eps 19

NUR FIRDAUS...19
wajajen karfe shida da rabi na yamma nur firdaus tashigo cikin gidan dat is unsually quiet babu motsin laylah bare kuma na sadaat koina yay wani irin shiru ahankli take tafiya rike da tulin tarkacen ababen data dawo musu dasu ta haura can sama dakin sun agajiye, anan tasamu lkcin layla na kwance akan gado tabi tatakure kanta waje guda kamar wacce tajima tana bacci, ajiye kayan tay agefe snn ta karasa saman gadon tadan dora hannunta gently a saman goshin ta jin alaman she is fine babu wani alaman zazzabi yasata sauke ajiyan zuciya me sanyi

mikewa tay tahau rage kayan jikinta dan yau tariga ta qudura aranta cewa bazatay bitan karatu ba zata zauna tashirya musu kayansu da zasu wuce kaduna da shi gobe. kwana biyar masu kyau zasuyi acan zaayi gasar cikin kwana uku ayi hidimar karramawa a rana na hudun rana na biyar zasu dawo Abuja.

tasan ba wani shirin tashin hankli bane but they have to pack alot sabida a wani sabon students hostel logde na annur zasu zauna acan. wanka ta fada ta hado da alwala kafin nan tazo ta tashi layla suka gabatar da sallan magrib da ishai

sede Gabaki daya yau bata gane kan laylah ba dan ko magana tamata sai kaga tana amsata ciki ciki bata wani walwala hakama duk wani abunda ta dawo dashi daga wajen adnan din bata tabashi ba da kyar ma nur firdaus ta sakata ta ci abincin na dole.

yau da wuri layla tay bacci dan bata son nur din ta fahimce halin tsananin baqin ciki da matsancin kishinta da take ciki..
domin kuwa dukkan abunda suka wakana ayau din sune kawai suke mata yawo acikin kwawalrta da zuciyarta sai tafarajin kamarma komi lefin nur firdaus ce da ta sace mata kalar rayuwar daketa so tay arayuwarta gabaki daya.

yau nur firdaus batay bacci da wuri ba saida tazauna ta shirya musu kayyankin tafiyarsu a trollenysu tsaff, dukkan wani abunda tasan layla zata bukace shi awajen bata mance shi ba..

bayan ta kammala ne suka danyi waya da Adnan yake gaya mata cewa hala bazai samu zuwa tare da ita har Kadunan ba sabida dayaje gida ya samu already mum dinsa tay booking musu 5:45am flight to London toh baisan ko zata amince ta masa uzuri ba. har cikin zucyar Nur bata so jin hakan ba sabida tasaka ranta sosai dan wani cikar babban burintane ace Adnan dinta ya kasance tare da ita ayayin datake wajen wann gasar me matukar muhimmnci gareta, sede kuma sam batason tasashi yay wata jayayya da umarnin mahaifyarsa akanta, dan haka ta ringa lallabashi tace masa yabar maganan zuwan kawai itadin zata masa uzuri..

haka suka sha hirar soyayyarsu cikin wann daren adnan shehuri ya mammata alkwarin zaina kiranta akai akai dan kar taji kewarsa acan kaduna, sosai taji sauki aranta daya furta mata hakan, ya kuma nuna mata rashin jin dadinsa na kasancewarsa acikin tafyr, yau har izuwa wajajen karfe sha biyu da rabi na dare suna buga sassnyar hira kafin can ya kyaleta tay alwala tazo ta kwanta bacci.

Washegari da safe ya kasance ranar da za su tafi Kaduna, Nur Firdaus ta farka da wani irin farin ciki a ranta Duk da cewa Adnan ba zai yi tafiyar tare da ita ba bcs dis competition is one of her wildest dream.

sassafe ta dan fita waje bitan karatu bata wani jima ta kammala tana kkrin dawowa ciki ta shirya kenan saiga malam liman yana kkrin tahowa ta wajenta cikin sauri nan suka gaisa ya mika mata wata yar jaka yace mata Adnan ne ya aiko mata da sako.

karba tay tana shan mamaki bata bude ba tawuce ciki da jakar inda ta samu laylah tafito wanka kenan tana zaune agaban madubi tana zuba wata mayyar kwalliya ranta har yanxu ba asake ba dan tun jiya take zagaye bata ji duriyar sadaat agidan ba dan da alama ma ko kwana agidan baiyi ba.

tsabar sake sake bata ma lura da shigowar nur dakin ba face saida taji ssnyar sallamarta akanta tana dan kyallara ido ta hango gucci gift bag a hannun nur firdaus nan tamike tsaye zumbur cikin hanzari ta tunkaro ta

"yaa nur meye wann kuma...?? cikin sauke ajiyan zuciya nur ta zauna abakin gado ta fara kkrin bude gift bag din tana cewa
Adnan ne ya aiko min

layla tay rau rau da ido cikin kyabe baki da alaman tambaya ayanyinta amma big sis i tot he will travel with us to kaduna ko ba abunda yasaka ya dawo jiyan ba kenan?

cikin sanyin jiki nur ta girgiza kai snn tace yeah but, Not anymore layla tun jiya yacemin wai mahaifayrsa tana dan bukatar attention dinsa wai they are going to london kuma inaga ma jirginsu ya tashi by now...

layla taji kamar zata fasa ihu dan tsananin farinciki da murnan jin wann maganar dan dama bakaramin kishin hakan takeji ba

wani phewwww taji kishin ya sauka akan kirjinta atleast adnan is not going to be around in kaduna bare aje acusa mata wani bakin cikin da zai iya kasheta, infact, kashi 70 daga cikin haushin dake kullata aranta tun jiyan saiynxu taji da alaman ya sauka atake

a fili kuma sai ta dan harde rai kai tana turo baki kasssshh amma banji dadi ba,nasan kin saka rai akan zuwansa gashi dama shikadaine fa zaizo mana mummy kam kinsan bazata zo mana ba wallhi

nur batace komi ba kawai ta kyabe baki tare da nuna yanayin bataji dadi ba, tana gama bude gifts bag din taga wasu sabbin kyautukan ne aciki still, sabbin notes na kudade 1k notes masu yawa sunkai Dubu dari biyar da kuma hadaddun hijabai guda hudu masu shegen kyau da aji iri daban-daban, da wani note mai tattare da sassanyar   kalamansa a handwritern note card na bada hakuri, koda takalla kyaun kyautukar saida taji wani irin sanyi na ratsata a zuciya.

Hijaban sun kasance masu launuka masu kyau tundaga kan launin fari har izuwa black, brown da blue da ruwan madara they are made of plain silk turkish material me kauri da tsantsi snn kowanne na da tsarin kalar design dinsa na alfarma. nur ta dan lumshe idanunta cikin godiyar zuci sannan tasake bude pprn ta karanta rubutaccen sakon da Adnan ya turo mata "My Noor, koda bazan iya zuwa tare dake ba ina son ki san cewa ina tare da ke a zuciyata akowani lkci Ki kula min da kanki please habibty, ki kuma sanya wnnan hijab domin ni". Ta yi murmushi tare da jin shauƙinsa ma ratsata Tana ji kamar ta kira shi taji muryansa sai kuma ta ji nauyin yin hakan dan tasan duk yadda akayi  by now sunhau jirgi tare da mahaifyatsa yanxu.

Layla kuwa tun da ta hango kayan kyautar tadan yi murmushin jin haushi da kishi a cikin ranta amma a fuska sai ta yi kamar tafi kowa farin ciki ta fara tattabawa tana daka tsalle kai kai wow wow ohh mmmy god Gaskiya hijaban nan sun yi matukar kyau big sis ni zan fara sakawa... tafurta hakan cikin tsabar zumudi nan take tafara gwagwgadawa ajikinta while cikin zuciyarta kuwa cewa take she wish all this money and gift it was hers.

at around 7:30am lokcin dukansu sun shirya kowa taci ado tafito fess fess har cikin ran layla tanata murnan cewa adnan bazai je kaduna da su ba,a fannin nur firdaus kuwa tunda sukayi waya da kawayenta su aysha da su jadidah saikuma tafarajin  wani iri aranta jin yadda kowa iyayensa da yan uwansa zasu taho kaduna dan su goya musu baya amma bandasu dan daga ita sai layla zasu  je gashi adnan data sakashi a rai akan zaizo mata shima din yace bazai samu damar zuwa ba.

bayan sun gama shiri  suka sauko tare da yar jakar hannunsu kowacce tayi kyau matuka acikin shigarsu ta black al layl abaya mai golden stones sunyi rolling veil din abayan a kansu kana ganinsu zaka dauka irin pure breed yaran larabawa ne da babu surki.....
acikin yaran larabawan ma sede ace musu yayan masu dukiya ko kuma y'ay'an gidan sarauta dan bakaramin kyau Allah yazuba musu ba

layla ta saka doguwar vinci shoes mai igiya, ita kuwa nur firdaus wani kyafaffen tombs na kamfanin bouchra jarrar kawai ta makala asawun kafarta shima baki da surkin kalar golden irin jakar data riko..

A booth malam liman ya loda kayansu suka shishiga suka zauna yawuce da su kofar gate din ICICE sabida ananne babban motar bus na makaranta zata debesu su wuce kaduna.....

Lagos state, Nigeria. 5:30am the same day.

*ADM Attah Mufasa Fortress, No. 1 Black Tide Boulevard, Exclusive Waterfront Edge, Lagos, Nigeria.*
*******

Babu wata shakku ko tantama duk wani dan nigeria yana sane da yadda Banana island tay fintikau wajen kere kowani gari a fadin nigeria darajar tsada da kuma kera kyawwn muhalli na zamani domin kuwa banana island wajene dake dauke da matattarar manyan hamshakan gidajen masu kaxamin dukiya dana boye dana fili ba area na masu kudin muna da kudi ba dan kuwa acikin wann anguwa akwai sashe sashe acikinta frm midle end billionaire to high ends elites wanda wani billionaire ma bai kai ya isaga zama ata wajen da suke ba...

ultra excluvise area kamarsu _the hidden billionaires enclave._ inda anynomous high ends nija billionaires wanda kwata kwata basa son asansu suke zama with extra layers of security da irinsu _VVIp zone dake kusa daf da Alexander road_ wanda aka fi sani da home of tycoons which is full of powerful and prestigeus personalities.

sai kuma arean dayafi kowanne muhimmci a banana island din wato _the exclusive coastal edge_ wanda ake kiransu da _water front mansions.,_ inda shahararen Ultra futuristic mega mansion din wani shahararen powerful mafia tycoon boss, a 69yr old business mogul and excutive plus ex Naval me suna ADM. ALHAJ ATTAH MUFASAH... .

muhalli ce me tsananin tsada with  the highest land value sabida kowani gida awajen an ginasa ne da wani irin top notch technology na zamani snn view dinsa yana kallon katoton tafkin nan na lagoon ne yadda private yatch, da speed boats zasu zauna akai dadin karawa they all have these underground bunkers and helipads inda suke aje jirgi.

Daga ka iso wann bangaren na anguwan dakanka zakasan cewa ka iso inda muhallin baqaqen kusosin kasa suke sann waje ne dayake da tsananin kebewa daga hayania tare da matsanancin sirri....

yau laraba ranar sa'a  wajajen karfe 5:30 na safiya wata sassanyar iskar safiya na msmn me tsananin sanyi ke kadawa ahnkli a wann kebetaccen anguwa dayay matukar shiru ayayinda baka iya sauraron komi face dadaddar sautin karar ruwan tekun lagoon dayake juyawa ahnkli.

ata can kusa da karshe karshen anguwan gida biyu ne zaka iya cin karo dasu wanda nisan dake tsakaninsu zai iya kaiwa daga wani anguwa xuwa wani anguwa cos each house is a mega size gari gudace ake deba ma kowanne.

daga kahau kan shararren street din dake wajen wata katuwar Signboard zaka fara kallo me launin baki da golden colour me tsananin sheki, ajiki an rubuta ADM Attah Mufasa's ultra mega Fortress, No. 10 Black Tide Boulevard, Exclusive Waterfront Edge, Lagos, Nigeria.

Wacce ba gidan mai kudi bace kawai a tsaye kuma bazaka ce dashi huge mansion ba, dan kuwa katoton shararren muhalli ne dayake dauke da massive 5-acre private estate me zagayi by 20foots,an katange su gabaki daya da wasu titanium plated walls me laser sensors da wasu mahaukatan surveillance drones da suke aikin bada tsaro kowani lkci.

abu mafi dauke ido acikin wann gida beifi babban masallacin su ba, its a golden dome design masjid me dauke da smart adhan system da marble fountains na alwala with touchless water dispenser system ajikinshi wanda akalla masallcin zai iya cin akalla mutane 50.

kai zaka iyacin sati guda kana zagawa baka gama karewa gidan kallo ba dan kuwa gari gudace...

it’s surely a futuristic kingdom strickly designed for a powerful mafia boss like adm. alhaj Attah mufasa who controls power, intelligence and military secrets.

kowani sashe na gidan in an inch is busy screaming of untouchable elites with dangerously powerful atmosphere.

zagaye yake da highly trained masu aiki da bindigoginsu ajikinsu kowannensu cikin bakaken kaya...

ata bayan gidan suna da Private Dock with three luxury yachts and a military-grade speedboat, a saman gida akwai Helipad an parker wata shegiyar private Augusta Westland AW139 helicopter dat is silent, fast, and ready for rapid transport. ata can kasan gidan kuma akwai wata kerarryayar Underground Car Vault (garage) me dauke da rotating display housing bulletproof Rolls Royce, mercedez Maybach, Bugatti, da armored SUVs. sai Cybernetic Security Tower inda ake aje cameras da cctvs with face-recognition na AI da kuma holographic access controls for VIP guests only.

bayan nan babu wani abunda zaka iya kalla a ilahirin gidan face wajajen ajiye dokuna, da kyawawan wajejen shan iska da kuma wajen wasanni masu daukar hankli.

daga cikin wann hadadden futuristic ultra mansion din cikin wata kebetaccen sashe wani ginannen mutum ne kwance luff luff akan lallausar 360 degree rotating king size bed dinshi wanda akay desining dinsa da AI controled galaxy view ceilings...

5:30am dot mutumin yafarka daga bacci dakyar shima dan sabida alarm din gefen gadonshi ne daya damesa da buzzzzzz ya tadashi

jiyan sam bai samu wani bacci ba sabida rubibin hidimar da aka yina karramashi tare da'kara masa girma
to a Brigadier general Javeed A. mufasa, the only son of a mafia boss Adm. alhaj attah mufasa, the only heir and captain of many relevant industries like health, media houses, bank, power, real estates, agriculture,  and he is just being crown the Brigadier general of nigerian millitary police NAMP under commissioned office after good 20yrs of his dedicted distiguished services and ecxeptional perfomances.

his strategic responsbilites is inteligence, hakama his specialised role in the nigerian army is counter insugency wanda suke yaki da manyan terrorist, da kuma yan ta'adda da suka addabi kasa.

saidai akowani lokci BG Javeed mufasa ya samu wani matsayi na musamman whether a military promotion, a successful operation, or even personal milestones baiya samun kwanciyar hankali aransa saidai yaji yana dada dulmuya cikin wani irin tsananin baqin ciki da damuwa, Instead of celebrating his succes sai mind dinsa yadinga memeto masa lokacin dayake dan shekara 6yrs a duniya wata baqar ranar da bazai taba iya mantawa dashi ba ayayinda wai shida hannunsa ya bawa mahaifyarsa madarar data sha ya kasheta.

tun daga lokacin javeed mufasa ya kamu da mental trauma iri iri aciki kuwa har da tsananin tsana da yayi wa madara.

dayake karamin mahaifinsa yasha matikar wuya kafin nan ya samar masa sauki dan javeed ya taso ne yana tsananin kaunar mahaifyarsa late hajiya Haifa saddam mufasa, datake nan tamkar abokiyar wasa agaresa, wanda mutuwar tata shiyasa Javeed’ yaci karo da chrnic mental trauma response than can be related to PTDS wato Post-Traumatic Stress Disorder with mild Survivor’s Guilt and Complex Grief.

wanda ya jima yana affectinng yanayin rayuwarsa kama daga kan emotions dinsa har behaviors dinsa,.

wata rana haka kawai zakaga yaja jikinshi da kowa ya kebe kansa na tsawon lokaci kuma duk wani hidima ta farinciki da wuya ne kagansa yaje, wani bin yana da tsananin fushi da kwarjini sabida kwakwalrsa yana iya cusa masa jin radadin zafin kashe mahaifyrsa dayakejin yay akowani lkci, he can be irritated very easily shiyasa bazaka taba kasashi acikin maza masu saukin kai ko sakin fuska ba

jiyan da ya samu karin matsayi sosai ciwon nasa ya tashi, dan ya jima bai samu bacci ba sabida yana fama ne da ciwon rashin baccin, inkuma baccin yazo masa very late toh mafarkin ranar da mahaifyarsa ta rasu kawai yake iyayi a kowani ranar farinciki agaresa wanda inhar be bar gidansu na lagos yaje can yay spending time akusa da ita yamata addua a kabarinta dake can garin kaduna ba toh bazai taba samun kwanciyar hankali a cikin zuciyarsa ba..
SURAYYAHMS
NUR FIRDAUS
08060712446
COMEBAK SERIES
2025

PLEASE SHARE..

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top