Different types of Kunu
🥛Kunun Alkama
🥛Kunun semovita
🥛kunun shinkafa
🥛Kunun Dankali
🥛kunun Gyada
🥛Kunun Acca
🥛kunun zaki
🥛 Kunun ‘Ya’yan itace
🥛Kunun Aya
“'🥛KUNUN ALKAMA“'
*Ingredient*
🔅Alkama
🔅Aya
*Method*
Ki gyara Alkama wato ki wanke ki rege ki surfa saiki shanya, ita manaya ki surfa ki gyara ki shanya idan suka bushe saiki hada guri 1 ki kai a niko miki ki tankade saiki debi garin ki dama da ruwan sanyin, sannan ki kwara tafashshen ruwan kamar dai yadda zaki dama kunun tsamiya,idan kika dama zaiyi kauri. Zaki iya sa lemin tsami idan kinaso saiki zuba sugar da madara in kinaso .
Zaki iya yima oga wannan kunu yayin buda baki ko karin kumallo. Wannan kunu yana kara ni ima.
“'🥛KUNUN SEMOVITA“'
*Ingredient*
🔅Semovita
🔅Sugar
🔅Madara
🔅Lemon tsami
*Method*
Da farko zaki dama garin semovita kamar yadda zaki dama garin kunu ki zuba ruwan lemon tsami amma ba da yawa ba saiki juya gasarar sosai. Sannan ki zuba tafashshen ruwam zafi ki dam idan yayi saiki sa sugar da madara.
Zaki iya yiwa oga wannan kunu ya sha da kosan doya
“'🥛KUNUN SHINKAFA“'
*Ingredient*
🔅Shinkafa fara
🔅Man gyada ko butter
🔅flavour
🔅inibi bushashe
🔅 sugar
*Method*
Da farko zaki wanke farar shinkafar ki shanya ta bushe ki kai a niko miki ki dora ruwa a wuta ki zuva buttet ko man gyada kadan. Ki dama garin shinkafar idan ruwan ya tafasa saiki zuba ki dama sannan ki sa bushashen inibi ki sa sugar da madara. Zaki iya yiwa oga wannna kunu da hadadden kulele.
“'🥛KUNUN DANKALI“'
*Ingredient*
🔅Dankalin hausa
🔅Gero
🔅Dawa
🔅kayan kamshi
*Method*
Da farko zaki jika gero da dawa idan suka jiku saiki kai a markado miki amma kisa citta da kanumfari da barkono kadan. Shikuma dankai manya guda 2 saiki goga ki markada ki zuba a kan kullin da aka niko miki. Saiki raba kullin biyu ba saikin tace ba sannan ki kwara wa rabi ruwan zafi ya damu kamar koko rabin kuma ki kwara masa ruwan sanyi kamar dai yadda kikeson yawan kunun bayan kamar 30min zuwa 1 hr idan kika juya zakiga kokon da kika damaya tsinke yayi tsululu saiki hada da wanda kika sawa ruwan sanyi sannan ki tace kisa sugar. Zaki iya sawa yayi sanyi sannan yanada saurin yin tsami.
“'🥛KUNUN GYADA “'
*Ingredient*
🔅Gyada
🔅Madara
🔅Shinkafa
🔅Lemon tsami
🔅Sugar
*Method*
Da farko zaki bare gyadar ki jika ta itama shinkafr ki wanke ki jika idan ta juku saiki hadasu guri guda ki kai inji a markado miki sannan ki tace. Saiki juye wanda kika tace kisa a tukunya kita juyawa har yayi kauri sannan ki sa lemon tsami da madara idan kinzo sha ki sa sugar zaki iya yin wannan kunu tare da kosai ko Alala.
“'🥛KUNUN ACCA“'
*Ingredient*
🔅Acca
🔅Tsamiya
🔅Suga
*Method*
Da farko zaki gyara acca ki rege ki wanke ki shanya ta bushe saiki ki kai a niko miki sannan ki jika tsamiya ki zuba ruwan tsamiyar akan garin ki dama, ki rage gasarar ki dama kunun kamar damun kunun tsamiya. Saiki sa sugar zaki iya yin wannan kunu hade da Jallop rice
“KUNUN ‘YA’YAN ITACE“
*Ingredient*
🔅Garin Alkama ko semo ko shinkafa
🔅Ayaba
🔅Kankana
🔅Abarba
🔅Tuffa
🔅Kwakwa
*Method*
Da farko zaki goga kwakwar ki ki zuba ruwa ki tafasa karki taxe garin tsakin kwakwar idan ruwan ya tafsa saiki dana garin da ruwan sanyi ki kwara tafashshen ruwan a kai ki dama kunun. Dama kin yanka ya yan itace kanana kana na saiki zuba a kan kunun kisa sugar da nadara wannan kunu yana da dadi sosai zaki iya yiwa oga tareda alalan kabeji ko lokacin buda baki
'KUNUN ZAKI’
*Ingredient*
🔅Gasara
🔅Sukari
🔅Lemon tsami
🔅kayan kamshi
*Method*
Da farko sami gasarar ki, ki dama ta da ruwan sanyi sannan ki dama ta da ruwan zafi kamar koko idan ta dan huce saiki zuba ruwa da sugari a gasarrlar wadda baki dama ba ki ta juyawa har sugar ya narje amma gasarra kamar yawan waddavkika dama zaki dauka, saiki juye ruwan gasarar akan dafaffen kokon kiyi ta juyawa zakiyi iya kara ruwan sanyi dai dai yadda kike so. Amma wasu gasarar kawai suke sawa ruwa su sa sugar ba sa danawa sai dai na danyar gasarar yana lalartawa wasu ciki.
'KUNUN AYA MAI KWAKWA'
*Kayan Hadi*
🔅Aya
🔅Sugar
🔅Madara
🔅Cocunut flavour
🔅Kwakwa
*Yadda za’a Hada*
Kamar yadda ake kunun aya haka zaki yi amma kwakwar zaki goga ta ki kwara ruwa ki tafasa ki tace ruwan zaki hada da ruwan aya da kika tace ki sa sugar ki kara coconut flavour idan kinaso sannan kisa madar.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top