Eps 16
NUR FIRDAUS...16
Arewabooks@surayyahms
zugar Manyan Mata
ne masu daraja da arziki suka rufawa hon hjy mariam kanem shehuri baya har izuwa wajen zamanta da aka tanadar mata na musmman masu mata kirari sunakan yi wasu matan na shera mata guda gwanin burgewa, kaf Kayan jikinsu da fuskokinsu na sheƙi wal wal wani irin tsantsar jiji da kaine da rantsatsar kasaita yake famar bayyana a fuskokinsu
laylah dake bin kowacce da kallo a fakaice tanaji aranta yadda matan suka matukar burgeta.
bayan waje ya dan lafa da gaishe gaishe nan mrs Haseena ta taho da fara'a tana tafiya tareda sanyin kasaita Layla kuwa tana gefenta cikin sanyin taku fuskar nan tata kuwa kamar antsaga ruwan madara.
kame kanta tahauyi na musammn dan kuwa tun daga shigowarsu hjy mairam shehuri laylahn tabi ta rasa nitsuwarta barinma da sukazo kusa dan sugaisa da tawagar familyn shehuri daga ita har mumyn nasu haka suka dan rusuna kasa da ladabi..
cikin mika jinjina mrs haseena tace ranki shidade honourable hajiya mairam kanem shehuri giwar mata Allah shi temake ki barkanki da shigowa.
hajya mairam ta dan jinjina ma haseena kai cikin shan qamshi da mulki bata wani amsa ba idon sauran mata kuwa kaf na kan layla da ta rusuna kai kasa da ladabi sosai kamar mutuniyar arziki....
haseena na murmushi takalle yan uwan hjya mairam din dake gefe
manyan hamshakan mata ne wanda suna matukar kama da hjy mairam din a fuska
cikin girmamawa tace
hjy amatu, hajiya ruqayya kanem, hajya mariya shehuri please ure welcome ma's
...dede nan ne layla ma ta gaggaishe su da ladabi sosai
hajy mairam dake jiji da wani irin mulki da kamewa bata wani kalleta ba yan uwanta irinsu hjya amatun ne suka amsa da fara'a nan da nan hajiya ruqayyan datafi kowa kama da Adnan tadan kalli laylan dakyau snn tace haseena Wannan fa?wata Hurul-ayn ce a duniyar namu!"..
Wata matar me kudi data sha leshi agefenta dake murmushi tace saura kadan ince hala kanwar haseena ce tsabar suna kama but she is soo young tafurta hakan tana kallon kyakkwan fuskar Laylan sosai suna yar dariya.
uhmm Gaskiya kam! Wannan ai ba kyakkyawa bace, ace mata dai kyautar Allah hjy amatu kanem ta furta tana kallon laylan da kyau daga sama har kasa
lkcin Laylah ji take yi kamar kanta zai fashe dan tsabar dadi, kanta na kallon kasa tay murmushi a hankali bakomai take tunani ba sai yuwar samun Adnan a rayuwarta nan ta rufe idanunta a slow tana mafarkin yadda hala wata rana zai riƙe hannunta yace wa wayanann manyan hamshakan matan cewa itace kaɗai a cikin zuciyarsa.
zuciyar mrs haseena kuwa cike yake da alfahari takara jan hannun layla zuwa kusa inda Hajiya Mariam Shehuri ke zaune cikin izza tare da sauran manyan matan snn tace
"ranki shi dade Hajiya, wannan ita ce Laylah Diyata ce yar albarka."
sauran matan duka suka kalleta irin ohh wow masha Allah.
da kyar Hajiya Mariam ta kalli Layla sama da ƙasa snn ta yi karamin kasaitacen murmushi.
muryanta kasa kasa tace masha Allah Gaskiya kyakkyawace amma itace ɗiyar ki ta farkon? Nur Firdaus, ko?" i hve heard so much abt her from my dearest son Adnan, kullum sai yamin zancenta, but i am quiet taken a back, inde itace wann to tabbas Adnan ya haukace, ta dada kallon layla up and down, "yeah she is pretty.. amma kyaunta bai kai yarikita min d'a na ba koya kika gani yan mata...?
sauran matan suka saka dariya haha haha haha nan aka maida maganan ya dawo raha kowa na fadin albarkacin bakinsa
mrs Haseena tadan haɗiye yawu jin abun ya bala'in cakkarta a kirji amma haka tafuske tabiye musu cikin rahar tace "aa, Adnan bai haukace ba ranki shi dade wann aiba nur firdaus bace, ita nur firdaus din tanacan makaranta you knw she is kind of very focused on her studies ta karashe da murmushi mara sauti.
hjya amatu ta dubi layla tace ohhh wow, so dis is the un- focused one?? cikin wata sabuwar raha aka sake fashewa da dariya sosai.
take Layla taɗan sunkuyar da kai kasa jin yadda zuciyarta ya dulmuya yakone da haushi danta tsani amata dariya kuma badon komai taji mugun haushi ba sai don furucin hjy mairam kanem akan kasawar kyaunta a idonsu da kuma ba taso a ambaci sunan ‘yar’uwar tata anan ba sam.
nan Hajiya Mariam ta gyara zama tana fuskantar Haseena so i am looking foward to see the focused girl, kinga haseena Daga zarar na ci zaɓen nan d'ana Adnan zai yi aurene batare da bata lkci ba dan haka kede Ki tabbata diyar kin can tanada daraja sosai." inde batun kyaune y'ay'an ki suna da kyau, amma sanin kankine we have so many young beauty queens around acikin dangin kanem so u have to earn it.
da barin jiki mrs haseena tace in sha Allah ranki dadi y'ay'a na duka ai kamar naki ne bare ma gida biyu maganin gobara za'a san yadda za'ayi.
Layla ta dan lumshe ido tareda jin fargaba jitake kamar saita dage sosai da sosai kafin nan Mafarkinta na kusantar rayuwar Adnan shehuri ya iya zamowa gaskiya!
bayan anyi taro lafiya an watse sadaat ya tura ma haseena sakon cewa zai karaso gidan dan haka ta gaggauta suka bar wajen domin taje tashirya masa abinci da suka taho dashi a take aways daga wajen taro.
Suna cikin motar Laylah tayi tagumi snn tayi shiruuu zuciyarta cikeda wasu irin tunani..
mrs Haseena ta dan kalleta da gefen ido aranta tanajin kamar layla is hiding sumting amma kawai sai ta share ahnkli tahau shafa kanta ahnkli cikin sauke ajiyan zuciya tace auta Da ace ke ce za ki auri Adnan ko, da na fi kowa farin ciki."
da matsanancin mamaki Layla ta yi murmushi tareda mikewa kaɗan dan takalle mum dinsu ganin she is serious cikin basarwa tace "whaat? haba mummy adnan kuma, yaa nur din fa??
mrs haseena tay dariya c'mon kema kinsan babu wacce zatace batason shi kuma naga kamar ke kinfi dacewa dashi sosai, kinsan fa yana yin aure zasu bashi babban matsayi, and in d future kuma sai kiji ya zama minister shima,shiyasa nake ganin kamar kece zaki fi dacewa agefensa, i wll be soo proud sabida nasan kekam u wll help mummy alot.
cike da yarinta layla tay murmushi snn tace of course mummy duk duniya kece akan gaba awajena i just want you to be even more than woman ..
wani irin dariya mrs haseena tay nan sai wayarta yay kara ta dauka kai tsaye suka hau tattauna batun ummi da mutanenta har suka isa gidan bata gama amsa wayar ba....
suna karasawa cikin gidan malam liman ya bude musu kofar mota suka sauko kai tsaye Layla ta shige dakinta zuciyarta cike da kulla sabbin dabaru dan bakaramin karfin gwiwa kalaman mrs haseena akan dacewarta da adnan yakara mata aranta ba wani bin laila sam bata da maraba da mahaifyarta they are so selfish and self centered, they all have one kind of desperate energies na mugun son sugansu asama snn kuma asan dasu a wajen hidima.
ata fannin nur firdaus yau kusan bata dawo gidan dawuri ba sabida bitam karatu tareda ribibin shiryasu da malam bello yake faman yi dan an riga ance musu mutane masu muhimmaci sosaine zasu halacci taron irin wanda an jima sosai ba agayyato irin su ba.
aciki kuwa har da familyn shahararen Mafia tycoon boss din nan the captain of many many relavant industries around the globe his excellency Grand Admiral Alhaj Attah mufasa and his entire filthy rich family members kasan kuwa cewa wann gasar ta su ta musamn ce.
wani irin training me tsanani ake wa nur firdaus kamar ba gobe. gashi daga an dawo daga gasar zasu fara shirin jamb da kuma waec exams dinsu nagama schll din befr deir grand graduation ceremony.
yau sai kusan wajajen karfe shida da rabi dede nur firdaus suka gama rehearsal ta kira
malam liman batare da bata lokci ba kuwa yazo ya dauketa ita da babban kawarta jadidah da suke da same age ya aje kowaccen su agida.
a mugun gajiye ta shigo cikin gidan jin qamshin soyayyan kaji ya mamaye ko ina gawata mayyar aroma na fried rice tana tashi daga kan dinning table dinsu she was so famished and tired gashi tawuni da tunanin jikin yar uwarta sosai ta damu.
sassanyar sallamarta ne ya ratsa falon jin ko ina shiru lokcin Haseena harta gama gyara fried rice da chicken da ta samo daga taron tawuce sama domin ta yi wanka da shiryawa.
Nur Firdaus Tana jin ƙamshin girkin cikinta yadan tsinke da azaban yunwa tana Allah Allah ta dawo ta samu ta ci itama, kai tsaye tawuce daki ta bude kofar da mamaki ta hango Layla zaune agaban madubi da alama harta watsa ruwa tana shiryawa cikin wata matsatsen jeans da top tana dan latsa wayarta time to time tana cancarawa fuskanta kwalliya.
Nur ta ɗan waro ido waje snn tace Layla?? bake ba ce kike cewa cikinki na ciwo har kin ji sauki kenan ko
Layla ta mike zumbur sannan ta kalleta da sauri tace big sis welcome back, ehmm ehmm naji jiki sosai amma ai yanzu na ɗan ji sauƙi.."
agajiye nur tace its okay i am glad ure' fine ta bude jakarta ta fidda wasu littfai gashi nan na amso miki notes daga ajinku saiki dudduba ki kwafa tunda kin ji sauki.
layla ta yi wani murmushin karya snn ta karba notes din da murna tahau dudduba wa a tsatsaye,..thank you yaa nur yanzu dai kiyi wanka kihuta nasan kin gaji ni zanje kitchen ina zuwa..nan da nan ta juya tafita cikin sauri kai tsaye tawuce hanyar dakin mahaifiyarsun.
Nur ta dan yi shiru, tare da bin bayanta da kallon shakku can ta girgiza kai ahankli kawai tafara rage uniform dinta ta ninke su tsaf tsaf akan loundry basket sann ta dora towel tanamai fadawa gidan wanka.
bayan kamar minti ashirin Nur firdaus ta kammala wanka ta shirya cikin doguwar riga baka plain jallabiya me 3qtr hands tafito tana jin yunwa sosai. Tana saukowa daga step ta ji ƙamshin abinci har yanzu yana tashi hakan yasa tayi sauri tanufi tawajen dining area domin samun abinci a nitse ta karaso ta tsaya cak
lkcin mrs taga Haseena tana zaune a dining din gefenta Layla ne da Sadat sunacin fried rice and chicken cikeda nitsuwa...
Ta ɗan ƙwalla ido ta yi sallama a hankali snn ta gaishesu ba yabo ba fallasa, ayayinda taga mrs haseena ta dauki warmer sauran last portion na abinci ta zubashi akan plate din sadaat..
nur bata saka komi aranta ba ta ja kujera ta zauna tsabar yunwa har wani jiri jiri takeji warmern ta jawo ta bubbude saidai babu wata alama da kenuna cewa an tanadar mata da nata abincin.
kamar zatay kuka ta kalle mrs haseena mummy ba a bar mini abinci ba ne? i am so famished tun safe dana karya ban sake cin komi ba.
mrs Haseena ta ɗago kai tanakan tauna nama abaki tace toh Ai ban san za ki dawo da wuri bane Kin san dai kullum kekike latti.
Nur ta haɗiye yawu tana kallon yadda Layla ke figar naman kazan cikin jin daɗi, kamar zatay kuka tace "mummy kina nufin ban da abinci? mrs haseena tace abinci fa kadan ne nur ya kare wallh, batace komi ba Sai ta ɗan sunkuyar da kai To amma ai layla tasan na dawo
Haseena ta harare ta. "and so what, ke dai Ba za ki taba daina mita arayuwarki ba yanxu so kike ace laylan dani duk mun cutar da ke akan abinci? why dont u go and cook it by urself nace miki wann kadan ne kuma ya riga ya kare wallh...
ahnkli Nur ta runtse ido zuciyarta cike da takaici ta san ba za ta taɓa samun mafita ba idan har za ta yi faɗa da mahaifiyarta a kan irin waɗannan kananan abubuwa.
mikewa tay jiki a sanyaye ta koma daki dukansu sukabita da kallo kanta na mata wani irin ciwo dan sosai ta saka ranta akan abincin.
Mrs haseena ta cigaba da mita tana cewa yar rainin hankali wai tun safe dataci bata kara ci ba yanxu saka samu taci
ta koshi wanda zamu cin ne take so itama sai taci.
sadat baice uffan ba layla ce take dan saka mata baki.
nur tana kwance akan gadon tsabar yunwa jikinta ya fara daukae zafi tunanin abunda zata dafawa kanta taci take saiga nan Layla ta bude kofa hannunta dauke da wani bowl me dauke da cornflakes tana karasowa ta ajiye bowl din corn flakes a gabanta.
yaa nur Gashi ki sha wann na hada miki" Ta furta cikin sanyin jiki.
Nur firdaus tana kallonta tace thanks layla amma Kin san ba na shan corn flakes.
Layla tayi wani irin da fuska toh ai shine kawai yarage agidan gara kisha da ace bakici komai ba...
Nur ta girgiza kai tay shiru Layla ta zauna kusa da ita tana dan murmushi kallo daya zaka mata kasan ta ƙagu ta bata labarin duk abunda ya wakana ayau.
ana daf za'a kira magrib nur na shirin mikewa layla tace yaa nur Kin san wani abu kuwa?hmm Wallahi yau ninaga bajinta
Nur ta ɗago kai kaɗan tace A'ina?"
Layla ta dan lumshe ido tana murmushi
nan da nan ta hau bata labarin fitar tasu...
yaa nur Gaskiya Adnan yana da gata. Mamansa Hajiya Mariam Shehuri, mace ce da komai na duniya ke tafin hannunta Wallahi idan kin ga yadda take tafiya, yadda take magana, yadda tayi kwalliya… ba sai an gaya miki ba itadin babbar mace ce
i also got a chance to meet all his anties wayyo big sis baki ga kaman da sukeyi da Adnan ba mum dinsa tace ma mummy wai daga taci zabe zaayi auren Adnan.
Nur firdaus ta ɗan yi murmushi kaɗan ba don komai ba sai don ganin yadda Layla ke kamkamba labarin kamar zata tashi sama, ita kuwa abun bewani darata ba dan kuwa haryanxu zuciyarta Yana cikene da wani irin nauyi da ba ta fahimcesa ba.
I WILL MAKE IT UP FOR THE FEW DAYS DAT WE LOST AYI MIN UZURI WANI ABUNE YAKE DAN SHAMIN KAI
THANKS. SURAYYAHMS
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top