38


    **A yarda suka zauna suke kula da Alhaji Bukar zaka yi tunanin dukkan su yaransa ne wanda hakan ke saka yaji wani irin nishaɗi mara misaltuwa,bai kasance na gari ba amma Ubangiji ya haɗasa da yara na gari ciki har da waɗan da ba nasa ba,kowa a cikin su kokarin faranta masa yake,.Tun yana jin kunyar Jannah da Jamal har yazo ya saki jiki dasu cos idan yana tuna sanadin mutuwar iyayen su sai yana jin kamar yana da ruɓin Alhaki.

Kamar kullum da safe yarda ake samun wani ya goge masa jiki yau ma hakan ne,Akram ke goge masa jiki yana ɗan basa labarin Abin dariya yana mai yi kaɗan kaɗan,bayan ya gama ne ya zauna yana mai kallan sa kafin yace.

"Baba Ina San na Auri Nafisa".

Da Mamaki Alhaji Bukar yace.

"Ni'iman mu dai?A'a Akram kada ka cutar da kanka ,kaga dai halin da take ciki ,duk da hakan bana so Wani yazo ya Aureta saboda tausayi,nafi so duk wanda zai Auri NI'IMAH ya santa ya san labarin ta ,ya so ta a yarda take,koda na mutu hankalina zai kwanta".

"Baba nine mutumin nan,babu wanda yasan Nafisa sama dani,nasan Nafisa tun tana zani,na sota tun bansan tana da dangi ba,na cigaba da santa bayan rabuwa,bayan haɗuwa na cigaba da santa ,da larura babu abin da zai rage a ciki ,a duk halin da Nafisa ke ciki Ni Bazan taɓa gudun ta ko na wulaƙanta ta ba."

Wasu irin hawaye ne suka fara bi masa kunci,kula da hakan yasa Akram ɗaukan handkerchief yana goge masa cike da kulawa ,riƙe masa hannu Alhaji Bukar yayi da mutukar kasala kafin ya ce

"Zan magana da Ummun ta sai ka faɗawa mahaifinka."

"Ai na faɗa masa ma Baba iznin ku kawai nake jira to dama yace zaizo ya duba ka,nace ya ɗan dakata,kana bani izini zan kira sa ya taho".

"Mun baka Akram,Baban Salman ba sai kayi wani shawara dani ba,hatta NI'IMAH ta amince da Akram koda bata faɗa mun ba a yanayin ta na fahimta,and babu wanda zai iya riƙe mana Ita hankalin mu ya kwanta kamar Akram ɗin dan haka ya faɗawa mahaifin nasa yazo da shirin Aure ".

Ummu dake bakin ƙofa tana jin su tun farkon maganar su ta faɗa tana mai ƙarasowa ciki da kunun Alhajin.

Wani irin daɗi ne ya cika Akram ,godiya mara adadi ya musu kafin ya tashi ya fita dan kiran Daddynsa,

Murmumshi Ummu tayi tana mai bin sa da kallo kafin take faɗin",yaran kirki ne Akram",.Kunun ta fara bawa Alhaji duk da shi kansa bai san inda kunun ke tafiya ba.

Kallan ta yayi kafin ya ce

"Ummun Salman mene yasa kika ce su zo da shirin Aure?"

Ƙasa tayi da kanta tana mai gudun haɗa ido dashi.

"Saboda ina san kaga Auren daya daga cikin yaran ka kafin kaga na sauran,ka sani ko daɗin hakan yasa ka tashi,gashi jikin ka ya fara ƙarfi,yara maza Huɗu akan ka wannan ya kama wannan ya kama sai suna sa naji ma bana da wani aikin".

Yar dariya yayi kafin yake cewa."Ki daina boye mun Hadiza na san cewa mutuwa zanyi,ki kalle ni fa,im just useless,naji kina faɗawa Nene Saddiqa tayi poisoning ɗina ,and a asibiti daga zuwa mun dawo wanda ya sake tabbatar mun da ciwan yafi karfin Asibiti,But Ahamdulilah koda zan mutu zan tafi a hannunku kuna masu sona da kyaunata,yanzu kina kallo yarda Salman ke nuna mun kulawa,I'm just happy da ta yafe mun deeds ɗina duk da kafiyar sa".Tari ya fara,saurin saka masa handkerchief tayi wanda tana cirowa taga jinin,

Ba ta bari ya gani ba ta ninke tana mai cewa ya daina magana da yawa .

"Allah ya bani ikon magana a yanzu kafin ya hanani,ko a yau na tsaya Alhamdulillah,na godewa Ubangiji,Allah yayi Miki Albarka da yaran baki ɗaya,And ina so kije ayi processing yau na adopting Jannah da Jamal,zan saka hannu na ɗauke su matsayin ƴaƴana,ina san nayi abu mai kyau,kiyi haƙuri zan kara miki nauyi bayan Nasan da wuya mu kula dasu tare".

Wasu hawaye ke san zubo mata amma tayi ƙoƙarin hana su,tashi tayi tana mai kiran Sultan kan yazo ya zauna dashi kafin tace masa ita zata inda za tayi adopting ɗin nasu su zama nasu legally .

******Bayan ta dawo ne Baba ya saka hannu kafin ta kira jannah da Jamal,cike da nauyi take sanar dasu kasancewar sun yi abu ba da yardar su ba,amma ga mamakinta cike da murna suka saka hannu akan sun amince,wani irin daɗi ya ciki Baba yana mai jin inama zaiyyi tsawan ƙwana ya bawa waɗan nan Marayun yaran rayuwa mai inganci.Duk da haka bai ƙasa a gwiwa ba wajen ware musu wasu kadarorin sa wanda Ummu bata ja ba tayi na'am ta masa godiya maimakon su.

Kamar yarda Akram ya faɗawa Baba mahaifin sa zai zo da zumuɗi ya kira Daddyn wanda shima murna ta hanasa zama ya biyo Flight ya taho Nasarawan shi da aminansa guda biyu ,Hotel suka kama da zummar washe gari zasu shigo in yaso sai ayi mai iyuwa,bai nemi jinkiri ba duba da fahimta da yayi abin da Akram ke so kenan,shi kuma a wannan lokacin baya san ɓacin ran Akram ,burin sa kawai yaga ya faranta masa a duk wani abu da ya nuna buƙata indai mai kyau ne .

******Washe gari suka iso gidan Alhaji Bukar wanda already shima ya kira wani yayansa ɗan yadiƙonsa ,bayan zuwansu da gaishe gaishe aka daura Auren Akram da Nafisa wanda a iya tsakanin su ne sai yaran maza,sosai kowa ke farin da Wannan haɗakar,daga baya ne Daddyn Akram ya tunkari Ummu da maganar fitar da Alhaji Bukar waje inda nan take mai faɗa masa matsayar ciwan sa.

Sosai yaji babu daɗi ,duk da irin labaran da ya samu bai ga laifin sa ba duba da shima he was once a victim of the two sisters,abubuwan da sakina tayi masa baya tunanin akwai ranar da zai manta,shi yasa ko ta kanta bai bi ba,duk da faɗa masa da Akram yayi a kan cewa sunyi zaman kotu na farko inda alƙalin ya daga zaman zuwan kwana uku dake gaba.

Allah ya kyauta shine abin da ya faɗa kawai dan baya da wani abu kuma da ya rage tsakanin sa da Saddiqa,dama da ace yaran dake tsanin su nasa ne at least yasan wani abu ya haɗa.

Dangane da ciwan Nafisa kuwa Daddyn Akram ya ɗauki nauyin fitar da ita India ta suggestion na Abokin sa da suka zo tare Alhaji Shuaib cos shima ya taɓa haɗuwa da larurar Makanta,da ikon Allah zuwan sa Chan ya samu lafiya ,dan haka babu ɓata lokaci Daddy yayi musu albishir na tayi wanda take ya kira dan a fara processing visa.

A ranar suka so wucewa amma Akram ya nace Akan Daddyn nasa ya bari sai washe gari in yaso sai su wuce tare chan kafin su tafi,dalilin nasa shine san Nafisa ta kimtsa tayi sallama da yan uwanta duk da abin yazo mata a bazata cos babu wanda yayi magana da ita.

Kaɗan ta nuna masa fushin ta ta sauko duba da itama tana san shi and Decision ɗin da ya dauka na shirya Aurenta a halin da take sai ya sake sama masa wani babban matsayi a zuciyarta..Suite ɗin da suka kama suka je da zummar washe gari su wuce inda ɗaya daga cikin abokan Daddyn ya wuce a ranar saboda Aiki.

*******Ƙarfe biyu na dare bakin station ɗin da Hajiya Saddiqa suke wata bakar Lexus ta faka ta sha tint,mutum biyu ne a ciki, wanda ke Driver seat sai na passenger seat Wanda ke ɗauke da Leather jacket and trouser,hannayen sa ɗauke da handgloves na Leather baƙaƙe,karɓar allurar da mai tuƙin ya basa yayi yana mai juya ta kafin yace.

"Wallahi Mafia babu Amana ,so yanzu King mahadeo matar nan ta gama masa amfani,i can't believe maigida Mamman ya haɗa hannu dashi a kawar da matsalar  " .

"Shine risk na sana'ar nan ,kaga ita tana da hot hand akan su and a personality ɗin ta mace ce wadda zata ja kowa ƙasa da ita,a bar Italian Mafia,babu wanda ya isa ya kai King Mahadeo ƙasa a circular na Mafia,amma Mai gida Mamman fa?,ko nine shi wallahi Italian Mafia suka miƙamun hannu karɓa zanyi ,yarda take da cover na business ɗin LGs kada ka manta ya fita reputation da yake san karewa,dama idan kana Mafia da ke dealing da Organs da drugs kuma kazo ka haɗa hannu da illuminati ai ka shiga gagari,muddin ka zama useless,they will waste you".Na Driver seat ɗin ya faɗa .

Fita wanda ya ƙarbi Allurar yayi bai sake faɗin komai ba ya nufi station ɗin,Mole ɗin su dake gurin ya buɗe masa ya shigar dashi har cell ɗin da Saddiqa take ,.Rashe take tana bacci har da minshari tsabar gajiya,ƙaramun tsaki yayi yana mai ganin dacewar ɓatar da ita if not zata ja da yawa ƙasa,.Baiyi wani tunani ba ya juye mata ruwan syringe ɗin duka a wuyanta wanda shigar allurar yayi dai dai da buɗe idanunta,suna haɗa ido tayi ƙoƙarin tashi amma ta gagara sakamakon jikinta da taji baki ɗaya yayi numb.

Fita yayi kamar walƙiya,.Bayan wani lokaci tana ta ƙoƙarin struggling na tashi ta kasa a hankali taji wani irin abu a cikinta kamar ana markaɗa mata kayan ciki,wani irin ihu da tasa ya tashi abokan kwananta yayin da waɗan da ke duty babu wanda yabi ta kanta dan sun saka wa rai bata da hankali,babban warning kuma daga ogan su shine kada wanda ya kuskura ya buɗe ta ko da wasa.

Ihun da take tana mai riƙe cikinta yasa sakina rarrafa gareta tana mai cewa.

"Yaya lafiya?"wani ihun ya take sakawa lokacin da taji kamar ƙwaƙwalwarta na Melting sakamakon wani baƙon azaba da taji ya ziyarce ta,ihu ta fara da shure shure ,tana wani irin gurnani wanda ya sake firgita Sakina,cikin Kuka take cewa.

"Khaffy kiyi ma yan sandan nan magana she's dying ".

Taɓe baki khaffy dake gefe tayi tana mai cewa."mene zan ɓata baki na when mun san tafiya zatayi,sooner or later dama mun san zaku wuce".

Da mamaki Sakina ke cewa.

"Mahaifiyar ki ce fa?khafilat she gave birth to you God damn it".

"Bayan haihuwa mene tayi min bayan bari na da tayi da abun kunya?I'm going to jail without knowing ta yarda zan fara rayuwa idan na fito,i don't even know who the hell my dad is,koda na sani ma Allah ya kyauta na fara tunkarar boka matsayin uba , I rather die, .that's her retribution,sai ki jira naki, kun lalata rayuwar yara huɗu amma kuna jin dai dai ne kuka yi,I'm 17 for God sake".

wata irin kururuwa da Hajiya Saddiqa tayi ce ta sake firgita sakina inda ita a kanta Khafilat sai da taja baya.

Jini ke bi ta idanunta,da kunnuwanta kamar irin an kama dukkan wasu halittu na kanta an mitsikesu guri guda ,take gefen wuyanta saitin inda aka mata allurar ya fara zaizayewa yana mai bayyana cikin naman wuyanta yana mai nuna alamu ta kamar an ɗora danyen nama kan wuta.

Ganin yarda cikin ta ke tashi yana kumburi yasa Sakina tashi a gurin a zabure ,lokaci guda ya bada wata irin ƙara ta fashewa wanda yasa baki ɗayan su suka ƙwallar wata irin azabbabiyar ihu ganin wannan mugun tashin hankali.

A tare yan sanda dake watch suka zo gurin wanda suma al'amarin ya firgita su sosai ganin cikin ta a wawake kamar an fafe ƙoƙo.

A hankali ɗaya daga cikin su yace".

Ya hayyu ya ƙayyimu, astagfirullah.

Ganin yarda baki ɗaya komai ya koma yayi collapsing daga jikin ta,ihu kawai Sakina take jikinta na wani irin karkarawa tana mai cewa.

"Dan Allah ku buɗe mu,ku cire mu daga gurin nan dan Allah".

Babu musu suka buɗe su yayin da ɗayar ya jawo hannun Khafilat wadda ta kasa koda Motsi idanunta kan gawar mahaifiyar ta wadda lokaci guda ta koma wata irin ɓakakirin,da ace ba a gabanta komai ya faru ba zata ce karyane ba gawar Amah bace.

Suma tsoran zuwa idan gawar take dan haka jiki na Rawa suka kullo Cell ɗin zuciyoyin kowa na daka tsalle kamar zasu fito saboda tsoro.

Bayan fitar guy ɗin da ya bata Allurar bai wata wata ba ya faɗa mota ɗayan ya ja suka bar harabar gurin yana mai faɗin.

"Kurunkus labarin Saddiqa,so sad I'm sure a yanzu Black Corpse acid poising ɗin nan yayi mata daga daga "..a tare suka saka dariya dan su nasu aikin ya gama.

Washe gari aka zo aka tatara ta aka fita da ita dan har ta fara wari,asibitin aka yi da ita dan tabbatar da dalilin sudden bursting ɗin ta kafin su iya bada gawarta ma family ɗinta Wanda taƙamaimai babu wanda yasan inda za'a gansu sai da Sakina ta bada numbern kawunsu wanda suka wofintar basu tunanin juyawa koda sau ɗaya.

Bawan Allah lokacin da aka kira sa babu gardama yace zasu zo su karɓi gawar akai ta gida a rufe.

(Wata tagayyarar).

Bayan anyi Autopsy aka gano Acid poison ne aka yi injecting ɗin ta dan haka after all necessary aka bada gawarta ga kawunanta biyu da suka zo bisa jagoranci Khalid da yaje chan wanda kinship kawai ya saka suka karɓi gawar cos baza su iya watsar da iyalan mahaifinsu ba duk bacin abin da suka musu.

Kafin su wuce ne ɗaya daga cikinsu ya nemi alfarmar ganin khafilat wadda tana ganin su ta saka kuka musamman da ya kasance basa da wata shaƙuwa dasu amma a karshe suna akansu.Tabbatar mata yayi akan duk lokacin da sentence ɗin da alƙali ya bata yayi da kansa zai zo har Nassarawa ya wuce da ita bayelsa taje ta fara sabuwar rayuwa da yan uwanta,Khalid,Nana A'ishah cos har a lokacin babu wanda yasan inda Hashim yake.

Haka suka kama hanya dan zuwa gida ayi nata Sutura,abin mamaki a garin suna cikin masu kuɗin kyauye sannan masu sarauta,baki ɗaya zuri'ar su suka zo dan mata sutura duba da mahaifin ta ya bada babban gudunmawa ga community ɗin wanda yasa har Allah ya saka ta samu Rahmar sutura..A kallon gawarta kawai sai ka zabura,tashin hankali bai ƙare ba sai da masu mata wanka suka ga irin yarda ta koma dan haka suka mata yayyafe aka luluɓe ta.

Duk da yarda labarin abubuwan da tayi ya shiga garin hakan bai hana su karbar Gawar tata cikin mutunci ba,shine kawai abin da zasu iya mata amma tsakanin ta da Ubangiji babu mai faɗin yaya ne ,Baban tashin hankali shine lokacin da aka kaita graveyard da galibin ancestors ɗin ta suke sai da suka haƙa kabari huɗu amma abu ɗaya suke gani na ƙaton kumurci kwance yana jiranta,hakan yasa yan gari da suka musu kara watsewa kowa yana ihu dan mugun firgici.

Babba daga cikin family ɗin su wanda shine alfa nasu yace su suka ta abokin zama ne,babu musu suka daidaita suka zura ta kowa da abin da ke zuciyar sa amma yana tsoran furtawa.

Allah yayi mata sassauci,still bamu da ikon ƙararwa , tsakaninta da mahaliccinta.

Da kyar aka fitar da Khalid daga grave yard ɗin dan hatta ƙasar da aka nemi ya fara zuba mata kasawa yayi baki ɗaya ta rikice komai nasa ya daina lissafi,wani irin fargaba da tsoron Allah ya sake kamasa ,Bama shi kaɗai ba duk wanda ya ga wannan al'amarin sai ya shiga cikin mutuƙar magagi na tashin hankali mai tsananin gaske,idan ka duba ta wani bangaren zaka gane shi ɗan adam ba komai bane,wata ƙafafa,wata burga,wani arziƙi muddin kace zaka taka haddin Ubangiji karshen ka zai zamo karshe mafi muni,mai munin labartawa.

********************************************

    Ita ƙaddara idan akace ta riga fata babu wani rairaya ko tankaɗa da zaka mata kace bari ma sake gyara tsayuwar ta ko kuma na daidaita ta,a gidan Alhaji Bukar kamar yarda Suka yanke shawarar washe gari zasu wuce Gashuwa hakan ta faru,kuka sosai Nafisa take tana maƙale da Ummu tana mai jin kamar zata rabu da ita har abada,a hankali Ummu ke shafa ta tana mai tabbatar mata da ace Baban su ƙalau yake da ita zasu wuce ta zauna da ita yayi jinyar ta,

"Yo Ni gani,kada ki damu Hadiza ,duk da jikina na ɓari zan hau abin Sama amma saboda jikata da wannan ƙyaƙyawan mijin nata zanbi su naje da duk wani kinibibi da nake da shi na yan matanci na ƙwace dan banza "cewar Nene dake ta aikin yage baki zata India taga masu dogon gashi.

Kamo hannun Nafisa Ummu tayi tana mai cewa "muje ku gana da Baban ku,duk da yayi maku nasiha jiya ya baku amanar juna ake a sake ganawa ".

Babu musu suka shiga ɗakin sa tare,Ganin sa a kwance peacefully yasa Ummu ƙarasawa tana mai cewa.

"Baban Salman ga Nan NI'IMAH zasu wuce,nasa da zaka iya takawa kayi musu rakiya zaka fita amma gasu nan kasa musu albarka ,bata yawa".

Jin shiru yasa ta matsa inda yake,wani irin bugu zuciyarta tayi ganin babu wani alamu na rai a tattare dashi,.Zama tayi ɗabar tana mai wa Akram alamu da hannu kafin tace"maza zo duba mun shi"

Yana duba shi ya tabbatar da abin da yake zargi tun ganin karayar Ummu,rai yayi halinsa,Nene dake gafe ne tace,"ku gitta Ni na tashe sa wannan bacci yayi yawa".

A kallo ɗaya ta bawa kanta amsa ,ƙokarin zubewa tayi Akram ya tare ta,wani irin kuma mara sauti tasa tana mai faɗin.

"Nasan lokaci kake jira Bukar,na sani ko ba'a faɗa mun ba,Allah yayi wa'adinka ya cika,na yafe maka Bukar ,na yafe Maka Allah ya yafe maka kurakurenka".

Jin haka yasa Nafisa fara lalube taba mai faɗin.

"Nene mene kike cewa,Baba ɗinne ya mutu?"faɗuwar da tayi ne yasa ta sake fashewa da kuka inda Akram yayi kanta yana mai kamota hawaye na bin kuncinsa,cikin kuka mai ban tausayi take faɗin.

"Nayi rashi lokacin da nake tunanin na samu,Na yafe maka Baba ,Allah ya yafe maka ". jin hayaniyar Kukansu yasa baki ɗaya yaran shigowa,ganin halin da kowa ke ciki yasa gwiwar kowa sanyi suka fara mararar ƙwalla,a lokacin da suke tunanin sun cika Lokacin kuma mai iyuwa ta iyu,.haka suka ringa faɗin sun yafe masa Allah ya yafe masa..kafin kace mene maƙota sun fara halattam gidan jin yan koke kokensu,Mintina kaɗa ya kawo Daddy da abokinsa wanda suka haɗu da maƙotansa suka masa sutura.

Bayan an kimtsa sane aka nemi su zo baki ɗayansu su masa addu'a,yaran suka fara kafin Ummu cos a lokacin nutsuwa ta ɗan saukar musu kaɗan kaɗan musamman da Ummu ta zaunar dasu tana mai kara jaddada masu imaninsu dan haka sai Addu'a tafi kukan yawa duk da suna san suyi ,haka nan sukayi ta matsar sa.

Ummu ce ta karshe baya Nene,tsaye tayi kansa tana zubar ƙwala tana masa addu'ar neman Rahma kafin ta ke sake jaddadawa ba ta yafe masa duk wani abu da yayi mata duniya da lahira.

A haka aka fitar dashi bayan sun gama ganawar karshe da iyalansa kafin akaje aka masa Sallah ba tare da an tsayar a matan daga joining ba.

Basu suka sake shiga sabon tashi hankali ba sai da suka ga da gaske za tafi ya bar su zuwa gidan sa na gaskiya..

Sosai yayi mutane cos suka abin sa mu'amalar sa da maƙotan sa bata yankewa kuma mai kyauce.

Haka komai ya faru kamar rufewar idanu da buɗewarsu .

Allah ka mana karshe mai kyau,Ameen .

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top