EP9

*NUR FIRDAUS....9* _Arewabooks@surayyahms._

#2024/2025

suna tsaka da jin dadinsu saidai karar waya dake famar ruri agefensu gabaki daya yafara hanasu samun nitsuwa, jim kadan hon farida Bala tadan ture saadat ajikinta da bacin rai tamika hannu tajawo wayar wanda kallo daya tay masa taga 25 miss calls daga PAs dinta da agent na siyasarta a kano..

kirjinta taji ya dan buga amma tsaki taja tadauka da karfin hali takara a kunnenta cike da giggiwa kai tsaye tace wai meye haka ake ta takuramin da kira kamar hanjin mutum na dauka?..

dan shiruuu tay tanamai saurarar abunda ake fadi ta daya bangaren saidai batace uffan ba, can takatse wayar ranta a mugun dagule tajawo wata arniyar silky  throbe dan dede  tarufe jikinta dashi, bayan nan atake take tasauka agadon ta dira kasa tanamai huci tare da daddana wayarta cikin tsananin tashin hankli da bacin rai cikin kuma sauri sauri, cewa take i knew dis will hapen.. hmm haseena sharrif kenan babban makira shegiya kariyar siyasa

sadaat dake kwance shataf yana kallonta a mamaknce yakasa gane mata cikin kyabe baki yace "mummy lfya kuwa? meya faru naga hankalinki ya tashi?..

farare sol din hannu kawai tadaga masa snn ta mugun hade rai a mugun dake ta kallesa snnn tace
"kai!!! ka tashi kawai kasaka kayanka ka fice min agidana dan baka da amfani kwata kwata, yoh amfanin me kakemin, ga can haseena a kano taje da tulin rundunar mutanenta tanata kkrin rushe min nawa siyasar acan tanamai tallata na abokiyar takarata da karyan data shirya wai live show bayan duk munsan makrci ne dan asamu kan talakawa thru her god damn emotional block buster programes,... haseenar nan shegiya ce azzaluma in aka toshe nan ta bullo tacan..see just get out kawai, i need to be alone right now zuciyata kamar zai fashe haka nakeji huuhhh huhhhhh.

kansa a mugun daure cikin rashin jindadin kananan maganganuntan yasauko kasa da guntun wandonsa ahannu baiko kalleta ba sabida wani irin harararsa takey da tsananin baqin cikinsa aranta, da har zai yi  magana ta wurga masa wani kallo cikin dakamai tsawa tareda tsananin jin haushinshi tatsaresa,

"sadaat kafita kawai. banason nagaya maka wata maganar da harka mutu bazaka manta ba "meye amfanin auran dana maka da haseena ehh? gindinta kawai nace kaje kaci cant u keep her away from all this??? sam bakay amfani da brain dinka ba, da ace ka iya takunka da tuni ka iya daukemin hanklinta daga harkan siyasan nan haba da Allah sai kace ba namijin dana raineshi da hannuna ba?..

da wani irin zzafan frustration take masa maganan cikin masifa tana diri sosai duk
kaikake jawomin koma baya a harkan siyasata, sadaat u cause dis mtsss sam baka cika namiji ba, i gave one simple job to do.. marry dat bitch and screw her, amma haryanxu nadaman aura maka haseena sharif kawai nakeyi, dat evil slut haseena sharif is getting on my nerves.. toh wallh dukanku daga kai har ita baku san wuta ba saikun taka dani farida bala ake ja..

sosai ransa yay baqi kirin da yadda take nuna masa kamar bai taba mata kokri ba amma baice mata komi ba yagama saka kayansa zaifita tawani rikeshi tanamai balla masa wasu munanan harara

cike da takaici ta dau waya tawurga masa ajikinsa tana mai cewa bangane ina magana kamin shiru ga yar iskanka ko?

ransa a harde yace mummy ni club zanje

wani irin mari takai masa abazata "wato ma zakaje club kasha giya ni ka lalalata min komi ko, toh babu inda zaka, u will "fix dis.. ga waya nan ka kira dukka yan jaridun mu a kano kabasu kudi konawa ne sumin aiki mekyau awajen taron da haseena zatayi yanxu, sumata wasu irin munanan tambayoyin da zai jawo hanklin jama'a akan makricinta..

karbar wayar yay adan fixge baice mata komi ba yafita dashi yana kukkuni tabi bayansa da wani irin kallo mai zafi me tafe da takaici

...wani tukukin tsaki taja ta bude drawer ta dauko hodar cocaine ta zuba kadan akan table tare da zubewa agabansa ahankli ta fara shaka saida taji yaje har cikin kwakwarlta

******
Ata daya bangaren daga mallam Aminu kano intl Airpot kano da misalin karfe 8:00 am dede nasafe nan take filin jirgin ya cika da hayaniyar manya manyan yan jarida da masu watsa labarai
ayayinda da jirgi me dauke da tawagar jaijtacciyar yar gwagwarmarya Mrs. Haseena Sharif wacce takasance wata gwarxuwa kuma shahararriyar mai fafutukar kare hakkin jama'a ta bayyana a garin kano domin zantar da live show a wani shiri mai taken "ina Adalci Ga Mata da Yara??..

live show ne da ake iya watsawa kai tsaye a gidan kowanne talabijin afadin nigeria daga bakin mai ita, wanda Taron ya karkatane a kan batun cin zarafin jinsi musmn na mata (GBV) akan wani sabon al'amari mai tayar da hankali dayake faruwa a kano state kai tsaye

yanxu lokaci ne na ganganmin yaqin siyasa dan haka mrs haseena shareef ta jajirce sosai wajen fidda salo salo na makircin siyasa tare da ganin tasamu shigar da sunan uwar dakinta hajiya mariam kanem shehuri me neman kujerar takarar ministan jinkai nakasa gabaki daya a xukatan talakawa batare da ta nuna a haka a fili ba.

tunkafin jirginsu daya taho dasu daga abuja yasauka a kano tuni manyan jami'ai data gayyata daga hukumomin kare haqqin dan adam kamarsu amnesty, Unicef, kano state ministry of women children and disabled, Citad, NHRC, IRC da kuma UNFPA ta kano duk suka hallaro.

saukowar mrs haseena sharif kadai ma abun kallo ne dan atsakanin kyaun sura da iya daukar wanka tare da confidence din dake tafe da mrs haseena bansan mezance yafi daukar hankalin jama'a ba.

dake hukamar human right na America ne ta dau nauyin shirin yasa tataho har garin kano da english wear wato peach versace suits dinta daya wani irin mata masifar kyau kai bazakace takai maka shekaru arba'ain da shida a duniya ba. saukarta ke da wuya kenan jami'ai tare da yan jaridu kala kala suka yanyaneta kowa na kkrin tofa iyakan albarkacin bakinsa akan shirin da tazo zantarwa wanda abune wanda basu sabayi a kano sosai ba.

Cikin nutsuwa amma da takaici Mrs Haseena sheriff ta fara jawabi tana cewa "kowa ya kwantar da hanklinsa, Yau mun zo nan ne domin tattauna wani abin da nasan zai girgiza zukatan al'umma. munsami labari cewa Yarinya 'yar shekara 13 mai suna Ummi ta fuskanci abin da babu wata yarinya da ya kamata ta fuskanta a rayuwarta. Wannan yarinyar an zalunce ta, an karya mata zuciya, kuma mafi muni, mahaifinta ne ya aikata wannan abin kunya...dani da mabiyana zamuyi iya bqin kkrinmu domin muga mun ceto ummi daga wann ukubar.

tambya ake jefa mata kota ina amma Mrs. Haseena bata kula ba ta cigaba da magana da karfi da kuma karfin zuciya Mun taho kano ne don tattauna yadda za mu dakatar da irin wannan zalunci a cikin al'umma. Ba zamu yarda wannan abin kunya ya zama ruwan dare ga mata ba.

sauran manyan mata mabiyanta da suke gudanar da aikin social activist din tare nan suka fara mata amshi in atare suna daga muryoyi.

wanda zuwansun sosai ya mugun daukar hankalin jama'a kai tsaye ita da tawagarta da jamian suka kama hanya zuwa wani anguwa dake cikin wata karamar hukuma a kano inda akaje har gidansu ummin aka fito da ita sarari snn aka fara fitar da bayanai kai tsaye daga bakinta, tare gabatar da shaidun abin da Ummi ta fuskanta live da kuma yadda za a dauki mataki kan mahaifinta daya mata fyaden shima wanda yanzu haka yana hannun hukuma...

Duk abunda akeyi kai tsaye ake nunasa agidan talabijin honourable farida bala ta gama kilewa da kwaya tana kan kallon haseena a tv tana kan dura mata ashariya manya manya.

misalin karfe 2 na rana Daga gidansu ummi aka wuce Dakin taron dake ministry of women children and disable na kano state wanda yana cike da jajirtaccun 'yan jarida, kowannensu dauke da littattafan rubutu, na'urorin daukar sauti, da kyamarori, suna jiran su tambayi Mrs. Haseena Sharif tambayoyi masu zafi. A gefenta, Ummi na zaune cikin nutsuwa amma da tsoro, tana makale da hannun Mrs. Haseena lkcin ko kanta bata iya dagawa

Bayan Mrs. Haseena ta kammala jawabin ta na farko mai karfi, nan take wani sanannen dan jarida mai suna Ibrahim Yusuf ya fara magana cikin muryar tambaya wanda daga ganinsa kasan shima hayansa akayi yace "ranki dade Mrs. hasena Sharif, kina bayyana wannan lamarin ne a matsayin fafutukar kare hakkin yara, ko kuwa wani kokari ne don inganta yakin neman zaben shugabar ki, Hajiya Mariam Kanem Shehuri, wanda ke neman kujerar ministar Abuja?"

Mrs. Haseena ta gyara zaman ta da murmushi sannan ta dubeshi da fuskar dake nuna karfin hali. tace " kusaurara, zan yi magana a sarari. Wannan batu na Ummi ba ya da alaka da kowanne irin tsari na siyasa. Batun kare yara daga zalunci da cin zarafi wajibi ne da ya wuce kowanne tsarin siyasa. Ko da kuwa ba ni tare da Hajiya Mariam Kanem Shehuri, zan tsaya tsayin daka don ganin an yi wa Ummi adalci."

Wata yar jaridar rataye da id card ansaka suna Fatima ajiki tadaga hannu tana tambaya cikin muryar zargi.. "hajiya haseena Amma akwai wata tambaya mai  mahimmanci, nace, Me ya sa sai yanzu ne aka fara watsa wannan maganar kai tsaye, alhali irin wannan cin zarafi ya dade yana faruwa? Shin kin yi shiru ne har sai lokacin ya dace don amfanin yakin neman zabe?"

Mrs. Haseena ta yi ajiyar zuciya,sannan ta ce cikin natsuwa
"malama, wannan abu ya shafi zuciyar kowa. Babu lokacin da ya fi dacewa don nuna gaskiya da neman adalci. Ba zan iya zura ido na ga yara kamar Ummi suna fuskantar irin wannan zalunci ba. Lokacinmu ne yanzu don mu tashi tsaye."

nan wani babban dan jarida frm no where ya bullo mai suna Ahmed  yayi magana cikin harshe mai zafi da karsashi kai tsaye ya miqe abainar jama'a yahau cewa "Amma gaskiya akwai babban shakku ga gudurinku  Shin kina ganin idan ba Hajiya Mariam ce ke takara ba, har yanzu ke zaki dage kan wannan al'amari haka? Kila kawai kuna amfani da halin Ummi ne don cimma burin siyasarku."

Mrs. Haseena ta dube shi kai tsaye tana dan murmushi mai nuna jarumta tareda nuna fahimtar inda ya dosa
tariga ta goge a wajen iya toshe caccaka da kuma farmaki daga yan jaridun dake aiki wa makiyanta, tana kan murmushin tace dan jarida kenan shin da gaske kake kayi mamakin irin wannan zargi?? Ummi ba wata alamar siyasa ba ce, ita fa mutum ce, yarinya ce da aka zalunta. Wannan batun ya shafi rayuwarta, ba wani yakin neman zabe ba. Zan yi kowane irin aiki don tabbatar da cewa ta sami adalci, ba tare da la’akari da wanda ya tsaya tare da ni ko wanda ya saba da ni ba."

Sai kuma 'yan jaridar suka fara magana da juna wajen ya fara rikicewa nan Mrs. Haseena tamike tsaye ta rike hannun Ummi dakarfi tanamai nunawa al'umma..

"ummi is a symbol of justice to all mothers, sisters, and the society, a woman derseve to be protected..give her the freedom, her right as a women count.. dan haka Idan kun gama tambayar ku game da siyasa, ku tambayi Ummi yadda take ji aranta yanxu Saboda ita ce wannan labarin ke da shi baku ba..

wani irin tsiiiit wajen yayi ayayinda Ummi ta kalli dakin da ruwan idanuwanta da suka cika da hawaye, tana juyawa wurin Mrs. Haseena don samun kwarin gwiwa idonta acike da hawaye yana sauka ahankli tace
"madam Dan Allah nide Kutaimakamini....

Wannan kalami ya sa wani shiru ya mamaye dakin sosaiii yanamai barin tunani mai zurfi ga duk wanda ke wurin.......
SHARE PLEASEEES

SHARE UR COMENTS
AND VIEWS VIA COMENT SECTION

JAXAKALLH KHAIRAN
SURAYYAHMS 08060712446

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top