8
_____Koda suka fita a ɗakin suka mara mata baya ,Jan basket ɗin take idanun ta da ƙwalla,da mamaki Khadija da ta cimmata tace"wai ina zaki da tilin kayan wankin nan?da nawa da na Hama dana Suwaiba a ciki ba naki ne ke kaɗai ba"goge idanun ta tayi tace"Sister Khadija ki ƙwantar da hankalin ki wankin nan bani zanyi ba mai wanki nace, ke dai ko biyo ni idan zaki je ,nama gabatar daku ga juna"Binta suka cigaba dayi har sai da suka isa bakin ɗakin su Asiya inda suka ci sa'a kuwa Asiya na zaune da Zainab ɗaya daga cikin yan ɗakin su suna hira ,Lokacin da Asiya taga Nafisa da ƙwandon kayan wankin sai da gaban ta ya faɗi musamman da ta tuna da yarjejeniyar su,Murmushin yaƙe tayi tana mai Kallan Khadijah tace" Hajiya Dije yanzu nake niyar zuwa ɗakin ku na ɓige nan ina hira da zainab"Ajiye ƙwandon Nafisa tayi gaban ta kafin Khadijah ta bata wata Amsa tace"Aunty Asiya ina wuni wai fa naga yau sati nace bari nazo na bawa Aunty na aiki,wanki ne nan na ƴan ɗakin mu,sabulu nan da Omo idan bai isa ba ki ƙara da naku,shikenan ta rage mana mu".cike da Mamaki Zainab tace"Nasan dai baki da kunya Nafisa ,amma ban zata rainin ki ya kai haka ba,Yaya Asiya ɗince zata miki wanki?hala kinsha wani abu kafin kizo nan?"...wani banza kallo Nafisa ta bata kafin tace"sai ki nuna mun inda rainin yake ,ina ce da nazo nan Aunty kikaji na kirata kuma har da gaisuwa,Ba ruwan ki to dan tsakanina da Aunty Asiya mun ƙulla Alaƙa mai kyau kada kice zaki saka bakin ki ciki,idan kuma so kike kiji mene yasa na kawo mata wanki sai na faɗa miki".da Sauri Asiya ta tare ta tana mai faɗin"ya isa dan Allah,ke Zainab mene naki,kamar yarda ta faɗa miki tsakani na da ita mun samu Alaƙa mai kyau da kuma fahimta mai kyau so Please".daga gira ɗaya Nafisa tayi tace "ai da kin bari na faɗa mata taji daɗin ɗorarwa,gasace muka saka tsakanin mu na cinye ta,kinga hakan yana nuna irin shakuwar da mukayi tunda har gasa zata shiga tsakanin mu,bugu da ƙari kuma Aunty Asiya bata cikin masu girman kai shi yasa ina cinyeta ta yarda da mun wanki duk kuwa yarda naso hanata,amma idan ba haka ba Ni ai mai taya ta wanki ce"..kaɗa kai Asiya tayi tana dariya tace"Aikuwa ,Wallahi dai,kada ki damu yar ƙanwata tas zan wanke kayan nan".
"Har da guga"Nafisa tayi pointing kayan tana mata murmushi,fahimtar da Asiya tayi na cewa ita tace harda guga yasa ta cikin wata Dariyar tace"harda guga ƴar ƙanwata".Tafa hannu Nafisa tayi tace "Ni bari na wuce ɗaki"koda ta fara tafiya kamar jela haka su Khadija suka bita kowa da tambaya fal a ransa dan sun san cewa tsakanin Nafisa da Asiya babu alaƙa mai kyau babu kuma yarda za'ayi cikin sati guda su ƙullata,tabbas akwai lauje cikin naɗi..Suna Isa ɗakin su Khadijah ta kamo hannun Nafisa tace"Nafisa mene ya faru yanzun nan?"ɗan juya ido tayi tace"mene kuwa ya faru?,Asiya ce zata mana wanki ,kunga satin nan babu abinda zamuyi illa rainan damuwa ta".Dariya Hamamatu tasa tana mai cewa"aikuwa sai dai rainon damuwar ki Nafisa,wane stunt ne wancan kikayi Abeg kada ki jawo mana matsala fa,babu yarda Asiya zata yi maki wanki a Asiyan da na sani ƙwanaki ƙalilan da suka wuce,idan kuma ta yarda da wannan Sabuwar drama ɗin tayi Maki wanki dole ne akwai abu a ƙasa dan haka zaki fara magana".zama Nafisa tayi tace"to tunda kun yarda akwai abu a ƙasa a bar shi a haka man idan baku san wankin kuje ku tsinnto naku ku wanke da kanku mana".zama Hamamatu tayi gefen ta tana Kallan ta kafin ta sauke Ajiyar zuciya tace "idan tayi tsami zamu ji ,and wane yaƙi banza,tunda ta karbi wankin zata yi har da guga mu ai Alhamdulilah,amma dai ki sani ban shirya zuwa amsa doguwar tambayar Big Mummy ba dama ba hannuna ciki"...Khadija da bata iya faɗin komai bane sannan ga mamaki fal ranta ta ƙada kai ta juya dan komawa ɗakin su Asiya taji Abunda yake faruwa,koda taje Zainab ta shaida mata tana backyard tana wanki babu ɓata lokaci ta nufi gurin ,abun yayi mutuƙar bata mamakin ganin Asiya na turƙan wankin su , takawa tayi gareta ,ba tare da tace komai ba ta zauna tana mai faɗin"sannu,Akwai Abunda zaki faɗa mun wanda ban sani ba?". Fuska ɗauke da yaƙe tace"kaji Khadijah ,mene za faɗa miki wanda baki ji ba ɗazun".hannu khadija ta ɗaga mata tace"kada ki fara wannan dani dan Allah Asiya,nasan cewa Ni dake muna da banbancin ra'ayi da hali amma ina so ki sani duk gidan nan babu wanda na bawa ƙawance na sama dake duk da kuwa babu abinda nake samu,i know you're using me,nasan Adadin amfani dani da kike yana da yawa Asiya amma ban taɓa ƙorafi ba, nasa you're a great Manipulator Amma still ban rabu dake ba and ba sai na tuna miki cewa nasan irin ƙiyayyar da kike wa Nafisa ba, babu yarda za'ayi haka kawai dare ɗaya ku kulla alaƙa da har zata kai ki da yi mata wanki,no wani abu is Off Dan haka ki faɗa mun mu samu solution,Ni nasan Halin Nafisa sannan Nasan naki,ita ɗin yarinyace har yanzu wadda tunanin ta bai kai naki ba sannan akwai abubuwa da dama da za tayi a kan kure wanda yake dole ne a ƙwabe ta,so ki faɗa mun mene yake faruwa ".
Goge kumfar dake hannun ta tayi tace"Fine,nasan cewa Ni ba mutuniyar kirki bace,I'm very bad and I know ,a ganina abuna ke dawo mun ta hanyar Nafisa,kalli nan Khadija duk abunda kika sani a kaina wanda na barki kika sani ne,wanda Nafisa ta sani kuma ban taɓa tunanin wani ɗan adam zai sani ba ,kama ni tayi ina Having sex da Hudu ma gadi har sau biyu amma sheɗaniyar yarinyar nan bata taɓa faɗa ba sai da Yusuf ya zo da batun Aure na,i wish zan iya kashe ta ta mutu da Sirrin nan musamman idan na tuna tayi sanadiyar rabuwa ta da Yusuf"..cike da Mamaki Khadijah tace"you're bad Asiya,and bana tunanin zaki chanza musamman da ya zamana har a wannan gejin kina batun kashe Nafisa,ba wai ban san da maganar ki da hudu bane ta faɗa mun amma bata bani full details ba ban Kuma san tana Blackmailing ɗin ki dashi ba amma Ni yanzu idan kin shirya gyara abinda kika ɓata sannan kin cire a ranki kina san ganin bayan Nafisa sai mu nemo solution,amma kafin nan ayi wanki lafiya".tana faɗin haka ta tashi ta bar gurin tana mai ƙin sauraran Asiya dake aikin ƙiranta, She's still bitter dole ne kuma ta sauke duk wani makamanta muddin tana nemarwa kanta mafita akan kuskuren ta..
Bayan Asiya tasha wanki da uwar guga bayan ƙwana biyu ta haɗo kayan dan maida musu ,koda taje Khadija kawai ta iske sauran sun wuce Boko,cike da damuwa ta kalli Khadijah bayan ta karbi Kayan tace"Dije ina san muyi magana".kaɗa kai khadija tayi ta faɗa mata tana sauraran ta,bayan sun zauna ne tace"ban san ta inda zan fara ba Khadijah ,amma nasan cewa a magana ta bazan boye miki komai ba,kiyi haƙuri da abunda zan faɗa wallahi daga zuciya ta ne kuma bana so nayi miki ƙarya,kinga Nafisa wallahi bana santa bazan boye miki ba kuma na yarda da cewa saboda halayyar ta na rashin ɗa'a da fitsara ne ya kai mu ga haka amma kamar yarda kika ce komai yana da magani ina so na gyara ƙiyayyata ko Allah zai duba Ni wani mijin ya fito mun muyi Aure, wallahi Khadijah ina san nayi Aure ,bana ganin Rayuwa cikin gidan nan zata fishe ni ,Ni dai na farko ba Karatu nake sha'awa ba idan ma nace zanyi wallahi bazan maida hankalina ba, yanzu Ni ki faɗa mun menene solution ɗin ,ko mene zanyi wallahi "...Kallan ta Khadijah take har a lokacin kafin tace "banji daɗi ba da naji kince baki san Nafisa ,amma kamar yarda kike san gyara ƙiyayyar ki Abune mai kyau,shi kuma Aure da kike ganin nufi ne na Allah, wallahi duk lalacewar ki idan Allah yace ga ranar da za kiyi Aure a ranar zakiyi ,kiyi haƙuri ki ƙwantar da hankalinki,Maganar solution kuma abu ne mai wahala amma nayi imani da Allah shine dai dai Asiya,na farko babu wanda yasan Hudu da wa yake mu'amala bayan ke ,da wane kuma zaiyyi nan gaba,mu marayu ne sannan duk soyayyar da za'a nuna Mana gidan nan wallahi baza ta kai wadda iyayen mu da suka haife mu zasu nuna mana ba,dole ne mu koyi san kan mu da kan mu kafin wani ma ya so mu,kinga already fa muna da tawaya bai kamata kuma ace muƙarawa kan mu wata ba,Ni yanzu abinda nake gani shine dai dai muje tare dake ki shaidawa Big Mummy Abunda yake faruwa , nasan kamar tonawa kanki Asiri ne amma ya kike ganin Tonan Asirin duniya da kuma lahira?kinga idan Big Mummy ta sani nasan zata miki faɗa sosai and ran ta zai ɓaci mutuƙa amma hakan yafi akan ayi ta boyewa,Amma shawara ce bazan miki dole ba".....shiru Asiya tayi tsoro fal ranta ,take taji wasu hawaye suna neman zubo mata ,a hankali kamar bata san magana tace"muje na faɗa mata".ɗago haɓarta Khadijah tayi tana kallan cikin idanun ta tace "kin tabbata Asiya?".,tashi tsaye tayi tace "na tabbata Khadijah muje ki raka ni kafin na kasa"...
Bayan Sauraran Khadijah da Asiya da Big Mummy tayi ba ƙaramin shock abun ya bata ba,tayi mamaki mutuƙa musamman da ya zamana case ɗin da hudu sannan wai har Nafisa tasan tayi amfani da gazawar ka tana saka abu,Tabbas yaran dake ƙarƙashin su abun tausayi ne saboda duk yarda suka so basu tarbiyya ba zai iyu kamar yarda zasu samu gidajen su ba da suna dasu,yara ne masu yawan gaske ta ina zaka fara?,sassauta Zuciyar ta tayi domin wannan case ne da yake buƙatar kulawa and case ne da ya kamata kaja yaran a jiki koda zaka nuna masu kurensu,babu ɓata Lokaci ta aika aka kira Hudu wanda tunda ya ga Asiya gaban sa yake faɗuwa,zama yayi yana faman zare ido yace"Ranki shi daɗe gani fatan dai lafiya"?Kallan sa tayi cikin ido tace"shin shekarun ka nawa Malam Hudu?"ɗan sosa kai yayi yace"talatin da Tara hajajju".."kasan Asiya dake zaune nan ko?"ta sake jefa masa tambaya.
"Na santa Hajiya,ai tana cikin yara masu ɗa'a cikin gidan nan,tana da kirki"ya faɗa a takaice.ƴar dariya Big Mummy tayi tace"zata yi kirki mana Hudu tunda kana lalata da ita".a zabure ya miƙe yana mai dafe ƙirji yace"lahaula wala ƙuwata Ni Hudu jikan ilya,Hajiya kinji abunda kike faɗa kuwa?,Ni kuwa mai zai sa nayi lalata da Asiya ƴar marainiyar Allahn nan"?.gyara zama tayi tace,nima ban sani ba Hudu shi yasa na tambaye ka,amma idan baza ka bani haɗin kai ba zan kira jami'ai ,nasan su zaka basu idan suka lillisa ka ."..dawowa yayi ya zauna yana mai rarraba ido yace"Dan Allah kiyi haƙuri Hajiya kada ki haɗa ni da Masu baƙaƙen kaya wallahi ina mugun tsoran su,na Amsa laifi na na Lalata da nayi da Asiya ,amma wallahi yanayi ne na sha'awa da kuma sharri na sheɗan Amma ki tambaye ta ,tunda mukayi sau huɗu bamu sake ba wallahi,dan Allah Hajiya kiyi haƙuri ki rufa mun Asiri,Asiya kema kiyi haƙuri ki tayani kuma bawa Hajiya"..wani kuka Asiya ta sake fashe wa da tana mai jin tsanar kanta, rarrafawa Hudu yayi Gurin Big Mummy dake binsa da kallon ƙyama yace"wallahi ko cewa kikayi na Aure ta zan Aure ta wallahi ".
"Ni wallahi bana sanka bazan Aure ka ba duk yarda nake san nayi Aure"Asiya ta faɗa tana mai sake fashewa da kuka khadija na Lallashin ta da hannu ta..cike da takaicin sa Big Mummy tace "kalli nan Hudu,ba wai baza ka biya laifin ka bane ,ai Abunda yasa aka kira ka kenan,Idan baka so wani cikin manyan gidan nan yaji mugun labarin nan to a yanzu ba sai anjima ba kaje ka aje aikin ka sannan ba sai gobe ba kabar gidan nan a yau".wata irin zuface ta ƙeto masa,cike da matukar tashin hankali yace"Wallahi ranki ya daɗe ina da iyali idan na aje aikina ban san ina zan saka raina ba wallahi,ki mun rai Hajiya , kamar Aban wuƙane fa ace na daɓawa kaina da kaina".
"Lokacin da kake almashar ka ai ba kayi tunanin kana da iyali ba,dan haka abinda ka shuka kaje ka rayu dashi"Big Mummy ta faɗa tana mai tsuke fuska,haka nan ya gama maggiyar sa amma daga ƙarshe dole ya tashi dan zuwa aje aikin sa da yake uwa uba a gurin sa.,bayan Wucewar sa Big Mummy ta dawo kan Asiya tayi mata faɗa sosai da Nasiha sannan tace zata ma Nafisa magana idan kuma ta sake jin magana makamancin Wannan bata san Abinda zata mata ba...Wata irin Ajiyar zuciya Asiya ta sauke lokacin da suka fita,bata iya cewa komai ba illa rungume Khadijah da tayi tana kuka,raba ta Khadijah tayi da jikin ta tana mai share mata hawayenta tace"ya isa Haka Asiya komai yanzu ya wuce ,idan Yusuf mijin ki ne zaki ga ya dawo da kansa"..matse idanu Asiya tayi tace "Wallahi Khadijah jina nake kamar an sauke mun wani gagarumin dutse a ƙirjina,,ban zamar miki ƙawa kamar yarda kika zamar mun ba,amma insha Allah zan gyara". Murmushi Khadijah tayi tana mai faɗin "Allah yasa Asiya".
Ana tashi daga boko kamar yarda Nafisa ta saba sauka ɗakin Big Mummy ta gaishe ta a kullum yau ɗin ma hakan ya faru,da murnar ta wannnan karan ta shigo bakin ta ɗauke da sallama,ba ta bari Big Mummy tace wani abu ba ta aje mata result ɗin ta na jarabawar da sukayi tana mai cewa"Allah yayi mun uwa ta yau naci ta biyar a aji,dama mai na faɗa miki,a bi komai a hankali"da Mamaki Big Mummy ta ɗauki result ɗin tana mai Kallan fuskar ta kafin ta mayar kan result ɗin ,direct gurin Position ta nufa wanda ya nuna mata tazo na Sha tara a cikin su Ishirin da uku, mutum ɗaya ta bige a kan result ɗin ta na baya,ninke result ɗin Big Mummy tayi tace"wato Bayan Blackmailing har ƙarya kin koya,ƙaryar ma gare Ni, shin mene kike san zama Ni ƴar nan?"ɗaga gira ɗaya Nafisa tayi tace"ƙarya kuma?shi wancan Blak wani abu da kika ce ban san mene ba turancin yayi mun girma amma bari kiga nazo na nuna miki wallahi ta biyar nayi"ɗaukan result ɗin tayi ta zauna gefen Big Mummy tana mai Nuna mata biyar ɗin dake jere da kwanan wata, Kallan gurin da take nunawa Big Mummy tayi,wani irin abu taji ya tokare mata ƙirji,cike da baccin rai tace"yanzu Nafisa 5 ga wata 8 shine kinyi na biyar ?"jin haka yasa Nafisa tashi tana ja da baya hannunta riƙe da result ɗin idanun nan kuwa take sun fara kawo ruwa ,cikin marairaicewa tace"Wallahi Mummy ki kalla fa kece kikayi kuskure"ganin Big Mummy ta yunƙura zata tashi ta zura a na kare zata gudu taci karo da Mummy Nadiya dake shigowa,
"Yauwa Nadiya riƙe mun ita dan Allah naci uban yarinyar na gidan nan kowa ya huta".
TBC
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top