Fish Balls
Kayan hadi
1-kifi babba
2-tarugu
3-mai
4-tafarnuwa
5-maggi
6-gishiri
7-albasa
Yanda akeyi
A gyara kifi yazama babu qaya acikinta a wankeshida lemon tsami yanda qarninsa zai ragu sai a Dora mai a wuta asa albasa a soya kifin sama-sama idan ya soyu sai a tsameshi a kwando a wanke tarugu da albasa a jajjaga sai a bare kifin acire qayar sai a hadashi a turmin tareda kayan miya azuba su maggi aci gaba da dakawa harya gauraye sai a kwashe aroba sai a dafa qwai a cire qwaiduwa amurmusashi akan dakakken kifi a juyashi ya hade da kifin sai adinga diba ana dunqulawa ana dangwalan mai idan aka gama sai a Dora mai a wuta idan yayi sai a dinga daukan kifin ana shomawa a qwai ana soyawa sama-sama zaiyi kyau Dan ba a so ya soyu sosai.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top