EP 6
_*NUR FIRDAUS.....6*_
_Arewabooks@Surayyahms_ .
A can kusa da closed windown farko ita kadai take zaune bata da abokin zama littafanta ne kawai agefenta ta bubbudesu wanda kallon farko in kayi mata daga nesa kusan dolene gabanka ya fadi dan nur firdaus kyakykyawa ce kyau medaukar hankli a yadda takillace duka sassan jikinta wanda yasaka ta matukar banbata da kowa wanda inka matso kusa da ita kuma sai kaga tafi yadda kake tunani tsabar kyau.
Wani Rau rau tay da idanunta calmly akan dukkansu da suka juyo suna kallonta ayayin datayi nitso acikin karantar fuskan kowa, it feels like the mind of the crowded sss 3 litereture class students are waiting for her to froth koda zata bayyana musu wani rauni datake dashi wanda basu taba gani ba atattare da ita ba.
nitsatsassun ruwan idanuwanta kawai ta zuba akansu kamr wacce bata da wata matsala a rayuwarta duk ma her mind is really suffocating under the weight of memories na tunanin matsalar mahaifryta dana uwarta laila wanda dr ibrahm ya tattauna da ita akai few hrs ago wanda tasan yana da alaqa da darasin nan da akeyi musu dayake kkrin tuna mata baqin cikinta datake boyewa which is threatening to snap in at any moment. inda Daga ganinta zaka fahimci ita kanta bata san cewa tay tsakin ba.
Shirun da taji ajin yayi da kuma feeling na cewa duk an zuba mata idanu ana kallonta yasaka ta dada dago kanta da sauri ta mike tsaye dara daran idanuwantan ta sakasu a cikin na malamin da yake tsaye a gaban aji cike da jarumta suna kallon kallo..
Can sannan malamin yce mata "yes, nur fidaus kamar naji kinyi tsaki I dint knw u cud be this disrespectful..
da dan sauri ta girgiza masa kai da fuskar nadama ahnkli ta furta "my Apologies sir. i Will work on my Reflexes.
Wayanda suke jin haushin confidence dinta a ajin take suka dan kau dakansu wasu kuma suna mamakin yadda wann topic din ya hatsalata duk uwar hankali da ntsuwartan nan hartakai gayin tsaki.
Malamin Baice uffan ba ya koma kusa da board ya tsaya yana kallonta sannan yace "ke yar wata gari ce?" kanta ta sauke a kasa snn tace "Abuja" yace perfect "menene ra'ayinki game da abunda muke tattaunawa akai shin Kina ganin duk abunda iyaye sukeyi akan yaransu a arewacin nigeria sunyi dai dai ko kina da wata gyara?"
dan Shiru tayi na wani lokaci, sannan tayi karamar murmushi ta girgiza kanta sigar jarumta duk da fuskarta na nuna cewa akwai abinda yake damunta aranta sosai. Ahnkli kuma sai tayi magana tace "Da farko de haihuwa abune da Allah ya tsara mana shi acikin rayuwarmu dan haka duk abunda Allah ya tsara shi dedene kuma rahma ne a garemu, snn Annabi muhammad s.a.w ya umarce mu da muyi aure mu hayayyafa kodan yay alfahari da mu al'ummarsa ranar karshe..yara amana ne awajen iyaye.. so, all these parental laws and wisdom da ake lissafawa anan a iya nazarin dan adam kawai suke iya bada ma'ana or maybe for the sake of academia and other educational purposes. amma ba wai amfani ne dasu arayuwa ba.
malamin ya kalleta yace Toh gaya mana yadde ke kike ganin gaskiyar abun? What does it even feel like to be a child in northen nigeria.
yana furta hakan Nan take kirkirarren murmushin dake kan fuskarta ya dauke ta hadiye wani abu a makogwaronta sannan ta sunkuyar da kanta tana kallon rubutun dayake gabanta masha Allah she have a very beautiful italic and bold handwriting duk ta rubuta points dinta daga abubuwan da sauran daliban suka tsalleke basu kafa hujja dashi ba.
Muryanta daya fito da kuma sanyi wanda da kyer yake fita tace to be a child in northen nigeria "It means to be.."a Burden" a "terrible priviledge"..to never be a enuf". A commodity..Or an object".
daga nan dan shiru tay dan kusan furtawa tay batare da tasan ta furtasu duka ba, her words are like a fragile confession that left her exposed and vulnerable wanda takejin kamr ita kadai ta fahinci abunda take kkrin furtawa yanxu
Class din ya dada daukar shiru but she can feel the weight of her secrets begining to shift so slightly into her heart.
"Go on munajinki"
taji muryar malamin kamr a kunnenta, as clear as if a kusa daf da ita ya furta mata hakan. Ta dago kanta cikin shanye komi cike da nitsuwa snn tace " sir, Ppl alwys have a choice. Addinin mu yana da tsari..even to be a parent itself is a choice. and legally, nobody will force u...duba da haka toh ba meyasa mutum zaiyi aure, snn ya kawo wani halitta duniya Bayan yasan zai zame masa silar takuri, nauyi da damuwa? Why dont ppl who feel they wanna live life to the fullest, away frm all these buddens, Mental Abuse and parenting exhaustions, childcare stress, and unresolve childhood trauma, ppl who dont wanna lose their identity or "have so much desire for autonomy...just forget abt bringing thier children whom they see as the burdens to this world, inhar kasan abunda zaka haifa zai zame maka tsaiko, damuwa da nauyi toh me zaisaka kay auren kakuma haifa???
dedenan hanklin yan aji gabadaya ya koma kanta data furta hakan, musmnn Abdul oyebanji daya kureta da kallo me ban haushi wondering why she alwys steal the spot light dan hatta wadanda ada can suke yan rubutunsu yanzu sun juyo suna masu kallonta jin yadda tafurta maganan nata da gasken gaske cike da bada darasin maana..
Ta cigaba cikin yaren turanci mai dauke da slight fulani accent dinta me sanyi"tabbas rainon ciki da haihuwa da kulawa da yara abune me matukar wuya da gajiyarwa amma kuma akwai tarin farin ciki, girma da daraja aciki. hypocritacally, our parents even celebrate to have us amma yawancinsu a baki suke tsayawa murnan baya karasawa har zuciya dan daga zarar an kawo yaro duniya 80% parents will have a feeling similar to feeling din da colonials suke ji a lokacin da suke sayan bayi, Like since I fed u, cloth u, and gave u life it means I own your dreams and realities, i tell u wat to do, and wat not to do, cos you belong to me. Duk an manta da cewa we both belong to each other.
Sir, Iyaye sabida wahalar da sukasha na raino da haihuwa suke da hakki akan yayansu, muma ƴayan sabida rauni da biyayyar da Allah yace mu musu yasaka muke da haqqi akan iyayen namu...
wasu iyayen we are like total strangers to them they hoard all the right like gods..
they opress sabida sunajin cewa koma me zaifaru in sukace Allah ya tsine maka shikenan sun gama dakai..right frm birth su zasu gaya ma yaro komi, wen to eat, wen to sleep wen to bath, wat school to go, wat to study. Ambition. Who to marry.. and ure neva going to be enuf if u dont meet their expectations!
"Na sani cewa kusan more than 80% na mutanen mu na arewa musulmai ne, kuma na sani cewa a Alqur'ani da hadisan Manzon Allah dayawa sun fayyace hakkin iyaye akan yaransu da haqqin yara akan iyaye. The whole purpose of this is to becme blessings and have mercy on each other and not to condem the natural process. Amma a halin yanzu more than rabin iyayenmu mu basa iya daukan wannan nauyin da Allah ya dora musu akan mu. Yara dayawa su suke daukar nauyin rayuwansu, wasu su ciyar su shayar su kuma su tufatar da kansu wani lokacin ma harda iyayen nasu. koda ta hanyar sata ko karuwanci ne...ina amanar da Allah ya bayar inde a duk hakan har ana bawa iyayen irin haka dukan uzuri?
Lets not even dwell into the poor presentation of almajiri system of education in northen nigeria" wanda yake tàmkar child labour and abject slavery. Underage children begging and sleeping on the streets for food, unsheltered, exposed to all sort of sexual abuse, and immorality, harmful drugs, cultism...who is respnble for their health and well being? What is the fate and fault of these little Vulnerable children?
...Snn yara dayawa da ake haifansu wanda ake tunanin suna da gatan ma a gidajen iyayensu yawanci labarin ba haka yake ba a zahiri, sabida iyayen nasu sunyi arxiki ko matsayi dan haka sun zama tamkar dodonni agaresu wanda yara bazasu iya ma tunkararsu da kowacce irin matsala ta rayuwarsu ba, snn iyaye a wani bangare sun zama sila na damuwa da kunci ga zucyar yayansu a kullum, they dont care how domestic violence, divorces, family conflicts..or even Death" can affect their children"..
Ta goge hawayen da yake shirin ya taru a idonta ta cigaba Danne shi da murmush me sanyi...har ranta takejin cewa inda ace ayau mahaifinta na raye atare dasu sam da ba haka rayuwarta dana yar uwarta leila zai kasance ba..
Ahankli tace Daga iyayen har yaran we are a big privilage and blessing to each oda, so why dont we focus on being better...why must we support and justify parents who neglect their parental duties??? was God, the master of mercy and sufficiency, ever wrong???
duka yan ajin kusan atare sukace "No!.
...wani tambayar shine tsakanin iyaye da yaransu shin waye yafi rauni waye yafi bukatar kulawawa???
...gaskiya kuma itace "we both need each oda", we can do this of we both intend.. rauni da bukatar kulawa ke zagaye da yaro ayayinda yake danyen shekarunsa iyaye kuma rauni da buktar kulawa yana zuwa musu ne ayayin da suka tsufa.
cikin katseta Abdul yace "ooh please" i strongly disagree with all ur points..this is all fucking emotional manipulation...haka yan arewa kuke rudar kanku da karya kuna zama da talauci da rashin ilimi da yunwa kamar wasu bayi
Duk yan class din da maganganunta suka ratsa musu zuciya suka juya suna kallonsa da mmkin Yadda yay maganan with utmost disgust for northen nigeria
itace kawai bata kallesa ba dan tasanshi tana ganinsa a ajin amma basu taba magana ba dan haka ko sunansa ma bazata iya cewa ta kamaba sabida Abdul cikakken bayarbe ne amma irin yaran nn ne da suka taso a lagos masu tsatsauran raayi akan northen nigeria da kuma addininsu.
Abdul oyebanji tun daya gane cewa nur firdaus hausa fulani girl ce kuma tana da farin jini da gwazo, then he began to feel threaten by her personality and each time she speaks with exceptional english grammer zainajin kamr ya tashi ya shaketa dan takaici take bashi bana kadan ba, itace kullum me zuwa na daya ajin shine na biyu shiyasa ya tsaneta bana wasa ba, dan a inda suka taso ce musu ake jahilcii, addinin ta'adanci, kauyanci, yunwa da almajiranci sune kadai suka cika arewacin nigeria.
Ya juyo yana kallonta yace " u think this as a justification sabida kin tasone a inda yara basu san darajan kansu ba. girl, nobody owes u anything. Our parent dint owe us a thing!!..kmr yadda kike mutum da dreams naki haka suma suke mutune da dreams dinsu duk abunda suka yi da yaransu is justified ba dolensu bane cmn think abt it if ever u had a real brain.
Cikin dakewa ta juyo ta dan kallesa a dakile snn tace "sure,, no, i cud use ur empty brain whenever i lost mine.
Tsakin kasar wuya yaja snn ya bude novel din dake gabansa mai taken "The perks of being a wallflower" by stephen chbosky, A Thought provocking coming of a age novel. Ya kalle malamin snn yace sir inhar abunda take cewa gaskiyane to meyasa chapter 17 yace."we are all Damaged, and we all beautiful" ? hakan ya nuni da kowa yana da dama yay rayuwarsa witout any child burden
Kafin malamin ya amsa nur fidaus tay murmushi tare da cewa Sir, But The same author said" _We accept the love we think we derseve"._ inaganin hakan ya isa yabada cikakken amsa akan tambayarsa.
Malamin ya dubesu duka snn yace well then ure both right.. things change, and they dont alwys get better..but sumtimes they do.
cikin rashin yarda da hakan nur firdaus tace in book of 'The bell jar" by sylvia plath, Chapter 7."..and I qoute. " _"I dint knw what i wanted but i knew it wasnt this"...._ sir, Wnn kalma ce da kowani yaron da aka haifa cikin rashin samun kulawa inya samu dama zai iya furtashi ga iyayen da suke da irin wann tunanin na jin cewa yaransu ba kayan amana bane akansu..
Abdul ya kalleta snn ya bude wani littafi mai taken "the glass castle by jeannete walls. dede Chapter 1 ya tsaida idonsa kai tsaye yace _"you should never complain about your life, bcos der are alwys ppl who have it worse_ ya furta hakan yana dubanta...
cikin littafin daya duban itama ta kalla ta bude shafi na goma snn tace Well, then _."I was begining to realize that our way of life wasnt normal"...._ snn ta kalle sauran yan aji snn tace "Can we all agree that this is not normal ?
Dayawa suka amsa da yes wasu suka hau mata tafi dan tabalain burgesu data cinye abdul da points masu zafi
Dede nan lkcin lectures din ya kare with alot of heavy murmurs from the class..da alaman kowa kansa yadau caji da tunani.
malamin yanata murmushi yana kallonsu can ya kalli agogonsa yana snn yace Toh shikenan zamu dora a darasi na gaba....
ke uwa...
"1: rayuwarki bata kare ba dan kin zama uwa.
2: rayuwarki gabaki daya kinayinsa domin abunda kika kawo duniy which is yaranki
3: team kowa yay ta kansa i am just a portal of delivery na kawoka duniya amma bata kai nake ba.
BABBAN TAMBAYAN AKAN MU DUK SHIN MATSAYINKI NA "UWA" KO NA Y'A MACE"...DA WATA FUSKA KIKA DAUKI WANN MATSAYIN NAKI??
INA SAURARAR AMSO SHINKU A COMENT SECTION, YAR UWA KARKI RAINA KALAMANKI WATA KILA TSOKACINKI YA ZAMA WATA SILA KO SHIMFIDAR GYARA LAMARIN WASU ANAN GABA.
CONTACT 08060712446 CHAT KAWAI BANDA KIRA OR
FOLLOW WATTPAD OR AREWABOOK APP AT *@SURAYYAHMS*
COMEBACK SERIES OF SURAYYAHMS 2024/25
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top