Epilogue


10 years later

Gashuwa, Yobe state ,Nigeria.

    Shiga da fice na ma'aikata a cikin babban sabon mansion na Alhaji Muhammad Tukur Gashuwa shi zai tabbatar maka da ana wani taron ne duba da yarda ake ɗorawa da saukewa,

A hankali motoci na alfarma suka fara shigowa cikin gidan wanda suke ɗauke da iyalan cikin gidan waɗan da duk wanda yazo wucewa ka kalesa kasan Kwanciyar hankali da arziƙi sun zauna.

Da gudu wata budurwa mai kimanin shekaru 20 ta rugo ganin yan uwanta da ta jima bata saka a ido ba,ware idanu ta fara from one person to another tana tunani wane zata fara hugging, kan sister ɗinta wadda ke dariya kaɗan kaɗan sanin ita zata rungume tayi,da tsallenta ta ɗane ta tana mai cewa.

"Sis Jannah I really really do miss you "

Dariya matured Jannah of 28 years tayi tana mai rungume sister nata tana faɗin.

"Oh little Samrat kada ki karya ma mijina ni" dariya tasa tana mai Turo baki idanunta na komawa kan yayanta wanda shine mijin Jannah tace.

"Ya Salman I'm sure you won't mind right?shekaru Uku fa ban saku a ido ba ,Allah yasa Yan yarana Aunty Suwaiba ta ɗauko su ta kawo if not kaina sai ya ƙi tsayawa guri ɗaya".

Gyaran Muryar da akayi yasa ta mayar da hankalinta kan ɗaya set of couples ɗin kafin ta saka dariya ta isa gare su tana mai cewa.

"Ya Jamal,Sis Saimah I'm sorry cos ku ban missing ɗinku da yawa ba cos idan ban manta ba last week tare muka dawo daga Brazil".

"Well ki godewa Allah i was there last month ɗin ki na karɓan hutu,kike nan kike cika mun baki,zamu gani ai ,Allah yasa Ni da Hubby mun gama contract ɗin da ya kaimu Brazil and you still have Two years to go".Saimah ta faɗa tana mai saƙala hannunta a arm ɗin mijinta Jamal ne yake gumtse dariyar ganin yarda Samrat ke san fashewa.

Dariya suka saka baki ɗayan su kafin suka fara takawa dan shiga ciki Samrat na bin su a baya tana mai cewa.

"Ba sai kun shigo motocin daban daban ba bayan daga destination daya kuka zo".

Jamal ne ya amsata yana ma cewa.

"Well dear sister akwai dalili,kin san taro biyu muka zo,ga na Auren babban Gwauron gida mu ga kuma na dawowar mu gida baki ɗaya".

Dariya kawai take tana mai binsu a baya tana mai sake faɗin"well bamu buƙatar yawan motoci ku duba compound ɗin mu. "

A haka suka shiga suna ta dariyar iya shegen Samrat.

Shigar su ke da wuya kowa ya fara ɗaga kan neman Ummu cos babu wanda bai kewarta ba.

"Tana ɗakin ta, nasan kun fara manta hanya ,ku zo na raka ku".cewar Samrat wadda ke jin daɗi kamar ya karta.

Yara shida ne suka sauko daga kan staircase kowa yana nema iyayen sa,suna ɗora idanu kansu suka nufesu suna masu ƙwala masu kiran oyoyo,Guda biyu da basu ga iyayensu bane sukayi turus kafin Macen ta juya da gudu tana mai cewa.

"Aunty Suwaiba,why will you say Pa and Ma have arrive,I'm not happy with you".Namijin ne ya juya yana mai cewa "Ayra don't be rude kin san idan grandpa ya ji zai daina baki sweet da chocolate,after all idan Pa and Ma basu zo ba favorite uncle's and Aunt's are here".

Takawa yayi ya isa gare su yana mai kasa ɓoye murnar ganin su..Daga saman da take ta haɗe hannayenta biyu .

"Aryan I'm being Rude Amma bazan manta ɗazu wannan zachria mai sunan old people yake ce mun Ai Daddy Jamal ba shine Daddy na ba".takowa tayi tana sakkowa tana mai ƙarawa da cewa.

"He even said Mum Saimah is not my Mom, that it took us 3 years bamu ga Pa da Ma ba,he pissed me".

Kallan Zachria Jamal yayi yana mai cewa.

"Zack mai yasa ka faɗawa sisternka Ayra haka,go and apologize right now and Ayra is my daughter and I'm her dad,wane ma ya koya maka wannan?"

Kamar Zach zai fashe ya isa gurin Ayra yana mai faɗin I'm Sorry kamar zai kuka,.kowa yasan Ayra da shegen san girma,kamo sa tayi tana mai hugging ɗinsa tana faɗin",it's okay little brother kada ka kuma,Nima Bazan kira ka da mai sunan Old people ba".

da haka ta isa gare su tana hugging kowa ɗaya bayan ɗaya,. she's just 10 Amma kinibininta yafi karfin ta.

"So a yanzu kunga dalilin da Daddyn ku ke nacin ku dawo gida ko?so that yaran nan zasu so juna su shaƙu da juna,after all the family is meant to be large".

A tare dukkan suka mai da hankalinsu ga Ummu wadda take fitowa daga wani ƙofa dake ƙasa,a tare Saimah da Jannah suka Nufeta da gudun su suna mai faɗin Ummu yayin da mazan ke aikin washe baki.

Ɗaga hannu Ummu tayi tana mai faɗin "Jannah ban san gudun nan, you're expecting a baby".

Cike da excitement na ganin ta jannah ke bata amsa da baza ta iya calming kanta ba gaban ta.

Haka suka gama exchanging gaishe gaishe kafin suka nufi Babban falon dake cikin sashen na Ummu ,ganin yarda Ayra ke naci yasa Salman sake kiran Akram wanda kafin su shigo suka yi waya ya sanar musu suna hanya,bada jimawa ba kuwa sai ga sallamar su ,Akram ɗauke da Carrier da baby a ciki yayin da Nafisa ke gefen sa hannunta ɗauke da baby bag,da gudu Ayra da Aryan suka tashi suna masu ihun murna na ganin su yayin da Jannah tayi sauri wajen karɓan 3 months Baby girl ɗin mai Suna Ummukulsum ,bayan kowa ya nutsu ne suka fara tambayar Sultan wanda Ummu ke faɗa musu suna Chan wai bachelor party,.

sosai Nafisa tayi murnar sake ganin Suwaiba duk da ganin ta na karshe bai shekara biyu ba.

¿Shin mene Ummu da tawagar ta suke gidan Alhaji Muhammad Tukur Gashuwa,mahaifin Akram?.

Bayan rasuwar Alhaji Bukar Ummu ta shiga wani irin halin wanda ba domin yaran dake gabanta ba babu abin da zai hana ta faɗawa ciwan damuwa,a kullum bata wasa da bin sa da addu'a tana mai nema masa Rahma da sassauci gurin mahaliccinsa,.a hankali abin ya fara sakin su duk da tabon bai goge ba,a iya zaman su dashi sun san menene daɗin mahaifi duk da lokacin buƙatarsa ya kau amma a haka sun ɗan ɗani daɗin sa da daɗin kulawa da shi.

Da fari Nafisa ƙin bin Akram tayi su tafi India dan a cewar ta baza ta iya tafiya ta bar mahaifiyarta a halin da take ciki ba,sai da Ummu ta bata baki ta ƙwantar mata da hankali sosai kafin ta amince da tafiyar ba dan zuciyatta ta lamunci hakan ba,.

Sosai mutuwar ta daki Nene wanda ta saukar mata da wani ciwon na daban inda ta ringa ƙokarin dannewa gudun kada ta sake jefe Ummu cikin wai hali,da suka dawo mata da maganar tafiyanta Tare dasu sai cewa tayi ai ta chanza shawara baza taje haka nan ta mutu a garin masu bautar gunki ba aje a binne ta chan zunubinsu ya shafe ta,da barƙwanci suka ɗauki abin amma fa ita Nene har zuciyar ta domin tunda ɗan ta mafi soyuwa a gareta ya rasu ta cire tsammani da rayuwa .

Haka nan suka wuce tare su biyun domin nema mata lafiya wanda Akram yaji daɗin kasancewar hakan cos yana san yayi using wannan damar idanun Nafisa na buɗewa ya nuna mata India sanin tana masifar san garin duk da yarda yake faɗin babu wani abin burgewa a baya,amma a yanzu duk wani abu da Nafisa ta ke so koda shirme ne a gurin wasu ,shi zai ara ya yafa muddin zai burgeta.

Suna isa da kwana uku akayi admitting ɗinsu a asibiti ,bayan two months of being taken care of Allah yasa tai gaining ganin ta duk da first week haka take gani dishi dishi kafin daga baya ta fara gani da kyau,.

A duk wannan journey ɗin Akram na tare da ita hannunta cikin nasa yana mai bata kulawa fiye da zaton ta,a time ɗin da suka ɗauka a tare yana kula da ita bangare guda kuma yana mai ƙara ruɓanya soyayyarsa cikin zuciyar ta a hankali a tsanake,after ta warke baki ɗaya kuma sai aka dasa Honeymoon inda Akram ke ji kamar ya mayar da Nafisa cikin sa saboda soyayya,sai da ya tabbata ya bata romantic moments da tayi deserving ta yarda idan tana receiving dukkan wani affection nasa takan godewa Allah.

Da fari bata da family,Tazo ta samu ,tun da ta rasa big mummy take tunanin babu wani wanda zai sake nuna mata soft side na uwa,then cikin hukuncin Allah ya sadata da mahaifiyar da ta haifeta,.Jarabtar makanta ya same ta wanda ta ma cire tsammani na sake ganin waɗanda take so da idanunta,cikin hukunci na Ubangiji ya sake ara mata dama ya dawo mata da idanunka ga kuma nutsuwa da soyayya ya saka mata cikin rayuwa,babu wata godiya da zata yi ga Ubangiji ta isa domin yayi mata komai cikin Rahamar sa a lokcin da ta cire tsammani da Rahma.

Bayan watanni shida a Indiya suka dawo Nigeria,duk Wanda zai kalli Nafisa sai ya sake kallanta duba da yarda ta ƙara wani irin kyau tayi bulbul abin ta yayin da Shima Akram ɗin ya sake wani fresh na kwanciyar Hankali.

Nassarawa suka sauka domin shima yafi feeling at home a gidan Ummu,duk yarda mahaifinsa yayi akan ya dawo Gashuwan ƙiyawa yayi dan haka ya siya masa gida a nan GRA ɗin da gidan su Ummu yake,baki ɗayansu sun ƙi zama guri ɗaya dan hatta abinci gidan Ummun suka dawo ci,a ƙwaɗayin da Nafisa ke mugunyi yasa Ummu gano cikin dake jikinta duk da bata tabbatar ta,kafin kace wani abu sai laulauyi ya fara mai wahalar da ita,haka suka dawo da dukkan kulawarsu gareta kar ma mijinta Akram wanda a yanzu baya jin kunyar kowa ta bangaren nunawa Nafisa kulawa da soyayya.

Bayan wasu watani shi da Salman suka samu aiki,duk da Salman kanyi yan buga buga ,samun aikin sai ya kara musu karfin kula da kansu da yan uwansu.

Bangaren Jamal shima bai zauna ba ya cigaba da desgings ɗinsa yana Saidawa manyan Companies har daga bisani wani babban Company suka singing Contract dashi inda Alheri ya buɗe masa.

Koda suka fara samun nutsuwa sai soyayya ta fara shiga tsakanin Jamal da Saimah hankali duk da yarda suke boyewa hakan bai hana sauran ganowa ba ,ganin ana tsokanar su ne Saimah ta tona soyayyar da Salman suke da jannah tana mai faɗin.

"Sai dai ayi mana dariyar a tare".

Abun yayi wa Ummu daɗi musamman na Salman da Jannah ,tasan tabbas Salman zai rufe asirin Jannah ya ƙaunace ta da dukkan rayuwarsa,sosai ta jinjinawa al'amarin lokacin da ta kira Salman ɗin tana mai san jin ta bakinsa gudun Azo ayi abin kunya dan muddin ya rabu da Jannah baza ta lamunta ba ,shi yasa ta tuhumesa ta san matsayar inda ya dosa kafin abin yayi zafi.

Ta gamsu da soyayyar da yake ma Jannah ɗin dan haka ta godewa Allah ta bisu da Addu'a tana mai jin farin cikin yarda komai zai faru cikin gidan su babu wanda yaji babu wanda ya gani,tayi imani da hakan shine zai sake musu danƙon mai ƙaimi da zumunci mai ɗaurewa.

    Suna Wannan Rayuwa mai daɗi Mahaifin Akram ya sake bijirowa da Ummu yayin Aurenta wanda ya jima yana yi amma take ta boyewa dan ta saka a ranta abin kunya ne idan yaran sukaji bata san ina zata saka kanta ba dan haka ta roƙesa da ya rabu da ita,.Ranar tana zaune tana yankewa Nafisa da ta fara nauyi fare dukkan yaran maza suka shigo a tare bayan ,a kallon su tasan da wani abin suka zo ,kamar yarda tayi tsammani maganar Aurenta da mahaifin Akram ne.

Da mamaki ta kallesu tana mai tambayar su inda suka ji ,babu tsoro suke masu shaida mata Daddyn Akram na garin yace ba zai koma ba sai ta amince da Aurenta sannan a matsayinsu na yaranta sun amince masa,.

Galala ta saki baki tana mai dismissing ɗinsu da hannunta dan a baki ma maganar nauyi take mata,yaya za'ayi ta Auri sirikin ƴarta?Bama wannan ba a tsarinta a lokacin babu Aure kwata kwata hankalinta yana kan yaranta da sirikarta ,bata buƙatar namiji tunda Alhaji BUKAR ya tafi ya barta ,zata iya a haka.

Sai da Nene tayi mata da gaske tukunna ta amince, daga ƙarshe aka daura Aurenta da Daddyn Akram duk da kuwa tace baza ta bishi Gashuwa ba ta bar ƴaƴanta ,.Koda ace bata yi maganar yaran ba dama yana da niyar mayar dasu nashi ya ginasu ya basu rayuwa mai kyau,duk da bai haifesu ba yasan su ɗin masu jin ƙai ne a irin tarbiyyar da suka samu da kuma yarda suka tsayawa Alhaji BUKAR har ya koma ga ubangijinsa.

Wata rigimar suka yi da Nene daga bisani ta amince duk da Nenen tace baza ta bisu ba,Hakan yasa suka dawo kuma lallashinta domin babu mai zuciyar da zai iya tafiya ya bar Nene cikin halin da take na tsufa.

Bayan kwana huɗu da wannan ja'injar suka wayi gari da Rasuwar Nene wadda ta gigitasu,sai a lokacin suke tuna yarda take faɗa musu bata ji a jikinta ƙasa zata kaita Gashuwa,idan zata tafi a garinsu inda ta girma take san cikawa,.Abun wasa da dariya suka maida abun sai bayan tafiyarta maganaganunta suka dawo masu sabo dan haka Ummu ta nemi da Alhaji Muhammad yayi mata Hakuri baza ta bisa Gashuwa a lokacin ba har sai sun gama jimamin tafiyar Nene sannan sun jira haihuwar Nafisa duba da yarda ta kusa.

Bai ki tata ba ya amince saboda yarda yake girmamata da mutuntata.

***** A kwana a tashi ba wuya a haka Nafisa ta haifo yaranta biyu mace da namiji waɗanda suka ci suna daban daban,namijin BUKAR sunan mahaifinta inda suke masa laƙani da ARYAN yayi da macen taci sunan Nene MARYAM ake mata laƙani da AYRA.

Hidima sosai dukkansu sukawa yan biyun dan arziƙine da Allah ya ƙara musu cikin zuri'arsu,sosai suke jin yaran har ransu kada ma kakansu Da kakarsu.

Bayan sun yi Arba'in suka koma garin Gashuwa baki ɗayan su under legal adoption cos ya shirya basu soyayya ta mahaifi wanda basu samu ba baki ɗayan su,da sabon gidan ya fara a cewarsa yana buƙatar zuri'a guri guda sannan gidan na baya bazai ɗauka ba duba da yana san su wadata bugu da ƙari kuma ya yarda da cewa Bad energy na cikin wannan gidan da Sakina ta zauna.

Lokaci guda ya haɗe Jamal da Salman ya musu Aure wanda ya kwashi jama'a duk da kuwa yarda Ummu ta nuna basu tsaya da ƙafarsu sosai ba kada ya ɓata su,sai ce mata yayi Allah ya masa arziƙin da dole ya wadata yaransa.

Lokaci guda ya bawa Kowa Capital ya ɗora sa a abin da yake so bai masu dole da su karbi business ɗinsa ba duba da babu mai interest akai,matan kuma ya nema masu suka cigaba da karatu banda Nafisa wadda tasan dyslexia da ake ikirarin tana da ita a da gaskiya ne,babu karatun da zata iya ɗauka dan haka ta fara aikin da take ƙauna tare da Jamal,.Ganin Alherin sa sai da yasa Ummu kuku,ganin yarda yake nuna mata so ƙauna da kulawa da yaranta da waɗanda ba ita ta haifa ba,yarda yake mutuntata da darajatata da kulawa da ita sai take jin tayi missing abubuwa da dama dan rabonta da samun irin wannan tarairayar tun mijinta Alhaji BUKAR yana nata,

Ganin haka yasa itama ta dage wajen kyautata masa da yi masa biyayya wanda shima yake jin daban tunda abu ne wanda a baya bai samu ba baya ga wahala bauta da rashin ɗa'a da ya sha gurin matar da yake kira matarsa,baya jin kunya wajen kamawa Ummu aikin gidan Musamman girki dayake bata yarda da ko wanne ɗan aiki ba bayan masu gadi da masu gyara compound,idan yana cikin su baki ɗaya jin sa yake a lokacin ya cika mutun wanda yasan daɗin iyali.

    Bayan wani taro da sukayi holding ma Alheri orphanage Nafisa ta haɗu da Suwaiba wadda take jin tayi Aure ta fito,sosai Ummu taji tausayinta dan haka koda Nafisa tayi ma Ummu tayi Suwaiban tazo su zauna tare bata ƙiyaba dan altleast ta samu mai zama da ita gida don baki dayan su suna Chan daga wannan kasar sai waccan da sunan aiki.

Sosai Suwaiba taji daɗi ta saka a ranta baza ta taɓa abin da zasu Allah wadai da ita ba,zamanta dasu har online business ta fara tana mai samun kuɗin ta yana shigar mata duk da bata rasa komai ba.

Zaman su Ayra hannun Ummu ya fara ne da wani contract na shekara uku da ya tasowa Akram a Portugal,dole suka bar yaran sanin sun fara makaranta.

  A cikin shekarun goman abubuwa da dama sun faru ciki har da haife haife inda Jamal da Saimah suke da yara biyu maza Zachria da Fu'ad,Zach ne babba ya bawa Fu'ad shekara biyu,yayin da Jannah da Salman ke da Yarinya Maimoon a yanzu suna expecting wani rabon,dawowarsu dawowace a da suka shirya zaman gidan yarda Ummu ke damuwa a kullum tama mai faɗa musu bata san kansu ya rabe,hakan yasa sukayi amfani da Auren Doctor Sultan da wata Female Doctor junior ɗin sa Doctor Suhaima.

Shin ina yan prison da tawagarsu ?

Lokaci da aka shigar da Sakina da Khafilat zaman karshe Alƙali ya yankewa Sakina life in prisonment yayin da aka yankewa Khaffy Shekaru biyar,bayan ta cinyesu kamar yarda kawon ta yayi mata alƙawari da kansa yazo ya tafi da ita Bayelsa,chan ta tarar da dan uwanta Khalid wanda a yanzu har yayi Aure da yarinyar da ya haɗu da ita wajen amsan magani,sosai suna tsaya masa dangin mahaifiyar sa emotionally da Physically,Nana A'ishah kuwa ta Auri yaran Sarkin tribe ɗin su yayin da Hashim gudu a ƙasar bayan ya tattare sauran dukiyar Hajiya Sakina da tare saving, dawowarta da yarda komai ya chanza yasa itama ta chanza ,babu abin da take buƙata a wannan lokacin bayan peaceful life ,karatu ta cigaba har takai mataki na zama professional Counselor ta ɓangaren masu fama da Damuwa.

Babu wanda ya nemi da sanin yaya rayuwar wani take domin a haka hankali kowa yafi kwanciya.

Saffiya kuwa bayan barinta gidan su Salman ta yanke contact da kowa dan nemo Tata Rayuwar.

******

    Ranar Juma'a da ya kasance ɗaurin Auren Sutan gida ya ɗauki mutane yawanci family ɗin mahaifinsa ne daga ƙyauye Yayin da ƙanwar Ummu ma Atika tazo da nata zuri'ar,

A tare mazan gidan suka fito cikin getzner's ɗinsu farare kowa ya sha kyau,a tare suka wuce inda suka daurowa Sultan Aure da matarsa da yake ƙauna.

Anyi shagali iya shagali dan taron babbane wanda ya haɗe da dawowar zuri'a Alhaji Muhammad gida,ba sai ka tambaya ba a kallo ɗaya zaka san yana cikin nishaɗi da farin ciki,babu abin da yake masa daɗi irin yaga baki ɗayan su sun haɗu a table ɗaya domin cin abinci,yanzu kuma ga jikoki wanda yake jinsu kamar ransa ,ya yarda da cewa Alherin da yakewa yaran wasu yasa Alheri ƙwankwasa masa ƙofa ,ni'ima ta yawaita cikin gidan sa,shi mutum ne wanda baya da kowa bai san kowa nashi ba ,Allah da Rahmar sa sai ya bashi zuri'a da yake alfahari da ,wannan ma kaɗai Arziƙine.

    Bayan kowa yayi settling baki dayan su suka wuce sashen su mai girma da kyau dan ya tsara ya kashe kuɗi dan ya faranta rayukansu,basa da wani abin biyansa baya ga yi masa addu'a .

Zaune Akram yake yana mai jiran abar ƙaunarsa ta shigo cos yau yini guda bai samu ya keɓa da ita ba,kamar tasan abin da yake jira ta shigo falon tana mai yi masa dariya ƙasa ƙasa,tasowa yayi ya karɓi Ummu Kulsum ya kwantar da ita kujera kafin yasa hannunsa a ƙugunta ya jawota jikinsa yana mai ƙokarin kai hancinsa wuyanta,saurin saka hannu tayi ta tare shi tana faɗin.

"SUGAR I'm stinking ka bari naje nayi wanka bana san kaji wani abu apart from ƙamshi a jikina".

Yar dariya yayi yana mai kallon cikin idanunta ,lokaci guda ta juyar da idanta rana dariya ƙasa ƙasa kafin ya ce da ita.

"Dole ki juyar da idanunki SUGARxdan kema kin san babu wani abu da kike apart from ƙamshi,bad odor baya da gurin a jiki ki da wannan tsafta taki da san ƙamshi kawai kice wayau kike san min and I can't help it Hajiya babba har ta fara kiran sunanki "

Saurin ɗauke hannunta daga kan member dinsa da yayi yana mai magana cike da shagwaɓa.

"Ni Allahu Sugar wanka zanyi".

Sakinta yayi ya na mai gyara kwanciyar Ummu Kulsum kafin ya dawo gareta da ɗagata chak yana mai mata raɗa da.

"We can also do it in the bathroom "

Narkewa tayi jikinsa tana dariya kaɗan kaɗan sanin wane mijinta,mabuƙacine wanda ta saba da rayuwarsa bata gazawa wajen ganin ta ɗauke dukkan wata buƙatarsa.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya musu cikin kwanciyar hankali ,soyayya ,shaƙuwa da nutsuwa duk da a wani bangare dole rashin daɗi yazo.

ALHAMDULILLAH....

Nan na kawo karshen labarin ba duk kyalli bane gwal,ba duk wani abu da zaka ga yana kyalli bane zai ja ra'ayinka ka isa gare shi kana tunanin arziƙi ne kai ka wuce,ba komai da ke kyalli bane GWAL.

Kuskure da nayi a ciki Allah ya yafe mun ,abin amfani kuma Allah ya bada ikon Amfani dashi,duk wanda ya amfana yaji daɗin sa ya saka mahaifiyata a addu'a Allah Ubangiji ya ƙara jadada Rahma a gareta.

Mu haɗu a sabuwar tafiya

Nice taku a kullum.

Amina Jamil adam✍️

08130229878

Wattpad: Chuchujay

Arewabooks: Chuchujay

Instagram:Chuchu_jay_

Facebook:Ameenatuh Jameel.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top