Fruit Salad
Kayan hadi:-
•Abarba
•Gwanda
•Ayaba
•Kankana
•Leman zaki
•Kwakwa
•Leman tsami
•Suger
YADDA AKE HADAWA
za’a yanka duk kayan marmarin kanana-kanana(cubes). Za’a bare leman zaki sala-sala sannan acire kwallon a zubar,a tara totuwar leman da ruwan leman a kofi.
Goga kwakwa kanana.
Matse leman tsami a kwano,yanka ayaba kanana-kanana sai a zuba cikin leman tsami (yin haka yana hana ayabar tayi baki).
Dafa suger da ruwa ajiye gefe daya.
Za’a hada duka yankakkun kayan marmarin waje daya acikin abun da ake hada fruit salad.zuba suger aciki juya sosai.
Idan za’a sha zaka iya zuba condensed milk akan fruits din.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top