Meat Balls 1

Kayan hadi:-
•Nama
•Mai
•Koran tattasai
•Albasa
•Tafarnuwa
•B/pepper
•Citta
•Kwai
•Maggi/Gishiri
•Curry

YADDA AKE HADAWA
Dafa nama da albasa,citta,maggi da Gishiri.idan ya dahu luguf sauke shi.
zuba albasa da Koran tattasai,daka sosai sannan a zuba naman ci gaba da dakawa har su daku sosai.zuba curry da b/pepper chakuda so sai,sai a dinka mulmulawa kamar ball[round] ana bade shi cikin filawa haka za’ai ta yi har agama. 
kada kwai a kwano ko ruba,zuba mai a kasko yayi zafi,dinka saka wannan naman a cikin kwai ana soyawa a mai mai zafi. 

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top