eps bonus
BONUS PAGE FOR COMENTERS..
bayan sun kammala wayar nan hajy mamy ta karasa isowa cikin gidanta batare da ta nemi inda simran takeba tawuce sashenta tay wanka dama kuma batajin yunwa ko kadan kawai tahada tea dinta me shegen qamshi ta zauna a daki domin samun isasshen hutu.
fannin Nur Firdaus kuwa sosai tafara gajiya da irin cece kuce da kuma zafafan muhawarar da akatay akan yanayin karatun ta a hostels din mata musmmn na sauran makarantun da sukazo.
inda wasu daliban hassada ya sakasu suke ganin kamar aidan nur ta samu jaaa me tattare da kalmar "mutuwa" shiyasa nata ya fi daukar hankalin kowa awajen taron, wasu kuma sukace ai daga yanayin yadda tay karatunne cikin fidda maanan ayan tare da shauki da bada haqqi ga kowani haruffa.
kowadai na fadin raayinsa akanta amma babu tantanma yau mahassadarta na fili dana boye duk saida suka bayyana dan zancenta kawai akeyi ata ko ta ina
can da dare tazauna a gefen gadonta tana tunanin abunda ya farun saikuma tafara jin son ziyartar wani kawunta da ake kiransa Alhaji Abubakar Ciroma dake nan kaduna.
gani take duk dama mamansu ta hanasu muamala da yan uwan ubansu be kamata tazo kaduna har tay gasa ta tafi bataje ta duba elder brothern mahaifinsun ba, tun tana karama tasani cewa alhaj abbakar ciroma yafi kowa shakuwa da mahaifinta and is a very wealthy business man yana da mata biyu, amma yarsa guda daya ne tall ana cemata Razia Abubkr ciroma wanda aka fi sani da (Razia abu), yana zama ne a GRA barnawa and is not really far from them dan haka ta gudura aranta cewa gobe bayan angama karatu zataje ta dubasu.
har hajiya mammy ta gama shan hadadden shayinta bata cire ran cewa yauma javeed zai dawo ya kwana agidanta ba,ita kuma simran wuni tay agari tana famar yawace yawacen shopings da wajajen shan iska dana ciye ciye dan babu wani abu datake matukar darajawa arayuwarta kamar bacci, kashe kudi, da kuma hot coffe, sanin cewa javeed ba kulata zaiyi yadda takeso ba yasaka zaman shiru agidan yafara damun ta amma dake hajy zuby tace mata lallai tazauna anan din har sai javeed dakansa yabaro kadunan tare da ita kafin nan tay wani motsi.
wajajen karfe 6pm saura na daren ranar lahadin Javeed A. Mufasa yafito daga dakin wani meeting a kasar egypt dan tun da asuba daya wuce nan batare da sanin kowa ba baiyi wani waya da kowa ba sai kakarsa hjya mmy.
within few hrs prvt jirginsa ya dawo dashi cikin kaduna alokcin ana neman 10pm na dare suka sauka a tashar jirgin sama inda motocinsa dake jiransu suka wuce dashi dakin hutu
after while baijima awajen ba ya shirya yafito domin duba wani abokinsa mai suna Sultan Khaleefa da suka dau lokci basuga junansu ba.
Sultan mutum ne mai tsananin hatsari da zurfin ciki tareda ilimin dabara da Allah ya zuba mashi,yana daya daga cikin few mutanen da Javeed ya tsananin aminta dasu snn ya ke iya kwana yana tattauna wasu maganan dasu.
sultan khaleefa yana da underground club a kaduna sabida shidin tamkar jarabawa ne ga kusosin yan siyasa da kuma mugayen dake addaban kasa.
he works for the Central intelligence agency as a senior undercover, amma a fili kuma shidin kamar dan daba ne dake saida bindigogi da tsadaddun alburusai ma amintattun sojoji da mutane masu powerful personality kamar su BG javeed mufasa, Dr. nashwan wamako etc, dan haka babu wata sirri ko wani shige da fice dake yawo a nigeria da baisan dashi ba.
wajajen sha daya da rabi on d dot suka iso, Parking hadadden motarsa bodyguard dinshi yayi a parking lot din babban pub din
lkcin javeed yana zaune a owners coner baima san sun isoba sabida wayarshi dayake ta famar daddannawa.
Casual dressing yay Inda yafito a cikin wata tsadaddiya kuma shegiyar unbuttoned shirt na kamfanin Hermes fara kall kall da ita datamai kyau banawasaba,ya hadeta ne da dawani brown carmourflage trouser kafafunshi sanye da wani black boot na hermes din shima.
sabida sanyin dare yasa yataho da jacket duster coat sai wann hadadden kamshin turarensa na mufasa noir da yakeyi kai kaman ka lashe shi tsabagen qmshin dadin dake yawo ajikinsa duk inda ya ratsa.
budemai kofan motar da akayi yasaka ya dagokansa ahnkli ya kalli bodyguard din dake tsaye agabansa yanamai jiransa ya sauko. Karamin Ajiyan zuciya ya sauke baice komi ba ya sauko din
ahankali tareda zuba hanayenshi a aljihu, gaba yyi suna binshi abaya yana taku cikin nitsuwa da kamewa kamar Dan sarki
body qurds uku suka biyo bayanshi suka nufi cikin undergrnd pub din tare dashi, can ya juyo fuskarshi adan daure jin karan takalman su daf daf da shi, wani irin haushinsu yakeji yanda suke binshin kaman wani karamin yaro daga yay korafi sai ace ai aikinsu sukeyi na kareshi,but he already knew dat Babu mai Kare shi a duniyan nan sai Allah
but wani bin dole ne yakansa yaKe bada hadinkai domin akare rayuwarsan gudun Duk abunda ake tsoro din ya faru.
Ahankali cikin strong bold voice dinshi ya juyo yakalle gurds dinsa dan baison yamusu tsawa ya janyo attention din mutane yace musu wait for me outside give me a break...
Kaiwa nan yawuce yay ciki cikin daure fuskan sukuma babu yanda suka iya suka koma kofa suka tsaya suna masu lura da komi dake shige da fice
javeed yana karasawa aka Budemai kofar shiga VIP securityn wurin ya matsa masa yashiga har cikin club falour din dayake tashi da hayaniyar maza wasu na harkan business, wasu na buga bar games, dan dauke kansa yayi yana dan cije lips dinshi har yahaukan stairs din yay sama can ya doshi wani waje da aka rubuta Danger da jan fenti asamansa.
security dake wajen suna ganin shi suka matsamai yashige ciki yana shiga yaga wasu kattin mazaje su hudu a zaune dukansu Americans suna kan aikin jera bindigogi
ak47s,sniper riffles, x22, granade lunchers, difrnt kind of guns kala kala aka shimfide akan table agabansu da manya manyan bottle din hernessy strong Martini da wine glasses a hannun su.
suna ganin shi suka dan dakata da aikin su har ya karaso..
nan sultan ya mike tsaye yanamai mika masa hannu yana murmushi yace my one nd only friend we all glad ure here But you are late.
zama javeed yayi kusada dashi suka gaisa dan shikadai ne ma yay kama da yana cikin hayyacinsa sosai ahankli yace sultan i cant stay long sabida nagaji, u wanna grab a drink??...
sultan yace sure snn yakalle sauran mutanensan yace musu excuse me guys kucigaba da aiki ina zuwa, nan suka bar wajen suka koma gefe tareda javeed suka fara magana ta sirri kafin nan suka dawo na abokanta, nan inda suka zauna suna shan wata strong shayi me cike ganyen itatuwan daga china masu kara lafiya ga halittar maza. nan sultan ya shiga kawo masa tattaunawa akan aure da kuma mata sabida shima baijima da yin auren ba, yace javeed najima ina aiki akan wann fannin for the likes of u amma kai baka aminta dani ba, and you knw Not just any type of girl can come in to my list. kasani ko?..
ahkli javeed ya kurbi shayinsa ya hadiye tareda sauke double smirks yace "toh shikenan, i need one,.
da mamaki sultan yace what? youu joking??
javeed ya masa wani kallo adan tsime yace no..hajiya tace tana son wai nayi auren nan kafin karshen shekara.
sultan dake kallon yanayinsa yace wow finally..the great mrs mufasa is abt to come
into light.
cikin haɗa yatsu javeed yaja tsaki yace u going to get me wat i want or not, sultan just paper marriage ne,but not with a gold digging slut dat will end up dead if she dares me.
sultan yay murmushi
"i wundnt even dare joke with this one., duk dama na so maka auren soyayya javeed
you're 42 but ure really hot men.. u need a cunny little girl dat will handle you manly..
karo na farko da javeed ya daga girarsa sama with a friendly smirks tare da yin karamin murmushi yace" ohhh, ai zanyi na soyayyar a lkcin danakeso. sede Wani lokacin bana tunanin da akwai wata ya mace da zata iya shawo kaina wai dan na so ta kamar yadda kake tunani.
Sultan ya yi dariya mai sauti yace Kayi shiru kajira mana ka gani. amma ina tabbatar maka akwai yarinyar, kuma Bazaka san lokacin da zuciyarka zata kamu da soyayyarta ba. just let the ryt girl come your way zaka ce na gaya maka abokina.
cikin basar da hirar Javeed ya share zancen duk dama kalaman Sultan sun tsaya masa a zuciyarsa kuma yasan hala hakan zai iya faruwa tunda har ya kalle wata yar halittar yarinya karama data sakashi tunani batare da ya shiryawaa hakan ba.
guy lets focus on fullfilling hjys wish.
sultan yana murmushi yace toh babu wata matsala Ka bar komai a hannuna i have one perfect girl in mind a kaduna nan take zan hada maka file inta ka duba..
javeed baice komi ba ya ciro wani Memory card a aljihunsa ya mikawa sultan, yace look into dis and tell me wat you got..i will be in Abuja on thursday muhadu acan.
sultan ya mike tsaye yace okay i will come with the report on "this" and "that"..
...javeed ya dan kallesa yace, i trust u with "this", but on "that" karde kaje ka kawomin file din wata katuwar bakauyiya me rawan kai.
wani irin dariya ne ya kufce ma sultan dan baiyi tsammanin cewa har javeed ya fahimce "that" din dayace din a dunkule ba.
cikim kyabe baki yace alryt we will see
daga nan sukayi yar sallama around 12:40 am na dare javeed ya fito daga club din ya same securitynsa awaje suna jiransa within few minutes ya shiga mota suka dawo dashi gidan hjy mammy.
sun iso lkcin sosai gidan yadau shiru da alaman kowa yay bacci, kai tsaye ya wuce dakinta ya tura kofar ahankli ya shiga yasameta a ringine akan fankacecen gadonta me taushi tarike wayarta tsamm a hannunta ta manne akirji hawayenta da sukata zubowa akan kumatunta haryanxu basu bushe ba tana famar sharar bacci
cikin nitsuwa ya karaso cikin dakin yanamai kare ma yanayinta kallo, kai tsaye ya gane kallo takeyi awayar sai bacci ya dauketa ahaka, ya rasa me take kallo haka da zai sakata hawaye har tay bacci rungume da wayanta a kirji..
lallausar hannunsa ya saka yazare wayar very gently dan kar da ya tasheta ya katse mata baccinta, yana cirowa ahankli ya mike tsaye saidai dake akwai security a jikin wayar yasaka ya fito da nashi hadadem wayar daga cikin aljihunsa ya daddana wata shegiyar nano technology da ake cemata share screen
nan daman wata transparent scanner ta bayyana daga wayarsa ya haska screen din nata wayar dashi kafin kace wano abu har scannern ya kwaso masa duk wani abunda take kalla ixuwa kan nashi wayar kai tsaye batare da yabude wayartan ba.
ganin kamar zata fara motsi yasakashi aje mata wayar agefenta snn ya jamata bargo me shegen laushi ya rufeta ya rage iskar Ac yazauna agefenta ya mata addua ya shafa mata akai da fuska kafin ya kashe mata wuta ya kara dagaba..
yana kaiwa dakinsa na gidan ya zauna calmy abakin gadonsa da aka lailayata da off white silk bedshet me shegen kyau.
kai tsaye ya zaro wayarsa daga aljihu snn ya kunna share screen din yaga ashe ma video recoding ne take kalla, nan yaga wai annual qur'anic competition chapter dan karamin tsakine ya kufce masa da har zai katse wayar ya aje sai kuma yatuna irin labarin shirmen data dinga bashi dazu baiyi kasa a gwiwa ba ya sake kunnawa dan yaga menene haka a muryan yarinyar da har yasa taketa kuka.
yana kunne videon yaji kansa ya dan sara mashi, nan take kuma camera ya hasko kan nur firdaus data sha bakin niqabi, shide baiga fuskarta ba amma a kallo daya dayay mata saida ya lumshe idonsa sosai
jin tsikar jikinshi na tashi ahankli tamkr wanda yaga wata aljana.
nitsuwa yay akanta dan yana jin larabcin shima sosai dan haka ya najin duk wata abar da ake fada mata na qa'idar karatun, kafin nan ta fara rerowa wanda tunda yaji dirar sautin qira'ar dake fita a sassnyr muryanta, dodon kunnuwansa gabaki daya suka dena jin motsin komi, bai farga ba harsaida videon yay replaying kansa kamar sau biyar ana shidan ne ya dawo hayyacinsa ya katse, snn ya bude lumasashen idanunsa yakurawa screen din manyan idanunwasa masu cike da kwarjini dan ji yake zucyarsa tanawani irin harbawa can sama sama tana kuma daka tsalle ta ciki tamkar wanda yakeda wata spritual alaqa na musamn dame wann karatun..
a daren ranar duk sai yaji yakasa samun bacci dan ya rasa meke damunsa kwana biyun nan gabaki daya, tunani yake akan fuskar wacan yarinyar da kuma Muryar wannan yarinyar, they all better get along cos he is loosing his focus on both their aura's.
wani abu na musamn yadinga ji aransa wanda bazai iya fassarashi kai tsaye ba wanda akarshe dai duk ya tarkatasu ya ajesu waje daya ya tarasu a matsayin shirmen banza amma inaaa tunaninsu sam yaki ya rabu dashi duk yadda yayi karfin halin fixgewa.
juyi yadinga yi akan gadon shikadai har yakai wajajejen karfe biyu na dare Wannan muryar da yaji na me gasar Qur’ani yana ci gaba da kai kawo a cikin kansa, A karshe, ya mike daga gadon da misalin karfe biyu da rabi na dare, kai tsaye ya shiga wanka waikoda kansa zai sakeshi inya jikashi da ruwan sanyi.
Da ya fito ma still bai koma barcin ba, cikin daren javeed yaja tsaki yafi buhu goma kafin nan can ya sauka akan gadon yaje yabude wani katoton woody drawer yaɗauko wata babban allon zane ya jawo wata black arniyar expensive cryon akwalinta ya rike
yanemi waje a tsakiyar dakin ya dasa kujerarsa agaban allon zanen ya zauna yanajin zucyarsa na ingizashi taciki akan daya fito da fuskar abunda kemasa yawo akansa..
batare da yasan me zai zana ba, bai kuma san dalili ba ya dasa cryon din akan board din ba, ya fara zana fuskan yarinyar can daya ganota a makarbarta.
cikin nitsuwa ya hau zana fuskar nur firdaus zak zak ya bata wani kamilallen fasali na Fuska mai tsarki, Idanu masu cike da haske, da Lips dinta masu matukar daukar hankali yadda yay shaping dinsu zarr kamar shine asalin wanda ya tsarata.
yadau lokci yana perfecting din zanen saboda yanayine yana tunawa da faruwar komi,ahankli har saida ya kammala zanen snn yazauna akan chair din yanata kallonta, kiran sallar asuba ne ya katsesa.
mikewa yay ya shiga closet ya dauko wata farar rigarsa me dan tsayi yarufe kan zanen dashi kafin nan ya shiga bayi yay alwala yasaka kaya ajikinshi tsaf tsaf snn ya nufi masjid domin sallahn fajr kai tsaye.
Da misalin karfe biyar na asuba, Dr. Simran na sheka bacci a dakinta wayarta ya dinga kwalla kara misd call yakai 30 wanda duk nauyin baccinta sai data hakura takatse ta farka a mugun fusace kamar zatay kuka ta dauki wayar tana huci dan batako duba waye me kirar ba tace wani dan babban bura uba ne wann ne haba haba
daga can hajya zubyn ma ta kwarara mata ashariyar dayaci uban nata wanda saida yasata tadawo cikin hayyacinta atake
cikin saussauto da murya tace yaa zuby kiy hakuri bansan ke bace.. hajya zuby taja tsaki me sauti. babu wani bata lokaci tafara gaya mata akan cewa maza ta shirya
yau din nan tafara bin hjy mammy wajen gasa..
jiya da dare hj zuby ta makale tanajin duk wani hirarsu da alhaji attah mufasa yadda hj mamyn take korafin cewa ita kadai take zuwa wajen gasar, kuma gashi ita anan ta tura mata simran sai yazama kamar ma babu amfanin turata.
hanklin hjy zuby sosai ya tashi tahau gaya ma simran irin kayan mutunci da zata saka yau,snn tace mata in anje wajen ta cire kudi me yawa ta bada gudumawa itama.
tareda kashe mata warning cewa lallai ta kasance ashirye dan duk inda hajy mmy zataje itama ta shirya tabita wajen.
simran bata wani so hakan ba danyau spa taso zuwa amma kuma duk wani abu da zaisaka ta samu shiga wajen javeed zatay iyayinsa dan haka zata daure taje.
abunka da lazy kuma slay queen kasa komawa baccin tay dan tasan inta koma lkcin bazai isheta ta gama shiri ba. nan gidan babu dump bell dolene ta fito waje neman masu aikin da zasu tayata shiryawa
Da wani tsinannen guntun rigar bacci mai matuƙar tsantsi ta fito
tana tafiya akan matakala taci karo da wata mai aiki tanata sauri zata kai mint tea dakin da javeed ya kwana.
mai aikin ta gaishe ta bata amsa ba tabita da harara, can tace ina zaki kai wann?
tace Hajiya ce tace akai ma Sir javeed mint tea data hada masa..
simran cudnt hide her shock dan bata san javeed yadawo harya kwana agidan ba, da wani irin zafin nama tare da harara me zafi takwace tray din tea din tace toh jeki zan karasa masa dashi.
cikeda tsorata mai aiki tabar wajen
simran tabita da tsaki tana bacewa ta aje tray din ta dada gyara zaman nityn inda zukada zukadan nonowanta zasu dada fitowa fili dakyau dakyau snn tacire cap din baccinta ta yar akasa tabar suman kanta a fili babu dankwali ta dauki tray din ta kama hanya tana wani tafiya cikin karairaya hartakai kofar dakin..
duk rawan kanta tasan halinsa sarai he is a very mean and private person ba ashiga masa dakin sa gatsau komin rashin kunyar mutum kuwa haka zai jira seya bada izini.
Dr simran ta buga kofar takai minti 10 tana kiran sunansa tun tana rigima tana jayvee jayveee har ta dawo javeed javeed, Javeed…"shiru babu amsa karshe shahada kawai tay ta tura kofar kadan ta leka ciki kirjinta na bugawa sai taga ashe ma baya ciki, tsaki taja sann ta shigo kai tsaye da tray din a hannunta tanamai karewa dakin kallo dan sai yanxu data ga yanayin dakin sann ta dada yadda cewa ya kwana anan.
da can har zata zauna ta jirashi abakin gadon sai kuma ta tuna masifarsa sai ta hango kujerar dake tsakiyar dakin taga abu an rufe da farin riga, ahujajan ta sauke tray din kasa tayo wajen ta tsaya tanata kallon rufaffen board din da tunanin ko mene wannn din.
ahankli tazo gaban board din data kai hannu kai ko kadan bata kawo tsamnin ganin zane ba face har saida ta fara yayewa ahnkli ahnkli
fuskar dake jikin zanen na bayyana mata inda nan take Fuskarta ya wani canza da matsanacin mamaki da tuhuma.
bakinta harna rawa rawa tun bata gama yayewa ba tace "Wace ce wannan????iyakan rabin zanen fuskar nur firdaus kawai tagani amma sai taji atake wani abu me nauyi yashake mata hanyar fitar numfashinta acikin yanayin kaduwa take kallon zanen jin tsananin kishin da bata tabajin irinsa a duniya ba ya turnuke ta.
I HOPE U ENJOY THE PAGE..COMENTS AND SHARE. GOBE IN SHA ALLAH HALA ZAMUYI SHAFI NA KARSHE SAI KUMA BAYAN AZUMI IN SHA ALLAH
*NUR FIRDAUS BY*
*SURAYYAHMS*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top