eps22

NUR FIRDAUS....22
SURAYYAHMS
Daga conference hostel kuwa rayuwa medadi tareda nishadi su nur firdaus sukeyi tareda kawayenta, tun ran da sukazo akanyi hira ayi wasa da dariya time to time haka nur zata zame taje can baya inda babu surutu snn tay bitan karatunta ko tay waya da adnan acan agefe dan tun da jadidah tafara saka idanunta sosai akan reactions din laylah akan adnan sai abubuwa dayawa suka fara bayyana musu a fili, wanda yajefa nur firdaus cikin tunanin ko da gaske ne laylan bata son soyayyarsu da adnan.
gabaki daya sai ta dan rage daukar wayarsa agabansu yakansace chatting kawai suke yawan yi dashi batare da tabari laylahn tana lura da hakan ba....
aranta tabari akan sai sun koma abuja snn zata lallabi laylan taji meye matsalarta da Adnan privately batare da tasako opinion din kawayenta acikin maganan ba sabida batason ta zargi yar uwarta akan namiji snn bata son laylan taji babu dadi.

*******Friday...
yau ranar jumu'a da asubahi javeed ya farka da wani irin zazzabi me tsananin zafi sosai wanda da kyar jikinshi ya dena rawa..

bangaren nur firdaus anan kuma bayan sun karya aka sanar musu cewa karatun gasa ta farko zaa fara saurara ne da ga ranar asabar daga 8.00am- zuwa 8pm na dare, amma sabida hidimar sallar jumu'a da sauransu yau din za a kaisu cikin gari suyi yan gaishe gaishe da ziyara ma excos din su.

they where all very excited sabida baba driver yace musu duk su shirya da wuri yau zai kaisu babban masallaci suyi sallahn jumuar dukansu acikin gari dan kowa yaga gari kafin su dawo su shirya zuwa wajen gaisuwa.

Dan haka tun farkawarsu suka hau shirin fita da zabar irin kayan da zasu saka kusan dukansu sun fitone da abayu masu kyau kuma bakake.

javeed bai bari ciwon sa na daren jiyan ya bayyana wa kakansa ba sabida yariga da yasan maganin matsalar aransa.

Da safe tunda suka gaisa ya barta da likitan ta bai sake lekowa ba sai da ya gama shirinsa tsaf

wajajen 12 ya fito a kimtse Cikin sauri tareda ƙwarjini irin na soja,.. da sallama Javeed A. Mufasa yashigo dakin kai tsaye ya nufi gadon da kakarsa ke kwance. Yana sanye da wata pure black slim fit suit data mugun amsar jikinsa fiyeda da wadda ya saka jiyan as usual fuskarsa a daƙile yake babu alamar wata rauni ko damuwa sai dai idanuwasa suna nuni da wani nau’in tausayi da ba a saba gani a tare da shi ba.

kallo daya yama likitan ta tashi cikin sauri da girmamawa ta basu waje, snn ya kalle kakarsa dake kwance muryansa atausashe sosai yace  "hajiya likita ta gaya min cewa jikinki yay kyau yau. tana dan murmushi ta riko hannunsa cikin lumshe ido tace "Babu laifi jikina ya warware, all thanks to you. tana kallonsa da kulawa take maganan, Javeed ya dada durƙusawa kusa da gadon, yana saka hannunsa cikin nata kamar yaro mai neman nutsuwa daga wajen uwarsa. ahankli yace zan tafi amma ba lallai bane ki sake gani na.

cikin datsar numfashinsa tareda lumshe ido muryanta me cike da rauni tace "Javeed bana jin daɗin zuciyata tun daga ranar da aka naɗa ka Brigadier General. Na san da kaunar dakakewa aikinka da dakuma  sadaukarwarka ga cigaban kasa amma ka san wani abu?"

yana kallontan amma ya mata shiru cikin sakin ajiyan zuciy tace ba ƙasar da kake bautawa ce matsalata ba, tuggun Zubaida da Simran ne. Javeed ya dada yin shiru bai ce komai ba dan shi sam wayn kananan kwarin basu gabansa.
hjy mammy ta cirkita laɓɓanta tana kallon yadda jikinsa ke daɗa samun ƙamewa da girman basira duk dama tasan yana rayuwane da dumbin nauyin zuciya da kuma damuwa.

tace "Kai ba ƙaramin yaro ba ne, Javeed. and very soon zaka kawo mana matar aure. Idan kana jin magana ta, ka zauna ka ɗauki matakin kare kanka nide Ina jin cewa akwai wani abu da ke yawan faruwa a bayan idonka dan Zubaida ba mace bace da na yarda da ita snn yar uwartan can kuma tana da mugun nufi irinnata, ni dai na shaida hakan bana kuma fatar sharrin su ya shafe rayuwrka."pls do not trust them javeed, ta karashe magnan cikin tari me dan kara, nan ya dau goran ruwa ya bata tasha cike da kulawa snn ya dan kwace hannunsa anata alamun ba ya son su ci gaba da wann zancen..

adan takure da kuma yanayin basarwa yace hajiya karki damu ina sane da komai tun ma kafin a faɗa min, kedai kidena yawan tunani akansu, duk wanda yake tunanin zaiyi wasa da ni zai sha mamaki nan gaba

dan shiru hajya mamy tay na dan wani lokaci snnn ta cirkita yatsun hannunta, tace "toh shikenan "Na yarda da kai amma bana son ka yarda da mutanen da suke kewayenka. "Ka sani, duk da kai soja ne, kana buƙatar kariya ta ruhaniya. yau ko gobe zanje ni wajen malamai sumin istihara da adduoi dan masu iya magana sunce Kada ka sake ka bar duniya tariga ka sanin kai waye ne."

Javeed ya lumshe ido dan Bai saba da jin irin wnn maganganun ba, ta ɗaga hannunsa a hankali to zan wuce ki kula dakanki. da sauri tace ka tsaya mana Javeed...acikin maraice murya tace jiyafa na maka mgana akan zuwa wajen gasa amma bakace min komi ba,..jikana ina sonka yi min alkawari cewa zakazo muje tare dakai dan Allah it wll mean alot to the family..ance min gobe ne yaran zasu fara gasa, sann marigayiya mamanka fa babban exco ce a wann organisation din nasu na kkrin daukaka  ilimin addinin islama da karatun al'qur'ani musmn wa yara da suke tasowa. cikin murya me cike da rauni ta kallesa ahnkli snn tace please and please u shud honour her choices javeed nasan baka da lkci amma tunda dai sun gayyace mu yakamata muje wajen kodan sabida mamanka..

shiru yay baice mata komi ba dan saida yadau minti kamar uku kafin can ahnkli ya dawo hayyacin sa tare da bata amsar a murde.. yace zan dawo in ganki, Zan tabbata kin koma gida lafiya..yana furta hakan yajuya ya fice ayanyinsa na nitsuwa securitynsa suka rufa mai baya har waje.

bin bayansa ta yi da murmushi mai cike da godiya tasan tun da yace zaizo din toh zaizo, dan tasan javeed baya taba sabawa magananta it doesnt really matter if he says yes or no directly.

bayan tafiyarsa bada jimawa masu aikinta suka fara shirin kaita wajen malamai kamar yadda ta bukata dan tunda mahaifyar javeed ta rasu ta saka aranta cewa zubaida ce kawai ta kashe mata surkuwa wanda duk duniya takejin kamarna ita ta haifeta sabida tasota fiye da yadda taso danta Alhaj attah mufasah,

lkcin da mahaifyr javeed take raye rayuwa me tsafta da dadi sukayi bazaka taba iya tantance ko ita da surkuwanta ba yan uwan juna bane.

shiyasa mutuwar mahaifyar javeed din yafi mata ciwo fiye da yadda suke zato amma haka ta cije ta danne dukkan zafin aranta sabida lamarin ciwon kwakwalwa me tsanani da javeed yayita fama dashi dayake karami.

yau fiye da shekara talatin da shida kenan amma itakam tarike fushi aranta, tanajin bazai taba wuce cewa zubaida bace ta kashe  mata surkuwa shiyasa duk sanda javeed din yazo wajenta toh sai ta gargadesa akan zamansa a lagos tareda su zubaida.

wata private masallacin jumua javeed suka wuce kai tsaye sede har sukayi sallahn zuciyarsa bai daina tunanin tarin maganganu kakarsa ba, ji yake kmr yana bukatar cikakken nitsuwa kafin ya iya yanke wani hukunci
akan request din nata
na zuwa wajen gasar
dan har yanxu bai san ko zai iya daurewa ya iya zaunawa acikin taron mutane irin haka ba cos most of his life schedules are really private and mysterios

aftr jumuat pryr basu bar masallacin ba har saida yay sallahn asr daga nan kai tsaye shida convoy dinsa guda biyar din suka wuce hanyar wata makabarta, wajajen 4pm saura na yamma suka iso wajen inda masu gadin harsun riga da sun saba in javeed yazo akan dan katse zirga zirgan masu shige da fice
dan shikadansa yake takawa da kafafunsa  har ya isa inda kabarin mamansa yake while all his security men remain outside by the car.

a fanninsu nur firdaus
kuwa dukansu sunsha wanka sunyi kyau all in black abayas yau itace kawai batayi kwalliya ba tabar fuskarta soo natural and charming baka ganin komi sai baqin kajol data shafawa idonta yay baki da kuma chapette din ta goga ma lips dinta wanda baiya nunawa sosai shima.

bfr 12.30pm na rana suka fito daga hostel aka kawosu msallacin cikin gari bayan an idar da sallah aka fara zagawa dasu garin suna mika gaisuwa wa excos kowa yana saka musu albarka dan wani babban international islamic organisation ne a kadunan yake sponsoring din competion din tare da few secret indivisuals kamar top families irinsu mufasa's, king sujamal of hadejiya and safeey Allah foundation a abuja da dai sauran great great generational wealthy billionaire families wanda suka fi bada himma akan dukkan wata hidima na addinin musulunci.

gasar ya zama yana da muhmmci saboda ana kashe masa kudi sosai wajen shiryashi snn ana kuma bada kyautuka ma yaran da suka halarta masu dumbin daraja da ma'ana.

tunda suka bar masallaci yau gabaki dayansu basu huta ba gaishe gaishe da ziyara kawai suke kaiwa daga nan anguwan zuwa nan anguwan, wajen manyan xcos ana saka musu albarka
wasu suna kara musu karfin gwiwa akan abunda ya kawosu.

wajajen karfe 4:30 suka kamo hanya zasu bi hanyar da zai sadasu gida ta karshe
saidai sabida tension din insecurity da ake fama dashi kasa kasa agarin yasaka baba driver yayita zagaye dasu har yabiyo dasu tahanyar makabarta sabida samun cikakken tsaro.

lkcin kusan kowa ya gaji amma surutu kawai daliban suke anata hira a mota can basu hankara ba motar tay wani kara inda baba driver yay saurin jan burki suka sauka akan titin dake daf kusa da babban makabarta aka paker su..

sama sama nur firdaus ta bude lumsashun idanunta dan ita kadaice ta bige da bacci bayan ta toshe kunnenta da karatun qur'ani data kejinshi da earpiece dinta.

..motar yana jan burki tabude ido ayayinda taji jadidah ta dafa kafadunta tana cewa
"ki fito kisha iska ko abarki aciki tayan motar mu yay faci.

'ahankli nur tace subhanallah garin yaya...?? duk suka mike tsaye da yar jakar hannunsu aysha tana cewa toh Allah yasa dai yana da extra tire dan wallh nagaji ni yunwa nakeji..agajiye laylah tace Ameen ta riko hannun nur, har suka sauko kasa suka tsaya atare, laylahce tafara kallon kofar gate din grave yard din dan basu da wani nisa da wajen tace laaaaaa big sis kuga yau gamu ga wani babban makabarta...cikin katseta da wasa jadida tace "toh sai akayi yaya? badama kuga makabarta sai kun nunawa nur..

ikon Allah."ohh toh me hadin nur da grave yard ni ya su?? aysha ta tambya cikin tuntsirewa da dariya...

nur firdaus ta danyi murmushi tace kibari kawai aysha kinsan ko wani jummua a abuja nasaba nakan kai sadaqa maqabarta shiyasa in sukaga makarbata ako ina sai su fara tsokanata..

Dariya sukayi atare ayshan tace Lallai nur firdaus sai kace wata tsohuwa? kakata ce fa me aikata irin wann dabiar har wani burga take ma mutane wai taje makabarta kai sadaqa,nikuwa nace  mata Allah sa wata taci karo da fatalwa su sakata gudu zata gane.. jadida da layla suna dariya, nur tace toh ai harkan samun lada babu wani tsufa ko yaranta..kaiwa sadaqa maqabarta  yana da amfani bayan hakama ai da shi ake toshe wasu abubuwan ake kuma inganta wajen da yan uwanmu musulmai suke kamar kabarukan da suke fadawa ko rushewa ko wata matsala na security kunsan fa akwai grave robbers, ga natural disasters etc indai zaku bayar kawai kuzo muje tun yanxu mu bayar kuma kudan samu lada tun kafin baba driver ya gama gyara mana mota, dan naji ana cewa wai saima an kira mechanic agari....

tana gama rufe baki laylah tace nide bazan je ba banyi niyya ba

aysha tace kinga jadida kuzo muje mudan gangara gidan antyna atacan musha ruwa kafin hajiyan sadaqa ta dawo dan ban isa inje inga abunda yafibkarfina inzo ina mafarki da dare ba

nan jadida ta ciro kudi a jakarta ta mikawa nur kawata kisaka min sadaqar kinsan nidai da zanbiki muje amma banason na jawo aljanuna su tashi kinsan da kyar aka magance min

nur firdaus tana dan murmushi ta amshi kudin ta saka ajakarta sann tace mata bakomi, ta kalli layla da aysha tace ku kuma kuyi hankali kar baba driver yazo yagane baku nan ya kai sunanku gaba ai kunsan masfr malam bello wallh baya wasa.

aysha ta jawo hannun laylah tace bakomi in sha Allah koda ma bai ganmu ba ai nasan hanyar da zamubi mu koma hostel batare da ansani ba...

daga nan sukayi sallama su ukun suka sace jiki suka tare abun hawa sukaje gidan antynsu aysha batare da kowa ya lura ba..

nur firdaus kuwa kai tsaye taje ta samu Ameer dinsu, dake suna dan shiri itace amirah, tajashi gefe tace masa zataje cikin makabarta yanxu zata dawo yace mata bakomi, daga nan tay wucewarta gaban gate din morque din tana lura da yadda tsayuwar securityn javeed mufasah ya hana c'mon mutane motsawa ata wajen duk da haka bai hanata karasowa ba.

ahankli take tafiya tana kallon hadaddun convoy na motocinsa guda biyar masu daukar ido dan inba a film ba bakasafai ne zakaga irinsu a fili ba

wajen ya dau shiru tana lellekawa koda zataga masu gadin wajen amma bata gansu ba sai body gurds din javeeds wanda kowa yake jin tsoron karasowa kusa dasu dan karfafa ne gawasu muguyen riffles amd sniper guns a hannunsu ready to shot onsite.

kafafuwanta harna harhadewa tadan dawo da baya ta gefe can can ta hango wani mutum yana zaune ya rafka tagumi

cikin nitsuwa ta karashe wajen sai kuma taga tarin mabarata ne sunkai su ashirin mata da maza da alama dik jira suke wani ya fito daga grave yard din ya basu sadaqa.

nur ta karaso cikin nitsuwa ta samu wata yar jagora data riko ta mamanta sanda tace  "sannunki yarinya ko kinga masu gadin makbartan nan???

yarinyar ta kalleta snn tace ayyo sunje tacan suna tattaunawa yanxu zasu zo..

tun kan nur ta budi baki daga gefe taji wani kuturu yana mita
"tirr tirr wai inda a taimake ka sai an cuceka ni wallh da zanga wann mufasan da sainagaya masa cewa duk ranar dayazo ya bada sadaqa abamu toh rabawa mukeyi da wayancn matsiyatan
wanda basa da tausayi.

wata mata tace kai talle da Allah kayi mana shiru da muka samu ana kiranmu ma
inda basu kiranmu a ina zamuna sanin me kudin yazo shida baiya zuwa nan sai an shafe lkci me tsawo.

makahuwar tace toh kuyi ahankli de kar suji mu dan kunsan koyaya ne ma ai muna samun me tsoka ni kudin makarantar ya ta nake nema kar ku jawomin salalar tsiya

kamar zombie haka nur ta tsaya tana jinsu suna musayar yawo tsakaninsu they all look desparate and hopefull.

Allah de yajikan iyayen mufasa yasaka kuma yafito lafya dan yauko dare zaiyi acikin makarbtan nan muna nn muna jiran fitowarsa.

nur ta rasa gane kansu ta kalli yarinyar tace ki nunamin ta inda masu aikin suke kinji ina sauri ne..

cikin gyada kai yarinyar ta nuna mata wani siriryar hanyar dayabi bangon makabartan tace kibi nan akwai wata yar karamar kofa da ake shiga makarbatan ta baya masu aikin duk suna wajen suna tattaunawa akan yadda zasu cucemu.

cikin kyabe baki nur tace toh nagode, ta juya kamar zata wuce sai kuma ta dawo ta babbasu sadaqar naira dari biyar biyar
makahuwar da tace kudin makarntar yarta take nema sai ta dunkula mata dubu goma a hannunta ta wuce cikin sauri..

Allah ya miki albarka
Allah ya hadaki da sa'a
Allah ya biyaki
Allah ya sadaki da rabo

babu kalar adduar da basu mata ba dan hartay nisa tana iya jiwosu daga can.

cikin sauri take tafiya da tunanin kofar na nan kusa ne sai taga kuma tanata tafiya har yanxu bata iso ga kofar ba, gabaki daya sai taji hanklinta ya fara tashi duba da bata da wani lokcin jimawa amma dake babban katanga ne ya zagaye wajen gabaki yasata fahimce tsarin wajen dan kuwa makabarta babbane sosai.

ta baya baya ta dinga bi cikin sauri hartana haki da kyar taci karo da kofar nan ma tayi tsayuwar minti biyar bataga kowa ba, nan ta bude kofar ahanklo shiga ciki gabanta na wani irin bugawa dan bata taba shiga cikin makabarta ba sede ta tsaya a gate ta bada da sadaqa ta wuce abinta.

tunda ta shiga cikin makarbartan taji tsikar jikinta yana wani irin tashi, gashi sai kwana kwana takeyi tama kasa gane ina ta dosa, ahnkli take tafiya kirjinta na bugawa da mugun karfi, har ta danyi nisa aciki kafin nan ta kalli wani ma'aikaci yana tahowa a fusace da murtukkaken fuska cikin sauri ta iske shi  yanayin yadda tamasa sallama da nitsuwa yasashi ya dan sassauto atake yace "ke yarinya meya kawoki nan kiyi mar maza ki fice anan kar akamaki a harbeki

cikin katsesa da sauri tace "baba na kawo sadaqa ne akace min kunata nn, nan ta ciro sabbin kudi daga jakarta ta mika masa da yanayin tsoro tsoro atattare da ita yace aiho, Allah sarki Zaa saka miki asusun sadaqa Allah ya amsa

ahnkli tace Ameen

yace toh maza kibi nan ki fita da sauri akwai baqin security kar akamaki..

tace toh, tare da duban agogonta taga wai har 5:30 da wani irin speeed ta juya tabi hanyar daya nuna mata tafara tafiya har ta kai bayan wani lobby da dan tankan ruwa awajen hanya sun kaso kashi biyu agabanta sai kuma ta rasa wanne zatabi

kirjinta na bugawa cikin rasa nayi ta karaso cikin bangon dake kusa da hanyar lobbyn ta tsuguna ta kunna famfon dake jikin tanka da niyyar wanke fuskanta da ruwan sanyi wai kodama nitsuwarta zai dawo jikinta dan duk sanda taga kabaruka sai tafara jin rauni da kuma zafin mutuwar baban ta yana tsttsafo mata kamar ruwan wuta.

*******
daga cikin cikin makabartan kuwa
Kuka yake sosai gurfane a gaban wani kabari wanda yanayin kukan nasa kadai zai iya tabbatar maka cewa haqiqa wannan mutumin yayi babban rashi, musamman ma yanda idanuwansa suka kumbura sukayi wani irin jajur ta yanda duk wanda ya kallesa bisa kallo daya to dole ne sai nashi idanun shima sun ciko da qwallah tsabar tausayi.

A nan gurfanen da yake yake ta tunawa da ranar da abun ya faru yana kuma jin tsananin nadamar faruwar hakan, jikinshi yayi matuqar yin laqwas bai wani iya daurewa ba yabi ya rungume kanshi sosai ackin wata kasalallen shauki da rauni mai tafe da ciwo mai azabtarwa, babu abunda yake zubarwa  face hawayensa masu saukowa da turirin numfashnsa mai zafi da ciwon rashinta daya jima yana damunsa, da kyar ya soma iya bude idonsa yanamai rarrashin zcyrsa da kalamai masu taushi da sanyi duk da kukansa yafi yawa awajen amma yafi awa daya da rabi yana mata addua.

rashin mahaifiyarsan wani irin ciwo ne da bazai taba warkewa a zcyarsa, ahnkli ya tashi daga wajen yabi wata karamar hanya inda akwai lobby ya jingina bayansa da bangon lobbyn ya lumshe idanunsa yana wani irin girmamman nishi nishi me cike da kunan rai da radadi,

zafin wutar dake ci cikin xuciyarsa yasaka labban bakinsa yin rawa rawa yakasa iya daurewa hannunsa ya zura cikin gefen tsadadden tux dinsa yazaro wata abu kamar key din mota kirar lamborghini wanda in kasheka za'ayi bazaka san ligther bane face sai da ya danna tsakiyar abun wata tsiririyar blue flame ta kunno,

daga cikin aljihunsa ya zaro cigarete guda daya ya danna akai snn ya jefa tabar a bakinsa tareda wani irin lumshe idanunsa inda zaka gane cewa bai saba shan taba ba sai yanacikin wani mayuwacin yanayi

wata irin zukar hayakin tabar yay da uban yawa ya fetsata sama yanamai dada manna bayansa ajikin bango,tulin hayakin daya zuka na fita masa hanci da baki a lokaci guda sai yafara jin nauyin dake kan kirjinsan na raguwa sosai kamr yanabin hayakin taban ne yana washewa.

Nur firdaus data rufe idonta gam da suke cike taf da hawayen fargaba mai nunnuke da tsananin mararin mahaifinta tafara shako warin tabar tamkar wanda a fuskarta ake busawa.

idanuwanta dake zubda hawaye na lumshe, bata ko budesu ba sabida wani iri da ta dingaji dan bakaramin tsanar warin taba tayi ba, ta jima da karantawa a wani littafi datake bi a library angaya musu cewa warin taba yafi illa wame shaka akan wanda yake zukarsa kai tsaye, wanda shiyasa wayanda yake tarayya dame shan taba, ko suke zama a kusa dashi kullum ders great posbbility kai da kake shakar ka riga me busawar mutuwa daga effect dinsa..

warin ya isheta sabida bata yi tsammanin me busa wann tabar yay
nesa da ita ba,fararen hannunta ta dora akan fuskarta tadan share hawayenta ahankli cikin sanyin jiki tay kkrin bude lumsashun idanunta tun bata gama budewa taga wani irin hayaki tamkar na silencer mota yana fitowa ta baya daf da ita, a firgit tajanye daga jikin bangon jin kirjinta ya wani irin bugawa da karfin tsiya kai tsaye kwakwalta ya kaiga tunanin ko gobara ne yake shirin tashi ata wajen dan da akwai ciyawa babu lefi..

gabanta na bugu ta taho da matsanancin sauri zatay wajen da tunanin kar wani dan iskane yasha taba ya yar akan ciyawa iska ya dauka, da wani irin sauri sauri ta harzuko kafafuwanta harna harhardewa, bai dauketa five secnds ba ta dafa bangon da wani irin faduwan gaba ta dan leko, duk sanda javeed yake shan taba a boye a hankare yake face yau dayaji kamar baqin cikin dake cinsa aransa yake busawa waje ba hayaki, nur fidaus na juyowa ta wajen ta hangosa, cikin tsayuwar cak wanda tafi ta minti biyar bata iya motsi ba dan ko iya dauke idanunta akansa na scnds daya bata iyayi ba.

idon javeed a lumshe amma wani irin bugu kirjinsa yaji takara kamar zcyarsa zata ballo waje da mugun karfi abun da bai taba ji arayuwrsa ba kenan..

gabobin jikinsu kusan atare yake sarewa tawainiyar bakon yanayi me rudarwa yanamai ziyartan gangan jikinsu da kwakwalwaru cikin salo na sanyin shauki datazo musu iri daya kuma a lkci daya.

busar tabar kawai yake like typical Mafia gangstar, kai zaka dauka yana da shegen jiji dakai da rudeness, dan tsam yaki ya bude idonsa,and with each scnd idon nur firdaus yay spending akansa numfashinta takeji yana sarkafewa dan bata taba ganin irin cikakkun mazan nan kyawawan gaske da ake gani a fictional movies ba saiyanxu

sai duk tarasa menene ya rudata game dashi dan kuwa fallasashen kyaun surarsa da bata taba ganin irinsa bane, koko wnn busar taban mafia boss din dayake with all the strong emotions swaying in his face and muscular body.

cikin tattaro makanta nitsuwa ta dauke idanunta akansa ta saukesu kasa lkcin kirjinta kamar zai fashe, aranta taji wata murya nacewa tunda ba gobara bane kawai ki juya ki tafi tun kan wnn mutumin ya bude idonsa. aikuwa kmr an tunkudata ta wani irin juyawa cikin sauri sauri zatabar wajen abazata taji inuwar mutum abayanta kamar an jefosa, da tsananin tsorata ta rike kirjinta tana shirin sankamewa da gudu
taji dirar"excuse me?!!!
kiris ya rage ta saki fitsari ajiki dan strong husky voice dinsan da ya dakatar da ita bata tabajin nau'insa ba karfin muryan yasa taji jikinta ya dau rawa rawa dan ba a cikin hayyacinta ba ta juyo saikuwa karaf suka hade idanunsu waje guda..atake javeed ya rike numfashinsa kamar wanda yaga fatalawa agabansa

nur firdaus kuwa tuni tay sumewar tsaye dan wani abu kamar sihiri ne yake fixgarsu ayayin da suka gama karewa halittar junansu kallon tsaf tsaf acikin scnds guda..

kwayar idanunta is as deep as an arabian coffee amma nashi is deep grey yana da wani iri hazo hazo aciki kamar hayaki ne yake tashi aciki.

ruwan idanunsa cikin nata bai cire ba, da wani irin karfi yazuko hayakin tabar saida ya kusa kai ta karshe ba'a cikin hayyacinsa ba yawani fetsa mata hayakin akan fuskarta dan bai taba ganin wata nitsyr halittar data dakatar masa da bugun zuciyarsa kai tsaye ba saiyanxu,

jikin nur na rawa tari me nunnuke da tsorata ya shaketa
saikuma taji mugun haushin kanta data tsaya gaban wann dan iskan, kusan ahatsale tay yunkuri zata juya

idanun javeed din na kanta da wani irin kallo probably he havent gotten enuf of her arabian coffe eyes,tana juyi taji wani abu me mugun laushi da taushi an kamo hannunta dashi batasan ta ina wata tsorataccen kuka ya ballo mata ba dan ko adnan shehuri datake mutuwar so bai taba rike mata hannu ba

muryansa yakuma razanata with a stiff comanding voice yace
"keee, me kike anan?? "are you lost?????????amugun tsorace ta kwace hannunta da masifa muryanta na rawa sosai tace mishi "let go off me, toh toh ina ruwanka, and do not touch me okay??

dan yatsar data nuna shi dashi yana rawa sosai yawani irin kalla fuskarsa a dore jinbe saketanba ta daga ido takalle idonsa da mugun haushinsa a idonta, atake ya dan lumshe ido ya bude cikin ransa yace mmm ""ohh, she is turning into a volcano? dan sauran hayakin tabar dake bakinsa yawatsa mata a fuska dan ya dada bata haushi

aikuwa wani irin fushi taji ya kara gumeta tafarajin dama bata zago ba sai hawaye takeyi tana kkrin kwace hannunta bata san sanda ya saketa ba saida taji wajen daya riken ya kuma daukan dumi, tana lura da hakan tadaga kai a fusace tun kan wani hayakin ya fito a bakinsa cikin tsaurin ido da karfin hali ta daddage ta talla masa mari for holding her hands, snn ta juya aguje cikin tsoraccen kuka tana cewa "Ass wipe"...kawai.

tsananin mamaki ya rufesa yabi bayanta da ido ganinta yay tana kan falfalawa da gudu babu shiri tagane hanyar sai gata tadoshi kofa a guje.

murmushin gefen baki me sanyi ya kwace masa abazata sai kuma yaji abun yabashi takaici da dariya a lokaci guda.

ahnkli ya sauke hannunsa daya dafe akan kuncinsa with double smirks cikin ransa he cudnt really belive dat a child just slapped him on his face and called him an ass wipe. COMENT PLS #SURAYYAHMS
SHARE PPL HELP ME AND SHARE THE NOVEL TO YOU GROUPS....08060712446.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top