan nan amma kinki gaya min komai wallhy da kince maman ki zaki kira bata da lpya da zan baki wayar ki..meyasa kike yin haka? Yanzu kinji dadi kenan da muka sata a wannan halin? pls speak to me now meye kuma kike boye min wanda ban sani ba ena so na sani....
Ta razana saboda maganan ya taba ta sai ta sunkuyar da kai a hankali tana zubda hawaye ya dago ta suka sake maida ido kan juna ....kamar ya taro hawayen nashi ne take suka soma sauko masa "
ya shashantar da face dinsa gwanin tausayi yace "ok please im sorrry nima na san darajar aure amma na mance da shi ranar dana aure ki.
Ure right bana son aure na dake amma yanzu bazan iya sake ki ba din nasan darajar uwa i love my mother too nasan me kike ji a zuciyan ki....
Ta fashe da kuka a hankali yanayin sa ya karya mata zuciya gani take a mafarki ne ko rurin yunwar cikin ta ke sata kizo...ya riko hannun ta dake karkarwa ya dan matso kusa da ita...yace suhan...ya kira sunan ta a hankali bata iya amsawa ba sabida a hakan ma ita tasan kalar kukan da take dannewa da karfi azuciyan ta...
yace im tired of all this maybe wata rana zan iya yafe ma kaina in kuskure na ya jefa rayuwar ki wani hali amma bazan taba yafe makaina ba in har nayi sanadiyar raba soyayyar uwa da da. Ko a'ina mahaifiya take tawa ce....
ba wani bata lokaci a kan gwiwar sa ya zube gaban ta daf kamar zasu gogi jikin juna yace am soryy for making you fell this way...kiyi hakuri ki bani dama na gyara kuskure na give me just one chance nayi abunda ya dace a rayuwa na bazan sake takura miki ba amma bazan sake shiga hakkin ki ba
..bance ki so ni ki ko so aure da ni ba amma na dauki qaddara ce zan bi shi kan tsarin daya dace
Abu daya nake neman agare ki ki daure kema ki cika mace mai gudun bacin ran mahaifiyar ta corect your mistakes kinji? Abunda kike yi ba daidai bane.....
Ta kasa amsa shi amma har cikin ranta taji maganan nasa kuma tasan tayi kuskure sosai"
sai da suka yi maganan taga shima ya bi bayan ummah wajen nuna mata illar rashin sanin darajar aure da sukayi ta dada shiga zulumi tunani take yi sosai tana sauke tears a hankali duk jikin ta yayi sanyi tan kan kuka ...har ya taso bata sani ba..
Hannu biyu ya sa yana dan shafa gefen fuskanta sigar rarrashi a hankali ta sake ta fada kan kirjin sa" tana so ta itama ta gaya masa abunda ke ranta amma sai ta soma jin nauyin yin Haka it seems like zuciyan ta bai amince da shi ba tukuna..but abunda ya fada gaskiya ne dole ta nitsu ta gyara kurakuren ta....
Akan kirjin nashi tana ji yana shafa gadon bayan ta yace"shhhhhh kiyi shiru ki dena kuka bana sake takura ma decisions dinki i promise bana sake hana ki yin komai ke dai kawai kiji tsoron Allah kuma kiyi abunda zai sa mahaifiyar ki farin ciki kinji?
A hankali ta gyada kai ba tace komai ba ta lafe jikin sa tana maida boyayayyen nunfashi...
kusan minti 30 suna manne da juna har ta dan yi shiru daga bisani yace mata taje ta shirya taci abinci tayi wanka ...
Ba tayi musu ba ta fice...
Sauke ajiyan zuciya yayi ya shige bathrum ya watsa ruwa ya sa aka kawo masa abunci yana gamawa ya koma kan gadon sa ..lumshe ido yayi tare da matso trow pillow kadan a kirjin sa "
har cikin ransa ya so ace wuta wuta yayi mata dazun amma that wilk onky complicate the issure..don shi kawai ya lura suhan ba mai iya zama da ita sai mai dabara..hakan ne kawai zai iya daure ta da jijiyon jikin ta. He knows definately in ya takura ta bazata bari ya kula da ummah kamar yadda yake so ba sannan idan ya fito fili sukayi muhawara akan auren nasu duka zasu bata ran iyayen su so its best a zauna a hakan...
Washe gari ko da ta tashi bata same shi..
Har wajen 8 sai ta shigo dakin sa duba sa shiru...
ga numbers sa a phone dinta amma bata so tayi dialling kawai sai t kira na anty jamila suka gaisa..
Tace anty kinje wajen ummah ne ya jikin ta?
Tace da sauki suhan yanzu haka ma muna wani waje ne.... cikin mamaki mai dauke da nishadi tace Allah? Har ummah na ta tashi kunje wani waje...? Murmushi mai sauti anty jamika tayi tace ah a suhan..da ni da mijin ki ne..
ummahn ki ta tashi amma bata bude ido ba so mijin ki yana so ya kaita chan inda zata ga kwarraren likita wai nan ba zasu iya ba
Tayi ajiyan zuciya tace ohhh ena kenan haka anty kinga jiya haka ma ya hanani shiga na ganta
. Tace shhhhhh ke bana son taurin kai kinga anty na fushi da mu akan irin haka ke dai ki nitsu...
Naji dai doc na masa bayanin wani shaharraen likita a chan kasar yamen wai sunan sa doctor carrene singrover ance shi kaidai ne german doc da yake iya handlng wannan cases din succesfully gashi ance na ummahn ki yayi tsanani..
.shiruu suhan tayi tace kuna nufin fitar da ummah wani kasar ma za'ayi? AntyTace eh ana kan shiri ma yanzun nan..
A hujajan ta sake wayar ta rarumi hijabin da tayi sallah ba ta tsaya ko ena ba sai asibiti.
Adai kara hakuri ..im stil reco-operating.. coments and share pls
Oyah Vote🥊
*surriem*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top