Egg Specials

NAMA CIKIN KWAI

Ingredients:

* Kwai
* Nama
* Gishiri
* Maggi
* Albasa
* Attarugu
* Mai

Preparation:

Ki dafa kwanki daidai yawan da kikeso, kowanne ki yanke kasansa wajen fadin kadan ki kwakule kwanduwar a hankali ki cire ta, ki tafasa namanki da curry, thyme, maggi, gishiri.
Idan ya dahu ki zuba attarugu kadan ki daka naman, sannan ki dinga debo dakakken naman kina turawa cikin kwai, idan ya cika sai ki debo kwanduwar ki toshe bakin kwan da ita, haka zakiyi tayi har ki gama, sannan ki dinga tsoma kwan a cikin ruwan kwai kina soyawa, idan ya soyu sai ki kwashe, wannan nama cikin kwan yana da dadi.

SUYAR KWAI MAI NAMA

Ingredients:

* kwai
* Nama
* Maggi
* Gishiri
* Curry
* Albasa
* Attarugu

Preparation:

Ki tafasa namanki da maggi, curry, thyme, albasa, ki daka shi sosai, ki fasa kwai ki yanka albasa, attarugu, ki zuba dakakken nama, ki karo maggi da gishiri daidai yadda kike so, ki kada sosai, ki soya kamar wainar kwai.

*WAINAR KWAI MAI ALAYYAHU*
Ingredients:

* Kwai
* Hanta
* Alayyahu
* Curry
* Maggi
* Gishiri
* Albasa
* Attarugu
* Mai
Procedures:

Ki yanka alayyahunki kanana, hantar ki daka ta, bayan kin dafe ki fasa kwai ki zuba hantar, ki zuba alayyahunki, curry, maggi, gishiri, da albasa, idan kina so, ki soyata kamar suyar wainar kwai.

*CI KAYI SANTI*
Ingredients:

* Kwai
* Nama
* Curry
* Maggi
* Gishiri
* Tumatir
Preparation:
Ki dafa kwanki, daidai yawan da kike so ki yanka shi kanana, ki yanka tumatir, attarugu da albasa akai ki yanka tafasasshen namanki kanana a kai, ki fasa kwan ki zuba akai, kisa maggi, curry, gishiri, ki kada ya kadu sosai, ki dora mai a kan wuta ki soya kamar suyar wainar kwai.

Yadda ake Awaran Kwai

Abubuwan hadawa

Kwai
Attarugu
Albasa
Man girki
Maggi
Leda
Yanda ake hadawa

Da farko zaki sami kwanki ki fasashi a kwanan ki mai kyau ki kadashi
Sai ki zuba kayan hadinki: attarugu, da albasa wanda dama kin yi giretin nasu da sauran kayan dandano dai dai misali
Sai ki dunga zuba kwan naki acikin leda kina yi  masa kamar kullin alalan leda
Sannan sai ki dora ruwanki cikin tukunya ki dafa kullallen kwan naki
Idan ya dahu sai ki kara fasa wani kwai, kuma ki cire wannan kwan naki na leda kina yankashi yankan tsakiya za kiga ya bada shef  din zuciya, watau ‘heart’ sai ki dunga tsomashi acikin wannan kwan naki
Sai kuma ki soyashi a manki mai zafi sosai, amma ki yi suyar sama-sama don ya yi suya mai kyau
A ci dadi lafiya. Na gode.

EGG SAUCE

INGREDIENTS:
1.Eggs
2.Albasa and attarugu/tattasai
3.Curry, Maggi, salt, garlic and curry powder
4.Oil.

PROCEDURE: Farko zaki jajjaga kayan miyan duka sy daku sosai, sai ki zauna ki yanka albasa dinki isashe ko kuma ki niqa.
Daga nan zai ki dauko frying pan ki sa a wuta, ki sa masa mai kamar 3 spoon, sai idan ya fara zafi sai ki juye dukkanin albasan ki, ki soya man dashi, daga nan sai ki juye kayan miyan, kisa maggi, gishiri, curry kadan. Ki cigaba da soya shi, kuma a lura da wuta, saboda ana so ya dan dahu kayan miyan musamman idan dayawa ne, zaki iya dan rufe kayan miyan koda na 2mnt ne saboda yayi taushi in ba ruwa zaki iya diga ruwa.
Daga nan sai ki dauko eggs din wanda already kin fasa kin kada sai ki juye, ki jujjuya su hade sosai. Idan kina so yayi dunkule dunkule, zaki barshi ne har sai ya fara soyuwa, sai kina juya shi ba tare da kin barbaza ba. In kuma kina so sai ki barbaza shi. Kwai din na gama soyuwa sai ki sauke kiyi serving.

Another method

Shi kuma wannan wasu suna fasa kwai ne a kwano, sai su juye dakakken kayan miya da albasa din su a cikin kwai din, sai su sa mai ya dan yi zafi sau su juye shi ya soyu. Ana cin egg sauce da Plantain, potatoes, yam, dama sauran su.
Note: Mata dayawa suna bata sauce din su ne ta hanyar zabga tumatir, amma ni ban yarda da tumatir ba a sauce. Idan ma zaki sa tumatir to kada ya wuce guda daya, saboda yana sa shi yayi ruwa, kuma yana sawa aji tsami, yana kuma bata taste idan wacce bata iya ba ta sa.
Egg sauce ana cin sa da abubuwa dayawa, ba wai dole sai dankali, doya ko plantain ba. Don haka In zaki yi na miya dayawa ne kamar yanda daya cikin pictures din ya nuna, sai kin gama miyan ki.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top