eps 20
NUR FIRDAUS...20
Arewabooks@surayyahms.
Ahnkli javeed ya bude lumsashun idanunsa da adduar tashi daga bacci abakinsa snn ya saukar da kafafunsa kasa cikin furta silent bismillah tattausar muryansa kasa kasa acikin nitsuwa,..
nan ya mike tsaye tare da shigewa cikin mega size futuristic glass wall bathroom dinsa wanda girmansa yakai yay dakuna biyu which is fully automated, you just need to press a button for hot, warm or cold bath da duk wani abunda kake bukata anan ma yadan dade aciki yana wanka kafin can yafito jikinshi nannade cikin wani fine pure cotton white bathrobe me tsananin laushi wanda tamugun amsar kalar sudadden fatar jikin shi dats so shiny soft and creamy dan shi ba irin fari fat din nan bane.
zama yayi acikin nitsuwa Abakin madubin nasa snn ya shiga shafa sweet soothing notes of smoky wood neroli moisturixing cream dinsa mai kamshin dadi ajikin sulbabben fatar jikin nasa yana mai bin koinansa a tsanake Can sannan yatashi ya nufi walk in closet dinshi which is a standard of a 5 star boutique with an automated clothing selector, shiba namiji mai son tarkace bane dan haka designers guda bakwai ne kawai suke masa kayan sawa, sai kuma armored safe dinshi na aje dukkan hadaddun watches da jeweries dinshi wanda sudin ma sunfi ta'allaka ne a designers biyu dan agogo in ba kamfanin rolex bane to kamfnin audermars ne, he barely uses the 5 precious stones for special occasions.
ahankli cikin nitsuwa automated cloth selectorn ya mika mai wani soft dark slimfit grey Sigma Royale double breasted pinstripe suit me dauke da dark shades dinsa tareda mahadin expensive wristwatch and a leather gloves wanda da yasakasu ajikinshi nan take sukazauna ajikinshin sukamai wani irin kyau bana kadan ba.
Designers fragnance dinsa ma designer bakwai kacal yake iya amfani dashi inda lallausr hannunsa ya sauka akan kwalban Dominus Tom Ford Oud Wood dat has this dark, smoky, and luxurious feel, ya fetsfesa ajikinshi sama sama sannan ya shimfida dadduma yay sallahn asubahi a cikin nitsuwa wanda bazakace ma baida lfiya a lkcin ba, yana sallamewa ya danyi adduoi waikoda ma saiji sauki aransa amma inaaa can sai yatuna cewa yabar wayarsa acikin private acreage dinsa.
nan ya tashi ya nufi wajen agaggauce dan wani dan karamin sashe acikin dakin nasa wanda yake nan kamar private room amma babu gado just daga L shape leather cushion sai katoton Smart tv a bango da kuma glassy center table, rabin bangon acreage din Hotonan mahaifyarsa ne ata ko ita na jikin kowani hoto akwai articial burning candles bcos the room is extremly dark iyakan fuskarta ne kawai zakana kallo inda ka shigo.
bakaramin kama yake yi da mahaifyarsan a fuska ba, kalar jikinta na larabawan middle east wayanda su ba farare suba bakake ba ga kyau ga tsayi ga kuma dogon hanci da sulbabben doguwar bakin suma dake babantan balaraben africa ne mahaifyarta kuma shuwa arab ce daga nigeria.
aduk sanda ciwonsa ya tashi sosai toh anan zaka samesa ya boye kansa a duhun tare da hotonanta for hours yana kallon fuskarta yanajin inama ace da shine ya mutu yabar duniyan ba ita ba dan ciwon in taso masa yana sashi yanajin kamr his life is just a purnishment and he shud have done sumting difrnrtly to save his mum.
Duk da uwar duhun dake mamaye da wajen yana shigowa yasaka hannu kai tsaye akan kujera ya dauki tsaddaden customise wayarsa ya jefa a aljihu.
ya tsaya agaban candle din kadan ya kalle fuskar mamansa a hoton ahnkli cikin lumshe ido da budewa yace i am coming maaaa, with his strong bold commanding and emotionally guarded aura ya juya kamar wani iska me iska
kafin kace kobo har ya fice a dakin, ta lifter yabi ya haura can sama inda helipads dinsu yake securities dake wajen tun be karasa isowa ba suka hangosa a cctv camera dan haka yana tahowa suka tattashi tsaye suna mikamai gaisuwa dan babu mahalukin da bayajin shakkarsa agidan. daga ganinsa kasan baiya cikin mood me kyau dan haka kallon arxiki daga wajensa yau basu samu ba gashi fuskrsan nan a matukar daure take tamau kamr be taba dariya a duniya ba.
babu shiri pilot yace "Destination sir.
batare da ya kallesa ba, yace to the mogue. yana furta hakan sunsan kaduna zaije dan haka kafin ya karasa rufe bakinsa har an fara kkrin bude mai kofar shiga helicopter yana shiga kuwa ko minti biyar kwakkwaara basuyi ba pilot din yay sama dasu.
tashuwar jirgin javeed bada jimawa ba yay dede da lokacin da mahaifinsa Alhj attah mufasa ya fito daga cikin kebebben dakin shiryawansa cikin matsancin sauri dan kamar wanda jikinshi yake ingizashi haka yafito cikin hanzari ya doshi hanyar daya sada nashi site din da babban sashen dansan cikin gaggawa
ƙasan bene na biyu mashigar wata babbar ƙofa da aka sassaka da zanen dabbar daji ta buɗu mishi cikin lumana ya haura bisa kan golden rail stairs me wani irin haskawa da hasken kwayayen mega chandeliers da akay jikinsu da wasu kanana duwatsun diamonds..
Adm. Alhaji Attah Mufasa is a towering figure at 6’3” tall with a presence that commands both fear and respect..shekarun sa 69yrs a duniya saidai sosai Hutu da dumbin dukiya tareda kwarjinin aikin navy dayay yagama ratsashi wanda kallo daya kayo masa kai tsaye bazaka iya kiyasce yawan shekarunsa dede ba sabida atsaye yake cikakken namiji kamar dakakken bishiyar mahagony.
kwantaccen gemunsa me dan tsawo dat is silver-gray in colour tasha gyara tanamai complementing piercing hawk-like eyes dinshi ga wann deep baritone voice dinshin dat is slow and deliberate, daga jiki har fuska ya gama manyanta sosai amma kuma yana da ƙwazon matashi. Dogon wuyansa da fuskarsa da ke nan a matuƙar daƙile sai jajayen idanuwansa dasuke cika da ƙwarewa suna masu tabbatar da irin ikon dayake mugun ji da shi.
jiya da da kyar ya samu bacci sabida tsananin tunanin dansa javeed daya saka aransa dan koda yafarka da wani irin wahamin damuwa matarsa nabiyu wato HAJIYA ZUBAIDA OTHMAN WAZEER ita tadinga dannesa tana dan sassaitashi.
jiyan addafe yay bacci yau da safe kuma sai yaji hanklinsa yaki kwancya, aggaggauce ya iso babban sashen javeed inda a take ya ankara cewa yaronsa bai nan. yana turo kofar ya tsaya cak cike da kwarjini yana zazzare ido "Javeed!" Ya furta sunansa da mugun ƙarfi a lokaci guda kuma ya danne tashin hnklinsa..
Ba shi da buƙatar tambaya yasan inhar javeed bayanan to ya wuce Kaduna dan Ba yaune javeed ya fara hakan ba dan duk sanda wani abu na cigaba ya gifta yasan cewa javeed bashi samun sauƙi a ransa sai yaje kabarin mamansa yay spending sumtime with her kafin ciwon yake lafawa.
Javeed ba mutum ba ne da ke da tsananin rauni, inkagansa a normal days dinsa ma bazaka tabayin gigin tsammanin cewa wani abu a duniya zai iya sakashi baqin ciki ko damuwa ba, infact dumbin ilimin addini da tawakkali ya mugun shigarsa sede shikansa mahaifin nasa ya san cewa jinin da ke gudana a jikinsa yana dauke ne da wani nau’in cuta mei matukar wahalar da zuciya...
tunda ya shaida baya gidan Baiyi wata wata ba ya haura can sama domin ya tabbatar da hakan awajen securities..
subtle scent of oud and leather cologne dake yawo ajikinshine ya kama iskan gidan lingering long even after he has left the room, tafiya yake irin na isasshin maza agefen hannunsa na dama ya riko wata sanda, black colour beautifully carved walking cane dinsa daya saba rikewa.
tafiyarsa yake cikin kasaita da mulki bai hankara ba sai da yaji taku abayansa wanda already yasan cewa hjya zuby othman ce ke biye dashi.
kallo daya zaka mata kagane cewa she is fashion goddes Ako ina zaka ji ana kiranta da inkiyar ban girma na yan gayu watoh the great ZUBY of the MUFASA'S dan duk wani harkan Kwalliya da abunda ya shafi kyale kyale na mata itace akan gaba.
Shiyasa a kullum zakaga ganta kamar wata sarauniya, she is infact a creme de la creme world class lady ga kyau da iya saka kayan zamani kwalisa da qamshi,
she is xtremely werstenized and highly educated dan business ta karanta har matakin phd2 snn tsaban iya tattalin jikinta zagaka fatar jikin ta fari fattt yake kamar na vampires ga laushi da tsantsiiiii kamar gonan auduga
,ayanayin yadda take daukar kanta can sama sama tana balain ji da kanta babu karya zakasan tana cikin niimar dukiiya.
sanye da dogon mayafi ta fito daga cikin ɗakinta ta biyosa cikin gaggawa dan tasan babu wani abu me iya daga masa hankli a duniya inba damuwar dansa javeed ba.
hjy zuby othman itace jajirtacyar matar da ta dauki sama da shekaru talatin tana aiki wa gidan Mufasa acikin hikima da dabara tareda nuna musu matsancin kwarewa da amana tarike matsayinta na babban amintaccyar sectarynsa wanda harse bayan rasuwar matarsa Hjya haifa saddam mufasa sann ya aureta bawai dan yana sonta ko ya taba hankara da boyayyr sonsa data shafi shekara 30 din tanayi ba, shide ya aure ta ne kawai sabida itace kawai ya aminta da ita dan ayadda ta jima tay dedicating life inta gabaki daya tana fama da al'amuran aikinta dana gidansa
kusan dolene kawai yazabe ya aureta ko dan ta kula masa da dansa javeed dayake mutuwar so aranshi
dan baison javeed ya taso acikin ciwon kwakwala snn kuma yayi gamo da illar rashin kulawar uwa shiyasa ya zabi auren zubyn duk dama beso ba kawai se dan ta cike masa nan, dacan ma da sukayi auren sam baiya kulata, sai dai yau da gobe ya wuce wasa ahnkli ahnkli hartazo ta samu wani matsayi na matar aure a rayuwrsa haryazamo tana iya baza mulki son ranta ynxu acikin gidan mufasa.
Fuskarta da ke da kyau yanzu yayi girbin sheƙarunta da sukaja dan she is in her mid 50s sede murya da salon rayuwarta na yan gayu na nan daram..
tun be kai ga isa sama ba kusan agaggauce ta dakatar dashi
Alhaji, alhaji slow down mana Meye kuma ya faru Alhaji? saurin me kakeyi" Ta tambayeshi a cikin sassanyar murya mai taushi, ɗaga mata hannu yay da ƙarfi alamar kada ta dameshi shi. "kece duk kikace min kar nazo wajen yaron nan jiya inbarsa ya huta toh gashi nan Javeed ya wuce Kaduna."
Hajiya Zubby ta ɗan tsare gabansa tareda lumshe idanu tanamai ɗauke numfashi ya salammm Alhaji ka tsaya kaji, kai da kanka kacemin babu wanda ya isa ya hana javeed yay motsi a gidan nan To mesa kake daga ma kanka hankli dan ya tafi kaduna???"
Alhaji Attah ya juyo a kasaitnace ya kalleta ido cikin ido yace "Saboda nasan halin da yake ciki ne zubaida,.. cikin cije haƙoransa, sai kuma ya daidaita muryansa cikin tashin hankli yace cutar danake tunanin zai warke tun javeed yana karami amma na fahimci kmr yaƙara shigewa jikinshi ne"...Hajiya Zubby tasake kallonsa cikin kulawa "To, ka kira shi mana. cikin katseta da kallo yaja tsaki.."ke yanxu Kina tunanin Javeed yana iya daga wayar wani mutum acikin wann halin dayake ne?. aiko zai dauka ma bazai dauki nawa ba. but i knw what to do, zan kira kakarsa acan
dan Inhar taji cewa yana kaduna zata jawoshi jikinta dama kuwa tanace tana min hirar wani muhimmin taron gasar Alqur'ani da aka gayyacemu duka tanason lallai muje kaduna amma nasan nikam bazan iya zuwa har kaduna ba, but since javeed is going to be der with her ai shiknan kinga kenan komi taxo mana gidan sauki
kafin ta amsa Ya juya yakara taku zuwa wata mahaukaciyar falo yana saka hannu a aljihu ya fito da sigari mai tsada snan ya kunna shi da na’urar wuta mai azurfa ya jefa abakinsa cikin kwacinyar hankli
Hajiya Zubby ta ɗan girgiza kai cike da wani irin yanayin rashin jin dadi dan kuwa taso ace sunje kadunan nan dukansu as a family sabida tana da wani babban burinta datake son cikawa acan kadunan insunje dan babu wanda javeed yake iya daraja maganan bakin ta akan lokaci kamar kakarsa wato hajiya fulani Siddiqa Taheer mufasa, also knwn as ( hajiya mammy) dake zama a pent house dinta na can kaduna.
fuskr hjy zuby wani iri ta dan saussauto da murya dan tafi kowa sanin cewa babu raini tsakaninta da mijinta snn dama a ba'aja da umarnin mufasa's, ba a gardama dasu bare musayar yawu, duk wani hukunci da suka zantar ya zaunu kai banda dansa javeed daya ke mutuwarso aransa toh kaf duniya babu wani mahaluki daya taba jayayya ko saba dokar alhaj attah mufasa snn ya zauna kalau.
cikin sanyin murya tace, amma Alhaji ika bani dama zan iya yi ma javeed waya sai muji ta bakinsa, kasan fa kanwata simran tazo all the way frm UK jiya dan sabida shi, wllh nasan bazataji dadi taji ace wai har ya wuce kaduna basu hadu ba, nide idan har hakan zaiyu kuma zai hanaka samun wani sabanin fahimta da hajiya Mammy sai itama simran din ta shirya kawai tabishi can suje wajen gasar.
a take Alhaji Attah ya ya juyo snn ya kalleta yace "kefa kinsan waye javeed, shi mutum ne da bai son atakura mishi, ita kuma hajya mammy ai uwata ce, bata da wani matsala kema kuma bai kamata ki damu da yanayin Javeed ba kawai mu barsa yay abunda yake so din..
kasa cewa komi tay ta zuba masa ido dan tasan baison ya amsa mata kai tsaye ne yace ehhh simran taje sabida kar simran din taje kaduna ran javeed ya baci ace shine ya bada izini sabida yana gudun bacin ran dansa sosai.
itade duk jimawarta datay da su haryau ta rasa gane wani irin naunin sangartaccen so yakeyi ma dansa javeed da sukansa basu gane irinsa ba,
kallonsa take ayayin da ya cirkita laɓɓansa yana fesar da hayakin sigari cikin sanyin iko da rashin bada reaction din nata wani muhimnci.
kedai zubaida kuyi abunda ke gabanku kawai..ku kyale min d'ana ya sarara.
yana furta hakan ya ajiye sigarinsa a burn out plate cikin nitsuwa ya wuce ya barta awajen tana tsaye tana bin bayansa da ido harsaida ya bace ma ganinta kafin nan ta iya sauke wata nannauyar ajiyan zuciya cikin jin wani sabuwar tashin hankali.
kai tsaye ta nufi hanyar wani babban shashe inda kanwarta DR SIMRAN OTHMAN WAZEER ta sauka jiya da daddare.....
ABUJA 8.am
ata fannin su nur firdaus kuwa bada jimawa da isarsu schl ba suka samu kusan kowa ya gama hallara sabida gudun masifar matron dinsu malam bello..
kafin 8. ya cika suka dauki hanya zuwa Kaduna tare da jadida da Aisha dayan kawar Nur Firdaus mai ɗan rawar kai acikinsu
da su da su layla duk zasujene officially a matsayin school suppoters club.
direbansu yana tukin motar cikin nutsuwa kafin kace wani abu har sun doshi hanyar barin Abuja, they are expected to reach in 3hrs max.
kowa yana abunda ya damesa acikin motar jefi-jefi jadidah take kallon madubin domin talura da yanayin Nur Firdaus kamr tana cikin damuwa da ke bayyane akan fuskarta karara.
Layla kuwa duk da cewa ta yi shiru a cikin ranta tana jin daɗin cewa Adnan ba ya nan tasan Wnn kadai ma ya isheta samun nitsuwa.
sunakan gurza hanya cikin tunanin zuci Nur Firdaus ta ɗaga waya ta hau rubuta sako snn ta turawa mrss Haseena.
mrs hassena tanakan waya da saadat taji shigowar sakon, har saida ta gama sann ta duba taga sunan nur firdaus akai taja tsaki dakamar ma bazata bude ba amma sai kuma ta daure ta bude, bayan tulin gaisuwa, ta sanar da ita cewa sun dauki hanyar kaduna ita da layla, tace mummy ina neman alfarma daga gareki don Allah ki yafemin kowani irin lefi nake miki wanda ni bansani ba, kuma ki san ba zan taba fatan wani abu da zai ɓata miki rai ba, dan kece abu mafi daraja a rayuwarmu duka and i hope you will wish me good luck in my competition.
wani rau da idanu mr Haseena jin text din yadan taba mata zuciya kawai sai ta dan korashi da tsaki tay shiru na dan wani lokci. can kuma sai tahau tuna irin baqar magana na karshe da mahaifin nur din ya gaya mata on his death bed wen he was fighting for his last breath ayayinda yace
haseena nasan kiyayyar dakike min ne ya shafi y'ata nur firdaus amma bakomi ba, kuma nasan kin tsaneta ne dan tana tattare da dabiu na. toh kisani yau ko na mutu wallh ban bar miki kiwon ta ba, wa Allah ubangijin talikai na nabarwa kiwonta kuma shine zai daukakata zai kuma kare min ita bake ba."...
tuna wann kalamai ma alhaj haroun ciroma yasata jin tsananin bacin rai ta kara jan tsaki me tsayi da takaici, daga wayar tay ta danna kira wa layin nur firdaus din inda kai tsaye taji ya fara ringing
da matsanncin mamaki nur ta kalli sunan mamanta dake yawo a screen ta kalle layla da farin ciki snn tace layla mummy ce
cike da murna layla tace big sis to dauka mana dan dama suka daine acikin motar wanda babu wanda ya nemesu a waya tunda suka kama hanya
jiki na rawa Nur Firdaus ta dau wayar tay sallama tahau gaishe da haseena cikin girmamawa.
bata damu da yadda mrs haseena ke amsata ciki ciki ba
"toh har kun hau hanyar kenan, Saura kuma kije kibaza musu rawan kai da munafurci kinsan ai ba lallai bane sai kullum kece zakixo musu na daya.
nur firdasu batacewa komi sede kawai tay murmushi, tace in sha Allah mummy i will try my best duk kuma abunda na samu shima nasara ne..
haseena taja tsaki
toh shikenan amma banason kisake tura min wani sako inba wani abu na emegrncy ne ya faru ba, dan na lura dake kina so ne kawai in bar aikina inzo wajen gasarki..i need to concentrate here dama can ai baban ki yace Allah ne zai rike masa ke bani ba ko...toh Allahn naku ya bada sa'a.
kibawa auta ta waya inji lafyarta.
nauyin kalmar tata ta faɗo a zuciyar Nur firdaus kamar dutsen da aka jefa mata ta dan runtse ido ta mika wa layla wayar sai ita taja gefe jin yadda zuciyarta yake suya duk da Hakan ba sabon abu ba ne a wajenta amma ya fi ci mata rai yadda mummynsu take furtashi da gatse da rashin kirki aciki kamar ba ita ta haifeta ba.
batace komi ba ta dan sunkuyar da kai ta share boyayyen ruwn hawayenta a hankali,
sannan ta cigaba da kallon hanya cike da tarin damuwa.
sama sama takejin yadda sukasha hira da laylah harsuna wani kyakaytawa da dariya itafa rabon da suyi hira me dadi har da dariya haka da mumynsu bazata ma iya tunawa ba.
after like 10min layla ta mika mata wayarta tace mata ai mummyn nasu ma yanxu zata wuce Abuja tace wai sadaat na nemanta cikin gaggawa.
nur tay murmushi batace komi ba suka cigaba da tafiya kanta jingine da seat ta saka earpod tana saurarar karatun qur'ani.
****** 1hr on d dot due to hazy weather brigadier general javeed mufasa suka sauka a babban filin jirgin kaduna inda yake da personal private parking space din helicoptersa.
jirginsa yana sauka kamar kiftawa da bismillah convoy din da ke daukarsa suka karaso su biyar dukan su iri daya kuma bakake kirin da bakaken tinted.
Mercedes-Benz G-Wagon Brabus 900 ce dat is Ready for high-speed retreat agaggauce security ya bude ma javeed motar kusa da na tsakiya ya shiga ya zauna wacce ita kadaice duk jikinta bulletproof sabida numerous assasination attack dayasha fama dashi a can baya.
sun dau hanyar makabarta kenan private wayarsa ya fara kara da alaman shigowar wata sako
tunda suka fara tafyar idanuwansa a lumshe suke baya kuma ko motsi.
dacan kamar bazai duba sakon ba sai kuma ya zaro wayar daga aljihunsa, kallo daya yay ma sakon dake yawo screen dinsa ya daga kai tare da cizza labbansa nan da nan yabada oder cewa awuce dashi gidan dabbobin kakarsa kawai dake nan GRA Barnawa...
#SURAYYAHMS
NUR FIRDAUS
PLEASE COMENTS AND SHARE DAN ALLAH🤲🏻🧎🏻♀️
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top