EP7
*"NUR FIRDAUS...7*
*_Arewabooks@surayyahms_*
Atakaice iya subject din daya rage musu kenan na ranar sai kuma gobe da safe kawai suke da ita shikenan sun gama litreture na satin. wnan yasa suna fitowa a ajin kowa yafara kokarin tafiya gida wasu already drivernsu har sunxozzo daukarsu kowa ya kama gabansa.
kusan al'adace wajen nur firdaus kullum dai ita take fitowa a karshe, yau dinma saida kusan kowa yabar ajin snn ta fito tana rungume da wasu takardu a kirjinta da hannu daya dayan hannun kuma tana rike da hadadden wayarta ƙira samsung tana dan waige waige kamar me neman wani abu sai kuma tafara tafiya a hankali tamkar mai jin tsoron taka kasa aranta tana Allah Allah yar uwarta laylah ta billo.
Daga can gefe inda yara maxa ke taruwa tafara hango yadda daliban ss3 suke fitowa daya bayan daya. nan saiga Abdul din ajinsu da gangs dinshi sun fito acikin salon takama, abdul din yariko wata expensive drink agora yana sha yanadan lumlumshe idonsa cike da jiji dakai yana tafya kamar zai huda kasa.
Dagangan yayotanan waidan ya kashe mata warning akan baqar maganan data masa aji dazu, cewa datay "she cud use his empty brain when she lost hers" dan shi haryanxu bai manta dariyar da akayi masa ba waiyau harshine mace macen ma yar arewa doter of aboki zata alaƙantasa da mai empty brain? ransa a mugun dagule ya danyi karamin tsaki.
Bazaiyu Haka kawai ta tazubar masa da aji a cikin mutane ba dan duk friends dinsa sunsan shi daga lagos state aka mai transfer acan din ma shi topper ne Banda aiki daya kawo babansa nan garin abuja da babu abunda zai hadashi da karatu a arewacin nigeria dan mahaifyrsa ma cikakkiyar yar Anambra state ce both jinin yaruba da igbo ne yake yawo ajikinshi
yaudinma shida gang din abokansa suka tsaya ajikin motarsu ya zuba mata ido yanata kallonta harta fito sarari, ta danyi dube dube sannan ta taho direct tana tafiya a hankali tamkar mai kirga takunta wanda hakan ya bawa dukkan mazan dake wajen damar karewa siffarta kallo.
Kusan ince babu wanda bai santa a schl din ba but she is too calm and too beautiful for their own thug life level, kuma dake kowama yasan wanda take soyayya dashi, duk suka zuba mata ido Har tazo ta wuce grp dinsu su biyar bata ko lurama dashi a gurin ba..
Laylah dake tahowa acan abaya tafara lura dasu kirjinta taji harna bugawa haka taxuba ido akansu subiyar din ganin kaf dinsu babu dan gidan talaka acikinsu. infact They are the Five flower boys of the schl, gang dinsu na da wani irin karfi dan tsabar tantiranci da jiji dakansu har wani shakkarsu akeji dan duk suna jan motoci ne masu shegen tsada ga kyau ga iya wanka ga karatu duk dama yara ne amma kusan sune big boys na makarantar.
Abdul, fahad, prince, abal da imran..cikinsu babu wanda mahaifinsa bai shahara a abuja ba kusan yarane da suka gagari uban kowa a makrntar dan kusan kowani wkends suna haɗa boyayyar night party da mates dinsu yan mata ayi ta tabe tabe da shaye shaye.
Laylah na tahowa can baya haka kawai tafara jin numfashinta na hauhawa ganin yadda dukakknsu su suka zubawa yar uwarta nur firdaus idanu suna kuma tattauna magana kasa kasa wanda ko kasheta za'ayi tasan hala akan kyaun nur firdaus ne.
Dan rage takunta tay ganin kamar sun ba da nur din damane tadanyi nisa sannan suka fara binta da dan sauri like a typical nerds they are..
sangartaccen cikinsu Imran ya karkata kansa yanamai cewa "Hey grumpy girl" yaga ko kulawa batayi ba...Abdl din ne ya wani hade rai yace "keee" dake ake
..nur ta dan tsorata kadan ta juyo suna hade ido dashi ta dauke kai ta cigaba da tafiyarta dan tasan basa magana, nan Akabarsu da binta da huci wanda daga ganin irin kallon da suke mata zakasan akwai wani abunda ke ransu game da ita.
daya daga cikin abokansa Fahad ne da dalibai ke mugun tsoro a makarntar ya kasa hakuri yabi ya daidaita takun shi dai dai da nata yace sssss "ke ji mana..", nan ta dakata tanata kallonsa cikin ido batare da ko alamar tsoro ba saima ce masa "Assalamu alaikum datay
..kallonta ya dinga batare da ya amsata ba
"how can i help? Yadda tay maganan a nitse yasa ya dan shafa kansa yana jin duk karfin izzar dayake ji dashi din yana neman draining msmn yadda ta dake tazuba masa idanunta has already makes him much uncomfortable yariga ya saba yan mata in sungansa agabansu 'barin baki kawai sukeyi ko sufara kuka kai tsaye.
Jin bai amsa sallamarta ba yasa ta sauke idonta kasa ta cigaba da tafiya wani irin ciza labbansa yay yasake shafa kansa ganin yakasa mata magana sai can yace "ohh God, this is embrassing. Why isnt She not like any oda girl" Daga nan shima ya juya ya tafi.
Laylah dake tahowa abayansu taji mugun dadin abinda ya faru ganin nur firdaus bata kulasu ba, daf fahad zai wuce Dagata bayanshin yaji tazo tawuce shi da sauri tana kira..
Big sis, yaa noori!! Wait for me".
Cak nur firdaus ta tsaya tana jiranta harta karaso cikin sakar ma junansu murmushi me sanyi suka gaisa sannan suka cigaba da tafiyarsu tare.
fahad yana satar kallonsu yanakan ciza labbarsa yace "Fuck!!!!! dis is damn embrassing ya maimaita yana matsa labbarsa, yana isa gabansu abdl yace wai me wnn yarinyar take daukar kanta ne kodan taga tana soyayya da Adnan dan gidan minister of Abuja?
Abdl yace 'i dnt care, is high time we look for a way to deal with her tunda ma ai zamu bar makrntar. sai kuma ya hau kan car dinsa ya samu guri ya zauna ya lumshe ido yafara lissafa musu hanyoyin da zasu bi..
Dagata can bangaren Kuwa Suna tafiya nur firdaus ta juya kan yar uwarta tana kallonta nan take taji maganganun Malam ibrahim na dawo mata ranta..
kallon laylah dake faman murmushi tay ayayin da takemai satar kallon su Abdul oyebanji cikin katseta nur tace laylah yau wani subject kukayi a ajinku Kingayau i have enuf time Adnan ma baya gari sai nakoya miki wasu abubuwan in munje gida ko???
Cikin turo baki laylah tace sis its english kuma na iya sosai..da sauri cikin son kaucar da maganan cikin hanzari tace uhmhmm big sis wayncn manyan yaran ke wai suke bi ne??? Naga kmr dayan ma har yamiki magana dazu..
tunkan nur ta amsata taji ankwala mata kira ta juya nan suka hada ido da babban kawarta Jadidah ahmed kawarta ce tun suna primary suka hadu lokacin suna yara sosai tare da wata Aisha omar saidai mode of life dinsu ne yazo ya dan rabasu da suka girma musmmn ma da daukakan yawan karatun qur'ani da kuma yaduwar labarin soyyar nur firdaus da adnan shehuri dayayi suna ya fito sarari.
...nan nur firdaus Tayi mata murmushi lokacin Jadidahn ta karaso suka jera suka cigaba da tafiyarsu a tare Laylah dai batace komi ba.
Jadidah tace "kawata yanxun nan akace min su Abdl da su fahad sun tareki.."nur ta kyabe baki tace "eh kamar haka, what about it?"dariya jadidan tay tace "kawai dai nasan baki magana da yan iska irinsu ne keee wallh bakiji badalar da sukayi a wekdn din nan bane cos one of ur class mate farida wata tana da manyan boobs haka toh yau batazo schl ba anata rade raden cewa jiya agurin night partynsu is like they have gang sex with her dukansu su biyar din
Kusan atare nur Firdaus da laylahn suka kwalo ido waje tare da cewa whaat??? Da Rawan jiki da kuma sauri laylah tace tell us more, so how does it happen hmm dama daga ganin faridar can tasan maza
jadidah na shirin budan baki Cikin lumshe ido da budewa Nur firdaus ta katseta da cewa ya isa haka jadidah. Ta juyo nitse cikin lumshe ido "keeee kuma laylah are u insane? badai gulma ba..toh kar na sake jin wann maganan abakin ku. Ku tuna fa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace _"Fal yakun khairan auli yasmuut"_ kafadi alheri ko kayi shiruuuuuuu. cikin taushin murya tace so please..lets not yab this dirty shit kawai de muyi fatar Allah ya shiryesu mukuma ya karemu daga aikata ba dede ba.
Dukansu suka tsaya kallonta baki a bude sai can jadidan tayi dariya tace shikenan Ameen, dama ai it wasn't such a good talk. Kedai make sure that guy is not going to talk to you again. Dan duk wacce ta tsaya dasu baa mata kallon virgin yanxu.
Tace Well i dont think he will. Nan ta dan tsakura musu labarin abunda ya faru ajinsu suka yi dariya baki daya dan jadida tana ss3B ne ajinsu da nur ba daya ba.
suna cikin tafiya nur ta dafa goshinta tace wayoo Allahna na manta ban ajiye lettern nan a office din malam bello ba...cikin rolling eyes Jadidah tace "ai sai mu koma...haka suka cigaba da tafiya suna hira laylah dai bata fiye yin magana sosai ba.
A haka suka je block din competition manager din suka hau step zuwa 3rd floor inda office dinsa yake suka kai masa letter after some minutes snn suka sauko..
haka jadida ta matsa suka sauka a gidansu dake baida wani nisa da schl din dan sai 2:30 oclk yawanci drivernsh malam liman yake samun isowa Sabida shine yake driving din mijin mum dinsu duk inda zaije shiyasa kusan kowani tashinsu a schl sai sunyi lattin zuwa gida msn in ADNAN SHEHURI baiya gari.
sunakaiwa gidansu jadida suka shiga a parlor duk suka zube a kan sofa saboda gajiya.
after a while jadidan ta fito daga kitchen dauke Da tray, layla ta zuba mata ido dan ita din black beauty ce, mai dan duma duman jiki da fararen idanuwa Kana ganinta zata yi maka kama da irin sangarttun shagwababbun yaran nan wadanda suka taso cikin naira..tana aje musu abincin tafara dariya tanacewa wato malam bello yaga Adnan bai rakoki wajensa kai letter yau ba shiyasa harma ya sake mana fuska akayi wasa da dariya da shi nasha mamakinsa wlhi.
Nur firdaus ta kalleta tace "kai JD amma baki da kirki Kawai de baku fahimce malam bello bane, shifa bawai crushing yakey akaina ba kawai de har adnan din ma gani yake he is not good enuf for me.. kallon yara yake mana wai bamukai muyi soyayya ba.
Jadida ta karkata kai gefe tace " so according to him nobody is good enuf for u, even adnan?
toh Amma Waye besan kalar kyaun tarbiyan da adnan yake dashi ba kowa so yake ace na adnan ne saurayin yrta ga kudi, ga gata, ga ilimi ga kuma nitsuwa beside Adnan is not even child he is 23 nd responsible.
agajiye Laylah ta dafa kafadun jadidah snn tace Hmm.."motive..!!! if i can't have her, then no one will... Nan da nan Jadida ta yunkura tayi pecking laylah a cheek dinta tana yar dariya tace "thank you my sister ashe kin gane, see dats exclty the point..kawai yaga shidin ya tsufane yanxu nur bazata kulashi ba shine yaketa kkrin hana adnan samun waje da wayo awon oloshi..
cikin kyabe baki laylah tace hmm sis JD wallh tsananin kishin big sis fa malam bellon yakeyi kuma kusan kowa ya ganosa amma sai yana wani makalewa da da'awa yana tsawa tsawa wai gashi uban yan tarbiya mtcheww
jadidah tana girgiza kai tace gashi babu ranar da xaiga nur da adnan atare bai yi wa'azi akan cikin shege a MSS ba nide wallh abun nadamuna dan nakasa gane inda malam bello ya dosa ...
Nur dake kallonsu batace komi ba for a while tana girgiza kai tanajinsu sunata fmr magana akan malam bello Who is actually another pain in her ass.
Shi ne kamar shugaban DC ( wato Da'awa chairman Disciplinary committe) he is also a religious extremist shi irin dan qa'ida da aqidah din ne yana da wani irin zafafawa da tsauri musmn akan lamarin addini shiyasa kusan kowa ya tsane harka dashi...
duk ilimin qur'ani da tarbiyan firdaus bai hanashi saka ma rayuwanta kahon zuka ba, daga an tabashi sai yace baison ta lalacene ai ansha samun yara masu kwazo irinta da lefin kauce hanya sabida bin samari..shine yasaka dokan cewa lallai kowa sei yakawo saka hannun iyayensa kafin aje kaduna wajen gasar qur'ani dashi....
Suna cikin cin abincin, wanda nur firdaus chakula kawai take kamar mai cin dole tana ta Allah Allah su gama su tashi....
wayrta ne yay ƙara tana daukawa taga adnan ne murmushi me sanyi ya kufce mata a kaykkwan fuskanta nan take ta mike tsaye ta koma gefe dansu sha soyayyarsu ayayindasu jadidan suka bita da wani irin shakiyar kallo sunata murmushi..
laylah Ta jinginar da kanta ahankli jikin kujera cikin tunanin zuci itade she alwys wish itace a matsayin da yayarta nur firdaus take musmn na soyayyrsu Da kyakkwan saurayintan nan Adnan shehuri.
*******
Dagata dayan bangare wajajen karfe 8.30 sharp hadadden matashin mijin mahaifiyarsu wato Sadaat ya sauka a inda zashi. wata sabuwar anguwace dake can can baya inda babu Wani hayaniya sai manya manyan gidajen zamani da ba asan suwaye ke yawan zama acikinsu ba
yawanci gidaje ne da yan siyasa kawai suka gina suka barsu sadaat yana sauka ya baiwa me abun hawa kudi baiko tsaya amsar canji ba kai tsaye yanufi gaban wata sharbebiyar mansion me wani irin tsayin gatanga da babban bakin gate ya ciro wayarsa a aljihu yanata daddanawa.
saida yaci kusan minti goma a gate kafin nan aka budemai ya shigo ciki. baice uffan ma security ba ya wuce ciki cikin wata dankarariyar falo dataji kayan alatu an kunna tv an kure volume anbarsa ahaka.
Dankareren photo album din wata babbar mace isashshiya ce manne da bangon falon dayay wani irin mugun kyau yana mai dauke idon duk wanda ya shigo falon kai tsaye dan bazaka iya dauke idonka akai ba.
matar dake kan hoto Farace soll ga kyau kamar sadaqa yalla tana murmushi fatar jikinta alrdy yariga yamurje takuma ji ruwan dukiya da kyaut tasaka wani irin jan kaya me tsada da daukar idanu Ajikin katon hoton aka rubuta
HON. HAJIYA FARIDA BALA.
Kallo daya matashin nan sadaat yay ma hoton ya dauke idanunsa akai tare da saukesu izuwa ilahirin tsakiyar palon gani yayi wajen a burkice anshasha strong energy drinks na motsa sha'awa da maganin karfin maza an barsu barbaje akasa
Wani irin danna hakwaransa yay akan labbarsa yanamai ciza Dan atake yaji ransa yay mummunan hargitsa ya baci yayi kamar zai shige cikin dakin dake kasa direct zuciya ta debesa harya daga kafa da wuri sai security ya dakatar dashi..
Yana ma securytin wani irin kallo.. security yace "sorry sir hajiyane tace duk wanda yaxo ya jirata anan palor dan tana da bako aciki.
cikin cizar labba akaro na babu adadi.. yace bako ko??? Security ya gyada mai kai, da kamar zaice wani abu sai yafasa acikeda fixga yakoma ya zauna akan chair din ya dora kafarsa daya bisa daya yanata huci shikadai ransa na mugun tafarfasa da ruwan kishi sanin cewa bazai wuce wani namijin take tare dashi acikiba...
#SURAYYAHMS.
CONTACT 08060712446 CHAT KAWAI BANDA KIRA OR
FOLLOW WATTPAD OR AREWABOOK APP AT *@SURAYYAHMS*
COMEBACK SERIES OF SURAYYAHMS 2024/25
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top