9


___Riƙe Mata kunne big Mummy tayi da ƙarfi lokacin da ta cimmata tace"zo nan Allah yau sai kin faɗa mun irin Abin da yake damun ki idan ba haka ba Ni da kaina zai nemo da duka ".Riƙe ta Mummy Nadiya Tayi tace"yi haƙuri Big Mummy tukunna kada ki dake ta,shin wai mene ma tayi ".Nuna result ɗin tayi tace"na sha tara taci amma yarinyar nan saboda tsabar har yanzu ɗaƙiƙanci bazai bar ta ba tazo da murnar ta wai taci na biyar,yanzu ɗakikancin Nafisa har ya kai bata banbance ƙwanan wata da sakamako?Bama wannan ba shi ai ba sabo bane gare mu sabon abun shine wai  Nafisa har ta iya murza gishiri a ciwan wasu,abu ta sani kan Asiya ta room 15 wallahi yarinyar nan da yake tasan Asiyan baza ta so a sani ba shine take amfani da abun kan Asiya,mene Nafisa ke san zama? Ina jin zan sake duba Applications na Adoption nasaka sunan ta ƙila idan wani ya ɗauke ta zata nutsu lokacin da tasan cewa rayuwar waje ba rayuwar cikin gidan nan bace".Kuka sosai Nafisa ta rushe da lokacin da taji Abunda Big Mummy tace ,ƙafafunta ta kama tana mai cewa"dan ƙaunar ki da Ubangiji kada ki bada Ni wasu su ɗauka, Wallahi idan akace na rabu da ke da gidan nan zan mutu ne ,bazan iya ba,dan Allah kiyi haƙuri,wallahi zanje na bawa Asiya haƙuri"fahimtar cewa Asiya ta faɗa kai tsaye yasa tayi saurin Girgiza kanta ciki kuka tana mai cewa"Aunty Asiya,dan girman Allah Mummy kiyi haƙuri wallahi zan gyara halayena yarda zasu dawo burge ki,bazan ƙara yin abinda nayi ba,dan Allah kada ki bada ni,Sakamakon nan kuma wallahi jikina har yanzu bai daina bani na biyar naci ba kawai an min cuwacuwa ne an bawa Salihin Ajin mu ".hannu Big Mummy tasa a fuskar ta tace"kina ji ko Nadiya,har yanzu bata yarda na Sha tara tayi ba ,ki barni dan Allah na zane ta ko hankali,nutsuwa da ƙoƙari zasu shigeta".Haƙuri Mummy Nadiya ta cigaba da bata dan tasan in Nafisa batayi wasa ba zata sha duka.

Shiru Big Mummy tayi tana mai Kallan Nafisa dake faman zazzare ido daga nesa kamar an kaɗa jaɓa a buta,wani irin tausayin ta da a kullum take ji ne ya bijiro mata,"zo nan ki zauna"Shine abinda ta faɗa tana mai nuna mata gefen ta,duk da tsoran da Nafisan ke ji bai hana ta zuwa ba tana mai cewa",na yarda dake ai baza ki dake ni ba ɗan Allah kinji".Naji bazan dake ki ba"ta bata amsa tana mai sake nuna mata gurin da tace tazo ta zauna..kamar wata ɓarauniya haka Nafisa tazo ta zauna tana ɗan Gunjin tsoro.cike da kulawa Big Mummy ta kama hannun ta tace"Nafisa ba zan dauwama dake a Duniya ba,wata rana zaki wayi gari kiji babu ni,to idan na tafi ya kike ganin zakiyi da Wannan Halayyar taki?ita rayuwar nan da kike gani ana so ka kasance cikin mutane masu iya zama a duk inda Rayuwa zata kaisu,kada ka zama maƙaryaci,ka riƙe gaskiya da Amana,Kada ka zama munafiki ko mai tura hancin ka a inda ba a gayyace ka ba sai kiga Rayuwa tayi maka inganci kowa kuma zai soka,bana cewa zaki dauwwama cikin gidan nan Nafisa!domin kuwa kowa dake gidan nan in one way or the other zai tafi,Ni bani na haife ki ba amma a zuciya ta Ni mahaifiyar ki ce ,yarda nake jin ki babu wanda zai faɗa mun ba wai soyayyar ƴa da uwa bane,kinga kuwa dole a rayuwa na so miki abu mai kyau mai amfani,dole ki gyara halin ki Nafisa kada lokaci ya ƙure miki"ganin idanun Big Mummy ɗauke da ƙwalla ba ƙaramin tada ma Nafisa Hankali yayi ba,da sauri ta ta rarrafa ta faɗa jikin ta tana mai cewa"Allah zan gyara Mummy,wallahi zan gyara Halina ,ki dai na faɗa mun idan kin mutu,ni Wallahi abun bai kai nan ba ,bari ma kiga yanzu na tashi naje na bawa Aunty Asiya haƙuri" bata jira cewar su ba ta tashi da gudun ta dan zuwa gurin Asiya.Share ƙwalla Big Mummy tayi tace"ko dai ban bawa Nafisa tarbiyya mai kyau ba Nadiya?". mummy Nadiya da itama ta zama emotional ne ta riƙe hannun Big Mummy tace"Babu inda kika gaza dangane da Nafisa dama sauran yaran dake cikin gidan nan,kawai dai kin san ƙuruciya kowa da irin tasa ,insha Allahu wata rana sai dai Ayi labari".Sniffing Big Mummy tayi tace"Allah yasa mu bada labarin".

    Bayan fitar Nafisa da gudun ta ta nufi ɗakin su Asiya,tana isa ta tarar da Asiya zaune tana Danna waya ,gurin ta ta nufa ta tsaya kan ta tana Kallan ta kafin tace"Aunty Asiya gurin ki nazo"tashi zaune Asiya tayi tana mai kalla Sa'adatu dake zaune kan kujera tana Kallan su musamman ganin Nafisa ta shigo tana kuka,"mu fita waje ne"?Asiya ta tambaye ta dan bata san Sa'adatu taji mai zasu tattauna wanda tasan zuwan Nafisa maganar da bata so ne wani yaji.. jin Abunda ta faɗa ne yasa Sa'adatu saurin tashi tana mai cewa"Aunty Asiya bari naje na samo ruwan zafi kinsan water heater din mu lalace,Nafisa ina zuwa"tana faɗin haka ta fita a ɗakin.

Hannu Nafisa ta saka ta goge idanun ta tace"akan abinda nayi miki kiyi haƙuri dan Allah,nasan ban kyauta ba kuma bai kamata nayi hakan ba,amma tunda nayi ƙiyi haƙuri ki yafe mun,insha Allahu bazan sake ba,ganin ki kuma da nayi da Hudu Mai gadi nima ban yi niyyar faɗa ba ,tunda da ace nayi niyya tuntuni zan faɗa kece kika jawo,Kinga na farko sai kiyi ta girman kai a gidan nan kamar ke din ƴar Gidan Alhaji Muhammad Tukur ce mai gidan nan,sai kina ji kamar kinfi kowa ,ko kin fi wani kyau,gashi kina san aibata mutane kamar ke kin cika goma baya kin san mutun tara yake bai cika goma ba,gashi ƙiyi tama Sister Khadija magana da isgilanci da sunan ƙawance,abun yana bani haushi sosai shi yasa kike mugun bani haushi,baki da Aiki idan kin zauna kika ji ana magana ta ki zage Ni ki tsine mun,yana ɗaya daga cikin abinda yasa na faɗawa Saurayin ki Abinda ya faru,kin bani Haushi ranar sosai musamman da ya zamana kin gama faɗa wa sister Khadija magana Mara daɗi ke wai kina da farin jini ana sanki ,shine ɗaya daga cikin abinda ke shaƙamun dangane dake ,kiyi ta wata tafiya kamar ɗawisu bayan kin gama zuwa kinyi iskanci da Kazamin nan Hudu mai gadi kuma...ɗan tari Asiya tayi tace"ke Nafisa its okay mana,naji bani kyautawa,amma haƙuri ne kika zo bani ko kuwa tone tone,its okay ya wuce".shaƙar majinan dake neman gangarawa Nafisa tayi tace"haƙuri nazo baki amma ina san na faɗa miki gaskiya ne kada na baki haƙuri na tafi kuma ina jin haushin ki idan kika cigaba da abunda kike, kinga idan kika san abinda kike yi mara Kyau ba sai ki daina ba mu daina faɗa,nasan baki sona nima kuma ba wani birgeni kike yi ba,amma idan kika koma mai hali kamar na sister khadija nima sai na dawo salaha kamar Sa'adatu,Yauwa kada na manta ban faɗa miki wannan ba,kina da shegiyar mugunta da ƙeta,Ni duk abunda nake wa Sister Khadija ko sister Hamamatu babu wanda yake mun Abinda kike wa Sa'adatu,kiyi ta cin zalinta kina bata wahala,ita kuma kamar banza tayi ta tsoran ki kamar zaki datsa mata rayuwa,ke ba wani kyau ba,Allah Aunty Asiya da zakina Kallan Mudubi na minti Goma duk bayan Awa biyu zaki gane yarda hancin ki ke kamar Alkaki wani ɗan ɗus kamar ke da umma Shehu ta Film ɗin hausa yan gida ɗaya ne ido kawai ta fiki mai kyau,Ni ba ba'a nake miki ba amma baki da kyau ga halin ki bashi da kyau,amma idan kina hali mai kyau sai kiga ana ganin kyan ki"ƙwalla ta sake matsa kafin tace"ki yi haƙuri ki yafe mun insha Allahu bazan sake miki Abunda zaki ji haushi na ba da ikon Allah,Allah kuma ya shirye ki nima ya shirye Ni,kin yafe mun?".Asiya da ta rasa abinda zata yi ne tace"na yafe miki Nafisa"kafun ta sake cewa wani abu Nafisa ta juya tana cewa"nagode"Sannan ta fita a ɗakin,da saurin Asiya ta nufi bakin Mudubi dake ɗakin tana mai Kallan kan ta,hannun ta ta saka ta taɓa hancin tace"aikin Banza ina ce irin hancin mun ake yayi"sake shafa hancin tayi kafin tace"kuma fa ɗan ƙaramin ne,kai amma wannan Yarinyar ƴar iskan yarinya ce,Wane irin haƙuri ne wannan mai ɗauke da cin mutunci"?okay Asiya calm down kada kiji Haushi kada kiji Haushi,ke kyakkyawa ce ke.."ke kuma lafiyar ki kike magana da kanki ke ɗaya bakin Mudubi"?Aunty Maryam da shigowan ta kenan ta tambaya tana mai zubawa Asiya ido,takowa inda take  Asiya tayi tace"wai Aunty dan Allah hancina irin na Umma Shehu ne?"dariya Aunty Maryam tasa tace"sai yau kike sani?ai na Umma Shehu ma yafi naki kumari"takawa Asiya tayi ta fita a ɗakin tana cewa"bari naje nasha Iska".

Shin ina mutanen Yankee?

    Already suna da accomadation ,isar su ƙasar kuwa Abune wanda Yayi ma Akram daɗi musamman ganin yarda Saffiyya ke faman basa wahala daga wannan sai wancan ,she's very demanding wanda ya tabbata tana taking advantage ne na Alƙawarin da yayi mata, guri ne aka sama masu Mai Apartments da yawa ,yaji daɗi sosai da ya zamana daƙin Saffiyya ba Floor ɗin da yake bane,yana 3rd floor tana 2nd,Sosai Safiyya bata ji daɗi hakan ba amma ta ƙwantar da hankalin ta akan it doesn't matter .kafun su fara processing komai alƙawarin sa ya fara sauke wa na Kaita aka yi mata fixing haƙori kafun suka fara processing Abunda Basu gama ba na School,a tare suke a  Bangare Science inda suke karantar Software engineering ,duk da tsaurin da course ɗin yake da shi amma Safiyya ta nace dan bata san abinda zai raba ta da Akram ko kaɗan ne,she wants to be all over him a koda yaushe wanda a ƙwanaki ƙalilan Abun ya fara shigar wa Akram hanci musamman da ya zamana abu kaɗan zata kawo alƙawarin sa na cewa zai kula da ita na tsawan shekara guda..dawowar su kenan daga class ko wane a gajiya ,tare suke cikin Lift ɗin da zai kai su floor ɗin su kowa yayi shiru da abinda ke dauke zuciyarsa,shi yana tunanin Yarda Nafisa take ita tana tunanin yarda zata samu ya zama nata ita kaɗai dan ita da san samu ne ma suyi zaman su nan kada su koma Nigeria,Ajiyar zuciya ya sauke yana mai cewa "nayi kewar Nafisa ko yaya take ciki,ɗazu na kira Big Mummy Bata kusa,ina san naji muryan ta".wani irin Tsaki Safiyya ta saki wanda Bama tasan ta saki ba.kallan ta yayi yace"lafiyar ki ?"haɗe rai tayi tace"lafiya ta mana Akram,kai dai kasan wacece Nafisa a gurina idan da san samu ne ka daina mun maganar ta dan wallahi tsanar ta kake ƙara mun,ai abun murna ne ma ace yau mun rabu da Nafisa kaima Allah ya yaye maka liability"ƙarar sautin Isa second floor ne yayi, kallan ta yayi lokacin da ƙofar ta buɗe yace"bismillah"juya idanun ta tayi tace"naji an jima zan zo ka ɗan mun Bitar Abunda muka ya yau cos wallahi ban gane ba"bai ce mata komai ba ƙofar ta kulle,shafa fuskar sa yayi yana mai Furta"ya Allah"shi kansa ya san zuwan Safiyya gurin nan was a very bad idea.

********************************************

NASSARAWA STATE

    Dambe ne ake sheƙawa tsakanin Khafilat da Saima a harabar gidan kamar zasu kashe kan su ,cikin ikon Allah Saima ta samu galabar Khafilat ta buga mata kan ta da bango ,wani irin ihu Khafilat ta saka lokacin da wata azaba ta ziyarci dukan sashen jiki ta,da wani irin gudu Hajiya Saddiqa dake saman Balcony tana Kallan faɗa ta fara saukowa tana mai faɗin "innalillahi waina ilahir rajiun"koda ta fito bata yi wata wata ba ta gwara kan Saima da bango sannan ta riƙe ta tsam tace wa Khalid wanda ya fito shima da yaji ihun da yaje ya ɗauko mata dorina wadda ta aje ta ne dama dan dukan yaran Hajiya Hadiza,da gudu ya shiga ɗakin sai gashi da bulalar yana mai cewa"AMAH ki barni na fasa mata kai mana yarda babu kowa gidan nan ta mutu kan su dawo"kaɗa kai Hajiya Saddiqa tayi tace"ina ai ba sai ka kashe ta ba,idan ka kashe ta zalin wa zakucii,maza Khafilat karɓi bulalar nan ki fara zuba mata har sai kinji Nutsuwa tare dake"kamar kuwa Khafilat na jira ta ƙarɓi Bulalar ta fara zulawa Saima wadda ke hannun Hajiya Saddiqa gam,ihu kawai Saima Take tana kiran Ummunta wadda bata gida.sai da Khafilat ta zane ta sosai kafin Hajiya Saddiqa ta sake ta tana mai cewa dan Allah gobe ki sake buga mata kai da bango ki gani ,shegu gayyar tsiya,ki yi kneel down Kuma anan har sai uwarki ta dawo,babu musu Saima ta yi kneel down ɗin tana ta kuka kamar ranta zai .,tunda Salman ke buɗe gate ya hango Kamar Saima bakin corridor da Mamaki ya koma cikin motar ya shigo dan shigo da ita ciki yana mai cewa "Ummu Saima ce fa ke Kneel Down ƙofar ɗaki jikin ta ko uniform Bata cire ba"Sultan dake bayan motar ne ya buɗe kafun Salman yayi mata Key ya fita ya shiga gidan inda Ummun nasu bata ce komai ba illa kallan gefe da take,ganin haka yasa Salman shigar da motar ciki.koda isa gurin Sultan ne tsaye kan Saima yana balai yana cewa"uban da ke sawa baki tsayawa a makaranta muzo ɗaukan ki sai kin biyo su shine zai sa kina shan wahala"takowa Salman yayi gefe Ummun su hannun ta riƙe da hannun Samrat."tashi muje ciki "shine Abunda kawai tace tana mai ɗauke idanun ta daga kan Jikin Saima da yayi ruɗuruɗu da bulala.bayan sun shiga bangaren su ne Hajiya Hadiza tace"mene kika yi?"cikin kuka tace"Ummu driver fa yaje ɗaukan mu makaranta muka taho tare shine kawai a mota Khafilat ta ƙwace mun pen ta ɓalla ,ban kula ta ba ,ina duba Assignment Kuma ta yaga mun littafin saboda kawai na fita cin mark,shine fa muna dawowa gida ta ƙwace mun Lunch box wai sai na bar mata, dan ina san ƙwacewa ta cilla a cage ɗin Patrick kuma duk yayi kashi a ciki,muna faɗa Amah ta sauko a riƙe ni tasa Ya Khalid ya ɗauko mata dorina Khafilat tayi ta duka na.kuka ta sake rushewa dashi,sosai abun yayi ma Hajiya Hadiza ciwo amma tayi ƙoƙarin dannewa ta hanyar faɗin"kiyi haƙuri to,lunch box Kuma ai kina da wani,Allah zai saka miki"jin Abunda Mahaifiyarsu ta faɗa ne yasa Sultan cewa"wai Abunda zaki ce kawai Kenan Ummu?mu kullum sai dai ace muyi hakuri,haka jiya sabon Sneaker na na gani Khalid ya saka bakin Patrick yana lalata mun amma da na faɗa miki cewa kikayi nayi hakuri,ai wallahi dan kince mu daina biyesu muna faɗa ne wallahi da sai na wula sa Kejin karan nan"Salman dai bai ce komai ba illa fita da yayi a ɗakin kai tsaye ya Nufi Sashen Hajiya Saddiqa, yana zuwa kai tsaye ɗakin Khafilat ya nufa fitowar ta kenan a wanka ai kuwa ya cire belt ɗin jikin sa ya fara zula mata,ihun da ta rafta shine ya jawo hankalin kowa,da gudu Hajiya Saddiqa ta shigo,ganin abinda Salman yake yasa ta buga ihu tace"Salman Fyaɗe kazo ka mata?"aikuwa hakan yayi dai dai da shigowar Hajiya Hadiza biye da yaran ta,jin Abunda Hajiya Saddiqa ke faɗa ne yasa Hajiya Hadiza faɗin"Haba Saddiqa ,wane irin magana kike haka".nuna ta tayi da yatsa tace"idan Alhaji ya dawo zaki tambaye sa"Hannun da tasa ta riƙe Salman ya buge yana mai cewa"dan Allah Aunty Idan kin kira sa yazo kisa ya kashe ne ko ya Koreni cikin gidan na shine zaki burge ni,a cikin yaran ki Duk wanda yace zai ci zalin ƙannena wallahi sai naci Uwar yaro,ke kawai zaki taɓasu na kyale shima darajar Baba ne"marin da Hajiya Hadiza ta sharara masa shi ya tilas ta masa yayi shiru,nuna masa hanya tayi tace"fita"babu musu ya fita ransa na tafarfasa,Dariya Hajiya Saddiqa tasa tace"wallahi kun shiga uku yau a cikin gidan nan Hadiza,bari Alhajin yazo baku ga komai ba"

TBC

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top