Donut

DONUT
Kayan hadi:-
•Filawa
•Kwai
•sugar
•Madarar Gari
•Yeast
•Ruwan Zafi
•Butter
•Man suya

YADDA AKE HADAWA
Kwaba filawa da madara,butter,sugar,yis da kuma ruwan zafi,kwaba ruwa ruwa kamar yadda ake fanke rufe da lada zuwa minti 30,asa a rana.
idan kwabin ya tashi,shafa mai a farantin silba,zamu dinka mulmula wannan kwabin kanana kamar [ball] muna dorawa akanfarantin haka za’ai tayi har agama,mayar da shi rana ko bakin huta,idan yayi zamuga yana tashi dakansa.  
zuba mai a kasko yayi zafi sai a dinka dauko wannan filawar ana sawa a mai amma kafin asa sai a dinka bula tsakiyar ana sawa a mai,idan angama a barbada sugar.
Da sabon oil ake frying donut banda old oil.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top