Different types of Kunun Aya

Yadda ake kunun aya mai kankana

Da farko xan jiqa aya na surfa na wanke na yanka kwa kwa qanana na wanke na bare dabino qanana na hada naxuba kayan qamshi nasa kan kana kadan saina markada na tace nasa suga da flavour nasa a frige

*KUNUN AYA MAI MADARA*

Abubuwan Hadawa
Aya
Dabino
Kwakwa
Madara ta ruwa
Suga
Kayan kamshi

*Yadda ake hadawa*

Dafarko zan gyara ayar na wanke na cire tsakuwa sai na cire kwallon dabino na wanke na zuba akan ayar sai na kankare kwakwa na zuba akai tare da kayan kamshi sai akai a markada kona markada a blender bayan an markada sai a tace a zuba suga da madarar ruwa sai a juyashi asa kankara ko asa a fridge

*KUNUN AYA MAI DABINO*

Aya
Dabino
Kwakwa

*Yadda ake hadawa*

Dafarko zaki wanke ayanki ki surfa kibare dabino da kwakwa kiwankesu kisa kayan kanshi kikai a markada mikisu sai kitaceshi da kwauri saboda inkika taceshi yayi ruwa bazakidinga jin gardin ayanba sai kisashi a fridge yayi sanyi sai a kawowa oga nasan wata zatace ba za'asa flavour ba nide gaskiya bana sawa saboda inde harkinyi shi da kauri to kanshin ayanma ya isheki nagode

*KUNUN AYA*

Aya
Kwakwa
Dabino
Citta/ kanumfari
Madara (ruwa /gari)
Sugar

*Yadda ake hadawa*

Farko in zuba aya a turmi a daka kadan acire baqin, sai a wanke sai kuma injiqa ta idan ta jiqu sai in saka kwakwa, dabino ,citta kanunfari dan kadan, sai inyi blending inda wuta ko inkai markadai, sai in zo in tace ,sai in zuba madara ta ruwa ko gari, duk wadda nake da, sai sugar, sai kuma in sanyaya shi.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top