EP10

*"NUR FIRDAUS..."10*
_Arewabooks@surayyahms_

Abuja.
Dagata dayan bangaren daga cikin karamin falo na gidansu abokiyar nur firdaus wato jadidah bangon talabijin ne ya haskaka fuskar Mrs. Haseena Sharif yayin datake fuskantar tarin caccaka da tambayoyi masu zafi daga 'yan jarida...yarta Layla dake zaune a kan kujera take taje  tajawo hanklin dadarta nur firdaus izuwa kan tvn, Suduka biyu suka kalli juna cikin jin mamakin abin da suke gani na live show da mahaifyarsu take zantarwa akan yar yarinya karama wanda hakan yay musu kama da tozarta asirin wnn yarinya wa duk duniya dan abune me zafi da nauyi amma akeyinsa a bayyane

Layla ta kyabe baki ta danna kumatunta da hannu tana girgiza kai ahankli, xucyarta na racing cikin numfashi tace "Yaa Nuri Duba mummy fa, ni Wani lokaci ma nakan manta cewa itadin yar gwawarmayar kare haqqin dan adam ce amma haka dama ake kare haqqin dan adam a bayyane???huhh god, i dont like this.

Nur Firdaus wacce ta kasance tana rike da babban wayarta adede wannan lokacin ta ajiyeshi a gefe snn takalli talabijin din da kyau Fuskarta nanuna takaici da rashin jin dadi atakaice tace "Na gani Layla. Amma ki tsaya ki ji abin da take cewa, mummy tana nuna cewa ita tkmr shugabar al’umma ce, mace me kare haqqin y'ay'a mata, amma sai gashi bata da lokacin y'ay'anta. wata uku kenan tana yawonta na kulla karfin siyasa bata tare damu amma yau da safe wai har taje kare haqqin wata daban, Ba za ta ma iya tsayawa tambayar yadda muke farka ba, tawuce ta tafi kano duk dai harkan siyasa ne wnn kuma kowa yasani..."

Laylah ta sake kallon fuskar Mrs. Haseena a talabijin, tana sauraron kalamanta game da adalci da kare hakkin yara sai kuma taji kamar maganganun na taba mata xuciya.

tace "Amma big sis duba irin karfin hali da yadda take magana da jajircewa, Mutane sunayi mata tambayoyi masu wuya amma tana amsawa da jarumta. Amma, meyasa mummy ba tanuna wannan kulawar agare mu?"..

Nur Firdaus ta gyara tsayuwarta tana jin zuciyarta tana kuna.

"Wannan shi ne abin da ke matukar damuna Layla. Kullum tana magana akan yadda ake kare haqqin y'ay'a mata, amma mu fa, yaran ta? Bata ma san abin da ke faruwa da namu rayuwar ba. Tabar mu  duk saboda ta tsaya wajen wannan yakin neman zabe da siyasa, Adnan ya riga ya sanar dani komi..mahaifyarsa tana bukatar strong advocacy, kujerar datake nema na minister is very competitive sabida akwai wata yar siyasa me hatsari datake son dalewa, shiyasa suka dawo da abun yakin neman zaben kujera, suna neman Votes daga party advocates, da kuma voices of the vulnerables, kuma mahaifyar adnan ta daura mummy akan wann matsayin ne sabida itace kadai zata iya amfani da kowani irin yanayi, dominsu samu kyakwwan advocacy da votes din da sukeso aranar da za'a voting din kujerar a majalisa againts their  opponents. shiyasa suka maida abun ya zama kmr makrci cos i wondering ai ba a siyasar neman kujerar minister amma adnan ya min bayanin komi

abun ya taba zuciyar layla amma jin sunan adnan yasaka kawai ta kyabe baki batace komi ba

nan itama nur firdaus ta yi shiru na dan lokaci, tanata kallon talabijin yayin da aka mayar da kyamara kan Ummi da Mrs. Haseena ke kula da ita. dukansu basu ce komi ba dan da sukaji yanayin labarin ummi nacewa mahaifinta ne fa yay mata mummunan fyade ayar shekara 13, duk take dukansu jikinsu sai yay mugun sanyi.

laylah dakejin wani irin rauni tabudi baki ahankli cikin yin kasa da murya, tace "big sis nifa inaga kila mummy tana kokarin gyara kurakurenta ne tawajen temakon wannan yarinyar duk dama nasan yana da kyau muma ta duba rayuwarmu, ba wai kawai mutane na waje ba." dont u think??

Nur Firdaus ta murmusa, amma ba wani murmushi na farin ciki ba."Za mu jira Layla nima ina saka ran haka. Amma har yanzu, zan ce ki guji dogaro da ita. sabida itadin yar siyasa ce, Duniya ce kawai ke koya mana yadda za mu kula da kanmu."

Layla ta kalli 'yar uwarta cikin damuwa, amma ta kasa cewa komai. Suka ci gaba da kallon shirin cikin shiru, kowanne da tunanin da yake yi a cikin zuciyarsa, yayin da tambayoyi game da uwa da yanayin halinta suka ci gaba da mamaye su.

kano state..

taro yayi taro jama'a duk sun rajaa akai musmmn ma da Mrs. Haseena Sharif tayi tsaye cikin nutsuwa yayin da tambayoyi masu zafi daga ‘yan jarida ke cigaba da harbuwa Fuskarta na nuna jajircewa.

kokari take wajen kare matsayinta da maganarta akan batun Ummi. Sai dai al’amura sun canza yayin da ta ji karar wayarta na daukar hankalinta daga abinda ke faruwa.

Wayarta tana ruri a cikin karamar jakarta, kuma idanunta sun sauka kan sunan mai tura sakon wato mijinta Saadat datake mutuwar muradi aranta.

A yayin da take kokarin mayar da hankali kan tattaunawar, ta kasa daurewa saida ta bude sakon wanda ya bayyana cikin sauri,

"Haseena kidawo Abuja kawai akwai matsala. i cant hide this anymore is enuf nagaji nagaji nagaji.. bazan iya ba musmn ma da yarki take fmr kokarin jan hankalina akan zina, nagaji, wallh Ba zan iya ci gaba da boye wnan abun ba. Ki dawo gida kawai don mu taru mu magance shi ko kawai mu raba auren yau yau inyaso kowa ya kama gabansa.." in kuma kece kike turomin yarki dan tanazuwa min tsirara ina wanka tana nema na da sharrin zina, haseena kisani baxan taba yafe miki ba and u have no idea how dis is going to affect ur politics. pts insane!

a tsandare dede kan kalman "Zinan ta kafe idonta dan kanta taji yamugun sarawa Jikinta ya dauki rawa taciki nan take. Fuskar ta, wadda ke nuna karfin hali minti daya da yawuce, ya sauya zuwa wani yanayi na fargaba da mamaki.

ga tambayoyi daga yan jarida sun dau zafi amma zuciyarta ta cika da zullumi.

Ayayin da aka mayar da kyamara kan wani bangaren shirin ana hira da mahaifyar ummi, nan mrs Haseena ta samu daman rike wayar ta sosai sede Kalmomin Sadat sun hanata sakat suna masu ci gaba da maimaituwa a cikin kwakwalwarta.

aranta bata kawo tunanin kowa ba kuwa sai babban yarta Nur Firdaus sabida tasani sam ra'ayinsu baya jituwa, take kuwa ta fara rike haka aranta, dan gani take yarta layla is too naive and young bata san komi game da zina ba tukuna.

amma toh A ina wannan abu ya samo asali? duk da bata kulawa da su amma ai tasan yarta nur firdaus da akwai tarbiyan addini da kuma nitsuwa, wnn halin kuma daga ina ya fito? or..is she doing this to ruin me?
dama nur ta tsane ni

tayi kokarin boye damuwarta daga ‘yan jaridar, amma jikinta ya kasa boye fargaba da ke bayyana mata, nan Daya daga cikin tawagarta ya zo kusa da ita don tambayar ko tana bukatar ruwa, amma ta girgiza kai cikin hanzari. Ta san cewa wannan ba lokaci bane don nuna rauni. Amma tunanin cewa tana zargin ‘yarta da irin wannan abin ya fi karfinta, sam takasa cigaba da mai da hankali kan abin da ke faruwa a wurin. Kusan mintuna goma kacal, ta samu uzuri daga shirin, tana mai cewa..."Ku gafarce ni, amma dolene inyi wata kira mai muhimmanci..

nan tanufi wani bangare da ke bayan daki ta tsaya agaban madubi, sannan ta lalubo lambar sadaat saidai switch off ta dingaji, hanklinta ya matukar tashi, cikin danne fushi ta kira wayar Nur Firdaus. Tanasa hannu don kira zuciyarta na bugawa da karfin gaske. Lokacin da ta fara jin ringing din wayar ta dafe goshinta tana jin wani mugun fushin da ke taruwa a cikinta.

lkcin yay dede da time din da Nur Firdaus da Layla suke famr kallon shirin talabijin jikin su duk yay sanyi suna jin yadda tambayoyi masu zafi ke shiga kan ummi da kuma mahaifiyarta abun da taba zuciya sosai..

karar waya ne ya katsesu Da tsananin mamaki Nur Firdaus tadauki wayar ta rike snn ta danna cikin nitsutsen sallama saidai muryar mrs Haseena tayi rauni tana cike da fushi

cikin yanayin daure fuska tace bani da lkcin amsa sallamarki Nur, kawai ki gayamin wai Menene nake ji haka? shin meyake faruwa tsakaninki da mijina, Menene ya sa za a zarge ki da wani abu mai muni haka?..

Nur Firdaus, wacce ta rude tarasa gane abin da mahaifyarta take furtawa ta amsa cikin rawar murya mummy ban fahimce abin da kike magana akai ba ni me zai hadani da mijinki, shin  Wane irin zargi ne haka?...

mrs Haseena ta yi shiru na dan lokaci, tana kokarin tattara abubuwan da ke ranta. cikin saukar da murya tace "Sadat ya rubuta min wani sako yana cewa kin yi wani abu da bai dace ba! i dont want to say it out loud now, ke kinsan me kikayi ai, so nake naji abakinki shin Da gaske ne?"...

hawaye suka ciki idon Nur Firdaus kirjinta ya dau zafi tace mummy bansan me kike zargi na akai ba, bayan haka ma mijinki bai taba kulawa da mu ba mezai hadani dashi?? Kawai maybe yana son yajefa ni cikin wata matsala ne cos i dont knw what ure tlking abt...

mrs haseena tay jim sai dai batace komi ba taja wani dogon tsaki tare dakatse wayar sabida taku takun dosowar mutum datakeji a kofar bayin.

Maganar Nur Firdaus ko kadan bai shiga zuciyarta sabida ta riga tacikashi da zullumi da fushi.

Ta yi ajiyar zuciya mai karfi, tana jin nauyin halin da ke kanta. Idan da gaske hakan yana faruwa to tabbas lamarin zai iya zama karshen komai gareta, her reputations, her career, ba kawai siyasa ba, har ma da mutuncinta a idon jama'a..

tana ficewa a bayin ta kasa hakuri nan ta rubuta sako me zafi..

"Nur Firdaus, zan bi jirgi zan dawo Abuja zanzo gida yanzu. Amma zan gaya miki abu daya, idan wani abu daga zargina ya tabbata akanki kada kiyi tunanin zan kalle ki haka kawai. Amma idan ba gaskiya bane, toh Sadat zai gane kurensa dan bazaku min wasa da mutunci na da aikina ba.."

bayan ta tura ma Nur firdaus sakon nan ta kashe wayar cikin sauri tana mai komawa cikin taro inda take zaune,...

murmushi take a fili amma azuci sam ta rasa nitsuwarta dan kuwa aranta cewa take dole ne ta dauki mataki  kafin lokaci ya kure mata.

****
daga dayan bangaren kuwa bakaramin fargaba da daurewa kan Nur firdaus yayi  da jin magnganun mumynsu ba

Layla na kokarin fahimtar abubuwan da ke faruwa yayin da Nur Firdaus ta zuba ido ga wayarta ta yi shiru cikin takaici. nan kuwa Sai karar wayar ta katseta tana dan haskakawa taga sakon mummynsu

Nur Firdaus ta duba sakon da sauri, sai jikinta ya dauki rawa.
Tana karanta sakon, idanuwanta suka cika da hawaye, kuma ta mika wa Layla wayar, tana magana da murya mai rawa rwa

"Layla, karanta wnnan
meyasa mummy take furtamin hakan??

Layla ta karanta sakon kai tsaye itakam ta hasasho komi, amma sai bata nuna a fuska ba nan tamike tsaye cikin hanzari kamar wacce zata fadi wani abun kirki. ta dafa kafadun nur firdaus tace "yaa nuri karki damu da ita wannan zancen duk na banza ne, to uban me aka masa??

Nur Firdaus ta share hawayenta da sauri, tana kokarin kama kanta dan batasan zargin me ake mata musmmn data san ita da mahaifyata bawani fahimtar juna meyawa suke samu tsakaninsu ba..

"Dole ne mu koma gida. banason jadidah ta fito daga wanka ta same mu ahaka..
Amma, Layla kode akan abunda ya faru da safe ne akanki dan nasan iya abunda ya hadamu da mijinta kenan yau...

cikin shashntwrwa layla tace to me muka masa da har zai gaya mata ta dau zafi haka??mtswwww

nur firdaus tace bansani ba amma toh idan kuma mummy ta gaskata shi kai tsaye me zamu yi?..

layla na shirin budan baki saiga jadidan ta fito sai kawai sukayi shiru da maganan suka washe fuska nur tace mata zasu wuce gida.

nan Suka hanzarta daukar hijab dinsu da jakarsu suka yi wa jadidan sallama, snnan suka fito daga gidan cikin gaggawa.

tunani masu yawa cike da zuciyar nur firdaus amma layla har cikin ranta abun be darata ba, musmn ba da taga ba ita ake kkrin daurawa lefinba dan wani bangaren tana jin dadin rashin jituwar dake tsakanin nur firdaus da maman nasu sabida duk duniya awajen maman sun ne kawai nur firdaus bata da farin jini.

tafiyar 35 minute ya kawosu anguwansu ma gwarimpa sede Ayayin da suka iso kofar gidansun sun samu wasu makwabtan kurkusa suna tsaye kusa da kofar gidan nasu suna magana cikin karamar tada husuma snn Maganganunsu sun kasance masu nauyi da zafii.

"Wallahi Haseena Sharif samm ba ta da hankali,"

wata dattijuwar mata ta fadi hakan, tana girgiza kai...

ace tana mace amma Ta fito fili tana magana a talabijin abainar naasi akan yar yarinya karama ana tonon asirinta ga duniya amma ita fa tana da 'ya'ya mata  toh wa ya san me ke faruwa a cikin gidan nata tabarsu da gandadeden namiji..

Wata matashiyar mata wanda itama haihuwarta biyar da saki uku akanta amma ta dawo ana ce mata maman saeed ta yi wuf ta amsa maganan caraf cikin gungun mutane.

"hmm mama hauwa kibari kawai Wannan ai rashin imani ne. Kafin nan taduba gidanta mana, tana can tana maganar kare yara a waje. anan kuma yayanta na gantali a titi, ko Waye zai kula da yaranta datake wann uban gwagwarmayar siyasar oho

Nur Firdaus ta tsaya cak tana jin zuciyarta na kuna sosai. wanda akalla abune wanda aka saba, dan gabaki daya makwabtansu suna adawa sosai koma ince sun tsane  mahaifyarsu a fili badon komi ba saidan yanayin rayuwatta.

kullum suka kafa tantin gulma a kofar gidan babu abunda suke yi sai mugun fata da zaga zage.

mama hauwa da maman saeed da wata bayarbe maman bola sei dedekun mazan anguwa da suke iya tsoma musu baki suma.

Layla tayi kokarin jan hannun nur don su shiga gida amma Nur Firdaus ta kallesu snn tagaishesu cikin dan daure fuska ayayinda dukansu matan suka zuba musu ido

aranta cewa take Allah ya shiryeku, sam Ba ku gyara ta hanyar  gaskiya, dan Ba wanda ya san abin da ke faruwa a cikin gidanmu amma kuna magana kamar wanda kuke da hujja akai!"

Layla ta ja hannun 'yar uwarta cikin tsoron irin gulmataccen kallon da mama hauwa take musu

"Don Allah, yaa Nur, mu shiga gida kawai."

nan Suka bude gate suka shige cikin gida cikin sassarfa tare da barin  makwabtan suna masu ci gaba da maganganun su anan.... COMENTS AND SHARE

#SURAYYAHMS

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top