EPS12

*"NUR FIRDAUS...12*
_Arewabooks@surayyahms_

atake wani kakkarfan murya daga cikin zuciyarta yace mata "uhm uhm haseena kada ki bari son y'ay'anki ya rufe miki ido, Bazaki tabayin  kuskure ba, Nur is 17, akwai fallin balaga nd ur husband is hot, toh wata y'a mace ce ne ma a duniya bazata ji sha'awar cikakken namiji kamarsa ba??

tana gama raya hakan aranta taja wata nannauyar ajiyar zuciya mai sauti amugun gajiye ta sauke wata kasalallen tsaki me kara.

after a while mrs Haseena tana kan zaune a kan kujerar falon batama lura da inda layla tay ba, tagumi tay tana jin kwakwalwarta na luguden tambayoyi. zuciyarta ta yi nauyi tana jin yadda nauyin siyasa da matsalolin iyali suka fara kkrin shan kanta.

Ta yi wani dogon numfashi, tana kokarin daidaita tunaninta, sai ga Layla ta fito daga kitchen cikin sanyin jiki nan Ta taho ta tsaya kusa da mahaifiyartan tanata kallonta da idanuwanta masu nuna damuwa da tausayi.

adan firgit mrs haseena ta daga ido ta kalleta duk zaka dauka gaskiyar lamarin laylah tazo fada amma inaa wani abu daban ne aranta

cikin sanyin murya Laylan tace mummy can i talk to you..

agajiye mrs haseena tace autata menene?? ko kema zaki fara cika ni da mita ne kamar yar uwarki nur firdaus.

cikin sauri layla tace A'a, babu komi Wallahi na damu sosai da halin da kike ciki ne. Ba zan taba bari wani abu ya lalata miki siyasar ki ba. mummy Ki kwantar da hankalinki, zan kasance tare da ke a koyaushe. i promise.

mrs Haseena tawani kalle layla cikin mamaki tana jin wani irin dadin abin da Laylan kecewa duk dama dai har yanzu zuciyarta tana shake da damuwa.

tana murmushi tace ohh my Layla dats why ure my favourite, ki duba halin da muke ciki amma yayarki Nur Firdaus tana neman ta jefamu cikin wani abin kunya. Na rasa me yasa take min haka."

Layla ta zauna kusa da mahaifiyarta, ta kama hannunta cikin nuna kulawa da rage murya kasa kasa snn tace

"mummy ki daina damuwa da yaa Nuri Wani lokacin tana yin abubuwan da ba a fahimtarsu,amma ke kadaice mafi muhimmanci a gare mu, Wallahi, ba zan taba yi miki abin da zai bata miki rai ba. mummy Ina son ki sosai."

Haseena ta ji wani irin dadi a zuciyarta yayin da ta kalli karamar 'yar tata da ke nuna kulawa da soyayya gare ta. Ta taba hannun Layla a hankali, tana jin cewa wata kila itace kawai daga cikin yaranta za ta iya dogara da ita nan gaba.

"Na gode, Layla ta. Amma kin san ban da lokacin da zan bari wannan matsalar tana ci gaba da tabarbarewa kawai xan dauki mataki Ya kamata kowa ya san inda ya tsaya.

Layla ta gyada mata kai cikin nuna ta fahimce ta, tana murmushi cikin wata irin halin karya da ita kadai ta san dalilinsa.

"Kada ki damu, mummy Ni zan iya kasance miki kunne da ido a nan don na tallafa miki. Ba zan taba bari wani abu ya rushe mutuncin ki ba."

dede nan mrs haseena ta rugumeta sosai tana cewa Allah ya miki albarka autata

lafewa a kirjinta sosai layla tay cikin zuciyar tanajin dadin yadda ta samu damar shigewa cikin hankalin mahaifiyarta. Duk da cewa tasan ita ce ta jawo duk wannan rikicin, sede ayanxu da ta san cewa zargi zaici gaba ne da kasancewa a kan Nur Firdaus muddin ba ta tona asirin kanta ba. Wannan shi ne shirin ta, ta kasance "mai biyayya" da gaskiya ga mahaifiyarta yayin da ta bar Nur Firdaus ta fuskanci dukkan bacin ran mrs Haseena.

ahankli mrs haseena ta tallafo fuskarta tana murmushi tace "Na gode, Layla. Kin san kece karamar 'yata mai hankali. Ina fatar Nur Firdaus za ta iya koyi daga gare ki."

Layla ta sunkuyar da kai cikin murmushi, tana jin gamsuwa da yadda tasamu nasarar rufe gaskiyar da ke tsakaninta da Sadaat cikin wata salo, kuma ta bar mahaifiyarta cikin farin ciki da ita.

sede zuciyarta ta san cewa wannan rikici ba zai kare nan kusa ba.

karar wayar mrs haseenan ce ya katsesu sai kawai ta mike tsaye ta haura can sama izuwa dakin su domin ta bata daman amsawa.

ahankli take takawa har takawo kofar dakin nasu tay tsayuwar cak, inda tadau mintina tana kimtsa kalaman da zata fuskance nur firdaus dasu..

after like 3 mins ta turo kofar dakinsun ahankli ta shigo tana ƙoƙarin ɓayyana fuskr damuwa..

nan Ta tarar da Nur Firdaus zaune a gefen gadonsu idanunta sun cika da makallalun ruwan hawayen da basu sauko kasa ba snn fuskarta tana dauke da alamun bakin ciki da haushi.

jiki a sanyaye Layla ta taho kusa da ita cikin nutsuwa, duk sonta data boye gaskiya still wani bangaren zuciyarta natattare da nauyi da kuma jin zafi tareda sanin cewa ba takulla gaskiya game da abin da ya faru da yar uwarta ba. sede hassada mugun ciwo, a gaban Nur Firdaus, dole ne ta yi yar wasa da nuna hali na kulawa.

da murya mai laushi layla ta zauna snn ta fara kirkiran hawaye
kamar dagaske tace "yaa Nuri na san kin ji zafin kalaman mumy akanki, amma ina roƙonki kiyafe min da ban fada mata gaskiya a lokacin ba. wallh tsoro nakeji, bazan iya daukar irin zargin datake miki ba, ya nur Don Allah ki yafe min..maganan take tazauna kusa da Nur Firdaus,tana sanya hannu akan hannunta cikin nuna kulawa. Amma a zuciyarta, tana jin ba ta wani damu da haka ba. takuma san Bai kamata tayi hakan ba. Ba'a kan gaskiya take magana ba amma who cares?? itade tana son tasamu damar ɓoyewa da kariya ga sirrinta da kuma tabbatar da matsayin ta a idanun mahaifiyarta.

Nur Firdaus tadago fuskarta ahnkli da yay wani irin haske da kyau tana magana cikin nutsuwa duk dama tana cikin damuwa "haba Layla, na fahimci komi karki damu..Ina tare da ke har abada yar uwata, "kisani laylah, Duk lokacin da wani abu zai faru ba zan taɓa barinki aciki ba. Zan ƙaunace ki, zan baki kariya da dukkan rayuwata, even idan hakan yana nufin cewa zan rasa komai.

Kalaman Nur Firdaus kai tsaye suka ratsa zuciyar Layla fiye da yadda tay zato.

fuskarta wani iri Ta kalli fuskar 'yar uwarta  tana jin wani motsin zuciya me nauyi, wataƙila wani yanayi na gaskiya ya ratsata amma cikin ɗan lokaci shaukinsa yaɓace, saboda son zucya da sha'awa da ƙinyarda da inda Allah ya ajeta.

ajiyan zuciya me nauyi tasauke jin nur firdaus ta rungumeta, Layla ta ji kamar antsinke wasu ƙananan raɗaɗi acikin zuciyarta ta rasa yadda akayi tafara jin wann tsananin kishi da hassada ga yar uwarta sede kafin takaiga yin wani tunani mai zurfi game da wannan yanayi, wayar nur firdaus ce tahau kara, inda kusan atare suka kai idonsu kan wayar nan da nan sunan Adnan shehuri ya bayyana mrmushin bazata ya kufcewa nur firdaus, zuciyar layla kuwa take tafashe da wani irin zafi. Wannan ƙishi da sha'awar data ke ɗauke da ita aranta nan tamotsa cikin zuciyarta cikin sauri.

itakanta bata san ya akayi ta janye daga rungumar da nur firdaus tamata ba taja jikinta cikin dauke kai tana ƙoƙarin zama kamar bataga sunan  me kirar ba..

nur firdaus bata kula da hakan ba ta ɗauki kirar tanamai kirkiran murmushi. cikin wata iriyar sanyi da taushin murya tace salam alaikum habibi..

dagata daya  bangaren Adnan ya amsa sallamar tata da tausasshiyar
muryasan nan me shegen sanyi, bayan sungaisa kai tsaye yasaka muryan lallami yanamai cewa habibty Can i video call you ?haka kawai jikina yake bani kamar ure not fine...i really want to see you habibty..

layla data kasa kunne tana saurarar kirar kamar wacce aka tsikareta tamike tsaye tana ƙoƙarin ɓoye yadda zuciyarta ke bugawa dan ji take kamar akwai wani abu mai mugun rauni a fuskanta da bazata iya boyeshi ba, sadaf ta mike Ta fita daga dakin batace ma nur komi ba nur tabita da takaitaccen kallo batare da ta gane metake nufi ba..

koda tafice a dakin da har kamar zata wuce hanyar kitchen sai kuma taji Zuciyarta ta motsa ta kasa samun nitsuwa, komowa tay tamannu da kofar dakin nasu ta inda take iya leke da kuma sauraron kiran daga cikin dakin kai tsaye

ta bulin data saka ido ta hango Nur firdaus tana kkrin saka wata sky blue hijabi ajikinta daya killace mata ko inanta face yar kyakkwar fuskarta da bata shafa mai komi akai ba..

cikin zuciyar layla dake cike da kishi tace "zan yi magana da saurayina sai kuma in saka hijabi?? wann ai kauyanci ne, mtss narasa meyasa yaa Adnan ya nace sai yaa nuri she is not even classy, nd wild..nida na dace dashi sosai gashi inanan ina boye kaina.

tana cikin zancen zucin Ta ji muryar Adnan din yana fito wa daga cikin dakin kasa kasa yana magana cikin sanyi da kulawa yana tambayar Nur Firdaus ko tana cikin lafiya da kalamansa masu mugun taushi da ratsa zuciya da nuna ssnyr soyayya me balain shiga jiki.

nur tana amsa shi cike da kunya da kalamanta me sanyi saidai sam taki ta bari ya fahimce halin da take ciki kawai de tace masa tana missing dinsa ne sosai.

lallabarta yakeyi da dukkan imaninshi dan adnan ya mata wani irin so da ita kansa bata san yawansa ba.

habibty Ina so ki san cewa ina tare da ke akoyaushe, kuma Na damu sosai game da yadda abubuwa suke kasancewa, sede daga kin zama tawa in sha Allah bazaki sake baqin cikin rashina a kusa dake ko a rayuwarki ba. i gave you not only my heat my entire soul is all urs habibty.

nur tay murmushi 
kalaman soyayya masu zafi ke yawo acikin iskan dakin atsakaninsu

inda nan take Layla taji zuciyarta tana  bushewa dajin mugun haushin yadda yar uwarta Nur Firdaus ta riƙe hankalin Adnan sosai. 

Ta yi ƙoƙarin riƙe kanta dake juyawa amma inaa wani radaɗi tadingaji na kishi na caccakarta da ƙarfi. Cikin zafin zuciya ta juya cikin sauri ta bar wurin da sauri ta wuce kitchen tana ƙoƙarin ɓoye abin da zuciyarta ke haifarwa

akasa kan tiles ta zube a kitchen dafe da kirjinta tana jin kamar zata mutu aranta take cewa na shiga uku hala Ba zan taɓa samun wani abu daga gare shi ba muddin yaa nuri tana raye ni din tamkar wata fuska ce."

ahnkli ta jingina bayanta da bango tana jin radadin ƙiyayya da sha'awar Kwace duk wani abu da nur firdaus ta mallaka a zcyar Adnan shehuri, Duk da cewa ta haɗu da kalaman qaddara da jinkiri, da na nuna ƙaunarta ga yar uwarta Nur Firdaus, ta kuma san cewa babu abin da zata iya yi sai ci gaba da wasan kwaikwayo....

tajima a kitchen din har sai dataji alaman motsi snn ta mike ta wanke fuskarta ta rasa me zatay kawai sai tahau hada musu shayi, jim kadan nur firdaus ta fito duba ta, sukayi yar hira a kitchen din ayayin da suka sha shayin, babu abunda ke yawo a ran layla face yadda taga mood din nur firdaus ya sauya sosai, baqin cikin da suka qumtsa mata dazu duk ya gushe snn hanklinta ya dan kwanta.

yau din baccin kirki laylah bata iya samu ba tsabar ydda take imagining inama ace itace take soyayya da Adnan yake sakata irin wann farincikin
gashi kyakkwawa, young, ga kudi, ga familynsa sunyi suna a siyasa sosai. this is exctly how she want to end up. Adnan shehuri is her wildest fantasy amma kuma ba ita bace acikin rayuwarsa gabaki daya duk sai taji baqin ciki me tsanani ya gumeta sam ta kasa runtsawa..

wanda kusan hakane yake faruwa ata fannin mahaifyarsu mrs Haseena, wanda acikin daren itama babu abunda take yi sai juyi akan gadonta da tunanin abunda ya faru ayau dake duk hanklinta yana ga kan mijinta ne, sam bata kaunar abunda zai rabata da sadaat sabida bakaramin biya mata bukatarta yadda take so yakeyi ba...

she just cant bear to loose him, daren nan sam be mata dadi ba, hakanan ta dinga tura masa text a wayarsa tanajiran taga ya kira ko ya amsata amma inaaa har tay bacci be kulata ba..

bangarem sadaat din kuwa a club ya tare da abokansa suna tana taba yan shaye shaye da yan matan da zasu kwana dasu ko sau daya be tuna da wata haseena ba.

***** washe gari da safe.

gidan ya dauka da wani irin shiru, nur firdaus tun bayan sallan asubh ta fice tana can waje tanata bitar karatun qur'anin ta kamar dai yadda ta saba.

ko kadan bata da masaniya akan yadda yar uwatta layla da kuma mahaifyatta suka karace daren su da ita a zuciyarsu.

inda layla take ganin kamar itace barrier da raba ta da samjn babban mafarkinta na kasancewa tare da Adnan shehuri, mrs haseena kuwa ta kwana da haushin rashin mijinta sadaat wanda take alakanta sa da lefin nur firdaus ce.

yauma sassafe layla tay wanka ta taho dakin maman nasu da wani sabon salon makircin, sosai ta lura da cewa mrs haseena tana cikin damuwa game da fushin da sadaat yakeyi akansu, dan haka tadauki wann damar tadinga kwantar ma mrs haseena hankli tana mai wanke kanta da kuma shigar da tsanar nur firdaus aran mahaifiryarsun sosai cikin wata iriyar makirtaccen salo na yaranta.

bayan Layla tay nasarar kwantarwa mahaifiyarta hankali da kalamai masu dadi ta koma dakinsu tahau shiryawa hanklinta kwance.

mrs Haseena kuwa sosai ta ji tamkar ta samu sabon karfi don fuskantar sauran matsalolin ta nayau. nan ta mike tsaye da sauri bayanta kimtsa kanta da wasu uban sun manyan kaya tadauki jakarta me tsada, snn ta fice don dawowa bakin aiki kan shari'ar Ummi.

kusan a kofa suka ci karo da nur firdaus sanye da hijab ta riko qur'aninta ahannunta
wani irin takaitaccen kallo tamata sai kuma ta tuna mijinta marigayi haroun shima fa aikinsa kenan kullum cikin karatun qur'ani da sassafe, wani tsakine ya kufce mata taciki data tuna duk halin sa ne ajikin yarta nur firdaus.. and no wonder she is soo annoying..

cike da sanyin girmmawa nur firdaus ta gaisheta, kallon kirki bata mata ba ta amsata ciki ciki tayi wucewarta. nur din ma bata kula ba ta wuce ciki dan ta  shirya zuwa makarnta

yau zaay screening na zuwa gasa zasu karbi ID cards,competition customes dinsu, da sauransu, dan babban tarone da ake asalin gayyatan manya manyan mutane dake bada gudumawa wa addini bana kadan ba.

qamshin jikin haseena ya bule gabaki daya ilahirin tsakar gidan gata da son publicity tasan makwabtarsu da dan uban gulma dan haka har waje bakin gate ta fita da motarta tana amsa waya hankali kwance.

aikuwa hamshiyar magulmaciyar wato maman saeed tana hangota ta windown gidanta tay saurin dirkowa ta fito.

kafin mrs haseena ta gama amsa waya ta shiga mota, ta ji wata murya daga gefe, murya mai cike da tsokana da hassada, Tana daga ido taga Maman Saeed din ce, wacce takasance mai yawan barbada surutu da tsangwama ga mrs Haseena saboda kiyayya da hassada.

yi tay kamar ta fitone duba wani abu cikin tsokana da basarwa tace Haba Hajiya Haseena kin dawo gida shine babu magana,...

mrs haseena ta mata wani irin kallo kasar wuyarta tace.."uhum toh Sannu ramatu.

wani makakallen dariya maman saeed  tay yawwa sannu haseena daman ko ina son nagaya miki dan wallahi shirinki na jiya ya tabo inda yake mana kaikayi har munasa rai kema hala kiga girman abun a nan gidanki kya bar kwayawwan yan mata da katon saurayi agida sukadai?? toh amma dai Bari mu gani idan 'ya'yanki ma ba zasu kawowa duniya abin kunya ba..

Haseena ta tsaya cak, ta kalli Maman Saeed da murmushin takaici. dantasan cewa makwabtanta basa son ganin tana samun cigaba,kuma kullum suna amfani da duk wata dama don bata mata suna.

hankli kwance cikin jan aji tace "Maman Saeed kenan abun kunya ya wuce mace dake zama da namiji agidansa suna zaman dadiro bayan duk ansan saki uku ne a tsakaninku???

maman saaed ta hade rai sosai mrs haseenan ta fashe da wata muguwar dariya mai cin rai ahhhahaha
yanaha kin canza fuska ohh toh abar wann maganan, ke yanxu ramatu me kike nufi da wannan maganar taki ehhh? Ko dai ke ma kin fara shiga cikin wnn hirarce ta makiya da ba ta da ma'ana?"

cikin jin haushin abunda haseena ta goranta mata tace
in ma na shiga hirar maqiyarki Ai ba hirar banza ba ce, Hajiya haseena Na dai ga kamar kece kike fitowa a talabijin kina magana kan tarbiyyar yara musmmn ma yara mata. Amma inaa aimu sai mun ga abin nan da gaske awajenki, kuma Muna addu'ar 'ya'yanki su zama abin koyi, amma fa idan sun rushe ki, kar ki manta kema ki bayyana wa duniya komi kamar yadda kika bayyana maganar Ummi a idon kowa."

dede nan Haseena ta fusata tace Na san ke da sauran makwabtan nan nawa baku taba farin ciki da ganin na ci wata nasara ba. Kullum ku kuke nan zaune cikin hassada, matsiyata, yan dorin dosino a gwarimpa, jahilci ya kafe ku waje guda..kudai kuna jiran ganin na fadi kasa. Amma bari in fada miki, babu wanda zai iya rushe ni a duniyan sai ubangijin daya daukaka ni. Kuma idan kinada wani abu da za ki fada game da 'ya'yana, ki bari sai lokacin da abin ya faru, idan har zai faru kenan."

Maman Saeed ta kalli Haseena da wata irin murmushi mai cike da tsokana da tsananin haushin jin baqaqen kalaman data yafa mata.

"Ai gaskiya zata fito fili Haseena. Kuma fa sai mun ga yadda za ki kare kanki idan duniya tagane ke ma ba kida da cikakkiyar tarbiyyar da kike kokarin yada wa al'umma."

Haseena cikin zafin rai tace "Idan kika gama magana ramatu kike ko Mman Saeed, sai ki koma gida ki ci gaba da rayuwar ki ta dadiron ci. Ni baki kai nayi musayar yawu dake ba, kuma ba ki isa ki tsayar da tafiya ta ba. duk wanda yake bina da sharri dai Allah ya isa!"

Ta juya cikin fusata, ta shige mota tare da murda tayar cikin sauri tana barin wajen Maman Saeed tabi ta da kallo mai cike da cin fuska da haushi.

gidan dayan makwabcyarsu wanda tadan tsufa maman saeed ta wuce cikin huci da fushi dan taje ta barbada mata labarin komi..

dagata dayan bangaren kuwa Haseena tana tuki cikin hanzari zuciyarta cike da zafi da takaici.

"Wadannan mutane ba su da wani buri sai na ganin na fadi," ta fada a hankali tanajiin ranta na tafasa sosai.

seidei tariga taayi alkawari a zuciyarta cewa ba za ta bari su yi nasara akanta ba. Matsalolin cikin gida da waje duk ba zasu hana ta kai ga cikar burinta ba.

aikuwa nan da nan Ta sake mayar da hankali kan maganan shari'ar Ummi. tanamai  tabbatar makanta da cewa wannan yarinyar zatasamu adalci kodan maqiyanta su mutu Kuma idan suna tunanin zata rushe saboda 'ya'yanta cikin  karkda kai tace muje zuwa ba su san iya karfina ba....
SHARE AND COMENTS

FOLLOW ME AT SURAYYAHMS

08060712446

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top