part 21

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*


    ™/8/ 2018🔞
   *🌺SAKAMAKO🌺*
    _The pitch blunder_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_
  @ _IG:Surriem-sule_

*#Lovestory2018*
*#romance#fiction..*
*any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.*




*Page▶39-40*




Tafiyar sa ke da wuya suhan ta shiga daki ta rarumo kayan ta ta fice  a gidan
Gidan anty jamila ta soma zuwa  tana shiga wani dadi ne ya dada lullube ta ganin ummah zaune kan tabarma

..da murmushin ta ta zauna suka gaisa ummah tace " ah a suhan ..ya yau kuma naga kin fito da wuri lpya kuwa" lokacin suhan nakan mika hannu zata amshi gyaran domin ta cigaba da yi...

Tace "Ummah ai ni kadai ce agidan bakowa yanzu..dama yayi tafiya  ne shine nace
Bari kawai nima fito da wuri...

Ummah ta dan yi shiruu daga bisani tace" ah'a suhan, ni sam ban yarda da wannan sabuwar dabiar taki ba ai kamata yayi ki jira dai dai lokacin da mijin ki ya iyar miki sai ki taho bawai don ya fita sai kema kisa kafa kifito ba..wannan ba dai dai bane idan kuma kika fara daukar irin wannan salon Da haka fa zaku mike kuna ganin ba komai ba..

Ta Dan dago a sanyaye tace "Toh ummah naji bazan sake ba "... Ba kinji ba dai kidena kinji?... ta  gyada kai a hankali tace toh ummah...anan anty jamila ta shigo ta same su sai suka gaisa sauri take don haka ta fice ta kyale su suka cigaba da hirar su ..

  Chan wajen 10 suhan ta kama hanyar restaurant ranar gaba daya aikin ta take hankali kwance bata ko tuna zarah.

Haka rayuwa ta kasance musu yau kusan 4 days kenan da tafiyar captain amma sam suhan ta ki resuming bakin aikin ta na serving zarah abinci kamar yadda ya gindaya mata...

Zarah na sane da hakan amma sai ta fuske ta cigaba da zuba mata ido
Taso ace tayi ma suhan rashin mutunci amma sai ta ce bari dai ta fara neman shawaran kawayen ta..

yau da shike a office din ahmad ta wuni suna wani karamin meeting tsakanin su da acting board members na group dinsu ..

Sai Bayan nan ne suka samu zama tare da faiza..
Wacce ke kan tsokanan ta cos a lokacin ana neman karfe 9 saura na dare amma zarah bata ko motsa ba bare ta yi maganan komawa gida..

Tace" kawata watoh don majeed baya nan a gari shine zaki kwana mana anan ko?

Dan karamin tsaki zarah ta dan ja tana kan latsa computer batare da ta juyo ba tace" hmm faiza kenan.. u know that ko yana nan ma in naga dama zan iya kaiwa wannan time din so pls stop and dont make it an issure ta juya ta wata mata harara.....

faizah tayi dariya tace a da kenan amma  dai banda yanzu...zarah bata kula ba....  faiza ta kuma cewa ai na lura tunda aka kawo wannan amaryan nan naki sai abunda akaa ce dake kike yi ..zarah kin yi sanyi wallhy. Ta dan mayar da maganan in a  seriious tone.

Dan shiruu ne ya ratsa wajen cos har yanzu zarah na faman hadiye maganan da faizan tafada mata a ranta " babu abunda ta tsana kamar ace wani ya kawo canji rayuwar ta musamman ma in baiyi dai dai da ra'ayin rayuwar ta ba...amma ya zata yi? Gaba daya abun ya hau  mata kai ya dawo mata har kashi biyu.

....a zahiri tana mugun son ta daura career ta ko dan ta kere ma tunanin kowa sannan tana ganin wannan ne kadai hanyar da zai sa mum da majeed suna daraja ta su daina correcting dinta cos she literally take all her mistakes as fair and independant ba ruwanta da ko dai dai tayi ko ba dai dai ba..
awajen ta "in life kowa da ajin sa da kuma matsayin sa so talaka ya zauna a talaka mai kudi ya zauna a mai kudi sannan haka ma mutum kaskantacce da mai daraja basa taba zama waje daya..

Ta dan juyo ta kalli faizah
Tace :i dont have thy time faizah..  ni dai nasan nafi karfin su.wallhy kema ya ishe ki hada ni da wancan yarinyar she's nothing but a slave  to me .maganan miji kuma all i know iz mum ke cusa ma majeed  zama da ita  i dont think ma zai tabaa son ta ..ko bakisan yanzun ita ke mana girki agidan ba?.infact doka majeed ya kafa mata akan tana min food services ko baya nan so u see!! bawata sai ni kuma wallhy nasha gaban kowa.... Tana kammala maganan ta dan yarfa hair dinta baya stylishly tana yatsine..

Faizah ta tabe baki tace hmm i like that... amma kinsan ranar da mum tayi mana rashin m din nan gaba daya sai naji na rusuna yasa sai naga kamar duk suna bayanta an bar mana ke a tsakiya.

Hmmm mum ne fah kuma ya wuce kar ki damu faizah...dama buri na na sami hadin kan majeed wajen bude career ta kuma na samu so what? Indai wannan yarinyar ne kuma kar ki wani tada hankalin ki hadin kanku kawai nake nema by the time naci uban ta na wulakanta ta dakafar ta zata  yi parking tsummokaran ta ta bar min gida na..

Faiza tace"Of cous gal sai yanzu naji magana..wannan ai ba sai kin nemi ni ba ko bakki nan zamu iya miki komai.. matsalar dama wannan mother inlaw naki ne amma she's gone now so zan ma aneesaha magana zamu hada plan din yadda zamu gara shegiyar ai sai ta gane kuran ta...da haka suka cigaba da hirar su ranar sai wajen 12 na dare zarah ta dawo mansion.

Da shike ita kadai tasan majeed bai karasa US ba sai ta kira shi ta gama zuba masa makirci da hade haden da suka shirya da su faiza kafin nan tayi bacci..

Washe gari da safe suhan ta kammala shirin ta tsaf tana kwance tana jiran lokaci wayar ta ne yayi ringing..tunanin ta anty jamila ne ko zuby amma sai taga new number ..ta duba da kyau bata gane ba sai kawai ta ajiye a bugu na hudu ta dauka cikin sanyin murya mai dauke da dar dar tace salam"
Shiru ne ya biyo baya kafin ta tsinkayo muryan sa yana cewa wato ba kiji ko? Zarah tace baki aikin ki tunda na tafi baki taba serving dinta komai ba  "wai ma kafin na tafi me na ce kina yi agidan nan kin manta ne ko raini ke damun ki?

Ta dan turo baki kamar wacce ke gaban sa cos dayayi maganan saida taji faduwar gaba..tace toh waye kuma zarah ni  ban gane ta ba!!.. ..abun ya bashi haushi da mamaki yace "toh?baki san wacece zarah ba?hmm toh kar ki taba gane ta In kin ga dama"
en dai nazo na sameki ne dakai na anan zaki gane da kyau..ya dan ja tsuka

Dan shiruu tayi daga baya tace ...ni  babu abunda banayi ai kaima ba gani kake ba

c'mon quiet ya fada da normal voice dinsa cos rashin kunyar nata burge sa yake..yace "nidai idan na sake ji ance baki aikin ki just know that idan na dawo bazaki ji dadi ba.
Toh naji.. ta fada kasa kasa tana murguda baki....ya katse wayar sa dan karamin murmushi yayi yace kwaji da shi ai

Dan karamin tsaki ta sake ta dan tabe baki cikin ranta  tace:mm mmmm wai ankai kara kenan ashe ana jin tsoro na tunda ankasa zuwa a same ni...
Ai Sai dai nayi don ya dada sa baki amma karyan wata ta zo ta sani nayi mata girrki.

Ko da ta fita ta samu zarah har ta fice so sai ta bada izini masu aiki suyi abinci su ajiye mata kafin ta dawo..altho bata taba fadan hakan ba amma sai suka amsa mata a ladabce sannan ta fice.

Tunda ta fice sai Wajen karfe 6 saura ta dawo don haka ta shiga ta kimtsa kanta tsaf kafin ta dawo kitchen abincin da tasa aka dafa aka bar mata shi tayi musu warming ta jera su ta fito da sunkan dinning ta shirya tsaf ta koma kan kujera enda suke yawan zama da mum da  tayi zaman ta tana kallo

Chan wajen 8 Su zarah  suka shigo surutun data soma ji ya tabbatar mata ba ita kadai bace sai ta dauke kai bata sake kallon wajen ba..

Da wani irin  wulakantaccun kallo suka wuce kowace daga cikin su sai da ta ya motsa fuska kamar kashi suke gani yana zaune

..ko ajikin suhan don bata ko kalle su ba ma bare ta san me suke yi..su ukun suka wuce a gaban ta suna kaiwa daki suhan itama ta tashi itama ta koma site dinta...

In not less than 20 minute maid mai suna sarah ta buga mata knock tare da sanar da ita zarah ke kiran ta..

Ba musu ta fito sanye take da dogon riga baki mai shape ba ko kwalliya akan fuskan ta she looks preety and natural....

Sarah tace ma zarah gata nan madam tare da rusunawa ko amsa ta basuyi cos hankalin su nakan suhan dake  takowa hankali kwance ..

Aneesah ta dan tabe baki tace tabbbbbbb...

Nan Suhan ta karaso kan dining inda suka jeru agaban abincin kamar wasu yayan sarakuna
.
Bata ce uffan ba ta ja ta tsaya...bayan musayar kallon banza faiza ce ta daure tace" a gidan ubanki haka ake serving abinci da bazaki zo ki yi mana yadda ya dace ba...?

Zarah ta karbe maganan da cewa "pls hose down frnd kar ki bata yawun bakin ki kauyanci ne ke damun wasu amma kwadayi yaki barin su zaman wajen daya "
tace" cmon will u open this filty thing you call food..?

Suhan na shiru bata tanka ba bare ta nuna alaman bacin rai tankar bada ita sukayi maganan ba haka tayi....don ta lura intayi hakan sosai ransu yake sosuwa ..sai ta bude abincin ta shiga serving dinsu ko wanne ta sa masa komai a gaban sa neatly..tana yi baji su bai yi shiri ba suna mocking dinta da maganan banza cikin hirar su amma haka ta danne zuciyan ta har ta gama kafin ta ja gefe ta tsaya...

Aneesa ta dan leka kan abincin tace" model pls ki soma tabawa ki gani in yayi toh kar muje muci mu mutu..suka kwashe da dariya mai kulawarwa zarah ta soma chakka spoon akan abinci a wulakance tana watsarwa akan table sai ta dago tayi yalele da shi a spoon daga karshe tace uhm uhm no way..wannan abincin sai kace na almajirai? Cmon park it mun koshi.ta sauke nata harara masu zafi

Faiza tace wa?tab nikam ban yarda ba kawai taje dai ta kara mana wani kinsan fa idan bawa baisan aikin sa ba da wahala ake koya masa ta maida ma suhan wani hararan...

Anan ran suhan ya baci sosai tana ji zarah ta dago tace "ai kinaji kin wani yi ma mutane shiru.. sai kije ki dafa musu wani and mind you kika sake kawo mana chagwal zaki sake komawa kiyi mata sabo don nikam i cant eat dis dirty thing anymore..

A dan fusace suhan ta kalle ta ta watsa mata harara ...tace toh ni nagama aiki na kenan don haka bana sake dafa wani abinci a gidan nan U can say what eva u want wannan ke ta shafa ba ni ba ..
In kin damu da sai kawarki taci abinci ga hanya sai kije kitchen kiyi mata dai dai daku yan gayu ta bisu da kallon sama da kasa...ta dake tana binsu da ido babu alaman girgiza bare tsoro.

Bude baki sujayi galala suna binta da ido cikin mamaki..Iyeeeeee ? Zarah tace tare da mikewa tsaye lokacin faizah har rike aneesah take ita a dole zata
Zata tashi ta mari bakin suhan...

Uhm unm zauna aneesah kar ki bata lokacin ki ai na fi karfin nayi sa'insa da wannan da shi wanda ya ajiye ta da shi zanyi...ba bata lokaci ta danna call ma majeed"
Shikam yana chan yana kan hutawa tukunna cos awajen su dare baiyi ba

so yana daukar wayar ta shiga jero masa complain hade sa nasifa tana gunani ba ko kunya ta shirgo karya ta har hada maganganun wanda mafi akasari basu ma faru ba

'suhan na tsaye taji zarahn na cewa " tabb ni na bata waya ta  fa kace yarinyar da saura kiris ta zabga min mari ? Allah ya kiyaye.. ai tana da waya sai ki kira ta tayi maka bayani da bakin ta tunda baka yarda dani ba

....baice komai ba ya katse wayar sa cos yasan halin zarah sarai ba lallai bane abunda tafada gaskiya but he cant vote for suhan too so yake yaga ya wulakanta ta taji haushi..

kirrrr wayar suhan yayi ringing agabn su tsaban haushi da kamar ba zata dauka ba amma sai ta dauka...shiruu su kayi suka kasa kunne sosai ko zasu ji meyake fada mata amma shiru ..gashi tunda suhan tayi sallama bata sake tankawa ba sannan bata nuna wani alaman bacin rai aranta duk dama fada yake mata sosai...a ganin sa ko ba komai ai zarah kamar elder sis ne wajenta Tunda ta girmeta.

Naji..was the last word she said..sai ta katse wayar ta kama hanya zuwa kitchen adan fusace...

Anisah har tuntube take don leke faizah ko tuni tayi kasa don dariyar wayar suhan ..dan karaman nokia ce wacce tadan sha ruwa don haka gaba daya suka dukufa suna making fun akai kowa na fadan albarkacin bakin sa...

Haka suhan ta shirya musu wani abinci duk dama faizah ce kawai ta taba hakan ma dan su cusa mata bakin ciki dan kadan ta taba suka bar mata sauran

Haka zaman su ta kasance sumtyms ta zo da faiza  wani bin aneesa ko dukkan su a tare

...Abun na matukar bata ma suhan rai amma ta yanke hukunci bata kara ce musu komai amma duk randa suka kaita makura zasu gane kuran su..gashi kowani lokaci suka zo da salon iskancin da suke tahowa da shi.

Lokaci na tafiya yanzu captain yana neman satin sa na biyu da kwanaki 5 chas da tafiyar sa waje jinshi shiru ya tabbatar musu cewa ya koma bakin aikin sa achan us''

Around 2 suna zaune da zuby suna hiran su cos zubyn taje wani bikin cousin sis dinta a kano..tace suhan na kawo miki wani abu kuma zanso kiyi amfani da shi" tace me kenan?
Nan zuby ta dauko wani madaidaicin jarka mai dauke da wani abun aciki ta ajiye gaban suhan tace gashi nan"

Nan ta shiga mata bayaani hadi ne irin na matan aure mai kyau wanda amarya ta bata akan ta ajiiye makanta amma sai taga yafi da cewa ta barma suhan tundaa ayanzu haka itace matar aure..

duk yaddaa suhan take kaucewa akan bazata yi amfani da komai ba a haka zuby ta ki sam sai da ta sa ta karba..tace mata ai ba wai don mijin ki bane kawai wannan haddin da kike ganin sa natural ne babu  wani abu da bazai amfani jikin ki da shi ba..

da haka suka rabu ta je gida koda ta fada ma anty jamila sai ta karba ta taba taji anan itama ta kara mata bayanin muhimmancin  sa don kuwa da wuya ake samun sa sai a niger mafi akasari

sai tayi amfani da wannan dama itama ta sa ta amfani da wasu hadin da ta tanada mata duk wani tsafta da gyara da Tsumi da sauran su ta daura ta akai...a tunanin ta ko ba yanzu ba zai mata amfani wata rana

da kyar suhan ke yi abubuwan duk dama komai yazo mata da sauki saboda yanzu  kullum takan zo gidan kafin taje aiki ko en ta dawo 
sai ya zama mata kamar routine akai akai tana directing dinta tana using nasha kuma tana sha.

hankalin zarah a kwance yake tana aikin ta a tsanake gashi yanzu kam no daubts ta tabbatar ma kawayen ta ita isashhiya ce a gidan ta babu space din wata kishiya..

Haka ma suhan duk dama bata jin dadin yanayin zaman ta da zarah amma haka take daurewa...sai dai ga jikin ummah yana so ya tashi sosai amma da shike a karshen satin akayi mata biya bata daga hankalin ta sosai ba sai ta kai ummahn asibiti kwana biyu aka dan bata gado ana kula da ita...


Ranar da safe suhan ta tashi da matsanancin ciwon mara don haka bata samu taje ko ena ba tana kwance..
gaba daya satin dama ta dan gano kanta saboda cikar nonuwar ta da kuma zugin da suke mata ya sanar da ita al'adanta ne yake daf gashi kuma ya zo...

Bayan tafiyar zarah office da kyar ta samu ta kimtsa kanta tayi hanyar kitchen don ta hada makanta wani abun mai ruwa ruwa mai dumi ko zata danji karfi cos sosai period ke dauke mata appetite din ta sai taji bata shawa'ar cin abinci duk dama zata na jin Yunwa

..kitchen ta nufa lokacin ba kowa ko ena na bada fresh cool scent tamkar wani palace haka gidan yake ko ena neat komai a tsare...

A gaban food dressing table ta hango wani glass cup dauke da fresh milk an rufe sa kadan da filter paper yayi kyau take sai taji sha'awar abun ya taso mata sosai so sai ta sa hannu ta dauka"its warm dai dai yadda take muradi don haka batayi wata wata ba ta sa a bakin ta ta dan kurba

Dan lumshe ido tayi na dan mintina tana jin yadda yake shigan ta nan ta baje ta shanye tass ta ajiye cup..sannan ta koma sama abunta..

Tafiya take tana hiccups kadan kadan 'sai yanzu tunanin ashe fa bata san ma na waye tasha ba ya zo mata...
amma sai ta cigaba da tafiyan ta da niyyar anjima inta fito zata nema maishi ta sanar da shi ita ta sha.tana murda kofar dakin ta  bata ko kara one step ba "cikin ta yayi wani irin murdawa ya hau hutsinawa shikadan sa..
Take wani zufa ya keto mata jikin ta ya soma sanyi...ta rararrafa ta shigo da cikin ya dada wani irin murdawa ba shiri ta zube kasa tare da sake salati anan ta zube kasa tana murde murde kamar mai ciwon nakuda daga bisani wani wahallalen bacci ne yayi awon gaba da ita

Sai chan wajen karfe 1.30 na rana ta samu ta tashi dishi dishi take hango maids sarah akanta fuskanta cike da damuwa ...gaba daya jikin ta ya kasa samun nitsuwa bare ta tsaya waje daya..tace madam
m lpaya kuwa?

suhan ta bude ido tadan motsa kadan wanda ya sa ta farga " ta dada cewa " sannu madam lpya kuwa nagan ki haka tun dazu na zo nan kina kwance kasa baki tashi ba...
Suhan tadan ja kadan tace" am wani ciwon ciki ne yakamani ...bata bari ta karasa ba tace madam ko kece kika sha madaran tecy?suhan ta dan dubeta alaman bata gane sunan ba amma tasan dai ita tasha madara kafin tayi ciwon ciki"tace eh ni nasha waye kuma teccy? Ko bakuwa akayi na sha mata abunta..adan dame tafada..noo madam ba hakan bane teccy ai pet cat din gidan nan ne nike kulawa da shi 'bata da lpya sai na hada madaran da maganin su irin antibiotics din nan amma dana dawo sai bangani ba shiyasa na damu ena duba ko ena  ...amma yanzu ya kike ji madam?

Suhan ta dan zauna bakin gida tana dada duba lpyar jikin ta don kuwa ko ciwon menstral cramps din Yanzu ta dena ji..tace am fine karki damu na warke ..tace kiyi hakuri dan Allah ba dagan gan na ajiye anan ba in kina so yanzu sai nayi miki wani...

suhan tace ah'ah ki bari kawai ni yanzu ma zan fita kawai kije...tayi godiya ta fice...daganan suhan tayi wanka ta samu ta wuce asibiti wajen su ummah duk dama bata fada musu bata jin dadi ba ita dai suhan tunani take kala kala so yau da wuri ta bar asibiti ta zo gida .

Unfurtunatly yau sai gashi har tayi bacci zarah bata dawo ba cikin kwana biyun ma kwata kwata suka dauke kafa alaman Aikin su ya dan sha kansu..itama sai ta sake ta cigaba da abunda ke gaban ta

bayan kwana biyu ranar sunday da daddare tun 8 suka cika gidan sai dai yau suhan ta dawo ba dai dai ba... shes not in the mood cos jikin ummah dazun ya dan sa jikin ta yayi sanyi...duk dama sun kwantar mata da hankali amma gaba daya bata jin dadin jikin ta..

As usual zarah da su anisa suka shiga tsula mata rashin mutuncin su..bayan ta jera abinci
Anisah ta turje ita kam sam sai an kawo mata fresh coconut drink

suhan ta daure ta sanar da ita babu kalar ingredient din data lissafa ayi mata dashi amma sam taki hakura da kyar sai tace taje tayi mata kowanne as long as is chilled and hand made

Suhan Bata jin dadi sosai cos shes running out of patient ga tunanin halin da umman ta ke ciki abubuwa suka taru suka mata yawa...
amma sai ta danne zuciyan ta bata bari ta afka musu kamar yadda take shirin yi ba ta kama hanyar shirya musu yadda suka umarce ta

sukan abun na su ma sai ya dada yin tsamari don boro boro suke gaya mata bakaken maganganu wuce tunanin mai hankali suna shewa tsakanin su

Ba laifi suhan ta kama hanyar shiga kitchen" ko karasawa batayi ba ta sa aka kira mata maids sarah.

Tace dauko min antibiotics dinnan ena so nayi amfani da shi..duk dama tasha mamaki amma ba tantama taje ta dauko ta kawo ma suhan

Guda biyu ne babu acikin sachet mai dauke da gida 12..

30 minutes mai kyau ta dauka gaba daya da zuciyan ta ta sa wajen hada musu drink.... wani kayataccen carrot and cocumber drink wanda yaji kayan qamshi da flavors ta kammalaa ita kanta sai da ta ware nata daban a gefe guda don tasha kallo..

kafin ta sa nasu a cups ta yi arrangin dinsu gwanin sha'awa rediish green ne kalar drink din sai bai mata wahalan dura maganin ta yadda take si ba.

kowa ta sa masa yadda take ganin zai serving dinsa zarah guda uku sauran kuma biyu biyu ta dauko ta dosu falo..

Tun kan ta karaso faizah tace" wallhy wasu mata dai sai a hankali..yanzun har wani kwadayin duniya zaisa na zauna irin wannan bauta" chab lallai talaka mai kwadayi baida zuciya sam sam sai yau na yadda..suka danyi shewa lokacin daf da so suhan take..

bata damu ba ta ajiye faranti a gefe sai dai yadda sukayi tunani ba hakan bane sai ta dauka tana mika ma kowa a hannun sa yadda ta tsara

..suko sai zuba rigima suke a ganin su duk isar su yakai haka

da ruwan sanyi tayi drink din don haka qamshin da sanyi sai ya ja ra'ayin su ba wani jan aji suka shiga sipping...ta juya takai tray kitchen

ta fito da nata a hannu maimakon taje daki kan kujera ta zauna daura da su ta zuba musu ido drink dinta na daga gefe bata ko taba ba tukun

wajen shiru..kowa nasha ba wanda ya tanka jim kadan faiza ce ta soma reacting... abu wasa wasa ta zube kasa tana rike cikin ta cikin radadi duka suka yi kanta hankali tashe suna tambayar meya faru

ana cikin haka Sai zarah ta biyo baya da shike abun na zarah yafi yawa anisah taga karamin tashin sense don kuwa tuni zarah tayi wani yar karaman suma tsaban azaban ciwon cikin

sai aka bar anisah da abun da ahiek ita baiyi wani affecting dinta sosai ba duk dama tanaji kadan kadan ...gaba dayan su suka rikita wajen suka rude da koke koke kowa na neman agaji..kamar basu din ba

anan suhan ta harde kafa
Ta dauko drink dinta tayi relax kan kujera tana sha hankali kwance... tamkar wasan kwaikwayo a talabijin haka ta tsura musu ido tana binsu da ido suna tereren tashin hankali ...

ga zarah a sume
Ganin abun fa gaba gaba yake nan anisah ta shiga hada suhan ta Allah akan ta taimake su ta kira musu emergency ko zasu samu rangwami amma ena!! yadda kasan bata wajen haka ta basar da anisah.

karshe ma da taga faiza na neman dauke nunfashi itama sai ta mike tsaye data bar wajen da rarrafe anisa ta kamo kafarta ....tace su..han pls don go..pls kar ki bari mu mutu mana

ita kanta ta sha mamakin rashin tausayin su datayi sai ta dan janye kafarta tace wai meye ne kuma bana muku abunda kuke so ba?ni wannan ba aiki na bane so bazan yi ba... in kuna so na kira  emegency sai ku kira shi ogan naku ku fada
masa ya samun a list din aikin da zan na muku amma wai don ku?tabbb Kun san wallhy karyan ku kusani nayi darajan aure sa baku san dashi ba kuke ci...ta dan maida musu murmushi mai kularwa

Cikin radadin takaici da fushi anisah tace haba ke kuwa  ke wai wata irin marar imani ce".suhan tace iyeee to ni me zan muku ...da ni nace ku yi ciwon ciki koni na yaba muku ?ai mugun bakin ku  yasa cikin ku ya hautsine dakan sa ni ba ruwa na...

Wani azababben kuka faiza ta fashe dashi cikin ranta tace wayyo Allah na im dying here ashe haka yarinyar take da bakar mugun ta"so take tayi magana itama amma ciwon ya hanata tankawa
Ga suhan sai tsula musu bakar rashin mutunci take
ta ma nuna musu ita ba abunda ta sani game da abunda ke damun su don haka baruwan ta...dan dole anisah ta sauke girman ta ta shiga maqiya tana rokon suhan...amma fir haka suhan taqi  da Abun ya ishe ta tace:
kinga nifa wannan baiya cikin aikina na fada miki so ba ruwa na.... sai ku karata da shi ai ku a waye kuke kuma kunada arziki sai ku taimake kan ku ..ta ja tsaki mai sauti tace ni barci ma nake ji gud nite. Kaiwa nan ta haura sama ta barsu awajen..

A cikin dakin ta Dariya sosai tayi musamman in ta tuna yadda suka nuna rashin dauriyar su da mugun tsoron mutuwar su a fili cikin ranta tace muje zuwa"daga yau duk wanda ya shirya cin abinci na sai ya shirya fama da ciwon ciki..

da safe koda ta tashi jitayi ance a asibiti dukan su uku suka kwana...

Wanka kawai tayi ba bata lokaci ta nufi asibiti domin duba jikin ummah kafin ta wuce aiki.




*thanks for waiting fans wayan da suka min maga na a pc ban amsa su ba suyi haKuri na sauya waya ne .. so im using new chat babu kuma chat history repost if u can.. same goes to all masu cemin na basu book din sakamako daga farko wallhy ban dashi kamar yadda kuke tunani nima a wattpad nake dubawa mostly so u can also get  it @surayyahms"DONT ask me pls nagode💋*









*surriem*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top