5

BA DUK ƘYALLI BANE GWAL

(When their hearts collide)

Na

CHUCHUJAY ✍️

CHAPTER 5

    Koda Asiya ta shiga ɗakin su idanun ta na sauka kan Sa'adatu ba tayi wata wata ba ta hau kanta ta fara jinbga tana tsine mata,Maryam dake Babban ɗakin wadda a ƙalla zata yi shekaru Ashirin da tara ta shigo taga Asiya na Aikin jibgar Sa'adatu,da gudu tayi kan su ta janye Asiya da ƙyar kafin tace"wane irin hauka ne wannan,Hala kin shirya kashe ta ne?".Cikin wani irin kuka mai cin Rai Asiya tace"Aunty Maryam ki barni kawai na kashe ta ɗin dan ni ta riga ta kashe ni,kamar yanzu ke ce yarda kika kusa talatin ɗin nan babu wani tsayayyen,ki samu wani yazo ya ɓata miki ya zaki ji? "Haɗe rai Aunty maryam tayi sosai tace"bana san iskanci kuma,kada ki zage ni,duk Abinda aka ɓata miki dama baki chan chan ta bane,ita yanzu Sa'adatu mene ta ɓata miki?"cikin yanayi na mutuƙar tunzura Asiya tace"daga aikata ta taho da saurayina Yusuf shikenan ta buɗe wannan bakin nata mai kama da ɗuwawu ta fara faɗa masa maganar da Allah kaɗai yasa daga inda taji ta , Wallahi yau sai ta faɗa mun inda ta jiyo maganar da ta faɗa masa koda kuwa duk garin nan gatan ta ne".kan Sa'adatu ta kuma nufa tana faɗin sai ta kashe ta,cikin kuka da tsoro Sa'adatu tace"na rantse da Allah Aunty Asiya ban faɗa masa komai bai,Ni wallahi Bama Ni naje ɗauko sa ba Nafisa ce sai da suka taho na ƙaraso dashi kuma ki kirata ki tambaye ta".wani irin faɗuwa gaban Asiya yayi kafin tace"dan kutumar ubanki Nafisa na Aika ko ke?ina take ita baƙar shegiyar?wallahi yau sai dai ko ni ko ita"cike da tsawa ta sake maimaita "ina take"?..a tsorace Sa'adatu tace"wallahi ban sani ba amma hanyar sashen maza naga tayi".fuuu Asiya ta fita kamar wata Iska tana faman tafarfasa ɗan yau ko ita ko Nafisa sai ta faɗa mata inda ta san gagarumin Sirrin ta.

  Wai ina Nafisa kam?

Tun rabuwar Nafisa da Yusuf da sa'adatu kai tsaye sashen maza tayi dan ganin Akram duk da kuwa yayi mata kashedi akan zuwa gurin,kamar yarda ta saba tana zuwa ƙofar ɗakin su Akram ba tayi wata wata ba ta yaye labulan da suka sake,da mamakin ganin ta Abubakar ɗaya cikin ƴan ɗakin dake sanye da boxers brief ya tashi da sauri ya jawo riga ya fara kici kicin sawa yayin da Umar dake Kallan cikin wayar Isma'il ya ke Kallan ta da takaici kafin yace"ke wai wacce irin jakar yarinya ce mara nutsuwa da Zaki shigo mana ɗaki babu wani tunani kamar ɗakin Mata?"Isma'il dake Bin ta shima da kallo na takaici ne yace"kada ka sake kiran ta jaka Umar, Nafisa lafiya"?.haɗe rai Umar yayi yace"Amma Brother Isma'il kaima ka sani ba sai na faɗa ba ,yarinyar nan nayi mana Abinda baya dacewa kana kallo dai Yaya Abubakar ko kaya babu jikin sa amma haka nan ta danno kai,mu da ɗakin mu kuma sai ace baza mu zauna yarda muke so ba saboda baƙuwar da bamu tsammani"?.taɓe baki Abubakar yayi yace"to laifin wane idan ba na Akram ba?indai kaga yarinyar nan Rabi mutum rabi Aljan tazo nan ai kasan gurin wanda tazo,ai ya kusa tafiya mugani idan kuma zata fara biyo Isma'il tunda naji shi zai cigaba da mata lesson ɗin da ba'a ɗauka,asara da ɓata lokaci"..kallon su kawai Nafisa take kafin ta kalli Isma'il tace " Ismai'l ,Boda Akram fa?"Ajiyar zuciya yayi kafin yace"Yana garden tare da Safiya , Please Nafisa ki wuce gida idan yazo zan faɗa mashi kinzo neman sa ba sai kinje ba shi zaizo".da mutuƙar Mamaki tace"Aw Allah,Ashe maganar da nake ji na cewa soyayya suke gaskiya ne da har zaije gurin ta a gadin sannan ace mun kada naje,to Wallahi ko shi Boda Akram ɗin bazai iya rabani da shi ba ballantana wata Safiyya duk ƙyanta kuwa,ai ba fina tayi ba". dariya Umar yasa kafin yace"ashe dai kin san ta da kyau ɗin ,kuma ina faɗa miki Sosai Big brother Akram ke Santa,ga kyau ga ilimi,mene zaiyyi dake daƙiƙiya".wani irin Kallon baƙin ciki Nafisa ke binsa dashi kafin tace"bazan tsaya kula matsiyaci irin ka ba,kai ma kuma Abubakar ka sani wallahi nafi ƙarfin ka,idan kuma kace karya ne dan Allah ka cigaba da shiga harka ta,dama idan masoyina ya wuce mai zanzo nayi gurin nan,aikin banza sai faman wari kuke na gardawa".bata sake faɗin wani abu ba kuma bata jira wanda za'a faɗa mata ba ta bar ƙofar ɗakin ta nufi Garden tana tunanin irin tijarar da zata yiwa Safiyya.koda ta isa Garden ɗin kan swing taga Safiyya Gefe guda kuma Akram zaune kan wani dutse dake kusa da ita yana ta faman washe baki .kamar iska haka Nafisa ta isa gurin, kafin suyi aune ta cilla Lilon da Safiyya ke kai da ƙarfi ,wani irin ƙara Safiyya tasa bisa ga rashin shiri da kuma sakan kan cewa kan Lilon,kafin Akram ya farga ta faɗo daga kai,da sauri yayi inda take domin taimaka

Mata,a hankali ya ɗagota yana mai tambayar ta inda taji ciwo,Azabar da taji bakin ta yasa ta saka hannu a gurin ,tana ganin jini da kuma rabin haƙorin ta a ƙasa ta saki wani irin ihu tana mai cewa ta shiga uku .cike da tashin Hankali Akram yake ƙokarin taimaka mata yana mai cewa"tazo suje asibiti"ganin Hannun Akram kan kafaɗar Safiyya ba ƙaramin sake tunzura Nafisa yayi ba da gudunta ta je gurin ta ture hannun sa tana mai sake hankaɗa Safiyya da dukkan Karfin ta..,Kafin tayi Aune Akram ya ɗauke ta da mari,wani irin rikitaccen ihu ta saki hannun ta kan fuskar kafin tayi kan Safiyya tana cewa"wallahi tunda ka mare ni a kanta sai na mata illa,dama munafirta ta kake ashe shine akan ta har zaka mare ni".riƙeta Akram yayi yace"wallahi kina sake taɓa ta sai na zane ki tunda ke dai baki jin magana,mene tayi miki da zaki tura ta kan swing ta faɗo ta balla haƙori,hala kinyi hauka ne?".jin Abunda ya faɗa yasa ta riƙe rigar sa zuciyarta na mata wani zugi tace"wallahi yau sai ka kashe ni,tunda ka mareni kan wannan Tsigatsiyau ɗin to gobe Allah kaɗai yasan Abinda zaka mun,kawai ka kashe Ni kowa ya huta sai kuyi soyayyan ku hankali ƙwance".tashi tsaye Safiyya tayi kumatunta cike da hawaye ,bata ce masu komai ba ta juya da gudu tabar gurin,nuna ta kawai Akram yayi da ɗan yatsa kafin yabi bayan Safiyya da gudu yana Kiran sunan ta dan yasan definitely ƙarar Nafisa zata kai wanda yasan abun bazai daɗi ba,hannu yasa ya kamo nata lokacin da ya cimma ta ya kalle ta da idanun lallashi yace"dan Allah Safiyya kada ki Kaita ƙara".cike da takaici Safiyya tace"kada na Kaita ƙara fa kace,kana kallo haƙorina na gaba yanzu ya dawo rabi sai kace kada na kai waccan tsinanniyar yarinyar ƙara".ɗan runtse idanun sa yayi har lokacin bai sake hannun ta ba,kamar An saka masa wani abu mai nauyi ya buɗe bakin sa kamar yana tsoran Abinda zai faɗa kafin yace"kada ki sake kiran Nafisa tsananniya muddin baki so Mu samu damuwa".da mamaki Safiyya ta kalle sa kafin tace"sake Ni Akram,bana san na faɗa maka Abunda zan dana sani,God damn it nice aka yiwa illa instead a tsaya baya na kake tsaye bayan waccan Mischievous yarinyar,Who doesn't know irin shaiɗan cin ta,I'm not going to let this slide wallahi. "Runtse idanun sa ya sake kafin yace"look im sorry and da kaina zan saka Nafisa ta baki haƙuri sannan zan ƙokari wajen ganin anyi abu ma teeth ɗin ki,yanzu zamanin is expand da technology,after All tare zamu Yankee and insha Allah zan kula dake na shekara guda ,i promise ".wata irin dariya Safiyya tasa kafin tace"kana tunanin sorry na gyara komai Akram?no ko kuwa dama da haƙorin Technology ka ganni?i was doing fine few minutes ago kafin waccan yarinyar dake neman zama maka larura tazo,I was doing all I could naga ban shiga shirgin ta ba gudun kada ta shiga nawa mu samu damuwa but kalli inda muka zo". marairaice mata Akram Yayi yace"dan Allah Safiyya do this for your friend".wani hawayen takaici ta goge kafin tace ,ka sake Ni naje Amin dressing ciwona.. sakin ta yayi yace"muje na raka ki"murmushin takaici tayi tace"ba ƙarar ta zan kai ba,ba sai ka bini dan ka tabbatar ba,at least nasan zaka tsayawa alƙawarin ka na shekara ɗaya".shafa kansa yayi bayan ta wuce cike da damuwa kafin Nafisa ta faɗo masa da kuma marin da ya sharara mata,licking leɓansa na ƙasa yayi yace"oh shit".kai tsaye Garden ɗin ya koma batare da yasan ta inda zai fara lallashi Nafisa ba dan yasan ya taro Danja,turus yayi lokacin da ya hango Nafisa na dambe da Asiya duk da kuwa ita ke dakuwa amma bakinta bai mutu ba waje zagin Asiya da kuma ƙoƙarin kai mata duka,da gudu ya isa gurin yana mai ƙoƙarin raba su ,yana isa ya fincike Nafisa Wadda ke Aukin cilla ƙafa tana ihu tana mai cewa"wallahi bazan yarda ba ,wallahi sai na rama ".aje ta yayi ya riƙe ta gam ya shiga tsakiyar su yana mai tare Asiya da Hannu wadda ke faɗin yau sai ta kashe Nafisa..da ƙyar Akram ya samu Asiya ta nutsu kafin yace"mene ta miki dan Allah Asiya da zaki tsaya dambe da Nafisa da girma ki,?"nuna ta tayi da yatsa tace wannan yarinyar Muguwa ce,wallahi shaiɗaniya ce,Yau saurayina yazo taje tana faɗa masa wai ni da hudu Mai gadi muna iskanci tsabar Sharri"..."Aw shine Abunda yasa kika zo kina hauka ,to ai da baki tsaya faɗa dani ba kin kai ƙarata kinga idan ƙarya nake sai muji idan aka gayyato Hudun,sau nawa ina kama ku da daddare a bayan Babban kitchen idan naje satar yaji,saboda kunsan babu kowa ta wuraren da dare,nima sanin haka yake kaini satar yajin Baba delu na daddawa,wallahi kije ki kai ƙarata ,ke Ni idan baki kaini ba daga nan ƙara na tafi kaiwa ,iyakaci ace na saci yaji"cewan Nafisa da Akram yaƙi bari taje gurin Asiya...turus Asiya tayi kafin ta fashe da wani irin kuka ta tsugunna a ƙasa dan bata taɓa tunanin wai wani ya taɓa ganin su ba,wanin ma wai Nafisa...ganin Nafisa zata bar gurin ne yasa Akram kamo ta yace "tsaya nan muyi magana".tsuko baki tayi tace"Ni Babu Abunda zaka faɗa mun wallahi bayan mari na da kayi".shafa fuskar sa yayi yace"naji ba wannan zamuyi yanzu ba , maganar ki da Asiya, bana san ta wuce nan idan ba haka ba babu Ni babu ke,nasan daga Ni sai ke sai Asiya muka san zance nan bana so wani yaji".cike da karkaɗa kugu Nafisa tace"to naji Amma na faɗa wa ƙawar ta Khadijah,musamman da ya kasance tana mata gorin ta samu miji ita bata samu ba,sai tana wani ɗaga bakin ta tana zagin gidan nan bayan shine yayi mata komai,wallahi tur da mai cizon hannun da ya bashi abinci"ƙasa Asiya tayi da kai ta kasa dago ido ta kalli Akram Balle ma tace wani abu,amma fa ita ma bata so maganar nan ta fita,Allah ma yasa Garden din bai cika tara jama'a ba, kasancewar kuma yau weekend kowa yana chan yana harkar gaban sa,taji wannan karan ta faɗin ma Nafisa and zata yi ko mene domin Sirrin ta ya adana bakin Nafisa kafin ta samu wata hanya ta muzanta ta,cije baki tayi kafin ta ɗago kai tace"dan Allah Nafisa ki rufa mun Asiri zanyi ko mene kike so"ƴar dariya Nafisa tasa kafin tace"zaki na mun wanki".Akram na ƙoƙarin ƙwabar ta tayi sauri wajen faɗin"na yarda har da guga ma wallahi".tafawa Nafisa tayi tace "yayi kyau Sirrin ki yana ƙasan cikina babu mai ji ,tashi kije". Kamar wata sabuwar munafuka haka Asiya ta miƙe ta fara tafiya.dariya Nafisa tasa tace ",dana san zaki biyu haka ai tuntuni xan fasa ƙwai na more ki". kallon ta kawai Akram Yayi kafin yace"kin san dai hakan baya da kyau ko?Allah yana san mai rufa Sirrin wani,and Abunda kika yi ba hali ne mai kyau ba".wani banza kallo Nafisa ta bashi tana mai kwace hannu ta tace"dan Allah kada ka daman,ko kana tunanin zan manta marin da kamun ne akan Safiyya,dama ansha faɗa mun soyayya kuke ban yarda ba sai da na zagayo naganka kana faman washe mata baki, wallahi ko anjima na sake ganin ku tare sai na fitar mata jini idan ba haka ba ba sunana Nafisa ba ,kuma wallahi marin da kamun ban yafe ba".

Duƙawa yayi iya tsayin ta yace "maza Nafisa Rama marin da na miki sai kiji daɗi ,Ni kuma kinga daga nan sai na wuce na Auri Safiyya ɗin tunda ita dai tana da kunya bata ma mutane fitsara."juyawa tayi ta bar Gurin da gudun ta tana mai jin haushin abinda ya faɗa..tashi tsaye Akram Yayi yana mai binta da kallo kafin yace "she's just thirteen fa".bai san yaya zaiyyi da Nafisa ba a yanayin yarda take running Wild and rebellious a ƴan daƙikun shekarun ta ,he just hope a Yarinyata zai tsaya domin kuwa zai dawo ma Nafisa sannan yana buƙatar companion Mai halayya akasin Na Nafisa saboda yana san future ɗin sa ya zama free of rigima musamman idan yayi Nasara akan abubuwan da yake fata ,he just wish,yanzu maganar guda ce,muddin Nafisa tasan tare zasu Yankee da Safiyya akwai ƙura ,inda ya godewa Allah kuwa da ya zamana  recently maganar tafiyar Safiyya ɗin ya tashi,saffiyya itace mutum na farko da ta fara yunƙurin saka shi ya fara jin gurin matsayin gida da abotarta duk da kuwa a lokacin ba wai yana cika sake mata bane amma duk da haka bata rabu dashi ba har sai da ya fara sauraren ta,shi da ita wajen sa'annine ,koda zai girmeta kuwa baifi da shekara guda ba.

    Kai tsaye bayan Nafisa ta koma ɗaki wanka tayi ta fita domin zuwa karɓan Abinci,bayan ta karbo ta dawo ta zauna tana kallon Khadijah ,Hama,da Suwaiba naci tare taƙi kulasu ta fara cin nata,kaɗan taci ta aje ta ɗauki hijabinta da jakar Islamiyyanta ta fita tana mai ce musu ta tafi,taɓe baki Suwaiba tayi tace"Nafisa baza ta taɓa canza wa ba,ajin mu ɗaya fa ,mene laifi idan tace Suwaiba zo mu tafi,saboda tsabar baƙin hali kuma ita kaɗai take zama taci abinci".Aje cup ɗin Ruwan da Khadija ta ɗauka tayi tace"Suwaiba!!hala baki san hanyar islamiyyar nan ba sai Nafisa ta maki jagora?"karɓa Hamamatu tayi tace"Ni ai ban san ina neman maganar Suwaiba zai tsaya ba,da Nafisa inace Bama ɗakin nan take cin Abinci ba yanzu kuma ta dawo,wata rana da kanta zata zo taci tare damu ɗin mene sai kin yi magana,dan Allah ki iya bakin ki"cire hannu Suwaiba tayi cikin abinci ta shiga bayi ta wake kafin ta dawo ta ɗauki hijabinta ta fita ba tare da tace komai ba,koda ta fara Tafiya dan nufar Islamiyyan Idanun ta taji sun ciki mata da ƙwalla ga kuma wata sabuwar tsanar Nafisa dake dirar mata,mene zata yi ne tafi Nafisa?shin mene zata yi ace yau tafi Nafisa sannan me zata faɗa ayi ta Allah wadai da Nafisa?.a haka tana wannan tunanin ta isa Islamiyyan su,tana shiga Ajin su ta tarar da Nafisa zaune zagaye da ƙawayen ta tana musu hira suna dariya,gefe guda ta zauna inda taga Sa'adatu ta zauna ba tare da taje inda Nafisa take ba kamar kullum,haka zalika itama Nafisan bata zo inda take ba dan tasan tayi mata ba dai dai ba...dafa Sa'adatu Suwaiba tayi tace"hala kunyi faɗa ke da ƙawarki?mene tayi miki ne?tunda naganki nan zàune ke kaɗai nasan tabbas akwai abinda Nafi tayi miki,da yake kuma almura ce ta koma gefe guda tana shewa ". Kallanta Sa'adatu tayi kafin tace"ko ma mene tayi min babu ruwan ki ,kema baki ji Abunda kika ce ba,mene ya haɗa Ni da ƙawata dan haka ki bar mu koma menene ya haɗa mu ya dama".hannu Suwaiba tasa a haɓa tace"daga tambaya sai cibi ya zama ƙari?"gyaran Muryar malamin su shine Abunda ya katse Suwaiba,sallama yayi bayan sa biye da wani matashin Malamin,bayan sun gaishesa ya amsa ne ya kalli sabon malamin yace"to ɗaliban kirki ga sabon malami nan na kawo muku bazan samu damar ci gaba da koyar daku ba ,dan haka shine madadina,a yau kuma zai fara ta hanyar karbar haddar ku,malam duk wadda ta kasa ka kawo min ita na mata hukunci ,kada ma ace waccan Yarinyar Nafisa". dariya yan Ajin suka saka ban da Nafisa dake aukin Turo baki gaba..sabon Malamin ne ya gabatar da kansa matsayin Malam Muhammad Hashim sannan ya zauna domin yin abinda ya kawo sa,tun da ya aje wayar sa ƙirar iPhone Suwaiba ke kallo zuciyar ta na mata wata irin saƙa,Kallan Nafisa dake saitin Malamin da kuma wayar tayi,murmushi tayi ta ɗaga hannun ta tace "malam zan fara bada hadda ta".

08130229878

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top