part13
*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
™/8/ 2018🔞
*🌺SAKAMAKO🌺*
_The pitch blunder_
_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_
@ _IG:Surriem-sule_
*#Lovestory2018*
*#romance#fiction..*
*any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.*
*ORIGINAL PAGE ✅*
there has been a mixed Up ga asalin nan pls
*Page▶25-26*
[9/4, 13:40] Surayyahms🔥: 25 26
Mum tace zara yadai lapiyar ki kuwa where are you? Ta sake tambayar ta..Zarah kam sai ta dada kara sautin kukan nata dagangan ' tace ena abuja ne ..
mum ta sha mamakin jin hakan amma sai tace ohhh..
Zara ta cigaba cikin sigar kukan makirci har ta na jan shessheka"mum kiyi ma majeed magana..Wai shine dan na fada masa na tafi bai ma tsaya ya saurarani ba ya ce wai na dawo yanzun nan mumy na ce fa bataa da lapya tun jiya take kwance "" toh shikenan ni bazan kula da mama na ba kenan mum pls ki sa baki cewa fa yayi in 1hr na dawo ni gaskiya bazan dawo yau ba sai mumy ta warke...ta karasheh a karkace tana jan numnfashi...
Mum tagama jin ta batace komai ba ta tabe baki ta dube shi batare da ta katse wayar ba.."majeed kaji ai tace maman ta ne ba lpya?pls let her be mana...yayi dan karamin ajiyan zuciya ya dan kau da kansa cos yasani sarai ba gaskiya cikin lamarin zarah ....sau nawa mumyn nata ke ciwo bata zuwa ba shidai yasan akwai abunda ya kaita chan ba wannan ba amma sai ya bari kawai a haukan kishi ke damun ta...
Ya karbe wayan ba yabo ba fallasa yace.ena mum din take bani ita mugaisah ..zarah batayi expecting zaice hakan ba tuni sai ta daburce baki na rawa "tace uhmm ai..ai bacci take yi doc yace kar ta ..ta tashi sai chan chan anjima ..ta murkudi baki
Yace kk..i will call her bak anjima Allah kara sauki bai jira ta sake magana ba ya katse wayar ya ajiye ma mum akan gado..
Nan ba wani bata lokaci tayi masa rakiya private jet dinsa ne ya kaisa chan uS enda babban ofishin sa yake kafin ya fara setting operation
Zarah kuwa ko minti 5 bata kara ba ta danna ma mumy rabia kira ta dauka ""tace hello yar arbarka ta zarah tace good mrning mummy na amma akwai matsala fa.."
like how wani irin matsala kuma zarah?..
Zarah tayi ajiyan zuciya "mumy kedai idan captain ko mum dinsa suka kira ki kice ena tare dake baki da lpya sosai kinji?....
.mumy tace bangane ba where are you zarah...
tace ""ena scotland me tare da su Ahmad look mumy nasan bazaki fahimce ni ba yanzu dana so sai na dawo muyo magana ....
mumy tace "noo just tell me now meyakai ki scotland kuma ..
Ajiyan zuciya zarah tayi tace mumy naje meeting ne i want to start my career ko captain yana so ko baya so "can you imagine dat wai anyi auren captain jiya..?
Wani dum Mumy rabi ta ji a jikin ta gaba daya take ta sake kan wayar lakatar ya zame ta ja da abaya..cikin tsananin mamaki ta ce me kikece zarah?aure ,majeed din? ..zarah tace kwarai kuwa wannan muguwar mum dinsan ta sashi yi dan dole "but he claims he dosnt know the girl amma bazan zauna ya raina min wayo ba...
. Hmmm gaskiya ne wannan amma nasha mamaki "good kinyi dai dai mumy tace ranta a bace..
Dont worry mum cewqr zarah kamar bata damu ba "yawwa mumy shyasa ma kikaga na bisu Ahmad kema ki shirya min yanxu ena so na hada contacts ne daga sai na sama ma companyn da zam fara processing babban mafaka kinga koma wacece ya auro ta shigo gidan tasan nafi karfin ta
Nan ma mumy tace goood """...haka nake son ji ena bayan ki dari bisa dari "ashe dai banyi asarar haihuwa ba..zarah tayi murmushi mumy tace
sannan in kika dawo ki sa ido sosai
... duk abunda ke wakana agidan ki ki fada min karki kuskura ki bari wani yayi ruling dinki don an kawo wata daban... ure a special woman always remember that ke ba dai dai da kowace mace ba ne..
Zarah ta gyada kai cikin jin dadin maganan mumyn
"itama haj janan nasir din nan bawai na barta bane naga tana neman shige min gaba..zarah ta tabe baki tace just live her mumy banda lokacin ta kedai kiyi min back up din nan yanzu mumy 2 weekz zanyi daga nan na dawo ...
zan kuma aika miki cash anjim...mumy ta washe bakin tace "to yayi Allah ya miki albarka oya get ready to work....Suka katse hirar su.
Mumy da zarah Duk yadda suka tsara haka suka tafiyar don captain sai da ya tabbata ya kira kowa daga familyn sa cos dama in ya shiga bakin aiki musamman idan ma irin wannan ne ba'ajin motsin sa har sai ya kammala
Gefen suhan kuwa baccin ta mai kyau tayi ba ita da tashi ba sai wajen 11.30am
Kafin nan ummah ke tsaye bakin kofar gida da kayanta duka..wasu mutane agaban ta da alaman sunzo amsar key ne..batayi gardama ba ta basu key din gida...dama ita kam tunda ta karance letter baban suhan a daren jiya ta gane cewa gidan nasu ma ashe siyarwa yayi .. ..
Tana cikin tattarawa zata nemi adaidaita taga saukowar anty jamila ..
yar dattijuwa ce amma fes fes take don kuwa kallo daya zaka mata kasan idonta a bude yake ..yar kimanin shekaru 35 ne bazaura sannan itace kanwa kwalli daya data rage ma baban suhan..
Ta karaso daf jikin ummah tace .."ah ah ya haka ena sauka kina shirin fita ?
Ummah tayi murmushi tace "wata sabon gani yau kece dakafan ki anan jamila?..
Dan dariya aunty jamila tayi ""tace an kauda mushe dole masu hancin shan iska suyi shawagi...
ai naji ance azzalumin nan ya bar garin nam shiyasa nazo na dubaki wai shin dagaske ne ya aurar min da dota na suhan?
Nan ummah tayi ajiyan zuciya tace " eh jamila suhan jiya aka aurar da ita nikuma ya sake ni kinga har gidan nan ma ya siyar masu shi ne yanzu suka karbe key waje na...
cikin fushin bazata mai dauke da kunan rai aunty jamila tace "tsinanne mugu..toh Allah ya ture keya ta Allah bata shi ba..
ai naji duk abunda ya faru wajen wawan aminin sa oga siyasa wai yana cewa zai koma wajen zuwairah ko? Tohmm yafi ruwa gudu ..kekam muna nan tare dake yanzu haka gida zamuje tare dani ki huta naji dadin da kika samu yancin ki yanzu inba ma qaddara ba me zai sa ki hada jini da wannan azzalumin.
...ummah ta sauke ajiyan zuciya "tace ah a jamila bar wannan maganan kwara dai na nema waje nima na tsuguna don kaina kar na daura miki wani nauyi... don bazan iya barin inda suhan take ba ne dana koma garin mu..
Anty jamila tace ah a..wallhy bakomai waje na fa tamkar wajen ki ne nifa da chan halin yaya ibrahim yasa na yanke alaka da ku sosai bawai don bana kaunar ku ba wallhy ku kadai ne gata na da rufin asiri na a duniya shiyasa ma yanke hukunci tunda baya nan a gidana ai saimu zauna tare mu rufa makan mu asiri..
Da kyar ummah ta amince suka tafi" 2 bedrom ne a gidan aunty jamila sai dan pit toilet dinta mai hade da bayi suna kammala kimtsawa
Basuyi wani dogon hira ba suka fito da niyyar zuwa shamud residence don duba suhan..
abakin titi suka ci karo da zuby itama hankalin ta ya tashi sosai da kyar suka hadu suka kwantar mata da hankali "ummah tace ...kar ki damu zuby suhan tana lpya insha Allah kije muku aikin inyaso daga baya zata ki je ki duba suhan din kema..
Daga kan gado' Tagumi suhan ta buga har yanxu bata sauka ba tana kan wondering ya zasu kare da captain" sannan wani irin sharuda zai sa mata
Cikin haka mum ta shigo dakin... murmushi ta sake mata mai sanyi
suhan sai ta sulale kasa ta dan rusuna tace ena kwana hajiya? Tace yata har kin tashi baccin ya ishe ki kenan?Tana karasowa daf suhan ta gyada kai a hankali tace eh ..
toh tashi mana ai ya kamata ki kimtsa yanzun nan ma zamuyi baki ..
Suhan ta tashi sum sum batace komai ba ta shige bathrum sai dai still bata iya using ba.yau ma shower ta kunna tayi amafani da wani goat milk shower gel ta wanke jikin ta fes..
Mum na zaune a dakin cos dama tana so ta dan gwada ma suhan wasu abubuwan..
tafito sanye da kayan ta still bata daura towel ba
Mum ta mike tsaye tace ohh noo" ..ya baki daura towel din ba tayi shiru ta sunkuyar da kai mum ta ce to xonan na gwada miki wani abu..
nan suhan ta shiga bin mum ita kuwa tana nuna mata yadda zata yi in zata sa kaya ko amfani da wani abu a dakin ta a saukake
Bayan nan sai da ta zaba mata wata dalleliyar dark brown but simple gown sabo kal ta ce mata kisa wannan idan ya dawo zai kaiki kasuwa kizabi irin wanda kike so kinji?
Ta sunkuyar da kai mum tace toh ki shirya ga make up nan... tayi mata nuni da kan madubi ""in kin gama komai'saiki sauko ki same ni kafin bakin namu su zo
Tace toh hajiya..nan mum ta fice ta barta
Isowar su anty jamila da umma kofar shamud residence aka bude musu don dama ummah saida ta kira mum kafin nan ....Tafiya sukayi kusan minti 40 kafin suka kai cikin haraban gidan kalle kalle kam ba a magana musamman da suka dire cikin asalin gidan don saida aunty jamila tayi rikon hannun ummah...cikin zuciyan ta tace lallai wannan shi ake kira daula
Anty jamila "tace hmm ni fa banga mutane ba sai tarin securites kamar bariki ko dai mun bata hanya ne?...kan ummah ta amsa saiga wata mata ta bullo cikin uniform dinta tace musu su shigo, nan suka bi bayan ta. a falour na biyu aka sauke su ko zama basuyi ba sai ga mum ta fito da farar ta...
Suka gaisa cikin girmama wa da karamci ummah tayi introducing aunty jamila as kanwar mahaifin suhan..
Suka gaisa mum tace bari na dubo ta, ku zauna pls
Nan ta haura sama jim kadan saiga ta agaba suhan na bayan ta...
Tum daga sama ummah kebin ta da kallo tana Duban yanayin ta tsakanin jiiya da yau gaba daya sai tayi kalar tausayi
ganin su ummah ne yasa ta rugo a guje tafada jikin ta tana hawaye tace ummah na ashe ke ce kika zo? Hope dai lpyar ki lau ko.. kinsha magani?ya jikin naki? Ta karashe a shawagbe cikin kuka..
ummah ta shiga rarashin ta "tace lpya ta lau suhan tashi ki zauna ni ba abunda ke damu na da kyar suhan ta mike takoma gefen aunty jamila wacce ke kallon ta da sigar tausayawa nan suka gaisa ta riko hannun ta tana saisaita ta a hankali batare da tace uffan ba
.
Mum tayi gyaran murya tace ..alhmdullhi yakamata muje mu karya kumallo ko? dama danku yasa nace ajira suhan din ma yanzu ta tashi..
da kyar ummah ta amince ta taso da acewar ta ma da sun tafi kawai cos she wanys nothing to do woth arzikin gidan shamuf damuwar ta yarta ne kawai..
Bayan sun zauna kan dinning Mum dakan ta ta sa aka shirya musu break kowa akayi servung dinsa
anan ne mum ta samu daman fada ma su ummah tunbdaga farkon labarin haduwar ta da suhan har da dan tsabanin da suka samu da captain bata boye ba magana tayi cikin dabara hikima da dattako jar sai da ta tabbata su ummah sun fahimce ta sosai
ummah har tayi ma suhan nasiha,
"mum tace ai ba laifin ta bane ..kuma komai ya wuce
Nan ta gwada musu hoton captain daga jikin wall sanye da unifom dinsa anan tayi musu bayanin ay baya kasar yau da safe ya tafi amma yana dawowa har gida zai zo ya gaishe da su..
Haka suka cigaba da hira jifa jifa daga bisani mum tayi izini ma maids da ta kai su suje suga dakin yar su
Ummah tace tohh" jamila ki fara zuwa ni ena da maganan da xamuyi..ba shiri mum ta koma ta zauna sannan suhan da anty jamila suka nufa sama..
Itakam suhan dama abunda take so kenan don haka maids na fita suka dada rungume juna da aunty jamila....suhan tace anty nikam na shiga uku yanzu haka rayuwata zai kare anan?
Cikin sigar tausayi anty jamilah "tace baki shiga uku ba suhan in har ena nan bazaki taba shiga uku ba..
Nan ne ta dan soma saukar da hawaye ahankali anty jamila ta dafa kafadar ta"
Naji duk abunda suka fada dazun na fahimce komai suhan kiyi hakuri kinji?..ita kam bata iya cewa komai ba sai ta dan girgiza kai alaman abun na mata ciwo a ranta matika...
anty ta kamo hanun suhan ta dube ta""nasan zaman nan zai miki wuya wannan al'amarin bana wasa bane cos na lura auren nan naki duk akan makauniyar hanya aka daura ta su kuma iyayen naki gani suke wai suna lazimi da alkharin dake cikin sa nan gaba babu wanda ya damu da ra'ayin ki...kiyi hakuri ta dada damko hannun ta softly ..ni ma yanzu haka shawaran da xan baki kenan suhan... ki daure ko xauna anan din tunda yanzu ba yadda mukayi iya da su
Kar naje garin nema maki yancin ki ki tafka irin kuskuren danayi a rayuwa..
Nan anty jamila ta sauya fusaka kalar damuwa tare da sauke ajiyan numfashi "suhan tace kuskure kuma wani irin kuskure kenan anty?
dariyar takaici tayi a takaice tace suhan kenan " shiyasa nake son anty maryam mahaifiyar ki..tasan halaye na na boye tasan ni wacece amma bata taba gaya ma kowa ba..hmm tasha min magana na daina amma naki na bari har yau..sai inaga kamar har yanzu laifin rashin karban qaddara na ne ke bi na..suhan in baki manta ba shiyasa wata rana da chan zakiga bata son ki cika zuwa waje na. nima kamar ke nake..aka aura min wani mutumi mai suna alhj sule batare da na amince ba bayadda iyaye na basuyi ba don na zauna amma naki firr don na fahimci auren nasan duk su baba sunyishi ne don suna karban kudin sa basu damu da mutunci na ba
amma nikam na damu sai naki karban qaddara
na turje akan sai na rabu da gidan alhj sule
Wanda ba shi kadai ba hatta uwar gidan sa hajiya sumayya ta rike ni amana amma bana son shi a haka na rike buri na na barin gidan sa har sai da ya tabbata ....gashi na fito iyayena duka sun rasu yaya na mahaifinki ya guje ni rayuwa yayi min zafi na dawo bazaura kinko san illaj da kalubalen dake cikin zawarci? Da ana fada nakan ce sai dai in baka kama kanka ba amma dana fada ciki sai naga abun ya wuce tunani na..wani bin sai kinji kamar ko da cizon ki ake agidan miji zaki so ki zauna than kiyi zaman zauran ci ..mafi yawan maza sam basu daraja ki kowa kuma zai na miki kallo da kim saba da namiji koda baki saba ba..
Don na taimake kai na gashi Yanzu na fada yawon banza ma dauki kazamar rayuwa don nayi surviving.
nan suhan ta dago ta kalle ta cikin mamaki" tace yes.. shiyasa nake ji miki tsoro kinga rayuwar mu kusan iri daya ne wawan mahaifin ki yabi duniya ya barki...pls in har ba cutarwa anan ki taimaka makan ki kar ki fada irin nawa rayuwan
Ni zan taimake ki suhan babu abunda zai fi karfin zaman ki anan gidan insha Allahu!
shima mijin naki kamar uwar shin haka yake? naga matar tana da mutunci sosai tasan darajar dan adam..
suhan tayi ajiyan zuciya mai nauyi tace..hmm anty anan ne matsala ta yake ... nan ta shiga bata labarin yadda sukayi da captain gaba daya bata boye komai ba
Anty ta nitsu tana jin ta bayan tagama sai tayi shiru "chan tace ..wannan duk bakomai bane suhan ashe ma baki da wani matsala sosai.
Cikin zaro ido waje suhan Tace kashe ni fa zaiyi kuma kice banda matsala anty?..kuma fa yace kar na fada ma kowa
Dariya anty jamila tayi "karyan sa ya kashe ki shidin wa?kedai.. Duk wannan salo ne dayake bi don ya tsorata ki kuma yaci nasara ne don yaga kina tsoron sa...
Ni Bance kiyi masa rashin kunya ba amma da zarar ya gaya miki sharudan da yace zai fada miki ki tabbata kin sanar dani ko da ta waya ne..suhan na zaga duniya naga maza .maza sun ganni babu wani namiji da bazaki iya da shi ba koda kuwa qanin fir'auna ne ..nayi miki alkwari muddin zaki bani hadin kai ba mai tada miki sense.
Suhan ta dan murmusa tana share tears dinta" tace of cous my anty har kinsa naji karfin gwiwa..dan Allah idan zuby zata zo ta kawo min waya na fa uniform din aiki na..
tace toh shikenan
Anan mum da ummah suka turo kofar dakin minti 10 ummah batayi a dakin ba tace to zamu tafi
Tuni suhan ta sauya fuska..mum ma ta nuna rashin jin dadin ta har saida tasa aunty jamila tayi alkwarin zata sake dawowa a haka suka rabu
Bayan kwana biyu da zuwan su ..mum ta sa anty jamila ta kawo zuby saboda zaman suhan shuru na mugun damun ta gashi taki sakewa da ita sosai..
Daga nan mum ta yi nazari cikin satin sai ta jawo shirin ta na gyaran jikin amarya data shirya shi na musamman tun kafin aure akan za'a ma suhan idan suka sa lokaci..ganin yanzu the enviroment is convenient sai ta yi magana masu gyaran nata suka iso.
Mata uku ne kasaitattu wanda ganin su ma babban aiki ne don kwarancewar su akan aikin su..anan mansion din shamud zasu zauna don haka aka basu site don gyaran kwana 12 za'ayi ma suhan wanda ya hada da komai da komai na fatar jikin ta..
A lokacin auren zarah mum ta so tayi mata hakan amma haka taki firrr tace ita na spa na zamani take so bata son anything traditonal
Bayan kwana hudu da tafiyar captain aka soma shirya shiryen fara gyaran amarya agidan kamar biki haka aka tsara
babban daki ne aka tsara shi tamkar wajen bikin kamun amarya an shirya shi tsaf cikin dark red curtains masu shegen kyau da manyan pillows a jere akan tsari "shining gold colour ko ena an tsara shi tamkar fadar sarauniya
A tsakiyan wajen aka sa tubalin wajen zaman ta dan carpet ne mai laushi da taushi ja da baki wanda ya dan ban banta da sauran floor decor na wajen gaba daya a gefe gefe aka jere manyan adudun turaren wuta wanda aka kunna aka barsu suna fidda qamshi ko ena ya gauraye cikin tsumayi.
Daga nan Mum kullum sai tayi inviting din su zuby da anty jamila saboda su zama mata suna debe mata kewa.. it was lively saboda ba karya kowa na fadan albarkacin bakin sa a wajen musamman anty jamila ..ga safaran kayan ciye ciye masu aiki nayi ba sauki
Ranar da aka fara mata na farko tayi mata jagora zuwa bathrum tace ki shiga wannan ruwan... tayi mata nuni da damammen ruwan da alredy sun shirya shi yaji hadi kam ya sauya zuwa launin pink colour sai bada turirin gamshi yake..
Tace ki cire komai ajikin ki ..ki shiga ciki ko ena ya samu ruwan amma bansa fuskan ki..sannan
Kar ki fito sai kinji nayi knocking sai ki daura wannan... ta ajiye mata white yard mai dan shararara amma ba sosai ba iya gwiwa sannan ta fice..
Suna daga ciki dayan matar na kan dame kwabin dilka a wani kwarya su zuby da anty jamila ma ba a barsu abaya ba..kowa na sha'anin sa ..bayan kamar 20 minutes matar ta fito da suhan daga ita sai wannan kyalle dan fari babu komai a jikin ta nan wajen da aka shirya mata aka ajiye ta..
Daya daga cikin matan kuma ba bata lokaci ta soma warware suman kanta ta shiga aikin gyara sa tsaf tana sullube sa da nashi sinadarin hadin sannan ta nade mata shi cikin hair steamer..
Aka shafe dukkan jikin ta da kwabin dilka dayan kuma na faman turare ta da ta ko ena sai dai dakin ya soma gauraya yayi dim..
bayan kamar 2hrs lokacin da shike da safe aka fara wajen 12 saura kenan aka kankare mata dilka aka durje shine lightly akayi mata wankan madara da ga kai har kafafun ta..
A Haka rayuwan suhan ya kasance na kwanakin safiya da maraice ana mata irin haka har na kwana 12 chas kafin kace kobo fatan jikin ta ya tande ya gogo fes har na ban mamaki
Sukan su masu gyaran sunyi enjoying companyn su duk dama daga baya ummah ta hana su anty jamila da zuby zuwa gidan tace "su saurara haka kar su biye ma mum tana so ne kawai ta faranta ma suhan and den yakamata su tsaya su kare mutuncin su dan a daraja su nan gaba..
Sun gamsu da hakan shiyasa yanzu sai dai suyi awaya kawai ake gaisawa dan ..dole zuby tayi karya ma madam bola cewar baban suhan baida lpya rai a hannun Allah suhan na jinyar sa a chan garin su amma zata dawo soon duk dama tasha masifa kam amma hakan madam bola ta bari..
Dan kwanakin da basu zuwa ne mum itama ta samu daman gwada ma suhan wasu abubuwan daya dace musamman yadda zatayi amfani da highly modernised items na cikin gidan har dakunan su..
Tsaf suhan take yanzu sama samabita kanta tana enjoying new looks dinta..jifa jifa su kanyi hira da mum duk da ma bai kaiwa minyi 20 amma sosai mum take apreciating ladabi da kunya ga kuma sanyin hali irin na suhan..
Ranar da safe Mum tana zaune kan sallaya kira ya shigo ...da murmushin ta ta dauka yace"mum im back...anan ta dakata sai da tayi godiya ma Allah kafin "tace my boy bani labari mai dadi naji..yace aiki san adduar ki bata taba fadi kasa domin kuwa anyi nasara sosai yanzu haka wasu daga cikin yaran sun koma hannun iyayen su wasu an maida su garin su na damka su ma hukuma...
mum tace "masha Allah cikin tsananin farin ciki tana sa mai albarka ""Ena fatan kuma zaka dawo gida soon right?
Yace yau ma zan dawo mum shiyasa na kira na sanar dake kiyi min irin abincin nan naki mai dadi mum kinji?
Dariya ma yabata tace just give me time kamar anyi angama.. dan hira kadan sukayi sannan ya katse wayar sa..
Ko da ba ace ba yadda mum ta fito yau kowa agidan sai da yaga annuri akan fuskan ta ....
Suhan already ta gama shiryawan ta tsaf dogon riga ne na kanti mai guntun hannu kunya ya hana ta lekowa
Mum kam bata damu ba sai chan yamma lokacin tasan yana dap da shigowa gari
Cikin dabara da hikima ta sa suhan da ita kanta suka shiga kitchen anan suka shirya Masa abincin mai kayatarwa babu abunda ba ayi shi tamkar bana mutum daya ba haka aka jere su tsaf cikin tsafta ...
Suhan tace hjiya baki zamuyi ne..tace uhm uhm kije kiyi wanka tare zamu ci abincin nan bada jimawa ba.
Daga nan Suka rabu
Suhan na shiga part dinta motoci guda uku masu lpya suka dire a compound din... zarah ne da Ahmad da faiza suma sun dawo daga scotland sai suka biyo mata it was almost 7.40pm bayan isha'i..
As usual suit ne ajikin ta bakake kirin kanta a yashe yake da brazillain hair na zamani sai yarfa shi baya take cikin rigima da kasaita Surutun su ya gauraye gidan
Babu gaisuwan kowa da ta amsa daga cikin maids har suka kai palor da shike jirgi suka biyo babu alaman ko wani gajiya ajikin su sai suka zauna nan palor su kaci gaba da hirar abubuwan dayabkai su scotland bata damu ta duba kowa a gidan ba..
30 minute later lokacin mum ne ta soma lekowa tayi dressing irin na yan maiduguri dogon sari mai mayafi purple tasha mamakin ganin zarah a gidan unanounced amma sai ta fuske tayi murmushi fuska ba yabo ba fallasa ta karaso..
Su faiza da Ahmad suka gaisa da mum da kyar zarah ta iya gaishe ta ....mum tace ya jikin hajiya rabia ?zarah Bata ko samu daman amsawa ba sukaji dirin motoci da convoy din security alaman captain ne da tawagar sa suka diro ..mum kam kamar an tsoma ta a aljanna ko ta kansu bata sake bi ba tayi waje tarar danta..
Zarah kam ko ta motsawa batayi ba cos ta riga ta nuna ma friends dinta ita isashhiya ce wajen mijin ta. so.. shi yake binta ita bata zubda girman ta wajen bin miji
Bayan tsayuwar motoci ya fito suka rungume juna da mum suna dan hirar su na kewa .....
daya shigo ciki anan ma
Still ahmad da faiza suka gaisa da shi wacce tuni ta kasa samun nitsuwa don har yanzu captain bai fita a ranta ba musamman ma yau data ci karo da shi a uniform again.hes soo hot
Mum tace ai kuwa zuwan ka yayi dai dai the house is full now yanzu kowa ya tashi muje kuyi refreshing kanku a dinning table...suka danyi dariya musamman faiza dake cewa how lovely mum wallhy dama am starving ...dauke wuta zarah tayi hoping that captain shi zai soma mata magana amma sai ya dauke kai..
Mum ta wuce chan sama bayan yan mintuna kadan sai ga ta da suhan a bayanta sanye take da riga da skirt na kanti white and pink da mayafi sharara white sai sanyin qamshi dake fita ajikin ta.
Dukkan su maida kallo su kayi wajen ta barin ma captain daya soma comtaplating ko sauya ta akayi...
Suna saukowa suhan Ta dam ja baya ta tsaya
Mum tace yata taho nan mana kinga bakin namu sun zo sai ayi serving din su ko? ..a ladabce suhan ta gyada kai gaban su ta dan rusana kai fuskan ta dauke da confidence da gwarjini tace sannun ku da zuwa...murmushi ne ya kufce ma Ahmad jin angelic voice dinta aka bar faiza da sake baki hannn tana kare ma hallittan suhan kallo zarah kuwa zufah ne ya soma keto mata a ranta tace who the hell is this badai ace itace amaryan gidan nan ba?
Captain ya dakata kamar baya kallon ta amma a zahirin gaskiya ita din yake kallo.. jira yake yaga ko bazata gaishe sa personally ba ..ko kammala tunanin nasa baiyi ba tace sannu da dawowa sir..
Mum tayi murmushi a boye....shikuma tare da dauke kansa yace thanks..
Nan mum tayi mata umarnin ta yi serving tba musu tayi ma kowa dai dai ba kuskure ..dan dole faiza takawo hira don ta lura kowa hankalin sa nakan suhan ne alokacin
Musamman ma zarah.
Ana cin abinci kowa a ransa yana so yaji ita waye..suhan ko ji take kamar ta tsala ihu don bugun zuciya da fargaba takasa dago kai a hankali take kai abinci bakin ta cos kowani dagabido saita ga zarah tana watsa mata mugayen kallo.. ..daga karshe
Faiza ta kasa hakuri tace mum ..wannan kanwar captain ne ya naga bata son magana?
Mum ta danyi dariya tace lahhhh no my dear ai wannan itace amaryan gidan nan pls meet her.. ta dan dafa suhan wacce ta dago fuskanta da kyau dan dole "mum tace wannan itace suhan abokiyar zaman zarah..
Tare da droping spoon a razane zarah tace What? Kikace meye mum? Mum bata amsa ba
Harara ta watsa ma suhan bazata..kafin mum tace of cous itace amarya.. kinga badon kinyi tafiya ba dake ce zaki yi introducing nata ma freinds dinki i am right?..faiza ta maida wa mum dariyar yake tare da kai ruwan sanyi bakin ta..wow basu yi tsammanin haka ba..wannan kyakyawan karaman yarinya fresh blood ma captain? Lallai mum ta dauka da zafi faiza ta raya aranta
Ahmad ya dan tabe baki yace dats lovely she preety ya amida maganan kan captain wanda murmushin doe kawai yayi...sannan ya dawo kan suhan yace congrat mrs MJ junior "suhan tayi murmushi ...
captain koya ya sake daga ido abincin sa kawai yake bai kula kowa ba ...mum ta dan kalle sa tace my boy is enjoying the meal i ques
nan ya dago da karamin smile yace ure perfect mum i m totally loving this....nan ma mum ta dan dafa suhan da farar ta "tace all thanks to her im glad yau kowa yaci abincin amaryan gidan na
""wow!!!! Ahmad da faiza suka fada a tare cikin mamaki mai dauke da jinjina
Zarah data gama kuluwa..watsi da plates din gaban ta tayi cikin hatsala ta haura chan sama cikin fushi da fusata
kowa saida ya dago nan wajen ana binta da ta da kallo......
*More coments more tsayin pages tunda bazan samu dama yin sau biyu ba..i think long pages is enouhg ai😺😺*
*surriem*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top