Tuwon madara and gullisuwa
Tuwon madara
Madara Gwangoni4
Sugar gwangoni1(ya danganta da yadda ake so,zaki iya sanya2)
Gurzajjiyar kwakwa gwangoni1
Ruwa rabin gwangoni
Method
Za'a cakuda madarar da kwakwa.A ajiye gefe guda.
Sai a dora sugar a wuta a zuba ruwan.Abarsu su dafu,har ya fara yauki(sticky)
Sai adauko madarar da kwakwa,a zuba ayi kasa da wutar,ko a sauke kasa,a tuka su hade sosai.Sannan a samu ledar sugar ko faranti,a shafa butter a juye.Daya fara shan iska a yayyanka.
Gullisuwa
Madara gwangoni4
Sugar gwangoni1
Gurzajjiyar kwakwa gwangoni1
Ruwan dumi cokali5(idan yayi kadan a kara)
Sai a cakud'a madarar da sugar da kwakwar,arik'a zuba ruwan kad'an ana juyawa,har yayi daidai(kada yayi karfi,kada yayi ruwa dayawa)
Sai a mulmula,a d'ora mai a wuta,idan yayi zafi a zuba a soya.
Note
Ba'a cika wuta wajen suya,zasu k'one
Ba'a cika jujjuyawa zasu farfashe.
Ruwan dumin na sanyawa tayi dank'o(tafi dad'i)
A nemi madara mai kyau da dango tafi dadin Gullisuwa da tuwon madarar.
Za'a iya amfani da cookies cutter a fidda shapes da ake so
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top