Fried Rice 2

Kayan hadi:-
•Shinkafa
•Mai
•Peas
•Koran wake
•Kaza ko nama
•Albasa mai lawashi
•Maggi/Gishiri
•Dark soy souce
•Kwai

YADDA AKE HADAWA
wanke shinkafa tsane ta,zuba mai a tukunya sai a soya shinkafar idan tayi dan ja sauke ajiye gefe daya.
zuba mai a tukunya soya albasa da kwai wanda aka kada shi da maggi da Gishiri,juye a ciki har kwan ya nuna.ajiye gefe daya.
soya albasa da nama zuwa minti 3-5.juye shinkafar da ruwan nama idan yayi kadan a kara,zuba Koran wake da peas,soy souce da albasar da aka soya da kwai,juya har komai ya dahu sosai.dandana Gishiri idan ya isa sauke.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top