chapter 1

BA DUK ƘYALLI BANE GWAL🗾

(When their hearts collide)

NA

AMINA JAMIL ADAM(CHUCHUJAY)✍️

CHAPTER 1

BISMILLAHIR'RAHMANIR RAHIM

Gidan Marayu gida ne da a yanzu mutane da yawa Basu ɗaukar sa da muhimmanci ,bugu da ƙari Kuma Yawaitar sa da tasirin sa sunyi ƙaranci,Galibi na gidajen Marayu a wannan lokaci koda kaga maraya ciki Yana kan Yanayi ne na ƙila wa ƙala,shin shi ɗin maraya ne?Ina iyayan sa ?suna rayuwa ne duniya ɗaya bisa rashin sanin juna ?dalili kuwa shine saboda Yawaitar yaran dake cikin gidan irin waɗan da aka cillar ne aka tsince su ,Babu yarda za'a iya dasu duba da Yanayi na ƙarancin taimako dole sai dai a dangana su da gidan Marayu,duk wani maraya da ke gidan Marayu Babu laifin sa a hanyar samun sa ko Kuma ace Babu Laifin sa a rashin na iyaye da yayi Dan haka ya ƙyautu a jiƙan su a taimaka musu domin idan kai kayi girman maraici ƴaƴan da zaka haifa ba lallai su yi ba,Baushe yace Babu Maraya sai rago shin kana ganin idan Yaran dake kulle Basu samu ɗauki ba daga inda akayi masu katanga ba zasu fita daga wannan sahu na ragwaye?.

    ALHERI OPHANAGE gidan Marayu ne Wanda ke mallakin mutum guda ba tare da sa hannu na gwamnati ba,zugace wadda mutum ɗaya ke ja idan Kuma ka leƙa ka bincika zaka tabbatar da cewa ba ƙaramun mai gayya ke janta ba domin kuwa gidan na daban ne tsarin sa ma haka.Wani Kaya sai Amale ,ALHAJI MUHAMMAD TUKUR GASHUWA shine mallaki na wannan gidan ,ci ,sha ,sutura,karatu da duk wani Abu da mutum zai buƙata a Gidan Yana kan kafaɗarsa,Mutumun GASHUWA ne dake cikin gari yobe inda wannan katafaren gidan Marayu na ALHERI shima yake ,Kalmar wani Kaya fa sai Amale ta sake fitowa domin kuwa mai ɗaukar irin wannan ɗawainiyya sai Babban Kai Wanda ya Tara bai ma San adadin Abunda ya Tara ba,Ya ƙirƙiri wannan gidan cikin tsari na musamman,ya Basu ƴan uwa ,Iyaye ,rufa da rayuwa mai kyau , karatu Abunda yayi nursery zuwa senior secondary education zakayi cikin gidan idan ka ƙare kana da buƙatar bunƙasa karatun ka zai ɗauke maka nauyi a duk gurin da kake San karatu,idan Kuma kasuwanci kake so zai baka jari dai dai gwargwado ka Gina kanka kayi irin rayuwa wadda kake so muddin mai kyau ce,bangare na ilimin Islama ma bai wasa a wannan gurin,Mata idan Zaki cigaba da karatu zai tsaya Miki ,idan Kuma Tsayayye ya fito wala a Gidan wala a waje za'a chanchara Miki biki,haka bangaren adopting ,muddin akasan inda kake,san'arka da Kuma mu'amalar ka to za'a baka yaro tare da sharuɗai masu ƙarfi ,domin kuwa ba wai neman Kai ne ake da suba da za'a bawa Koma wane ya Raine su ba,ALHAJI MUHAMMAD TUKUR GASHUWA ya yarda da cewa su ɗin Ahalin sa ne tunda shima usulin sa maraya ne Wanda yasha gwagwarmayar rayuwa.

    Tun daga Bakin Gate ɗin dake ɗauke da Sunnan ALHERI OPHANAGE zaka San cewa a yarda ake faɗa gidan ya Kai fa ,tsaro mai kyau zai Fara tare ka kafun ka sada da ciki.Daga cikin ɗakin da ya kasance na horon su idan sukayi Laifin da ba dai dai ba kuwa wata yarinya ce da baza ta wuce kimanin shekaru Goma Sha uku ba Akan gwiwowin ta tana shararar ƙwalla, gefe guda Kuma dattijuwar mace da baza ta wuce shekaru Arbain ba da haihuwa zaune kan kujera hannun ta ɗauke da bulala tana mai bin yarinyar dake kneel down ɗin da kallo,Ajiyar zuciya ta sauke kafun tace"Nafisatu kin dage Akan sai kin kashe ni kafun lokaci na yayi ko?Hala gidan nan ke kaɗai ce mutum da kullum ba'a tashi a runtsa Babu rigimar ki,a kullum ke kinfi San Bakin mutane ya hau ki yayi Miki katutu ba?kin dage sai kin zama gagara badau ,yanzu idan ba neman balai ba Ina satar abun wani ya taɓa zama Aro?"cikin kuka Yarinyar da ta Kira da Nafeesatu tace"Big mummy su haɗa mu kawai a gidan nan kowa ya huta tunda Dama Abunda suke so ai kenan,ƙiris ake jira na bar wani gurin ban toshe ba azo a Tada hankalinki  ki Fara mun zancen mutuwa bayan kuma ni jikina Yana bani baza ki mutu yanzu ba sai nayi kuɗi na Gina Miki gida mai hawa uku kin goya Yara na kamar yarda kika goya ni".cike da takaici Big Mummy tace"a yaushe Zaki Yi kuɗin?shekara uku kenan har yanzu kina js1 saboda tsabar daƙiƙanci,sau uku Ana Miki repeating,Baki ɗaya kanki kamar dusa ce cikin ba ƙwaƙwalwa ba,yanzu Ina ɗan kunnen Suwaiba da kika sata,ki fito dashi kafun na tashi na saɓa Miki fiye da Wanda na miki".zuƙar majinan dake ƙokarin faɗo mata tayi tace"ni fa Big mummy Ara nayi ba sata ba ,Kuma ai na mayar Mata inda na ɗauka Amma duk da haka ta wani kawo ƙarata akan na sace,ni Abuna nawa ta ɗauka ban magana ba".

"Assalamu'alaikum,a'a yau Kuma mai ya sake haɗo uwa da ƴarta"?wata dattijuwar Mata da zatayi sa'ar big mummy ta faɗa tana mai shigowa cikin ɗakin.Nafisa na Ganinta ta fashe da kuka tana mai cewa"Mummy Nadiya raba ni ake San Yi da ita,ni ƙarar wane nake kawowa da kullum kamar jira na ake a zo a faɗa Mata tace jinin ta ya hau ko Kuma ta Fara zancen mutuwa,ni Kam sai na Mata gida mai hawa uku sai dai tace Bata so".Dariya Mummy Nadiya tayi ta zauna kusa da big mummy kafun tace"ai baza ma tace Bata so ba,ni da nake Adduar ta bani hawa ɗaya cikin ukun da zakiyi mata,Ƙwantar da hankalin ki sannan Kuma wane ya isa ya raba uwa da ƴa?Amma dai still Nafisan Big mummy dole ne ki koyi guje Abunda zakiyi mara kyau har a zo a faɗa Mata ta Baki hukunci, maza zo nan Bata hakuri kije kiyi shirrin islamiyya. Tasowa Nafisa tayi tace"kiyi haƙuri insha Allahu watan nan har ya ƙare Babu Wanda zai sake kawo Miki ƙarata Dan Babu shirgin Wanda zan shiga balle Amun sharri".kallo Big mummy ta bita dashi kafun tace ta wuce ta Bata guri.murmushi Mommy Nadiya tayi bayan fitar Nafisa kafun tace"Nafisa shagali,Allah dai ya ƙara Mata nutsuwa".kaɗa Kai big mummy tayi tace"Ameen Nadiya,wallahi lamarin Nafisa Yana bani mamaki da tsoro,ace Kai kullum baka jin magana Kuma ba'a isa ka karɓi Laifin ka ba,babban damuwa ta wallahi yarda kanta bai ɗaukan komai,kamar dai Nafisa ranar malamin bokon su ya Kira ni naga performance ɗin ta,wallahi wai yace 1+1 tace 11 ,wai shaɗaya, yanzu ko ɗan primary one ai yasan wannan lissafin balle ɗan js1 ɗin da akayiwa repeating sau uku,ban San Ina zan saka kaina ba,sai nake Jin kamar Lokacin da aka yarda ta Anya wani abun Basu hau kan ta ba?.dafa ta mommy Nadiya Tayi tace"Insha Allahu babu abunda ya hau kanta kawai Yanayin ɗaukar ta ne beside ai ɗaukar Islamiyyan ta abun godia ne tunda tana ɗauka,bagaren nan AKRAM baya Mata wasa,yaran Nan na mutuƙar ƙokari Akan ta ,sai dai Muce Allah ya saka Masa da Alheri".Shiru Big mummy tayi tana tuna Lokacin da ta tsinci Nafisa a Nesa kaɗan daga gidan,A Ranar taje kasuwa tana dawowa a nayin Ruwa Mai yawa wanda sai da ta samu ta ɗan fake ma Amma ganin ruwan yaƙi tsayawa yasa ta nufa gidan,tun daga Nesa take Jin kukan jariri ,a tsorace ta Isa gurin jikin ta na rawa,jaririya ta gani a duƙunkune tana tsala kuka ruwa Yana dukan ta,da sauri taje ta ɗauke ta tana rafta salati domin kuwa jinjiniyar Nan baza ta wuce wata ɗaya ba, kalle kalle ta fara dan ganin ko zata ga wanda ya aje ta dan ba sai an faɗa mata ba kawo ta akayi aka yasar da gangan ta tabbatar ba domin ruwa ake ba da wani zai tsince ta ,Allah wadai tayi da duk uwar da ta haife ta ta mata wanann watsin wulaƙancin.koda ta kai Nafisa gidan Alheri bata bawa Kowa ita ba ta cigaba da kula da ita kamar ɗiyar da ta haifa wadda soyayyar ta tayi mata naso inda ta bata suna Nafisa,.ƙwana biyu da kawo Nafisa suna bacci tare kamar cikin Mafarki taji kamar Nafisan na neman Nunfashi,ille kuwa data farka ta tsinci Nafisan cikin wani mayuwancin yanayi na sarƙewar numfashi,cikin tashin hankali ta fita daren dan ganin Babban likitan gidan,kallo ɗaya ya mata ya gane Pneumonia ne amma bai ƙasa gwiwa ba ya mata check up Dan tabbatar wa,tun daga wanann lokacin soyayyar Nafisa ta sake ninkuwa zuciyar Big Mummy ,a haka ta cigaba da rainon ta cikin Aminci tana bata kulawa dangane da larurar ta.bangare guda kuwa tun kafin Nafisa ta kai shekarun ta na yanzu ta Addabi Uban kowa,Ba'a sati ba a kawo ƙarar ta ba ,daga yau ta haɗo ta da wannan sai ta haɗa ta da wanccan,Big mommy kaɗai ke taka mata burki.

    Tafe Nafisa take tana tsalle domin komawa ɗakin su,a zuciyarta ta gama yanke hukuncin ƙin Faɗa da kowa cikin satin nan amma fa duk wanda ya tsokane ta baza ta barshi ba"NAFI"shine sunan da taji an kira,dakatar da tafiya tayi tana mai danne abinda ya taso mata dangane da sunan da aka kira ta dashi na Nafi,Juyawa tayi tana kallon mai kiran ta kafin tayi wani murmushin yaƙe tace"Boda Akram Wallahi dan kai ne Amma babu mai kira na Nafi na ƙyale sa,na faɗa ma kowa gidan nan Ni sunana Feenah ba NAFI ba ,ina laifin kace Nafisa ɗin idan kana baƙin cikin kira na Feenah ɗin,An cuce ni An saka mun sunan Tsaffi to a barni na gyara mana"ƙwafa tayi ta sake faɗin"dan kaine wallahi ,bazan iya yiwa mijin da zan Aura rashin mutunci ba".Kallan ta yake cikin nutsuwa kafin yace"to ai baki nemi a kira ki Feenah ba because Feenah sunan yan gayu ne yan boko amma ke kam sai dai lahaula walaƙuwa ta,nan Simple English" Brother baki iya faɗa ba sai Boda kamar kin ga wani bucket ,for God sake mene Wahala a Brother Kullum sai kinji an faɗa "taɓe baki tayi tace"eh mana kullum yan matan ka na gidan nan na faɗa,Ni bazan faɗa ba Boda na iya shi zan faɗa kuma ba hakan ke nufin wata zata Aureka ba bayan ni,meye ne a bokon Notin dey enta Amma ai na iya karatun Kur'ani kuma idan na mutu ai ba da boko za'a tambaye ni ba,idan ban iya boko ba babu mai ƙona ni,kuma ba shi ke nufin bazan kuɗi ba "juyawa tayi tana mai cewa"Ni bari naje nayi shirin Islamiyya kafin nayi Latti shima ka fara faɗa mun daƙiƙiya tunda kullum ƙaramin abu kake nema ka zage ni dan kana da kyau".hannu yasa ya juyo da ita kafin yayi ƙaramar dariya yace"zamu gani idan zan Auri mara san karatu ,and mene ya haɗa ki da suwaiba?"Turo baki gaba tayi tace"Boda Akram daga fa na ɗauki Aron ɗan kunnen ta shikenan wai na sata mata taci sa'a nayi Alƙawarin bazan faɗa ba watan nan duka wallahi da sai na ci mata zarafi".Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"bana San Aron ma kina Yi ,nazata na faɗa miki duk abunda kike so kina faɗa mun idan na fita na siya miki,dan Allah bana san rigimar nan Feenah".washe haƙoran ta tayi jin ya kira ta da Feenah kafin tace"ai tunda kace Feenah an gama ,yanzu dai nasan baka san nisa dani ne amma ai Islamiyya zan zo na sameka ka sakeni  bari naje na shirya".Kallan hannun sa dake riƙe da nata yayi, murmushi yayi ya sake ta yace "maza kije to".da gudu ta kwasa tana mai cewa Ina zuwa yanzun nan".Binta yayi da kallo yana mai girgiza kai,bai san yaya zaiyyi da Nafisa ba cikin gidan nan,duk yarda zaiyyi tayi karatu bata ɗauka duk da kuwa salo salo da yake bi ganin ya Mata lesson Amma abin yaci tura ,bata da magana sai cewa Shi zata Aura dan har dambe zaka tsince ta tanayi akan sa,Yana jinta a ransa sosai tun tana jariri Allah ya haɗa jinin su sannan yana so a rayuwa ya bata gudunmuwa sosai,kaɗa kai yayi ya bar gurin yana mai tunanin gwagwarmayar da zasu yi idan ta gane zai tafi Yankee karatu.

    Kai tsaye Nafisa ɗakin su ta wuce tana jin wani irin nishaɗi da ya danne haushi Suwaiba,shiga tayi tana yan waken ta,Abokan zaman ta babu wanda ke ɗakin,ɗakine mai girma wanda ke da madaidaitan Gado guda huɗu sai gefe wardrobe ɗin su na kaya then Set of kayan Kallo,ɗakin is a comfy room ,Khadija ita ce Babba a ɗakin wadda ke da shekaru sha Tara sai Hamamatu wadda bazata wuce sha bakwai ba sai Suwaiba dake tsarar Nafisa ,kowa na kiran Khadijah Yaya amma banda Nafisa haka nan take katse idanun ta tace Khadijah ,Hamamatu kuma ta kira ta da Hama,Babu wanda cikin su yake complain Dan sun San abunda Bata saka kanta ba babu mai saka ta.Nafisa na ƙoƙarin ciro hijab Suwaiba ta shigo,tana ganin ta tace"Yauwa Nafisa dama ke nake nema,Yaya Khadijah tace ba taga jambakin ta ba wanda na tabbata kece kike ɗauka cos nima ai kin ɗauka mun ɗan kunne,ki fito dashi ki aje mata bazan faɗa mata kece ba amma wannan karan kaɗai dan baza kije kina yin sata ba ina kare ki ,ace ke hannun ki ba zai zauna jikin ki ba ,sai kace wata ɓera,ko wadda ta haɗa iri da ɓarayi,wallahi ki gyara Halin ki kafin dare yayi miki,To shawara ce".

To be continue

08130229878

WhatsApp follow me on Wattpad and Arewa books @Chuchujay.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top