4


Authors Note

Hey everyone,rubutun littafi yana da matuƙar wahala wanda ina ganin makaranta da yawa basu ganin hakan,Akwai Abubuwa da yawa da rubutu ya ƙunsa muddin kana san bada perfection ,dole ne ka Haddace abu da yawa ka tuna,yawan tunanin yaya zaka rubuta abu da zai burge masu karatu, kayi ƙoƙari wajen zama diffrent characters lokaci guda duk dan ka burge mai karantawa,ba wannan kaɗai ba kullum kana faman yaƙi da toshewar basira ,kakarewa idan kiyi tsakiya,kama rasa ina zaka, juggling with writer's block and all,wani lokacin mu tsani littafin mu muna ganin baiyyi ba musanman idan baka da support na readers,kayi tunani ajewa,muna tunanin baza mu zama good enough ba sannan abinda muka rubuta a banza yake,bugu da ƙari ka gama ka haɗu da Negative comments ,bad energy,criticism wanda ke ƙarawa komai tsauri da wahala, idan da ace rubutu sauƙin ne kowa zaiyyi,dan haka idan marubuci na baku kuna jin daɗin dan ALLAH ku nuna,idan babu ku babu mu,be kind to your writers,ku gane idan bai muku update ba,Yana da rayuwa wajen rubutu,ku tafa musu ku nuna musu Ku basu karfin gwiwa,it won't take much.

Idan ke/kai marubuci ne kana karanta wannan ku Sani kuna ƙoƙarin ,keep the good work and you're doing great♥️♥️.

CHAPTER 4

Bayan fitar Nafisa Hama tace"kinji dai Suwaiba dan Allah mu zauna lafiya,"kaɗa kai kawai Suwaiba tayi amma fa chan cikin zuciyarta tana mutukar jin wani baƙon yanayi dangane da Nafisa wanda ita dai baza tace gashi ba amma tasan cewa koda yau za'a ce Nafisa ta mutu baza tayi kuka ba,kowa bashi da magana sai tata meye ne take dashi?daukan su dai bisa tafarki ɗaya suke zaune cikin gidan ,dan mene yasa za'ana banbanta wani?tunanin kala kala ta fara a ranta ta yarda zata yi Abunda zai gigita Nafisa kowa ya sake tsanarta cikin gidan,a zahiri kuma sai cewa tayi"insha Allahu bazan sake faɗa da Nafisa ba".

    Bayan fitar Nafisa sashen da ɗakin su Asiya yake ta nufa kafin ta kai ga karasawa ta hango Sa'adatu na fitowa ,tsaye tayi tana jiran ta har ta ƙaraso,washe haƙora Sa'adatu tayi tace"Feenah ina zuwa haka".wani irin daɗin Nafisa taji jin ta kira ta da Feenah,yana ɗaya daga cikin Babban dalilin da yasa take san Sa'adatu shi yasa ma bata da ƙawa da ta wuce ita,dafa ta tayi tace"Gurin ki zan zo muyi bita dama kin san Yau Hadda amma naga kamar fita zakiyi,ina zuwa?"sauya fuska Sa'adatu tayi tace"Aunty Asiya ce ta aike Ni na shigo mata da saurayin ta ina tsaka da hutawa na,baki ji yarda take aikin zagi na ba har da mari ,"cikin baccin rai Nafisa tace"Allah ya isan ki,kuma wallahi sai Allah ya saka miki matsiya ciya kawai,kinga dama kafin mu fara karatun ina so ki raka ni waje tunda yanzu gate zaki je badan na raina ki ba dan Allah je gun Big Mummy zata baki abu ki kawo min in yaso kafin kije ki ƙarɓo Ni sai naje na ma saurayin iso taya zan gane sa?ɗan shiru Sa'adatu tayi kafin tace"dan Allah kada ki yi wani gun yana nan tace yana sanye da farar shadda"kaɗa kai Nafisa tayi tace"Allah bazan maki wasa ba yanzu zanje na shigo dashi,inace ɗakin baƙi za'a kashi? " Ajiyar zuciya Sa'adatu ta sauke kafin tace to kiyi sauri nima bari naje na dawo.murmushin mugun ta Nafisa tayi bayan wucewar Sa'adatu ,tana Isa Gate ta hango Yusuf bisa ƙwatancen da Sa'adatu tayi mata,da murmushi ɗauke fuskar ta ta isa gare sa tana mai ɗauke idanun ta daga kan Hudu dake faman washe mata haƙora,Kallan Yusuf tayi tace"ina wuni Uncle yusuf dama Aunty Asiya tace nazo na tafi da kai"murmushi yayi mata wanda yasa ta faɗin"kan uba yanzu wannan mai kyau ɗin ke san Asiya"cikin ranta amma a zahiri itama sai murmushin ta mayar masa,tasowa yayi yana mai cewa 'ƴan mata ,yaya sunan ki?.."Nafisa ta bashi amsa tana mai juyawa dan masa jagora murmushi yayi yana Binta yace"sunan ki mai daɗi"..."Nagode"ta bashi amsa a taƙaice tana tunanin mai zata faɗa da zai sa ya fasa Auren Asiya,wata idea ta faɗo mata,cike da aminta da idea ɗin tace ,",daga ganin ka kana da kirki Uncle yusuf sannan ya kamata ace kaima ka Auri mace mai kirki".. murmushi yayi mai kyau yace"gata nan na samu ,Auntyn ku,ina san Asiya sannan Nasan na samu mata ta gari".

Wani kallon Nafisa ta bashi kafin tace" Bazan ɓoye maka ,amma Asiya ba matar Aure bace ba,kaga wancan malam hudu mai gadi da na tarar daku tare?babu irin biɗalar da ba suyi tare ba,idan kuma baka yarda dani ba ,kana zuwa gurin ta yanzu ka tambaye ta wanne Hudu,zaka ga yanayin mara da gaskiya a tatare da ita ,ni kaina da kake Kallo Asiya taso ɓata ni cikin gidan nan amma da yake Allah ba azzalumin bawa bane bata taɓa nasara akaina ba,amma fa sauran yara bana ce ba.

Cikin wani yanayi na tashin Hankali Yusuf yake kallan Nafisa kafin yace"ta yaya zan fahimci cewa ba haɗawa kawai ki kayi ba saboda wani abu dake tsakanin ku na rashin fahimta wanda ba zana ce gashi ba,Look here young lady,ko mene ke tsakanin ku ina ganin ya kamata kuyi sorting out ba sai kin haɗa zance mafi muni kamar wannan ba,ina san Asiya ,sannan burina bai wuce na Kaita gida na matsayin mata ba ,so Please don't spoil this for me,yanzu kizo muje da kaina zan ma Asiya magana duk wani abu dake tsakanin ku ya wuce,idan ma haƙuri ne ,da kaina zan saka ta baki,kina yarinya ƙarama mai kyau bai kamata ace kin iya karya ba and plus wannan ba ƙaramin allegation bane,I'm sure Bazaki so manyan ku suji ba".Matsar ƙwalla Nafisa ta fara tace"idan na mata ƙarya mene riba ta?shiyasa wani lokacin taimakon ma baya da Amfani,muje na raka ka kafun ta kasheni kuma "fara tafiyarta ke da wuya Sa'adatu ta falfalo da gudu tana mai faɗin"yauwa Feenah ina ta Allah Allah yasa kin kaishi already,kin dai sam bana san wahalar Aunty Asiya,and naje banga big mummy ɗin ba".dan taɓe Baki Nafi tayi tace"dama ai baza ki ganta ba,gwara da kika zo ,ki raka shi dama ba wani san zuwa ɗin nake ba, Akwai inda zani"juyawa tayi dan barin gurin Sa'adatu tace"dan Allah ki tsayani mana in waje zaki sai na raka ki".ba tare da ta juyo ba tace"na fasa,ke dai ki kai shi kafin waccan Azzalumar ta sake miki kama idan ya wuce"kasa faɗin komai Yusuf yayi illa bin bayan Sa'adatu wadda ta gaishe sa cike da girmamawa inda a zuciya ɗaya kuma yake dawo da batun Nafisa,anya ba ganganci yake shirin yi ba?

A rayuwarsa baya da burin ya Auri mace ya saketa shi yasa yake son ya Auri wadda yake so kuma ya yarda da tarbiyyar ta da nutsuwar ta wanda yake gani ya samu ga Asiya amma kuma yake jin wani labari daban dangane da ita baya ga sanin da yayi mata,har gwada ta ya taɓa yi akan taje gidan shi ta ƙwana ,dalilin haka yasa sukayi gagarumin faɗan da yasa ta ɗaina ɗaga masa waya tana faɗin dan tana gidan marayu ba shine yasa zai ɗauke ta ƴar iska ba dan yarda ake bawa Kowa tarbiyya a gida suma ana basu ninki,da ƙyar ya samu ya shawo kanta, taya zai fara yarda da magana akasin mai kyau Akan ta?amma bazai iyu mutum biyu su haɗu su mata sharri ba,sannan magana ake ta waɗanda suka fisa sanin wacece ita duk da kuwa yarinya ta biyun bata ta faɗi magana irin ta yarinyar farkon ba amma a maganar su ya fahimci Asiya na gwada musu zalunci.

"Mun zo"daga bakin Sa'adatu shine abinda ya fito dashi da zance zucin da yake ,murmushi yayi yana mai kallan ƙofar guest parlour da take nuna masa ,hannun sa yasa cikin Al'jihun sa ya ciro kuɗi yace"bari na baki wannan kya siya sweet ko"da sauri ta girgiza kanta tace "wallahi ka bar shi nagode".kafun ya sake wata magana Asiya ta fito a parlour ɗin an sha uwar ƙwalliya kamar za'a je biki,Sa'adatu na ganinta ta juya tana mai cewa"Sai anjima"da Mutuƙar Mamaki ya bi Sa'adatu da kallo ganin yarda ta tsorata da ganin Asiya,kallan sa ya mayar kan Asiya yace "Kinga yarinyar nan na ganin ki kamar taga wata dodo ta bar gurin nan har tana haɗa ƙafa"murmushin yaƙe Asiya tayi tace"kaji Honey wai kamar taga Dodo,kawai dai tarbiyya ce,idan Babban da babba na magana ƙarami bai tsayawa a gurin ,Bismillah mu shiga daga ciki mana"dan kallanta yayi a taƙaice kafin yace"muje".da wani yauƙi tayi masa jagora tana wani kararraya ala dole ita cika..parlour ne mai girma wanda yake ɗauke da Set ɗin kujeru set biyu ,yayin da makekiyar Plasma ke manne jikin bango gefe guda kuma agogo wanda Naturally aka jerasa,center Table ɗin da ta masa tanadin Abun taɓa wa na gefen two seater wanda tayi masa nuna da yaje ya zauna tana wani fari da ido da fake lashes ɗinta kamar wata barbie doll,kallan ta yayi cikin sanyin murya yace"kafin na zauna ina san tambayar ki Asiya,sannan bana so kiyi mun ƙarya domin tana ɗaya daga cikin abinda nayi masifar ƙyama"zama tayi kan kujera gaban ta na faɗuwa kafun tayi narai narai da fuska tace"Baby ban taɓa maka ƙarya ba,kuma bazan fara a yanzu ba,ko mene ka tambaye Ni zan baka iyakacin gaskiya ta".zama yayi shima yana mai cewa"Good,menene alaƙar ki da Hudu gate man din gidan nan?".wata irin yanke wa gaban ta yayi wanda ya haddasa mata mummunan tsoro,cikin kiɗimewa tace"Hudu?mene yace maka tsakani na dashi?Ni Ni babu wani abu da ya taɓa haɗa Ni dashi mara kyau,duk abinda ya faɗa maka sharri kawai yaƙe mun ,alaƙa kuma mai gadi ne ni kuma marainiyar ciki gidan da yake gadi".karantar yanayin ta na rashin gaskiya da yayi da kyau ne ya saka shi faɗin"Uhum,amma a tawa majiyar ba haka kawai abun ya tsaya ba,Alaƙar ku tafi ta mai gadi da marainiyar gidan da yake wa gadi,Kalli nan,na riga nasan komai so just cut to the chase ki faɗa mun mene ya shiga tsakanin ku,idan kuma kin gane kiyi shiru ne,zan wuce kada ki damu."wani irin kuka Asiya ta fashe da tana mai faɗin"dan Allah Baby kada ka rabu dani saboda Abinda ƙaddara ta ta ƙunsa fyaɗe ya mun bada san raina bane".cike da wani irin mamakin ya maimaita kalmar fyaɗe ɗin kafun ya ƙara da cewa"to wa kika sanarwa ?,dan ya kamata ace yanzu haka baya aiki gurin nan dan zaman sa Barazana ne ,Allah kaɗai yasan yara nawa ke victims ɗinsa,bai kamata ana barin mutane irin sa suna abinda suka ga dama ba , musamman gida irin wannan dole ne a cire baragurbi irin Hudu".cikin wata irin Muryar tausayin kanta tace"Ni tsoro nake ji shi yasa ban faɗawa kowa ba,amma dama ina shirin sanar da kai tunda magana ce tsakani na da kai ta Aure,Abu guda ke riƙe Ni wanda shine yanayi da zaka ɗauki maganar ,Sannan Hudu mutum ne mai hatsari dan har kisa zai iya yi,tukunna ma Honey wani abu ya faɗa maka da yasa ka tuhume ni Ko?"cike da nazarin ta ya tashi yana mai cewa"dole zan ɗauki mataki dan haka ki tashi muje kimun jagora gurin manyan ku,sannan ni bashi ne ya faɗa mun komai ba,yarinyar da kika aika ta taho dani ita ke faɗa mun wasu maganganu haka kanki wanda zuciya ta ke mun wasi wasi dan nasan ke ɗin mutuniyar kirki ce,dan haka dole ne na ƙwatar miki haƙƙin ki "ganin ya nufi hanyar fita ya saka tayi saurin shan gaban sa kirjinta na dukan Uku uku tace"ka rufa mun Asiri kamar yarda Allah ya rufa maka,wallahi ida maganar nan ta fita na shiga uku,kuma ma tsautsayi ne wallahi sau ɗaya kuma ya faru,ka yarda ƙaddara tace ka rufa mun Asiri ka taimaka mun kada ka fasa Aure na dan Allah"saƙeƙe yayi yana Kallan ta kafin yace"so gaske ne?"ƴar dariya yayi yace ban taɓa tunanin ke fuska biyu bace sai yau,kin san mene?I'm done"Yana kai karshen maganar sa ya juya ya fita,binsa tayi tana ƙwala masa kira yayi mata banza ya wuce.zube wa tayi gurin da take ta fashe da wani irin kuka mai shiga rai,maganar cewa yarinyar da ta aika ta taho dashi ita ta faɗa masa itace ta dawo kanta,kamar mahaukaciya ta tashi tana kaɗa hannu tace"Sa'adatu, yau mai ƙwatarki a hannu na sai ya shirya,tun daga gurin ta fara ƙwalawa sa'adatu kira har ta isa ɗaki inda tasan nan zata ganta.

Thank you for reading, please vote
TBC

08130229878

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top