EPS 13

NUR FIRDAUS...13

SURAYYAHMS

bayan tafiyar haseena aiki bada jimawa Nur firdaus tashigo cikin dakinsu da hadaddn qur'aninta rungume da lallausar kirjinta tana tafiya ahankli kamar wacce bata da laka, cikin sanyin jiki ta aje qur'anin akan desk dinta tabi ta kashe wayarta snn ta zauna ahkli a gefen gado tay yar tagumi.

har cikin kokon zuciyarta takejin wani irin nauyi da damuwa dan kokadan bataji dadin yadda jiyan bacin rai yasata maida magana mezafi da kuma tsawa wa mahaifyartan ba, duk da yawan rashin adalci da tunxirata da mrs haseena tay ders dis kindest part of her heart dayake tuna aya daya tak a cikin qur'a ni daga cikin Suratul Al-Isra’ tun daga 23 da Allah yace karka daga ma iyayenka murya koda kafurta musu kalman "uff", kada kuma kamusu tsawa..

sede tafi jin nauyin ayata 24 inda Allah yake cewa “Wa khfid lahuma janaahaz zulli minar rahmati wa qur Rabbir ham huma kamaa rabbayaani sagheera.", And lower to them the wing of humility out of mercy and say, ‘My Lord, have mercy upon them as they brought me up{when I was] small.’ haka kawai inta tuna ayar ya ambace humility saita dingajin kamar bata kyauta makanta data amsa ma uwarta magana a cikin rauni da tsawa ba, duk sai tarasa ya zatay, dan bata da wani dalilin tsaurara makanta duk dama tasan kowani dan adam a duniya raunataccen halitta ne sede ita din karamar yarinyace sosai data rike ilimin addininta amtsayin madogarar rayuwarta bana wasa ba.

duk wann guilt din datakeji a xcryrta shiyasaka tadenajin radadin ciwon abunda aka mata jiya sai bata tsaya duba yawan rashin adalcin da mrs haseena tamata ba da tunanin yadda Allah zaidubi nata reaction din aranta tahau yi makanta hisabi.

dakyar ta mike tabar tunanin snn tahau shiryawa cikin gogaggen uniform dinta dayake mata wani irin kyau within 30 minutes suka fito ita da layla duk jikin nur firdaus din a sanyaye sam zucyarta baya mata dadi dan hatta layla bata gane kanta ba har suka fito waje suka samu malam liman harya fito musu da mota domin tafya mkarnta.

as usual nur firdaus ta rusuna kadan cikin girmamawa ta gaishe da drivernsu malam liman ya amsata da fara'a, nan da nan layla tadauke kanta tay kamar hanklinta baya wajensu dan bata son yawan gaisuwa.

da fara'a malam liman yabude musu mota nur firdaus ta zauna agidan gaba tare da jingina kanta akan seat tanata tilawar karatunta acikin zuciyarta har suka kai makarntr bata lura ba saida layla taja wani numfashi me shegen karfin daya kusa razata " Yaa nur kiga ikon Allah yau za'ayi emergency assembly am very sure wani abu mummunane ya faru..

nur tay saurin daga kanta sama tana mai duban windon motar
batace komi ba tana observing Duka duka abunda ke faruwa can saiga wata mata da tawagarta a tsadadden mota sun taho tana hura hanci kai tsaye sun wuce offishin shugabar makarntar.

Ayayin da Nur Firdaus da Layla suka sauka kasa tare da sauran ɗalibai sun lura cewa akwai wani irin yanayi na tashin hankali.

dan Gaba ɗaya makarantar ta cika da kananan ƙorafe-ƙorafe da kuma hayaniya wanda bai saba faruwa ba.

suna gab da shiga aji, sai wata sanarwa ta fara fitowa ana kira ga dukkan ɗalibai da malamai su hallara marmaza a filin taron asmbly da alama za'ayi wani gaggan taron gargaɗi.

nan sukaji mai gadin makaranta yana jan tsaki yana cewa Wannan abu da akeyi yau akwai matsala Allah de ya kyauta.

Nur Firdaus ta kalli Layla da dan mamaki, amma ba tace komai ba. Layla kuwa tana jin wani irin mugun nishaɗi a zuciyarta, kamar tana jin daɗin ganin tasowar rigima.

nan da nan kowani dalibi ya isa pavilion nayin asmbly aka jeru yau kowa ya hallara cikin nutsuwa dedeku daga cikin wasu ‘yan mata da samari suna tayin surutai kasa kasa suna zargin akwai wata babbar matsala data faru a ss2b..

cikin haka saiga nan shugaban makarantar gabaki daya wato Dr. Malam Ahmed Yakubu nan wajen yay wani tsiittt, ya taho cikin shigarsa ta alfarma da kamala yasha farar shadda me tsada yahau saman pavement din ya tsaya tare da duka membobin kwamitin ladabtarwa wato Disciplinary Committe ko ince  DC

A gefensu wata shuumar yarinyace da aka fisani da Malika sa'id tana tsaye idonta cike da hawaye amma fuskarta na nuna  taurin kai da tsaurin ido. nan Akasa ta durƙusa a gaban ɗalibai gaba ɗaya.

shugaban makarntar Malam Ahmed Yakubu dake kallon ɗaliban duka da daurarren fuska yace
"Ku saurara! A yau mun taraku ne domin mu koya muku wata darasi mai muhimmanci. ya nuna  Malika, yace wann ɗalibar SS2 b ce, wacce ta kasa kiyaye martabarta kuma yanzu haka mun tabbatar cewa tana da ciki batare aure ba, wanda yazama abin kunya ga wann makaranta mai daraja da kima.

Malika ta sunkuyar dakai tana hararar kowa bakinta na motsawa kamar za ta ce wani abu muryan Malam Ahmed Yakubu ya dakatar da ita cikin jawabinsa yace "ICICE Academy ba makaranta bace da za azo mana da wasu shashanci har arena darajar tarbiyya da koyarwar Musulunci. dan haka Mun yanke shawarar korar Malika daga wann makaranta nan take, donta zama izina ga sauran yan mata. da maza, Kuma muna so mu ƙarfafa misali ga kowa kowane ɗalibi daya zama mai tarbiya da hali irin na nitsatsu daga cikinku, babban misali itace  Nur Firdaus haroun please where is she, can she come up???.

jikin nur firdaus take ya dau rawa amma dake tana da karfin zuciya hakanan ta sunkuyar dakanta kasa snn ta fito tana tafiya ahankli gabanta na faduwa sosai har takai saman asemblyn cikin sanyin jiki.

lkcin ji take kamar zata nitse kasa dan fargaba, dan kuwa idon kowani dalibi da malami na akanta kirjinta yana bugawa da balain kamar zai ballo waje

shugaban makaranta ya nuna nur firdaus agaban kowa yace ita ce wacce koyaushe take zama abar koyi ga kowace ya mace a wannan makarantar.

tun daga ambatar sunan Nur Firdaus da yay sai gaba ɗaya ɗalibai suka fara surututai kasa, Malika tuni ta dago ido da sauri fuskar ta cike da ƙiyayya datake kallon nur firdaus din dashi.

Layla kuwa tana tsaye daga nesa tana kallon yadda ake yabawa tarbiyan ‘yar’uwarta a fili tanata murmushi a fili amma a zuciyarta kamar ana zuba mata garwashin wuta haka ta dingaji

daga gefe guda mahaifiyar Malika ta fito tana wani irin huci tareda tawagarta da kuma Malam ibrahim dake shugabantar guidance and counseling session na makarantar.

duk binta da case din a mutunce da sukayi taki sam sabida ita macece mai matukar ji da dukiyarta, tun tana tahowa tawajen cikin fushi takejin abunda ake fada akan nur fidaus,ga yarta malika nan akasa tay kneeling agaban kowa

jitay ranta na wani irin kuna dan Ita mace ce mai alfahari,iko da  arzikinta duk dama bata da kyakkyawar tarbiyya ko kunya dan haka bata ganin aibu akan abunda yarta ta aikata. isowarta wajen asmblyn keda wuya ta  fara daga murya cikin hargagi da tashin hankli tana cewa "Wannan wace irin hukunci ce? A ina aka rubuta cewa idan yarinya ta samu ciki shikenan sai a wulaƙanta ta haka? Kun ɗauki wann munafukar dalibar ta nuna Nur Firdaus da yatsa cikin zafin rai tace kunsata agaba kamar wata mala’ika kuna yabata agaban kowa,..wai har yata ce za'a yi misalin rashin tarbiya da ita tou in sha Allahu watarana za kuga abin da zai faru da naku yayan kuma munafukai mts.

Daga nan ta juya da azama tafizgi takardar korar ‘yarta daga hannun Malam ibrahim wanda malam bello ne ya mikamai ta jawo hannun malika snnn ta dubi Nur Firdaus kai tsaye, idonta cike da ƙyama.

nan ta nuna Nur Firdaus da yatsa tace ohhh waikece me tarbiya ko, toh Idan har rayuwa tana da adalci, kema wata rana za ki san ciwon da Malika ta ji a yau. Wallahi, tallahi sai kin ci karo da abin da ya fi haka muni! munafuka kawai. matsamin mtswww.

malamai mata dayawa suka dau zafi suka amsa amma ko kulasu batay ba ta fizgi hannun Malika, suka fice daga filin taron suna haki da fushi..

malam bello  yafi kowa daukar zafi daga Dc comittee shine ya dada tsawatarwa wa dalibai sosai, yace sun yi ma malika haka ne a abayyane badon su tozartata ba, sede dan sun tsorata duk wata yarinya datake ganin zata iya dauko musu wani abun kunya da zai lalata musu darajar makarantarsu.

mafi akasari yay misali da dabiar nur firdaus akowani kalmansa musmn inda take kama kanta snn yayiwa dalibai nasiha sosai saida jikin kowa yay sanyi

Bayan taron ya watse nur firdaus na tafiya da sanyin jiki zataje aji nan wasu ‘yan mata daga cikin abokan Malika frm no where suka biyosu wata kusurwa wanda kallo daya zaka musu kasan suna cike da matsanancin haushin ta aransu sosai.

wa Layla suka fara magana amma Layla tanuna kamar ba ta ji su ba duk dama aranta tafara jin daɗin yadda wasu dalibai suka fara tsanar ‘yar’uwarta sabida abunda ya afku ayau.

Wata daga cikin kawayen malika ta dauki ruwan gora ta watsa ma nur firdaus a fuska, snn tace bada sallama nazo miki ba
Ke wato kin fi kowa tarbiya ko? Kina ji da daurin gindi a cikin makarantar nan toh wallah wata rana ke ma sai kin samu cikin shegen nan kuma wallahi naki tozarcin zai fi na Malika muni!"

Nur Firdaus ta tsaya cak zuciyarta cike da rauni da takaici amma Batayi musu magana ba sai dai ta juyo a hankali tanata kallon su da idon da ke cike da rauni sosai.

Layla kuwa tana tsaye a gefenta tana dan boye murmushin mugunta tana jin yadda kowanne kalma da suka gayawa nur yana sauka a kanta kamar sakon albarka.

a zuciyarta tace uhmm Haka nake so atleast yaa nur tafara samun makiya kuma ai sai an ƙi tane kafin in samu damar da nake so nima."

duk zagin da yan matan sukayi Nur Firdaus taki cewa komi kawai tawuce tabar wajen duk dama zuciyarta tana cike da damuwa da rauni Shin dagaske rayuwa za ta iya juya mata baya kamar yadda kowa yake furtawa?....

tadauki lokaci me tsayi cikin jin raunin dukkan abubuwan dake faruwa dakyar ta iya danne komi tayi abunda ke gabanta dan yaune zasu karbi ticket da kayan zuwa gasarsu da komi da komi..

************

dagata dayan bangaren bayan mrs Haseena ta bar gida harkokin siyarsata ne suka kuma shamata kai inda tuni harta watsar da komi ta cigaba da zancen matsalar ummi suna tashige da fice. karshe dai ynxun tana shirin dawowa da ummin abuja ne dan asata cikin ajerin help desk na humanatarian foundation din uwar gijiyarta wato hajiya mairam kanem shehuri yau kusan din kusan kominta na tafiya mata adede

atacan gefe kuma matashin mijinta wato Sadat yana tare da babban abokinsa a club yana famar buga sharholiyarsa dake wajen kamar private club dinsu ne dayake cike da hayaniya koyaushe sautukan kiɗa suna tashi sama sama kuma hasken wutar lantarki na yawo cikin launuka daban-daban.

anan suka kwana suna tashi aka cigaba da sharholiya, karfe 10 na safe Sadat yazauna a wani ɓangaren nesa da hayaniyar inda abokinsa Usman ya taho ya samesa da red wine glass a hannunsa yana fmr kurbewa ahankli, dukansu gayu ne iya gayu dan daga ganin siffarsu da ajinsu bazaka taba tsammanin cewa ba yaran manyar kasa ba ne.

Ussy yana murmushi, yanamai daga gilashin giya a shashance yace "Kai Sadat kaga yan mata kuwa inaga Wnn ranan namune fa

Sadat yay dariya dan kadan snn yace "Ba fa don ina jin daɗin jikina na zo nan ba ussy kaima kasani..

ussy ya dafa kafadunsa to meye

kai tsaye yace Akwai maganar Haseena da waɗannan 'ya'yan nata da nake so mu tattauna dakai amma jiya duk baka saurareni ba.

ussy yace i am sorry mehn yanxu de ina jinka what is going on with them??? haseena ta amince zata haihu makan, kai da nace maka ka zuba mata guba kawai tasha ta mutu amma duk kaki sabida tsabar tsoro

Sadat ya dan kwantar dakansa a kujerar yana ɗan tsiyayar giya daga cikin gilashin da aka ajiye masa. Bayan dan wani lokaci na shiru nan da nan ya fara bayyana wa Usy abin da yake faruwa Yayi magana game da yadda Hajiya Farida bala tabashi umarnin yayi amfani da Layla wajen rusa mahaifiyar ta, msmman ta hanyar ƙirƙirar matsaloli da rikici daga cikin gidan.

tun yana maganan Ussyn yafara gane cewa kamr sadaat bai damu da Layla sosai ba asali Zuciyarsa tana sha’awar Nur Firdaus ne wacce yake ganin ta fi Layla kyau da hankali.

Sadat yana maganan cikin furzar numfashi  yace Ina son ganin yadda wnn lamarin zai kasance min amma idan ina son wata host daga cikinsu, to ba layla bace Nur Firdaus ce nake tunanin zata fi dadin wann wasar, ita layla tamin karama, gata da  budadden ido she is kind of too desperate kagane ko??? nafison wacce bata son abun dan itace zatafi tsorata dani sosai and it will soo much fun

Ussy yatsare Sadat da wani mugun shuumin murmushi, yana jin tsananin sha’awar tayar da wani sabon rikici.

"To, idan haka ne abokina me yasa ba ka yi amfani da damar ka ba? Ai kai kake da iko a gidan yanxu, Sai ka fara motsa jikin kowaccensu a hankali da hankali kagane ko?

Sadat ya kalli ussy yanamai girgiza kai
hmm Kai fa da kake magana wallh baka san yarinyar bace. ba tama shiga harkata inbawai wani abu serious bane ya shiga tsakaninmu. amma ita layla har biyoni take da jikin nata ,kawai de Ina so inga Haseena ta lalacene ne sosai amma badon haka ba da saina san yadda zanyi da kyawawan yarantan nan dukansu biyu a lkci guda saina tarwatsu inyaso kome zai faru ya faru.

Ussy yana gyara zama yabi ya zuba mashi idanu hmm abokina cocaine din nan yahau kanka amma de kay a hankli, ka kuma ji shawarata wannan ne damanka da zaka samu abunda kake muradi har wajen hajiya farida bala, kadai yi tunani me kyau akan qudirinka ina tabbatar maka cikin sauki Zaka ga Haseena ta rushe daga gida har waje."

Sadat ya yi tsit yana tunanin maganar Ussy A zuciyarsa yana jin yadda zuciyarsa ke motsawa da tunanin yadda zai cimma babban burinsa akan Nur Firdaus amma a lokaci guda da yar uwarta layla wanda baisan ta ina zai fara ba amma kuma Ussyn yaci gaba da bashi tabbacin nasara tare da cusa masa  muguwar shawara akai.

Ussy yana kallon shi da murmushi mai cike da mugunta "Sadat just man up ka tuna cewa wnan tafiyar siyasace takarshe ga Haseena. Kai dai ka yi abin daya dace kawai Kuma kasan cewa idan ka yi wa yayanta duka biyun kamar ka kasheta ne a raye.

Sadat ya yi wani ƙananan murmushi mai cike da rudani, yana shan giyan cikin gilashinsa baice komi na.

ussy ya ci gaba da jefa masa maganganu daddaya da suka hau cike zuciyarsa.

cikin tunani yana yin murmushi yace  ma ussy toh naji Watakila hakane hanyar billewa Amma dai zan fara abun a hankali Ba zan yi gaggawa ba."

Su duka suka fashe da muguwar dariya me sanyi zuciyarsa ta cika da mummunan tunani game da makomar Haseena da 'ya'yanta musman ma Nur Firdaus da yanxu yasoma jin karfin gwiwa akan ta.

bayan kwana biyu......

coment and share pls

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top