part

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*


    ™/8/ 2018🔞
   *🌺SAKAMAKO🌺*
    _The pitch blunder_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_
  @ _IG:Surriem-sule_

*#Lovestory2018*
*#romance#fiction..*
*any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.*



*Page▶60 continued*

VOTE bEFORE reading pls coments and share views yawan votes yawan updates.

Murmushi kawai yayi ya mike tsaye tare da dauko ta duk da bedsheet din suka nufi wajen wanka...

Washe gari da safe zaune take  gefen gado ta kumburo fuska ta harde hannu don tun da suka tashi ta ta lura tun bayan sallahr asubahi yake ta waya da mutane daban daban wanda bata gane ba..

Wani bin sai taji Abun na bata haushi
Ba wani Abu bane kuma illah tana mugun jin tana bukatar attention din sa..

gashi bata ma fahimtar me yake fada hira ne oder ne oho abubuwan sa duk a hade..shikuwa meeting yake da su mahmud tun daga US akan wata muhimmiyar operation.

Yana lura da ita sosai Sai ya dauke kai ya share ta..
Daga bisani ma daya ga 10am ya kusan yayi sai ya fice waje alaman yana bukatar privacy....

Ranta ya sosu sosai..har tana neman ciko hawaye sai ta mike ta shiga hade chokolate ko zata na hadiya yana maida mata haushi..

Bayan ya gama meeting din su kayi magana da mahmud akan cewa  a abuja zasu hadu nan da sati guda..

Yace ba komai shi ma yau ko gobe zasu koma nigeria ya lura mum dinsa ta matsu su dawo gida...

Yana katse wayar ya sauke ajiyan numfashi ya kamo hanyar shigowa tun daga bakin kofa ya hangota ta dau katon ear phone dinsa ta kwama a kunne babu ko dankwali akan ta sai rawar kai take tana latsar chokolate din don dole..kallo daya zaka mata kasan da gayya ta ke yi sai ya sha mamaki shi dai yasan babu music  sai dai in gidan radio take ji... besides wannan abun ma yafi alaka da alerts din harkokin sa na wajen aikin sa..so whats is she hearing? Ya tabe baki gashi ta sa hankali kamar da gasken wani abu take ji...dariya ne ya so ya kufce masa sai yayi wani tunani..ya shigo ciki daf da ita yace preety girl yau ni bazan ci komai bane yunwa fa nake ji...

Tana jin sa sarai cikin ranta sai ta soma kukkuni"tace ace kusan 4hrs mutum yana waya baisan da yunwa ba sai yanzu" ai ba ruwa na ehe...ta dauke kai kamar tana jin abu tayi shiru ta kyale sa..

Yasan tana jin sa amma sai Ya cigaba da magana tana shiru fuska ba yabo ba fallasa yace toh shikenan

Wayar sa ya sa a kunne ya ci fuska ya juya mata baya ta bisa da kallo har ya zauna kan gadon nata.." bakin sa na motsawa yana kuma sauke killer smiles kamar yana magana da wata amma bata ji ko kadan..

kallon sa kawai take ta  ba bada lokaci taga ya shiga magana cikin salo yana dariya kamar ana bashi joke ko hira mai dadi... ajiye cup tayi ba tace uffan ba ta harde hannu..

Yana kula amma Ko ya nuna ya jawo pillow cikin shauki kamar baisan da ita ba anan ne ta soma zagowa inda yake a hankali don ma taji ko da 1 word ne..ya dan kyallero da gefen ido ya dube ta lura da reaction din ta ya sa yace ' naji sarauniya ta ki bari anjima zamu cigaba yanzu na gaji  a kasale ya fada murya kasa kasa sosai ..

Wani haushi ne ya balbale ta kawai sai ta yanke a ranta maybe ma da chan da wata yake ta magana .cikin rantan
tace tab di jam
Ace tun sassafe??? wannan wata irin tsinananiya ce haka" don ita kam tama mance akwai wata zarah duniya bare ta kawo masa uzuri Kawai sai zuciya ya debe ta fuuuu tayi waje cikin fushi....

tana bashi mamaki amma sai ya fashe da dariya ya ajiye wayar gefe har yana tuntsirewa... sai da ya dau kusan mintinuna 10 sannan ya biyo bayan ta da chokolate din a hannun sa..

Gaban ruwan ta zauna tana sa hannu aciki tana debawa tayi zugum ita kadai..

Dadi ke masa yawo a brain dinsa yanzu..yasan ko ba komai  hes important to her yanzu tunda shes becoming more protective of him..
.
Ya ajiye chokolate din gefe har yayi yunkurin zai zauna daf bata lura ba sai da ta shako qamshin jikin Sa...ta dada daure fuska tana kokarin kaucewa din kar yaga tears din ta..

Cikin nitsuwa da sanyin murya yace nayi miki wani abu ne ? Why are you crying preety girl..cikin rarrashi ya sauke murya

Maimakon taji fushi sai taji sanyi a ranta daya mata magana amma sai ta daure fuska tace im not crying ..me ma zai sa ni kuka..ya juyo ya kalle ta yace to meye ne?gaya min ...dazu Nayi miki magana baki amsa ni ba kuma kin fito nan..

Bazata hawaye suka soma sauko mata cikin wani yanayin shagwaba tace kar ka ma fara gaya min hakan ai kai ka fara share ni....ace tun safiyan safiya kana ta waya ita din bata hakuri ne ka kula mutane kuma ai ko kallo baka yi ta fashe da kuka mai dauke da takurrren kishi....

he likes that amma hankalin sa yayi mugun tashi daya ga suhan da gaske take har zuciyan ta abun yayi mata zafi...

sai ya kau da wasa ya dan ja hannun ta zai goge mata tears din ta tashi cikin masifa tace noo dont touch me..

Yace hey listen...ta mike a fusace kamar wacce zata masa masifa amma bata san me zata ce ba..

Ya ce ohh bazaki saurare ni ba ko? Ta kumbura fuska ta hade rai tayi shiru ..ya jawo chokalate din ya taho gaban ta ya sa hannu ya Zare head phone dinsa ya damka mata wayar sa da cup din ta yace have fun...ya juya ya koma ciki.

Kamar ta jefar akasa dan haushi don ta so ya jawo ta jikin sa ne ya rarrrashe ta .
Amma me zatayi masa da waya..?

Sai wani abun yace  ta bude mana taga munanan yan matan da yake bi har yake waya da su...kishin ke deban ta ko chokolate din bata kula ba ta shiga kokarin bude wayar..
Gashi nan dai ta samu ta bude ciki amma akwai security akan contacts ...

Ta rasa ya zatayi ta kai 30 minutes tana neman shawara da zuciyan ta
 
Chan ta zaburo ta shigo dakin ta same shi ya gama parking kayan su  tsaf..har ya koma gefe kan mat yana press up..

Cikin shagwaba ta zo gaban sa ta tsaya ...kallo kawai ya bita da shi suna hada ido ta dada bata rai..ya kamo hannun ta zuwa jikin sa yace wai meye ne kam..ta noke tana rigima murya kasa kasa tace ni dai ka bude min... yace mene? Ta masa nuni da contacts din sa  bai sha mamaki ba ya sa hannu ya bude mata ko thanks din bata gaya ba ta tashi ta fice...

Tun kan tayi nisa ta  soma dubawa da wa yayi wayan taga duk jeren call daya 6am to 10am Mmerah sai few of secret numbers figures ne ma ...but who is this mmerah.? Sunan yayi mata kama da indian cud it be wayancan yan matan ne tace nooo wani abun ya ce mata yess kawai garin kiriniya tayo dialing number take ya shiga ringing...

A firgice ta shiga rudani bata iya katsewa ba...kwata kwata sai ta shigo dakin da Gudu ta ajiye masa wayar sa kusa  ldashi ta ja ta tsaya tsuru tsuru...

Ya mike cikin mamaki yana duban ta..ya koma kan wayar sa ya dauka lokacin mahmud ya dauka har ya soma magana yana lura da abunda tayi sai ya ce oya zo nan ki amsa tunda dama ke kika kira.  Tace ahm ahm ni fa ban san na kira ba juma ena so na kashe yaki mutuwa.ta marairace ko ya kula ya dauko wayar ya damka mata yace oya talk now...dan dolen ta tasa a kunne..muryan ta har na rawa tace salam hello...

Mahmud yayi murmushi don ya saurara yaji maganan majeed din yace waslam amarya bata laifi...sai ta kasa cewa komai ta dago wayar a hankali ta ga eh fa mmerah din ne..amma ashe namiji ne ma.

Da kyar ta sake suka gaisa da mahmud altho shikan tsokanan ta kawai yayi..majeed ya karbe wayar sa ya fita..mahmud yace  kuna sha'anin ku majeed shiyasa baka da problem.

Yayi murmushi yace fitina dai fushi take don meeting din dazu shine taje ta danna kira hmm mata fa sai a hankali..mahmud yayi dariya abunsa yace ai yanzu ka fara ..talk later suka katse wayar ya dawo..

Kunya take ji sosai  amma sai ta fuske after oll ai ko ba din ma shi mijin ta bane shi bestfriend din ta ne so dole tayi fushi ko kishi...

Cikin tsokana yace wai ma wayace ki kiramin aboki na...tace ai na gaya maka mistake ne... yace mistake ?shi mistake din  Sai ya rasa wanda zai kira sai namiji meyasa baki kira yan mata ba....masifan neman tsokana yake amma kamar dagaske..a ranta tace what yan mata..? Ta juyo tace ban kira su ba ni shi din zan kira ki ta karashe kamar mai shirin fashewa da kuka... yace toh ba da waya na ba ni bana so

Tace saboda me? Ta zaro mai ido shima ya zaro mata nashi yace saboda ena da kishi gaskiya bana son double friendship ni nika dai nake so kar ma a hada ni da wani if not nima zan nemo wata kawa kuma mutum bai isa ya ji kishi ba ....tace iyeeeee da chan na san shi ne ma?
Wa ma zaiyi kishi
Da kai ni bana kishi.... yace ohhh da safen nan waya yake hura fusakn dan aboki na ya kira ni

Ta shagwabe tace lie..  ba shi bane ai cewa kake sarauniya mene mene zaka kira ta anjima kai kaji.....

ya fashe da dariyan tsokana mai ban haushi yarda ta fada kamar an sata dole hannu ta kai masa kan kirji zata maka masa ta sa kukan shagwaba tana bubbuga kafar ta a kasa..

Abun na dada bashi dariya suka shiga zaga waje har waje chan ya jata suka tsundumo cikin ruwa..
Gaba daya sai haki take ya gajiyar da ita shikuma bai gaji ba ya shiga watsa mata ruwa a face din ta dake shirin masa hawayen gaske...

Tsokanan ta yake and she knew gaskiya yake fada kishin sa taji sosai dazun amma take neman boye wa abun na bata kunya sosai..so she started criyng sillently ..

Ya matso kusa da ita ya jawo ta jikin sa ta lafe yace" preety girl yau kuma baki san wasa bane.?meye na batarai kina kuka Ni wallahy wasa nake miki na san kin fi karfin kiyi kishi besides we just frnds akwai irin wannan ai ko?..ko ajikin ta sai ma dada kankame sa data keyi suna tsaye cikin ruwan haka zalika bata amsa ba...yace toh ki dena kukan mana  nima zan fara yi fa sai ya shiga matso muryan sa irin nata ta dago zata kalle sa murmuahi ya sakar mata wanda ya sata sauke nata dan dole ya ce hey come here ya mata chakul chakuli tana dariya ..daga bisani ta juyo suna facing juna nan ta shiga sa hannu tana kan lotsa yatsan ta kan dimple points dinsa cikin wani irin shaukin so suke exchnging glances...

Yayi kamar zai fadi ta firgita zata ka mosa suna daf da gogar fuskan juna ya dago haban ta ya shiga kisssing dinta soflty..

Kankame sa tayi tsam a jikin ta sai da sukayi mai isar su ya dago ta chak suka dawo daki..

Nan ne ta lura ya gama kimtsa ko ena..ta mirgino zuwa bayan sa tace ya naga babu kayan mu...ya ce tafiya zamu yi ko baki so kije kiga su antyy jamila...?

Ji tayi kamar tace bata so amma sai ta tuna gida ta gyada kai tare da sauke karamin murmushi...

Tare da mayar mata yace oya lets dress up jirgi na zuwa nan da lokaci kadan...

Ta ce amma hakan zamu tafi babu kaya ni gaskiya ah a..ena hijabi na toh.

Yace nooo bazaki sa shi ba yayi datti  kinga nan ba mai wanki kuma ban wanke ba.....tace babu datti yace noo akwai..ya mike tsaye riga da skirt din ta ya ja gefe kadan ya dago atamfar ta da suka zo da shi tun ummah na raye..
ta gwalo ido ta kwabe fuska tace dama akwai kayana mai mutunci kace babu ?

Yayi dariya yace eh din...
Ai kuwa shika dai ne nima kinga guda daya ne tal dani mai mutunci yau ba gashi zai yi amfani ba..
Da haka suka ta shi suka kimtsa sun ma mance da wani abinci..

Wajen shiri Da kyar skirt ya shige ta ta dan karu sosai ta hips din ta sai rigima suke fama shan wajen jan zip...haka dai ta sa amatmmatse
Yayi dariya har ya gaji yace bata excisce irin na shi shiyasa.. daga bisani yace ko muje mu siya wani ne naga kamar wannan din zai takura ki ko?

Da ta dube kanta taga yadda ta mokade.cikin shagwaba tace eh amma ni atamfa nake so..

Baice komai ba sai yayi tunanin tunda ma dama bai yi na aure ba this is the perfect time suje ta making choices dinta kafin su tafi kaduna...

Yace ok...muje toh mu nemi atamfa haka suka bar wajen cikin kewa har jirgin sa ya zo ya dauke su zuwa dubai..

Ta rinka kiriniya da kyar ta kyale sa ya mata bayanin akwai irin atamfa laces materials da dik irin wanda take so a anan dubai ..

Suka je babban shoping mall tare duk abunda ta nuna sai an daga mata ko da kuwa cewa tayi yayi kyau badon tana bukata ba.

Fadin yawan kayan da aka mata babu iyaka akwai ..yasan da designers agida na musamman amma wayannan ya mata ne inform of kayan akwatin ta na aure..so komai sai da aka maimaita harta kayan kwalliya da jewerries da sauran abubuwan mata na kyake kyale babu dama..

Sun Dauki lokaci sosai a hakan so Kafin nan su iso nigeria sai washe gari..

da shike kayan ya riga isowa Sai aka tsame kusan set 50 aka bada dinki wajen one of the  first class designer nigeria wato hudayya fadoul a chan abuja...

Sukuma Sai wajen Karfe 9 saura na dare
Suka iso kaduna state nigeria.









*surriem*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top